HAJAR

Chapter 51 of 85

kiransa, bai ɗaga kiran ba ya sake kallon Hajar da har lokacin bata ɗauke idonta daga kansa ba, ya kalli Shirt dinsa wacca ya lura ita take kallo, jan Shirt din yayi kafin ya haɗe gira yace "hey what are you starting at..?", ganin bata amsa ba kuma bata dena kallon nasa ba kawai ya fara tafiya towards her, twisting fingers dinsa yayi a daidai fuskarta wnda ya bada sautin ɗas ɗas, ai firgigit ta dawo daga duniyar da ta lula, haɗe gira tayi ganinsa daf ta ita, ta ajiye spoon din hannunta kan takeaway din abincin da take ci, Calmly yace "what are you starting at..?", ta juya idonta tace "is there anything to stare at..", ya ringa kallon pink lips dinta da take mgana ta wani cokalosu, ya buɗe baki zai mgna knn wayar hannunsa tayi vibrate, ya ɗauke idonsa daga kallon lips dinta ya koma da baya, picking kiran yayi ya kara a kunne yace "ohh Hammad..", from the other side Hammad yace "are you coming..?", Nurain yace "wait ai nace ka turomin inda zamu hadu ko", Hammad yace "Oh c'mon gidana fa zaka zo Dr", Nurain ya sauke ajiyar zuciya yana shafa kansa yace "kawai mu hadu a wani Eatery or Coffee shop haka mna..", Hammad yace "No.. saidai ba ziyarar zaka kawomin ba..", Nurain yace "Alright you know i don't have the Address right...", Hammad yace "ohh i will send it to you right away", Nurain yace "better" da haka ya katse kiran yana sauke ajiyar zuciya, bbu jimawa message din Hammad da ya turo masa da address ya shigo, ya zauna kan couch bayan few seconds ya kwanta ya miƙar da legs dinsa, da hannunsa yayi pillow lokaci guda bacci ya ɗebesa, Hajar na gama cin abincin ta rufe ragowar, itama baccin ne ya tafi da ita daga ɗan miƙewa. Nurain ya farka wajen ƙarfe huɗu, stretching jikinsa yayi bayan ya miƙe zaune, da sauri ya wuce toilet ya dauro alwala gudun lokaci ya ƙure masa, yana idar da sallah ya juya yana kallon Hajar da ke bacci har lokacin bata farka ba, ya sauya kayan jikinsa daga ƙanana zuwa manya, text din da Hammad ya turo masa ya buɗe yana karantawa, shi kam dai yaso su haɗu a wani wajen ba gida ba, dama dai gidansu ne bazai damu ba, wayarsa ya saka a front pocket yace "damn it", ya sake kallon position din Hajar, duƙawa yayi gabanta yayi tapping dinta a hankali, ta buɗe sleepy eyes dinta, da sauri ta miƙe tana murza ido taja da baya, miƙewa yayi yace "hey ki tashi ki shirya.. idan kuma anan zan barki shknn", yana gama faɗin haka ya nufi door ya fita, reception ya wuce ya zauna, after 30mins ya dawo ɗakin ya tarar har ta gama shiryawa, black Abaya wcca bata taɓa sawa ba ta saka, tayi rolling kanta da mayafin Abayan, tanata faman zuge box dinta wacca ta gama shirya kayanta tsaf, tinda taji yace tafiya za suyi taji wani sanyi ya saukar mata don har ga Allah ta gaji da zaman nan din, yana kallon abinda take yace "are you done..?", ta gyaɗa kai tace "Eh" lokacin da ta miƙe tana gyara rolling din da tayi, door ya nufa yace "muje", box dinta ta fara ja tabi bayansa, juyowa yayi yana kallonta, ta saukar da kanta tace "ka manta bag dinka fa..", yace "kema ke kika sa kanki daukar wnn, lokacin da muka zo mu muka dauki kayan", girgiza kai tayi ba tace komai ba, ya buɗe ƙofa ya fita, sakin box din tayi tabi bayansa, bayan ta fito daga room din ya mayar da ƙofar ya rufe, wucewa yayi ya tsaya gaban Elevator tabi bayansa suka shiga tare, suna sauka ƙasa yana gaba tana biye dashi, ganin ya zauna a kujera bayan sun isa reception tayi turus tana kallonsa, shikam wayarsa ya ciro yana duba bolt da ya kira, can kujerar dake nesa dashi ta samu ta zauna, tinda Hajar ta zauna wani gentleman dake zaune opposite dinta ya zuba mata ido, ita kam kanta na ƙasa tana wasa da fingers dinta, Nurain ya ɗago kansa ya kalli mutumin, sosai ya lura da irin kallon da yake yiwa Hajar babu ko ƙiftawa, Nurain ya haɗe gira ya tashi ya koma kujerar dake kusa data ta, ɗago kanta tayi ta kallesa jin scent dinsa, yana latsa wayarsa ba tare da ya dubeta ba ya rage murya yace "baki taho da hijab ba..?", tace "ai baka sako hijab ba da ka haɗa kayan..", ɗago kansa yayi ya ringa kallonta without blinking, ta fakaici kallonsa ganin kallon da yake mata tace "ka dena kallona dan Allah..", yace "ohh really ke da wane idon kika san ina kallonki", tashi tayi ta bar masa kujerar ta koma inda ya taso a hankali tace "ai kallon batin ya isa haka", Nurain ya kalli mutumin a fakaice, gani yayi ya juya akalar kallon nasa zuwa inda ta koma, wani irin murtuke fuska yayi har saida thick eyebrows dinsa suka haɗe, kamar wnda aka fusata haka ya miƙe, babu wani jinkiri ya isa inda ta koma ya figi hannunta ya fara janta suka fita daga reception din, suna fita waje ta fixge hannunta tace "meye haka..", ta fara goge hannun a jikin kayanta, wata ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke ya shafa fuskarsa da palm dinsa, juyowa yayi yana kallonta from head to toe, wani irin haske ta ƙara barin ma da ta saka black din Abaya sai hasken ya ƙaru, sajen forehead dinta ya kwanta luf luf sai kace balarabiya, ya kalli ƙafarta that is so fair har wani ja take sbd haske ga nails dinta pink, da wata iriyar murya yace "wai ke ko socks baki ɗakko ba..", da mamaki ta kallesa tace "toh wai ni na haɗa kayan ne", idan ba ƙafa da hannu da fuska ba babu inda yake bayyane a jikinta, dressing dinta was more than decent, yana duba wayarsa yaga bolt din da ya kira tazo, a front seat Nurain ya zauna Hajar kuma back seat, da haka suka bar harabar hotel din, Hajar ta ringa kallon window wondering a wani gari take, wata unguwar masu hannu da shuni suka shiga, ƙerarrun gidajen dake unguwar sai kace a ƙasar waje, gaban wani danƙareren gida Nurain yasa mai bolt din yayi parking kafin ya fara kallon wayarsa yana duba house numbern na gidan dan ya tabbatar shi din ne, bayan ya tabbatar yayi dialing numbern Hammad, tana shiga Hammad ya ɗauka, Nurain yace "am at the gate..", Hammad yace "Ohk ka shiga mana Dr", Nurain yace "Amm ai bolt ne..", Hammad yace "Okay bari na yiwa gateman mgana kawai ya shigo ciki da kai", Nurain yace "Alright", babu jimawa aka zuge tafkeken gate din gidan, suna shiga fakeken compound din gidan drivern bolt ya parker motar, Nurain ya yiwa mai bolt transfer din kuɗinsa bayan ya masa doubling, back seat ya buɗe yana kallon Hajar da tayi wani lakur yace "come down", a hankali ta zuro ƙafafuwanta ta fito, daidai lokacin Hammad ya fito daga entrance din gidan, da sauri ya ƙaraso inda Nurain yake sukay hugging juna lightly, sai kuma sukay musabaha bakin Hammad har ear yace "i swear i pick a flag..", Hajar dai kawai kallon Hammad take don bai mata kama da ƴan Nigeria ba, kana ganinsa kaga halfcast, Hammad ya kalli Hajar yace "beauty Noor..?", Nurain ya dubi Hajar ya girgiza kai yace "she is someone else", Hammad yace "ohh", da haka yayi leading dinsu zuwa katafaren palourn gidan, Hajar dai ta samu sofa ta zauna bayan shigarsu palourn, sake gaisawa sukay, Hammad yace "ai this is better, koni da naje kano ai har gida naje muka gaisa kuma na gaisa da Mami..", Nurain yace "ya wajen su Ummi...?", Hammad yace "Ummi taje Yamen", Nurain yace "Ohk", Hammad ya dubi Hajar dake zaune kan sofa yace "Hi.. good afternoon..", Hajar ta saukar da kanta tace "ina yini", yace "lfy lou, how are you doing...?", tace "fine alhmdllh", Hammad yace "good", sai kuma ya dubi Nurain dake satar kallon Hajar yace "bari na kira my Madam tazo ku gaisa" da haka ya tashi ya haura sama, bai jima ba ya sakko ya zauna a position dinsa suka cigaba da fira da Nurain, after few minutes da basu kai huɗu ba matar Hammad Maysha ta iso palourn, she's so beautiful brown skin girl, gaisawa sukay da Nurain snn Hajar, bayan nan Maysha ta tashi ta shiga kitchen ta lafto snacks da drinks tray guda ta kawo palourn ta ajiye, ta sake komawa kitchen ta kawo warmers din abinci, Maysha ganin Hajar bata taɓa komai da ta ajiye musu ba ta ɗebar mata tace tazo su shiga ciki taci, Nurain kam yasha drink sai semosa guda ɗaya, Hammad na kallon Nurain bayan Maysha ta wuce da Hajar ciki yace "Please who is this young lady Dr, is she your wife..?", Nurain ya ajiye glass goblet din lemo da yake sha yace "wife.. no she's not", Hammad yace "then", Nurain yace "yah how will i get marry ban gaya mka ba, kasan zan gaya maka koda bazaka zo ba, kaima lokacin aurenka ina India ai ka gayamin right", Hammad yace "Okay then who is she..", Nurain yace "someone" da haka ya dauki lemonsa yana sipping. sai bayan magrib suka bar gidan wnda da ƙyar Nurain ya yarda ya kai time ɗin, bayan sun dawo hotel sun shiga Elevator Hajar dake riƙe da ledar da Maysha ta bata tace "waini ban gane ba fa me muka dawo yi anan?..", a lokaci na farko da ya dubeta, kamar bazai amsa ba can yace "zama mna", ta wani zaro ido tace "what zama fa kace", ya ɗaga shoulder irin yess, da haka ya fita daga Elevator din don sunzo floor din room dinsu, Keycard ya ciro ya buɗe ƙofar room din ya juya yana kallonta yace "get in", ta maƙe shoulder tana ƙoƙarin danne hawayen da yake shirin zubo mata, kallon few seconds ya mata kafin ya shige ɗakin ya barta tsaye nan, Hajar ta goge hawayen da ya zubo mata da bayan hannu, ajiye ledar hannunta tayi a bakin ƙofar ta juya ta koma cikin Elevator, bayan kamar minti biyar Nurain dake zaune kan couch ya miƙe ganin bata shigo ba, door ya nufa yana zuwa yaga wayam, ya kalli ledar da ta ajiye nan bakin ƙofa, lokaci guda ya kalli dogon Aisle din shima yaga babu kowa, da sauri ya shiga Elevator ya sauka reception, saida ya fara ƙarewa reception din kallo nan ma yaga bata nan, har zai fita daga reception din sai kuma ya dawo ya tsaya gaban receptionist yace "amm excuse me", receptionist din yace "yes sir" Nurain yace "Please ba kaga wata young lady ta fita ba..", receptionist din yayi jim yana tunani, Nurain da hankalinsa ya fara tashi yace "she is in black", receptionist din yace "ohh i saw her going out few minutes ago", Nurain ya juya yana kallon ƙofar fita da mamaki, direct exist door ya nufa ya fita harabar hotel din dake da haske tarwal kamar rana, ya sauke numfashi yana shafa kansa yace "damn it", kawai kalle kalle yake a harabar hotel din ko zai ganta, can ya hangota tana tafiya a hankali har ta kai babban gate din barin hotel din, bai san lokacin da ya fara zabga wani sauri ba ya nufi gate, lokacin da ya isa gate din ita harta jima da fita, hangota yayi har tayi nisa da tafiyar da take gefen titi, wani irin mugun gudu motocin da suke wucewa suke, duk motar da tazo a guje take wucewa, haɗe gira yayi yabi bayanta da sauri, yana daf da zuwa kusa da ita with husky voice yace "Ke!! where are you going are you mad...?", lokaci ɗaya ta dakata da tafiyar ta juyo sukay ido huɗu, tattare ƙasan rigarta tayi ta juya ta kwasa a guje, Nurain ya zaro ido ganin uban gudun fanfalaƙin da take wnda tayi masa muguwar zarra, ai kam bashi da wani option da ya wuce ya bita, gudu take ba ji ba gani, ta waiwayo taga ai ya kusa kamota, ganin zai cimmata kawai tayi crossing road, a lokacin da wata shimfiɗeɗiyar mota ta kwararo with high speed, Nurain yaci wani mugun birki yana jin tamkar an kwaɗa masa guduma a ka, da wata iriyar murya mai diri ya kwala kiran sunanta "Hajar"......✍️
💛 HAJAR 💛

{65..}
Saura ƙiris motar ta kwasheta amma duk da haka saida ta gogeta, wata iriyar hantsilawa tayi ta faɗi ƙasan kwalta, ta dauje a duka guiwoyinta da tafin hannu, da sauri Nurain ya ƙaraso inda take, damtsenta ya riƙo ya ɗagata kamar ƴar kaza, ba karamin tashi hankalinsa yayi ba kuma har lokacin kansa bai dena sarawa ba, tin daga sama har ƙasa ya ringa kallonta fuskarsa a matuƙar murtuke, sakinta yayi kafin yasa bayan hannu ya falla mata mari, bata gama dawowa hayyacinta ba ya sake mangareta, saida Hajar taga stars tsabar gigicewa, ta fashe da matsanancin kuka a gigice tace "na shiga uku", wata tsawa da ya daka mata saida ta koma ta zube a ƙasa sbd yadda ƴan hanjinta suka juya, with stern voice yace "you must be mad, wawuya kawai..", a lokacin drivern motar da ya samu ya tsayar da motar far away from them ya ƙaraso inda suke da ɗan gudu gudu, kana ganinsa kasan ƙuruciya ke ɗebansa don bazai wuce 25yrs ba, duƙawa yayi gaban Hajar dake rusa kuka kamar ranta zai fita yace "am sorry", Nurain ya figi hannunta ya miƙar da ita, sosai ta firgita ta sake fashewa da kuka, young man din yace "should I take her to the hospital...?", a taƙaice Nurain yace "no need" da haka ya ja hannunta suka bar wajen tana rusa kuka, a haka yana figarta har suka koma cikin hotel din, direct elevator suka shiga bayan sun wuce reception, har lokacin Hajar bata dena kuka ba, suna isa room dinsu ya wani wancakalar da ita a kan carpet, da sauri da haɗe kanta da guiwarta da take jin tana mata zugi, ya zauna kan couch ya dafe kansa, ynxu idan da motar nan ta bigeta fa sai yadda Allah yayi, ya ɗago kansa ya kalleta zuciyarsa na ƙuna, slight hiss yayi ya tashi ya shiga bathroom yayo alwala, bayan yayi sallah after taking his bath ya saka pajamas, making coffee yayi ya zauna kan couch, ajiye mug din hannunsa yayi kafin ya kalli inda take, har lokacin kanta haɗe yake da guiwa tana shessheƙa a hankali, ya taɓe baki yace "ke!!", ko motsi ba tayi ba bare ta amsa, ya ɗan daga murya yace "ke!", ta ɗago jar fuskarta ba tare da ta dubesa ba, ya haɗe gira yace "tashi kije ki cire wnn black kayan sai kace a palace din sheɗanu", ba musu ta tashi tana jan ƙafa ta janyo box din kayanta, wata soft sleeping gown ta ɗauka ta shige bathroom zuciyarta tamkar za tay bindiga, yabi bayanta da kallo kafin ya ɗauki mug din coffee ya fara sipping wnda daman haɗasa yayi don ya rage masa takaici, ba ƙaramin ɓata masa rai Silly girl tayi ba, sai kace wacca kwai ya fashewa a ciki haka ta fito daga toilet din, a hankali ta zauna gefen gado after few minutes ta kwanta ta rufe da duvet, babu abinda take hangowa sai irin stars din da ta gani, Nurain na gama shanye coffee ya juya ya kalli gado, lokaci guda ya miƙe ya isa bakin gadon, kallonta ya ringa yi kafin ya zauna gefenta, Hajar ta rintse idonta don ba bacci take ba, duvet din da ta rufe ya yaye, bata motsa ba duk da hakan yazo mata unexpected, tin daga ƙafarta zuwa knees dinta da suke a bayyane ya ringa kallo, ya lura da bruises din dake guiwoyinta, a hankali ya kai dubansa kan hannayenta, bai ga ciwo a hannun ba, ya janyo hannun da ta danne yana dubasa shima, a palm yaga taji ciwo, in banda bugu bbu abinda zuciyarta take, me yasa yake taɓata wai, wani azabar tsoronsa take ji shiyasa taƙi motsi, ya ringa kallon fuskarta musamman ma soft cheeks dinta da ya hango zanen yatsunsa uku, wajen yayi jajur, shiyasa ya saka mata bayan hannu idan da front ya saka mata tsaf zai fitar mata da haƙori, ya kasa withstanding abinda ta aikata ne, the girl is so stubborn, ji tayi ya dafa forehead dinta sai kuma ya tuge mayafin da ta rufe gashinta, tini ta buɗe idonta ta miƙe zaune, tashin da tayi bai hanasa cigaba da duba jikinta da yake ba, hakan ne ma yasa ya fara ƙoƙarin ɗaga ƴar rigarta don ya duba inda rigar ta rufe, wata gigitacciyar ƙara ta fasa ta fara ture hannunsa, ganin ko gezau so yake fa ya ɗaga rigar nan sai ta fara kokawa, haɗe gira yayi ya rutsa hannayen nata da hannu ɗaya, ɗayan hannun kuma ya ɗage rigar yana ƙarewa fresh bodyn ta kallo, ƙoƙarin sauka ta fara daga kan gadon ya hanata don katamau ya riƙe ƴar farka, ai kam ta rushe da kuka jikinta har na rawa tace "wayyo Allahna na shiga uku, dan girman Allah ka dena taɓani, Ummata...", sakinta yayi bayan ya tabbatar bbu ciwo a jikin, da sauri taja rigar ta rufe jikinta tana zaro ido, tashi yayi ya shiga bathroom ya fito da kwalbar Dettol, kwalin tissue dake ajiye kan table ya dauka snn ya koma gefen gado ya zauna, Hajar ta muskuta baya tana turo baki, sam bata bari sun haɗa ido ba, haka nan ya goge mata bruises din da taji a hannu da knees da ruwan dettol, tinda ya zare mata ido ta tsaya bbu wani noƙe noƙe, ya mayar da kwalbar Dettol din bathroom ya fito ya rage hasken ɗakin ya hau couch ya kwanta, wajen ƙarfe ɗaya ya farka, zaune ya miƙe ya ringa massaging neck dinsa da ya riƙe, yafi minti biyar yana massaging neck din, ya juya yana kallon gado, can gefen gadon yaga Hajar tabar space sosai, ya murza sleepy eyes dinsa ya tashi

Download complete TXT · Novel page