Showing 138001 words to 141000 words out of 252835 words
kusa da ita muryar ƙasan maƙoshi yace "hey", wata shegiyar harara ta shiga bankawa daga cikin duvet sai kace wata psycho, tapping dinta yayi yace "hey..", tini ta yaye rufar ta miƙe zaune tace "ni ka dena taɓani babu kyau fa, it's not proper", ta matsa baya tana harararsa ƙasa ƙasa, yace "then who said ki ringa kwanciya a nan..?", tace "ra'ayi", yace "everyone thinks you are a good gal basu san cewa you are just a hyena with goat skin ba, you gat an innocent face but you are so harsh and rude...", ya nuna mata box din da ya ajiye yace "from Noor ɗaya daga cikin mutanen da kikay deceiving don nasan bata san bad attitude dinki ba..", Hajar ta ƙura masa idanu tana jin zafin kalamansa, da kyar ta iya cewa "are you done.. please off the light idan zaka fita", da haka ta koma ta kwanta ta rufa har ka tana jin raɗaɗin abinda ya gaya mata, hawaye ya ciko idanunta ta fara shessheƙa a hankali, yess tasha zagi sosai a wajen siblings dinta don shegiya ma suke kiranta, gashi dai shi ba zaginta yayi ba kawai mgana ce ya gaya mata amma sosai ta taɓa mata zuciya, har lokacin yana duƙe gefenta yana jinta, duvet din ya kwashe daga jikinta, tayi sauri ta tashi zaune ta haɗe kanta da guiwa, ya haɗe thick eyebrows dinsa strictly yace "shut up... me aka miki zaki ɓarewa mutane baki", chaɓ mgnarsa wofi don cigaba da tayi da kukanta a hankali, ɗago kanta yayi tana jin hakan ta fixge ta ja da baya, kanta a ƙasa tace "Please dan Allah na roƙeka kawai ka sakeni, ka bani takarda ta ko kuma ka furtan da baki nayi tafiyata..", kallonta kawai yake cike da mamaki kafin yace "amm young lady you are asking the wrong person, i think i told you ni banida wata mata bare na rubuta mata saki", ta ɗaga kanta ta ɗan kallesa sai kuma ta mayar tana kallon yatsun ƙafarta tace "Okay toh kawai just imagine ni matarka ce kace ka sakeni shknn..", duƙar da kansa yayi to cover the slight smile on his face kafin ya ɗago girarsa a haɗe yace "never... i will never imagine you as my wife and you will never be.." yana gama faɗin haka ya tashi ya nufi ƙofa saida ya kashe mata fitilar snn ya fita, Hajar ta gyaɗa kai ta koma ta kwanta. Ranar Friday ƙarfe 1 Nurain ya fita zuwa mosque kuma bai dawo gidan ba sai yamma, yana shiga palour yaji wani ƙamshin turaren wuta ya huda masa hanci, ya ringa ƙarewa palourn kallon deeply in his mind yana appreciating, ƙofar Kitchen aka buɗe sai gata nan ta fito tana kakkaɓe hannunta, turus tayi tana kallonsa dan yau three days knn rabonta dashi, ta yamutsa fuska ta haura sama walking slowly, ɓangarensa ya wuce direct ya shiga bedroom, farin yadin jikinsa mai kyau ya cire ya shiga wanka, bayan ya fito daga wankan ya shiga closet ya ɗakko black Shirt na polo with trouser, yana gama shiryawa ya ɗauki car key ya fita, har ya sauka downstairs sai kuma ya tsaya yana kallon stairs din, lokaci guda ya juya ya koma saman, ƙofar ɗakinta ya buɗe, zaune ya sameta kan tiles tana yanke farce with nail cutter, ta ɗaga kai ta masa kallo ɗaya sai kuma ta cigaba da abinda take, Calmly yace "ki ɗakko veil dinki zamu fita..", with weird expression ta kallesa ba tace komai ba, ta sunkuyar da kanta tana kankare farcen, yace "kinji me nace kuwa..", a hankali ta gyaɗa masa kai, yace "toh ai banga kin tashi ba", jimm tayi sai kuma ta tashi ta ajiye nail cutter din a kan mirror, well ironed hijab ta ciro daga wardrobe ta saka, fita yayi daga ɗakin tabi bayansa tana harararsa ƙasa ƙasa, tana biye dashi har zuwa parking space gaban motar da taga ya tsaya, ya buɗe lock ya shiga, tsaye tayi taƙi buɗe motar ta shiga, fitowa yayi yana kallonta yace "get in malama kina ɓatamin lokaci..", ta maƙe shoulder tana jan fingers dinta tace "nidae saidai mu hau Napep..", zaro ido yayi yace "what.. tricycle..?", ta gyaɗa kai ba tare da ta dubesa ba, yace "toh me yasa zan hau Napep bayan ga car dina..?", tace "toh shknn ka hau motar naka nidae napep zan hau", kawai kallonta yake, she's so childish, wataran idan ta maka abu sai ka dauka wata babbar macen ce, daga zarar ta kwaɓa maka wata shiriritar anan zaka gane yarinya ce shataf, haɗe gira yayi yace "kee!! shiga mota bana son shirme", harde hannu tayi ta juyar da kai tana ƙunƙuni, zagayowa yayi ya buɗe front seat, ba tay aune ba taji ya fixgi hannunta ya sakata a motar ya kulle, ya zaga driver seat ya shiga, hawayen da ya zubo cheek dinta tayi ƙoƙarin gogewa da bayan hannu don kar ya gani amma kuma saida ya ganin, har suka bar unguwar suka hau saman titi zuciyarta bugawa take da ƙarfi, sosai ya gane ƙin hawa motar da tayi yasan speed dinsa take tsoro, with minimum speed yake jansu don karta hargitse masa kafin su isa inda zasu, suna karya kwanar gidan Abba ya juya ya kalleta for the first time yace "Ke!!..", ta ɗan kallesa tace "Hajar", yana driving slowly har ya tsaya gaban makeken gate din gidansu yace "whatever... na kawoki nan don ki yiwa Mami sallama cause gobe zata bar gari, nayi hakan ne sbd yadda suka daukeki amma ni dai a wajena you don't worth it" yana gama faɗin haka ya danna horn, mai gadi ya zuge masa gate ya shiga yayi parking a compound, ya kashe motar yace "and behave yourself..", ya buɗe motar ya fita, fitowa tayi itama, shi yayi leading dinta har katafaren main palour wnda ba baƙonta bane, ya nuna mata kujera yace "sit" kafin ya wuce part din Maminsa, three minutes da zamanta a palourn taji footsteps ana sakkowa daga sama, ta ɗaga kai sukay ido huɗu da Noor, Noor ta ware ido tace "Ohh my God... is this you Hajar", murmushi Hajar tayi ta gyaɗa mata kai, Noor ta ƙarasa inda take tana welcoming dinta sosai, Noor ta zauna gefenta tace "yaushe kika zo..", Hajar tace "just now..", Noor tace "amma dai tare da yaya kike ko..?", Hajar ba ta kai ga amsa mata ba aka bude ƙofar part din Mami, Nurain ne with a repartee yana kallon Hajar yace "come in" ya juya ya koma ciki, Noor tace "muje can din", tare suka shiga ɓangaren Mamin, Hajar ta gaida Mami da ladabi, amsa mata Mami tayi with care ta tmbyeta lfyrta, Nurain dai kawai satar kallonta yake ganin yadda ta koma wata saliha sai kace gske. kafin Magrib hajjaju Hajiya ta iso gidan tare da Farooq da ya kawota, a main palour tayi branching don daman idan tazo gidan anan take fara zama, zuwan Hajiya yasa Mami ta fita main palour wajenta, Nurain ma ya tashi ya fita, Noor ta riƙe hannun Hajar tace "muje muma mu gaida Iron lady". Hajiya ta ringa kallon duk wanda ya gaisheta ta ƙasan kantamemen glasses dinta, sai kuma ta amsa a fixge alamar ƴan rigimar ne a kanta, Hajar na gaisheta itama ta ƙura mata ido sai kuma tace "Ahh ahha wai matar Usuman ce..", Noor tace "Eh itace", Hajiya tace "ywwa yanxu naga kiwo mai kyau.. da Usuman yaƙi sakin abinci a gidansa gaba ɗaya yarinya ta tsomare har ta fara fita hayyacinta, ynxu kam alhmdllh ai ta mayar da komaɗarta har ma ta ƙara", Hajiya ta kalli Mami tace "wnn tuwon naki na alkama nake son ci wllh", Mami tayi murmushi tace "toh Hajiya bari na duba garin" da haka ta tashi ta bar palourn ta shiga kitchen, Hajar dake zaune gefen Noor ta ɗaga kai ta kalli Farooq da yake kallonta, saukar da idanunta tayi tace "ina yini", da fara'a ya amsa yace "how are you doing..?", tace "fyn alhmdllh..", Nurain ya ɗago kansa daga latsa wayar da yake ya dubi Farooq, miƙewa yayi ya saka wayar a pocket yace "mu wuce mosque lokacin sallah yayi punk" bai jira cewarsa ba ya nufi door, Farooq ya tashi yabi bayansa, a tap din dake compound suka tsaya yin alwala, Farooq na tsaye bakin pampon yana jiran Nurain ya gama shima yayi yace "naga ma ai ba a kira sallahn ba", Nurain na wanke ƙafarsa yace "Eh mu zama ready kafin a kira..", Farooq yace "Ohk", Nurain na gama alwalar Farooq ma yayi, daga nan suka fita zuwa mosque wnda sai ynxu ma aka fara kiran sallah. Hajar na zaune kan darduma bayan ta idar da sallahr magrib a dakin Noor, cikinta ne ya ƙulle tana jin kamar cramps amma dai bata tabbatar ba, Noor ta shigo tana murmushi from ear to ear tace "kixo inji Hajiya", Hajar ta ɗan zaro lulu eyes dinta tace "Okay", ta tashi tabi bayan Noor suka wuce part din Hajiya, turus Hajar tayi a bakin ƙofa ganinsa a palourn Hajiyar shi da Farooq, Noor dai ta wuce ta zauna kan sofa ta cigaba da chatting dinta a phone, Hajiya dake zaune kan lallausan rug tace "ƙaraso ciki mana ƴar nan", a hankali Hajar ta wuce ta zauna kan Carpet, Hajiya tace "yauwa ko kefa ƴar nan", Hajiya ta juya tana kallon Farooq tace "mai gidannn..", Farooq yace "Amaryasss", Hajiya tace "ina dubulan da Alkaki da ka kwana biyu kana ci a wajena...", Farooq ya gyaɗa kai yace "yess wnn masu daɗin", tace "ƴar Albarkar yarinyar nan ce ta ciko min leda dasu, ai naji dadin kayan zaƙin nan don duk ranar da na cii saina shi mata albarka... mai gidann na gaya maka sam fa batada rowa wllh tllh..", Farooq yayi murmushi yana kallon Hajar yace "ni kam rowa tamin da naje..", Hajar ta ɗaga kai ta kallesa tace "Ai baka zauna ba kana zuwa ka tafi", yace "Okay dana zauna da za a ban..?", ta gyaɗa kai tace "Eh", Nurain da ke zaune sai kace an dasa sa ya kalli Farooq sai kuma ya kalli Hajar, haɗe gira yayi ya tashi sai kace wnda aka mintsila yana kallon Farooq yace "i gat something to tell you...", Farooq yace "Ohk then tell me", Nurain yace "privately.." sai kuma ya nufi ƙofa ya buɗe ya fita, few seconds Farooq ya tashi yabi bayansa, a main palour ya tarar dashi zaune kan sofa, ya ƙarasa ya zauna yana kallonsa yace "what is it that you want to tell me...?", Nurain yace "nothing let stay here..", Farooq ya tsuke ido baice komai ba kawai ya tashi zai bar palourn, Nurain yayi saurin dakatar dashi da fadin "lets go to my room i will tell you there", Farooq dai ya kallesa baice komai ba, Nurain yayi tapping shoulder din Farooq yace "c^mom punk". Bayan fitarsu Nurain Hajiya ta taɓe baki tace "yau naga jalala shifa wnn fel wayar bai fiya san jama'a ba, yazo ya zauna min a kujera yayi wani ƙwamm dashi ba uhmm ba umm ummm sai kace bebe, kuma wnda muke ƴar firar ma ya ɗauke mana shi.. Allah dai ya kyauta da wnn hali", sai kuma ta kalli Noor tace "jeki amsomin tuwo na", Noor tace "toh iron lady" ta tashi ta fita, Hajiya ta zura hannu a ƙatotuwar jakarta ta ɗakko kwalbar man zafi tace "temaka min ƴar nan..", Hajar ta amshi kwalbar ta buɗe, albarka Hajiya ta shiga ɓarkawa Hajar bayan ta gama mulke mata ƙafafuwa da man zafi, Hajiya tace "tararrabin hawa jirgin nan nake don bana son zama a kujera kumburan ƙafa yake...". Ƙarfe tara saura Nurain ya fito daga great room din Abba bayan ya yiwa Abba sallama da cewar gobe da safe zaizo ya ajiyesu a airport don jirgin 8 zasu bi, Hajar ta shiga part din Mami don mata sallama, da ladabi tace "Allah ya kaiku lfy ya dawo daku lfy..", Mami tace "Ameen daughter Allah yayi albarka", har compound Noor ta raka Hajar, Nurain ya gama maganar da yake da Garba snn yaxo ya buɗe motar ya shiga, sallama sukay da Noor ta buɗe motar ta shiga, ta kalli window ko kallon position dinsa ba tay ba, driving ya farayi suka bar unguwar, koda ya hau babban titi baiyi irin gudun da ya saba ba amma dai gudun yake. gani tay kawai ya samu gefen titi ya tsaya, ita dai ta cigaba da kallon window ba ta kallesa ba, after few seconds taga dai basu cigaba da tafiya ba sai ta ɗan juya ta kallesa, kallonta taga yana yi without blinking, ta haɗe rai ta juyar da kanta, yace "So daman kinada manners..", ta juyo ta galla masa harara ta ɗauke kanta, yace "and kin kware wajen yiwa maza magana ko"......✍️
💛 HAJAR 💛
chapter 61
👇
Arewabooks....
Eager to read go there ☺️
💛 HAJAR 💛
{61..}
Hajar dai kawai kallonsa take da wani irin expression, tama kasa gane me yake nufi bare ta fahimta, har lokacin bai dena kallonta ba thick eyebrows dinsa a haɗe, sai ynxu ya fahimci tmbyar da yayi mata which is meaningless to him, to me yasa ma zai mata wnn tmbyar, ta juya ta cigaba da kallon window da sigar ko in kula, kawai ji tayi ya fixgota ya juyo da fuskarta tana kallonsa, ɗan buɗe baki tayi ta sha kunu tace "ni ka dena taɓani", yace "is there anything to touch...?", ta haɗiyi wni miyau ba tace komai ba ta gasa masa harara, ya ajiye numfashi yace "one day one time" da haka ya kunna motar suka cigaba da tafiya, suna zuwa gida ta buɗe motar ta fita ta wuce entrance, a bakin door ta jirasa har yazo ya buɗe mata ta shiga. shi kam kitchen ya wuce ya haɗa Coffee kafin ya haura sama, saida ya gama shan Coffeen snn ya shiga wanka, after ya shirya cikin Pajamas ya rage wutar ɗakin yabar dim, Laptop dinsa ya dauka ya hau kan bed, operating system din ya fara, after 40mins ya gama abinda zai yi ya kashe laptop din, ya ɗauke remote din AC ya ƙara mata gudu snn ya kwanta ya lumshe ido, buɗe ido yayi bayan minti biyar sai kuma ya miƙe zaune, zuro legs dinsa yayi ya zura room slippers ya tashi tsaye, door ya nufa ya buɗe ya fita, ya ringa kallon ƙofar room dinta bayan ya isa corridor, ya kai hannu jikin handle amma bai murɗa ba, after few seconds kawai ya murɗa handle din ya shiga, a hankali ya saki handle din ya shiga ɗakin making sure baiyi making ko wane sound ba, he spent almost 3mins yana kallon innocent face ɗinta tana bacci, kwance take a inda ta saba kwanciya kan carpet, ta rufe da duvet har zuwa wuyanta tana bacci Calmly, duƙawa yayi kusa da ita still looking at her face. Da asuba Hajar ta farka, ta taƙune fuska ta shafa laushin da ta jita a kai, miƙewa tayi zaune ta fara ƙarewa room din kallo sai kuma ta kalli gadon da take kai, zaro ido tayi ta dafe kanta to yaushe ta hau gado, ita da ta kwanta kan Carpet toh ya ta tashi ta ganta a gado, yaye rufar tayi ta tashi ta kunna fitila ta ƙara hasken ɗakin, ta ringa kallon gadon kafin ta girgiza kanta ta shiga bathroom, alwala tayo ta fito ta shimfiɗa dardumar ta fara gabatar da raka'ataynil fajr. Ƙarfe Shida da ƴan mintina Nurain ya fita compound da car key a hannunsa, Hajar ta gyara tsayuwarta a jikin window ta buɗe curtain din da kyau tana kallon compound, idonta ne ya kai parking space kawai ta hangosa, ta sha kunu tayi sauri ta rufe labulen ta bar wajen tana yamutsa fuska. kafin shida da minti arba'in Nurain ya isa gidansu, Already matafiyan sun zama ready, yana shiga main palour ya tarar da Hajiya da kwanon tuwon alkama da tasa akay mata warming, gaisawa sukay ta amsa masa a takaice sai kuma ta fara tambayarsa Hajar, a fizge ya bata amsa ya wuce ciki, box din Mami yaje ya ɗakko ya fita da ita, Drivern Abba ne ya ringa arranging luggage a booth din motar gidan wacca zata kwashesu gaba ɗaya comfortably, Nurain ne yayi driving motarsu Abba while Drivern Abba yayi driving motar Nurain din, Nurain bai bar airport ba saida su Hajiya suka shiga filin jirgi, car key dinsa ya amsa hannun Drivern Abba ya damƙa masa na motar gidansu. yana komawa gida daman kwanciyarsa yayi ya huta, ko da ya farka abinda ya fara faɗo masa shine wnn workshop din, shaf ma ya manta da wani symposium, slight hiss yayi ya janyo wayarsa yayi booking flight, azabar yunwa ce tasa ya fita eatery yayo takeaway, koda ya dawo gida tsattsakurar abincin yayi ya ture. Tin fitar da yayi kafin azahar ya siyo abinci bai sake fita ba, daman yau Saturday ba ranar aiki bace, Hajar kam ko gilmawarta bai gani ba, itama dai ta fahimci a waɗan nan kwanakin ne yake zama a gida shiyasa bata fiya warkajami ranar asabar da lahadi ba. wajen ƙarfe takwas na dare Hajar ta buɗe ƙofar room dinta, a hankali ta fito ta sauka downstairs, kitchen ta wuce ta buɗe fridge ta dauki bottle water ta fito ta haura sama, tana gama haurawa stairs din shima a lokacin ya fito daga ɓangarensa hannunsa riƙe da empty cup da ya sha Coffee, saukar da idanunta tayi ta wuce ta shiga ɗakinta, binta yayi da kallo lokaci guda brain dinsa ta amsa, ya zaiyi da ita knn.. gobe zai wuce Abuja fa, ƙasa ya sauka ya kai cup din kitchen snn ya koma saman, a palourn sa ya zauna yana neman one Solution, toh ya zaiyi da yarinyar nan, shi dai bazai barta a gida ita kadai ba hkan ma beyi making sense ba gsky, toh ko dai gidan Sakeena zai kaita, girgiza kai yayi don hakan shima bai masa ba, yayi tunanin ya kaita gidan Aunt dinsa Zulaihah, shima dai hakan bai masa ba... toh ko dai yace ta tattara ta tafi gidansu ne kawai, chab duk ciki ma