Showing 147001 words to 150000 words out of 252835 words
aka kawo mata breakfast, zama tayi ta fara ci bayan ta haɗa coffee kamar yadda taga yayi, wajen ƙarfe biyu tana kwance kan couch tana kallon wani american movie da ya ɗebe mata kewa, ta tashi zaune ta zame ƙasa ta dafe cikinta da ya murɗa, can dai bayan taji bazata iya coping ba ta tashi ta ɗauko wayar da ya bata wacca ta yasar akan mirror, ta kunna ta shiga call log ta danne 1, number na appearing tayi dialing, har ta gama ringing ta katse ba a ɗaga ba, ta sake dialing a karo na biyu. Nurain dake zaune a wani makeken conference hall tare da collegue dinsa da suka zo workshop din suma, ya dena kallon abinda aka haska musu a projector ya dubi wayarsa dake kusa da Laptop dinsa da take vibrate a karo na biyu, saida wayar ta katse snn ya tashi daga kan chair dinsa yayi excusing kansa ya ɗauki wayarsa ya nufi ƙofar fita daga conference hall din, a bakin ƙofar hall din ya tsaya ya shiga kiran numbern, Hajar ta kalli wayar hannunta jin tana ringing, har ta haƙura da taji ba a ɗaga ba, a hankali ta kai slim finger dinta tayi picking ta kara a kunne ba tace komai ba, silence ɗin seconds ne ya biyo baya kafin yace "what..?", shiru tayi masa taƙi mgana, ya ciro wayar daga kunnensa ya kalli screen dinta sai kuma ya mayar kunne yace "mene ne...?", tace "ni cikina ne yake min ciwo", jim yayi kafin yace "ohk.. na siya miki drug jiya sai ki sha..", juya lulu eyes dinta tayi tace "ni ban gansa ba..", yace "ohh ba kinyi amfani da abinda na kawo miki jiya at night ba.. so ki duba cikin ledar", Hajar tayi shiru tana tunani mene abinda ya kawo mata tayi amfani dashi, lokaci guda ta tuna ai kam ƙit ta kashe wayar tana turo baki, walking slowly ta isa gaban box din kayanta ta durƙusa ta buɗe, ledar da ta saka ciki ta buɗe ta fara ciro pack din sanitary pad din, a can ƙasa ta hango wata ledar tana buɗewa taga kwalin drug, ta ɓalli 2tablets ta sha da bottle water, ko 3mins ba tayi da sha ba ciwon ya sauka gaba ɗaya babu shi, ta koma ta zauna ta cigaba da watching movie din da take.
★Maama ta fito daga ɗakinta da wata fatattakakkiyar tabarma a hannunta wacca ta gama zarewa tass, inuwar dake gaban ɗakinta ta samu ta shimfiɗa tabarmar ta zauna, Nabilah dake zaune tsakar gida tana tankaɗe tace "Maama wace miyar za a kaɗa kuka ko kuɓewa..?", Maama ta juya hannu tace "duk wacca kika kaɗa..", Nabilah tace "bari na kaɗa kuɓewa kawai don Baba yafi sonta...", Maama dake susar kai ba ji ba gani ta dena susar tace "kuka zaki kaɗamin bana son wata kuɓewar banza kayan zawayi..", Nabilah tace "amma Baba yafi son kuɓewa kuma kinga baya jin daɗi...", Maama ta ƙunduma mata wani ashar harda daƙuwa tace "uban da ya haifeki ya hau fel waya ya diro, ni zaki yiwa tsarin banza, ince baya gidan tin safe ya fita da wani kike cewa baya jin dadi, wnda baya jin dadi ne zai fice tin safe..", Nabilah ba ta sake cewa komai ba ta cigaba da tankaɗenta, Sa'adatu ce ta fito daga ɗaki sai sharɓa uban gumi take, ta zauna kusa da Maama tana sharce zufa tace "kai ɗakin nan akwai zafin bala'i da masifa sai kace gidan burodi wllh..", Maama tace "uhmm tsakar gidan ma ba dama, idan iska ta kaɗo sai ta gama baɗaɗo zafin rana take zuwa sai kiji kamar daga jahannama ta huro", Sa'adatu tayi tsaki tace "shiyasa na tsani zaman gidan nan, zafi da kuɗin cizo ma kawai sun ishi bawa..", Nabilah ta ajiye rariyar hannunta ta juyo tana kallon Sa'adatu sai kuma ta taɓe baki tace "ya za kiyi tinda a nan Allah ya ajiye ki..", Sa'adatu ta hura hanci tace "Maama ki mata mgana kinga dai ban saka da ita ba ko", Maama tace "bari Nabilah..", Nabilah ta gallawa Sa'adatu harara ta juya ta cigaba da aikinta, Maimuna ce ta fito daga ɗaki fuskarta duk kumburin bacci da kwandon soso da sabulu a hannunta, ta wage baki tana zabga hamma babu a'uzubillahi bare ta rufe baki, bokiti ta ɗauka ta ɗebi ruwa ta shiga toilet. tin daga soro Balaraba ta shiga zabga sallama, ayam ta shigo gidan tana kiran sunan Maama, Maama ta turɓune fuska ta juyar da kai, Balaraba ta ƙarasa shigowa tana kallon Maama tace "haba ƙawalli romon jaɓa babu faɗa me ya kawo gaba Rabi", Maama ta haɗe rai tace "lfy zaki shigo gidan matan aure da hayagaga..", Balaraba ta wage baki tace "nidae zuwa nayi biko naga kwana biyu kin ɗauke ƙafa sam bana jin ɗuriyarki..", Nabilah ce kawai ta gaida Balaraba Sa'adatu kam ko kallon arziƙi ba ta mata ba tana danna wayarta, wayar nan da za a buɗe maka gallery ka shiga video to tsaf mutum zai iya makancewa don babu komai a ciki sai videos din batsa da shashanci, Balaraba ta zauna kan tabarma tace "kai wnn ma duk ta ruɓe cin jiki za tay..", Maama tace "da sai ki taho da wacca zaki zauna ai..", Balaraba tace "kyaji dashi dai.. idan da kinsan da mai nazo miki da tini kin fara nan nan dani wllh tllh..", Maama ta taɓe baki tace "haba Balaraba ke har akwai wani abin arziki da za ki zo min dashi har nayi rawar ƙafa nayi nan nan dake.. hmm wane dare ne jemage bai gani ba ai sai na mutuwarsa..", Balaraba tace "da dai kin taso mun shiga daga ciki..", Maama tace "mu shiga daga ciki a ina... dawa za a shiga daga cikin..?", Balaraba ta fakaici kallon Nabilah da Sa'adatu sai kuma ta marairaice fuska tace "haba Rabi ai kya bari kiji abinda nazo miki dashi tukunna", Maama ta tashi tana gyara haɓar zaninta ta shiga ɗaki Balaraba tabi bayanta. Maimuna ta fito daga wanka ta tsugunna gaban rariya tana goge kaushi, Nabilah da ta gama ruɗe tace "Maimuna ki ɗan temaka kiyi wanke wanke babu ko kwanunkan da za a ci abinci da daddare", Maimuna ta girgiza kai tace "chabɗi tin da baki gayamin ba saida nayi wanka..", Nabilah tace "knn dai baza kiyi ba..?", Maimuna tace "kwarai..", Nabilah tayi kwafa ta saka hijab ta fita zata siyo daddawa, Maimuna ta ƙarasa goge ƙafarta ta tashi zata shiga ɗaki, juyawa tayi tana kallon Sabrah da ta shigo gidan yanxu ta dawo daga islamiyya, Maimuna tace "ke zo nan..", a hankali Sabrah ta isa kusa da Maimuna tace "gani", Maimuna tace "ga can kayan wanke wanke wuce ki zauna kiyi", Sabrah ta kalli kayan wanke wanken tace "toh bari na cire kayan makaranta Umma tace ina dawowa na ringa cirewa..", Maimuna ta buɗe baki ta lailayo wata ashariya ta lafta mata tace "zaki wuce ko saina sumar dake shegiya..", Sabrah taja da baya tana ƙunƙuni tace "Umma tace na dena zama da uniform fa..", Sa'adatu dake kallonsu tace "kika tsaya wnn figigiyar yarinyar tana mayar miki da martani, shegiyar yayarta ma haka ta barmu bare wnn ƴar tsituwar, ci uwarta kawai..", babu tausayi Maimuna ta maƙure yarinya ta shiga gaura mata mari, Sabrah ta fasa wata gigitacciyar ƙara sbd har taurari take gani, cikin bacci Umma taji ihun ƴar autarta, ita bata ma san lokacin da baccin ya ɗebeta ba, da sauri ta fito tsakar gida, har lokacin Maimuna ba ta dena wankawa Sabrah mari ba, Maimuna na ɗago kai sukay ido huɗu da Naseer dake tsaye ya harɗe hannu yana kallonta, da sauri ta saki Sabrah ta kwasa a guje zata shiga ɗakin Maama, da sauri Umma da zuciyarta ke tafasa hundred degree Celsius tasa mata ƙafa. Maimuna saida tayi nadamar marin Sabrah da tayi, dan da Naseer ya ringa haskata da maruka saida ya fasa mata baki, kunnenta kam gaba ɗaya signal dinsa ta ɗauke, da kyar Maama ta kwaci Maimuna daga hannunsa, daman yanada cikinta, Umma dai tinda ta janye ƴar autarta ta wuce ɗaki da ita.
★Tini Hajar ta fara sabawa da zaman hotel room din, yau kwanansu huɗu kenan, tin ranar da ya bata waya kullum saita kira Ummanta sun gaisa, da daddare da misalin ƙarfe tara na dare, Hajar na zaune kan carpet tana kallon wani film na comedy mai suna home alone, Nurain na zaune kan couch da pajamas a jikinsa yana operating laptop, wayarsa ya ɗauka ya shiga lalubo numbern wani friend dinsa da sukay karatu tare a India, cikin numbers da yayi saving akan email ya samo numbern abokin nasa da yayi saving da Dr Hammad, dialing numbern yayi ai kam tana fara ringing akay picking, Nurain na sallama Hammad ya ganesa with his voice, bayan sun gaisa Hammad yace "how are you doing yasu Mami...?", Nurain yace "fyn alhmdllh..?", Hammad yace "to masha Allah sai yau aka tina dani kenan", Nurain ya shafa sumar kansa yace "Ai gani ma a garin ku", Hammad yace "really are you in town..?", Nurain yace "yeah, since Sunday ma ina..." shiru yayi jin wata dariya da Hajar ta sheƙe da ita, ya ringa kallonta tana dariyarta her eyes fixed on tv, ta ɗan juyo ta kallesa har lokacin annurin fuskarta beyi fading ba, ganin sunyi ido huɗu tayi saurin tsuke fuska ta juya ta cigaba da kallonta, jin shiru Hammad yace "hello are you there..?", Nurain yace "yeah" suka cigaba da magana, wani abin dariyar aka sake yi a film din, Hajar couldn't help it but to laugh hard, ta toshe bakinta da palm dinta tana ƙoƙarin tsaida dariyar, ta gefen ido ta fakaici kallonsa ai kam taga ashe kallonta kawai yake, ta turo baki tayi twinkling lulu eyes dinta, tashi yayi ya ɗauki remote din TV ya danna off ya koma ya zauna ya ajiye remote din a side dinsa, Hajar ta wani haɗe gira ganin ya kashe mata kallo, juyowa tayi tana kallonsa taga wayarsa ma yake ko a jikinsa, haka kurum don baƙin hali shine zai kashe mata jin dadinta shi kuma ya koma gefe yana wayarsa, wani irin turo baki tayi ganin yayi murmushi kawai zuciyarta ta bata ai da girlfriend dinsa yake waya, miƙewa tayi tana kallon remote din da ya ajiye gefensa, tafiya ta fara yi kamar zata wuce still tana kallon remote din, da sauri ta kai hannu zata wafci remote din, kafin ta kai ga ɗauka shi ya rigata ɗaukewa ya ɗaga sama, ai kam taci tuntuɓe da ƙafarsa gaba dayanta ta faɗa kansa, a gigice ta fara ƙoƙarin ɗagasa ta wani zaro ido, bai bata damar hakan ba yayi saurin dafe bayanta ta sake faɗawa ƙirjinsa, a hankali yace "i will call you back" da haka ya cire wayar a kunnensa ya ajiye gefe, mutsu mutsu kawai Hajar take alan a dole tana so ta sauka a jikinsa, daman da hannu ɗaya kawai ya riƙeta, jin yadda take motsi kawai ya zagayeta da ɗayan hannun, wani irin bugu zuciyarta ta shiga yi hancinta ya cika da ƙamshinsa gashi har saukar numfashinsa tana ji.....✍️
💛 HAJAR 💛
{64..}
Sosai yayi wrapping dinta a ƙirjinsa har saida ta dena mutsu mutsun da take, tayi lamo zuciyarta na tsananta bugu, gaba ɗaya ta gigice ta rasa sukuni, after a while taji ya sassauta riƙon da ya mata, ai kam tayi wuff ta fincike kanta ta ɗagasa, ta koma da baya tana jan fingers dinta murya ƙasa ƙasa tace "wllh bbu kyau haram ne..", tsuke piercing eyes dinsa yayi yana kallonta yace "mene babu kyau..?", ba tasan lokacin da ta galla masa wata shegiyar harara ba tace "me yasa zaka taɓani ai kasan haram ne..", ya haɗe thick eyebrows dinsa yace "Nah.. ohh naga ke kika faɗo kaina young lady or is it a coincidence", ta zuba masa lulu eyes dinta sai kuma ta haɗe rai, yayi slight smirk ya nuna remote din dake gefensa yace "you can take it..", kallon remote din tayi ta wuce ta bar wajen, juyawa yayi yana kallonta ganin ta nufi gado yace "hey ga remote din fa ko kin fasa kallon ne..", banza tayi dashi ta hau gado abinta ta rufa da duvet tana turo baki, taɓe baki yayi ya juya murya ƙasan maƙoshi yace "Silly girl..." ya ɗauki wayarsa ya kira Hammad, tinda Hajar ta kwanta take shaƙar ƙamshinsa da take jinsa a kayanta, ta ringa juye juye tana yamutsa fuska, lokaci guda ta miƙe zaune ta ja siririn hancinta, ko dai ta cire kayan ne ta huta, komawa tayi ta kwanta kawai bata dade ba bacci me nauyi ya ɗauketa wnda hakan yanada nasaba da ni'imtaccen ƙamshin da ta ringa shaƙa ita bata sani ba. da asuba ta farka, a hankali ta fara buɗe idonta jin wata qira'a mai daɗi tana shiga kunnenta, ta fara surveying ɗakin da ido, zaune ta gansa kan prayer mat sautin qira'ar yana tasowa daga wajensa alamar dai shi yake karatun, tarwal Hajar ta buɗe idonta tana kallonsa, a zuciyarta kam mamaki take ai tasha boko kawai ya saka a gaba, ita tinda take ma ta taɓa jin qira'a mai daɗin wnn, gashi kuma ba taga Alqur'ani a gabansa ba alamar da ka yake yi, ta yamutsa fuska a ranta tace ba wani nan ya sayyadi ya fisa, ta lumshe idonta tana tunanin ya sayyadinta wnda ɗaiɗaikun ranaku ne bata tinawa dashi. tashi Nurain yayi bayan ya hattama iya izifin da zaiyi, ya kunna hasken ɗakin sosai, ya ɗan fakaice kallon gado, da sauri ya ɗauke kansa ya wuce ya buɗe closet ya ɗauki kayan da zai saka ya shiga wanka, after 15 minutes ya fito already ya saka kaya a bathroom yana goge cikakkiyar sumarsa da small towel, Hajar da ta buɗe idonta tin bayan shigarsa bathroom tayi sauri ta rufe ganin ya fito, saida yasha white coffee snn ya ɗau jakar Laptop dinsa ya fita wajen bakwai da rabi, yana fita Hajar ta diro daga kan gado, da sauri ta shige toilet tayi wanka, tana fitowa ta kimtsa kanta tsaf don har combing hair dinta tayi, ƙarfe takwas da rabi aka kawo mata breakfast, kaɗan taci abincin don bata jin yunwa sbd tasha coffee, wayar da ya bata ta ɗauko tayi dialing numbern Umma, tana fara ringing Umma ta ɗaga, bayan sun gaisa Hajar tace "Umma yasu Baba da Sabra da Yaya...?", Umma tace "kowa lfy lou alhmdllh, kema ai lfyr kike ko..?", Hajar ta gyaɗa kai tace "uhmm", Umma tace "toh Alhmdllh... Allah yayi albarka sai anjima..", Hajar tace "toh sai anjima..", Umma ta katse kiran. har ƙarfe sha biyu Hajar na zaune kan couch tana kallon tv, daga wnn channel din zuwa wata channel din, ita zaman waje ɗayan nan ya fara isarta fa, ba chass ba Ass saidai kawai taci abinci tayi wanka sai kwanciya, ta dubi agogo taga ƙarfe biyu saura, ita lokacin ma baya mata sauri yanzu, kallon ƙofa tayi jin an murɗa handle, a hankali ya turo ƙofar ya shigo, ido huɗu sukay, da sauri Hajar ta ɗauke kanta, yayi sallama ciki ciki itama ta amsa masa ciki ciki, tini room din ya kaure da pure men scent dinsa, da yake yaune last day na symposium din shiyasa suka tashi da wuri, daman na kwana biyar ne so a yau da take Friday suka gama, tana ganin ya shiga bathroom ta tashi daga kan couch ta ɗauki ledar lunch da aka kawo mata ta koma bakin gado ta zauna ta fara ci, Nurain ya fito daga bathroom bayan yayi refreshing kansa, a fakaice Hajar ta dubesa, lokaci guda ta tsura masa ido tana kallon farar Shirt ƙal dake jikinsa, brain ɗinta ce ta amsa ta fara sinking, kallonsa take babu ƙiftawa tana so ta tina wani abu da yake mata yawo a brain, kamar fa ba lokacin da ya kusan bige yaron nan ta fara ganinsa ba, tabbas da ta ga wnn farar Shirt din tana ƙoƙarin tina wani abu, don ita gaba ɗaya ta manta encounter dinsu ta farko ta biyu da ta uku saita huɗu kawai take tinawa, ya juya ya ɗan kalleta, ganin kallon da take masa ya tsuke ido, wayarsa da tayi vibrate ya ɗauka yaga Hammad ne ke kiransa, bai ɗaga kiran ba ya sake kallon Hajar da har lokacin bata ɗauke idonta daga kansa ba, ya kalli Shirt dinsa wacca ya lura ita take kallo, jan Shirt din yayi kafin ya haɗe gira yace "hey what are you starting at..?", ganin bata amsa ba kuma bata dena kallon nasa ba kawai ya fara tafiya towards her, twisting fingers dinsa yayi a daidai fuskarta wnda ya bada sautin ɗas ɗas, ai firgigit ta dawo daga duniyar da ta lula, haɗe gira tayi ganinsa daf ta ita, ta ajiye spoon din hannunta kan takeaway din abincin da take ci, Calmly yace "what are you starting at..?", ta juya idonta tace "is there anything to stare at..", ya ringa kallon pink lips dinta da take mgana ta wani cokalosu, ya buɗe baki zai mgna knn wayar hannunsa tayi vibrate, ya ɗauke idonsa daga kallon lips dinta ya koma da baya, picking kiran yayi ya kara a kunne yace "ohh Hammad..", from the other side Hammad yace "are you coming..?", Nurain yace "wait ai nace ka turomin inda zamu hadu ko", Hammad yace "Oh c'mon gidana fa zaka zo Dr", Nurain ya sauke ajiyar zuciya yana shafa kansa yace "kawai mu hadu a wani Eatery or Coffee shop haka mna..", Hammad yace "No.. saidai ba ziyarar zaka kawomin ba..", Nurain yace "Alright you know i don't have the Address right...", Hammad yace "ohh i will send it to you right away", Nurain yace "better" da haka ya katse kiran yana sauke ajiyar zuciya, bbu jimawa message din Hammad da ya turo masa da address ya shigo, ya zauna kan couch bayan few seconds ya kwanta ya miƙar da legs dinsa, da hannunsa yayi pillow lokaci guda bacci ya ɗebesa, Hajar na gama cin abincin ta rufe ragowar, itama baccin ne ya tafi da ita daga ɗan miƙewa. Nurain ya farka wajen ƙarfe huɗu, stretching jikinsa yayi bayan ya miƙe zaune,