Showing 213001 words to 216000 words out of 252835 words
"Ya sannu da zuwa, ina yini...", a takaice yace "lfy lou Lil sis.. yaushe kika zo?", tace "ɗaxu da safe..", ya gyaɗa kai ya nufi part din Mami, Hajar tabi bayansa da kallo sai kuma ta kalli Khausar da ta cigaba da abinda take jikin laptop, Hajar tace "Hi Khausar...", ko kallonta Khausar ba tayi ba tace "Sannu fa", Hajar bata sake mata mgna ba ta zagaye ta shiga part din Mami, bata tarar da kowa ba a palourn Mamin don hka ta samu kan carpet ta zauna, kawai saita fara tunanin shin me ta yiwa Khausar ne da take mata haka, ita dai a iya saninta tasan bbu abinda ya taɓa haɗasu tin farko, ta taɓe baki ta zuge handbag dinta ta ciro wayarta, ƙofar bedroom aka buɗe Mami ta fito Nurain na biye da ita, Mami ta karkaɗa ɗan yatsa tace "kaga Nurain ka fita daga idona na gaya maka..", ya shafa kansa yace "Please our Mami just this one..", Mami ta haɗe gira tace "No" da haka ta ƙaraso cikin palourn tana kallon Hajar fuskarta ƙumshe da murmushi, Hajar ta ɗan russuna tace "Mami barka da fitowa...", Mami tace "yau daughter.. sai kuma kika zauna a ƙasa", Hajar tace "ba komai nafi son ƙasan ne", saida Mami ta zauna kan Sofa snn Hajar ta gaisheta cike da ladabi da nutsuwa, Mami ta amsa mata tana tmbyarta ya take, Nurain dai yana tsaye ta bayan kujerar Mami sai kallonsu yake, ƙofar palourn aka buɗe Khausar ta shigo da sallama hannunta riƙe da Laptop, ta ƙaraso ta zauna kan Sofa ta ɗora Laptop din kan laps dinta, Mami tace "rubutun project din ne dai..", Khausar ta langwaɓar da kai sai kuma tace "Eh.. wllh duk na gaji Mami..", Mami tace "Bature ne ya riga ya bar mu da kazar whala..", Nurain yace "project take yi ne..?", Mami tace "Eh... gashi kuma next week zasu fara exams shiyasa akay tafiyar bbu ita", Nurain ya gyaɗa kai yace "Su Aunt Zulaihah sun tafi knn..?", Mami tace "yeah yau da safe suka wuce", ya kalli Khausar yace "A chapter na nawa kike..?", tace "Two", zagayowa yayi ya zauna kujerar dake kusa da nata yace "Muga Chapter 1..", tace "Ohk" da haka ta fita duba inda Slide din yake, Mami tace "yauwa ka duba mata kafin tayi submitting...", Hajar dai na zaune palourn tana kallon wayarta, Khausar na nemo Chaptern ta miƙe masa Laptop din ya fara duba mata, ta zauna hannun kujerar da yake, Hajar ta ɗaga kai ta kallesu sai kuma ta kaudar da kanta, knocking door akay mai aikin Mami ta shigo, saida ta gaishe da kowa na palourn har Hajar snn tace "Hajiya an kawo kayan marmarin..", Mami tace "Ohk.. An gama haɗa garin kunnun..?", Laure tace "A'a shi dai nake haɗawa..", Mami tace "Jeki ki cigaba da aikinki don gobe da safe zanyi amfani dashi insha Allah..", Laure tace "Toh Hajiya" da haka ta tashi ta fita. Bayan sallar magrib Mami na zaune kan prayer mat da ta idar da sallah a bedroom dinta Khausar ta shigo, a hankali ta ƙarasa ciki ta duƙa gaban Mami, Mami na kallonta tace "ya akai daughter..?", Khausar ta saukar da kanta tana twisting fingers tace "Mami dman cewa nayi zanje gidan Yaya sbd na samu ya ringa dubamin chapters din dana rubuta, ko 5days nayi sai na dawo kafin mu fara exams..", Mami tayi ajiyar zuciya tace "Toh shknn ai kam sai kinfi samun lokacinsa a can gidan nasa tinda nan sai yamma yake zuwa, kin gaya masa ne..?", Khausar ta girgiza kai tace "No i ask you first..", Mami tace "Alright i will tell him..", Khausar tace "Toh" da haka ta tashi ta fita. Nurain na dawowa daga mosque sallar isha'i yaga Hajar ta shiga kitchen, murmushi yayi ya bita kitchen din, tarar da ita yayi ta buɗe fridge ta ɗauki ruwa tana zubawa a glass cup, ya ƙarasa inda take ya rutsa cikinta, sosai ta firgita don ba taji shigowarsa ba, ta zaro ido after perceiving his scent tace "This is not proper nan fa gidan Mami ne...", yayi kissing neck dinta yace "Toh mu tafi gidanmu..", zaro ido tayi don gani take tsaf wni zai iya shigowa ya gansu, ta marairaice tace "Moon ka bari please... Allah wani zai iya shigowa", ya sake manna mata wani kiss din yace "Toh ina ruwana, nida matana", habawa ai tini ta fara ɓamɓare hannunsu daga cikinta, sakinta yayi sai kuma yayi Chuckling yace "bari na yiwa Mami sallama sai mu tafi" yana gama faɗin haka ya juya ya fita, tana ganin ya fita ta sauke ajiyar zuciya, ta ƙarasa tsiyaya ruwan ta sha. Direct Nurain ya wuce part din Mami don yi mata sallama, bai sameta a palour ba don hka ya shiga ɗaki, sallah ya tarar tana yi, kawai ya ɗan kwanta rigingine a kan gado yana jiran ta idar, tana idar da sallahr ta juya ta kallesa sai kuma ta fara jan counter, Nurain ya ɗan ɗago kansa sai yaga ashe ta idar, Mami ta gaya masa cewa Khausar zata bisu gidansa, ɗan jimm yayi bai ce komai ba, Mami tace "Any problem with that..?", ya girgiza kai yace "No.. not at all..", tace "Okay", Hajar ma ta shigo ta yiwa Mami sallama snn ta ɗauki handbag dinta ta fita compound don already Nurain ya fita yana jiranta, a mota ta tarar dashi, ta buɗe front seat ta shiga snn ta kullo ƙofar, ya kamo hannunta yace "Baby wife..", ta juya ta kallesa tace "Moon..", yayi murmushi yace "Tare da Khausar zamu tafi, i hope baki da damuwa akan hakan ko?", ta girgiza kai tace "Ba komai ƙanwarka ce fa", babu jimawa sai ga Khausar nan ta fito da jakar kayanta a hannu, back seat ta buɗe ta saka jakar snn itama ta shiga, Nurain ya juya kaɗan yace "baki manta komai ba ko..?", tace "Eh i think so", slowly yaja motar suka bar harabar gidan, suna hawa saman titi ya ɗan kalli Hajar yace "Sweet pie mu siya seafood din ne..?", da mamaki ta dubesa sai kuma ta gyaɗa kai tace "yess", yace "Okay" da haka ya ɗauke kan motar ya canza hanya, firarsa kawai yake da matarsa cikin farin ciki da ƙaunar juna, Khausar dai na maƙale a baya tana danna wayarta amma fa kunnuwanta na kan firarsu, haba ai Nurain har sakin layi yke don a zahirin gsky ya mnta da wata Khausar a motar, Hajar ta juya idanunta ta matsa kusa dashi ta rage murya tace "Moon akwai fa back sitter..", sai a lokacin ya farga ya shafa kansa yana murmushi, bayan sunyi tafiya mai nisa yayi parking a katafaren wajen da foreigners din suke siyar da seafood, kashe motar yayi yace "what do we do... muci anan ko kuma muyi takeaway..?", Hajar tace "Takeaway..", yace "Okay", tace "with lot of Shrimp Moon", ya ja hancinta ya rage murya yace "shi Baby love yafi so knn..?", ta turo baki ba tace komai ba, Khausar dake back seat ya kalla yace "Lil sis kema kina cin seafood..?", Khausar tace "Eh Yaya", yace "Ohk", buɗe motar yayi ya fita, After 5mins Hajar tace "Khausar duk ciki Shrimp yafi daɗi ko..?", Khausar tace "Nope ni kam Octa yafi min daɗi..", Hajar tace "Ohk ni kam Shrimp din nafi so", Khausar ta taɓe baki tace "Toh ke kam ai ynxu bazaki gane wanne yafi daɗi ba tinda yaushe ma kika fara cin seafood din, nasan ba ci kike ba a da, koda yake a inama kika gansa bare kici, Ai sai kayi kamar 1yr haka kana ci kake gane best..", samm Hajar bata gane mgana Khausar ta gwaɓa mata ba, tace "Okay", 15mins Nurain ya ɗauka kafin ya fito, leda biyu yayo shi da Hajar sai kuma na Khausar ita kaɗai, Tara da rabi suka isa gida, Hajar tini ta wuce ɗakinta don so take tayi wnka saita zauna zaman cin seafood din, Khausar ta ƙarewa palour kallo sai kuma tace "where am I staying..?", Nurain ya nuna mata hanyar guest room yace "that room..?", ta gwalo ido tace "Na shiga uku, ni kaɗai zaku bari a downstairs..", yace "Ashe matsoraciya ce... Alright come with me..", da haka ya nufi stairs, ta ɗauki jakar kayanta tabi bayansa, extra room dake upstairs ya nuna mata yace "Are you Okay with this one..?", ta buɗe ɗakin ta leƙa sai kuma ta juyo ta gyaɗa kai tace "Sure", yace "Akwai bedsheet da blanket a closet, and if you need anything let me know...", ta gyaɗa kai tace "Toh", ta ɗauki jakar kayanta ta shiga ciki, ɗakin Hajar ya buɗe bai ganta ba, motsinta ya jiyo a bathroom don haka ya juya ya fita. Ƙarfe goma da minti shida Hajar ta sauka downstairs, hijab ne har ƙasa a jikinta wnda ta ɗora saman kayan bacci da ta saka, kitchen ta shiga ta buɗe fridge ta ciro lemon kwali da bottle water, ta ɗauki plate ta ɗora kan tray tare da ruwa da lemon, tana fitowa kitchen din taga Khausar na saukowa daga stairs, Khausar na matsawa kusa da Hajar taji wni shegen ƙamshi yana tashi a jikinta, Khausar tace "Amm ina house help room dina is so dusty inaso a sharemin..?", Hajar tace "we don't have one..", Khausar ta rumgume hannaye tace "ban gane ba toh waye yake aikin gidan...?", Hajar tace "Nice nake gyarawa", Khausar ta taɓe baki tace "chab snnu ni kam bazan iya donkey work din nan ba, anyway maybe kin saba da whala shiyasa", Hajar ta ɗan kalleta sai kuma tace "Uhmm ko baka saba da whala ba ai dai ka gyara gidanka", Khausar ta juya idanunta tace "Ohk ni ynxu wane zai gyara min ɗakin ina so na kwanta ne..?", Hajar tace "wa kwa zai gyara miki ke zaki gyara abinki ai" da haka ta zagayeta ta nufi stairs, da sauri Khausar ta sha gabanta tace "kince fa ke kike gyara gidan so ki gyara min room din mna", Hajar tayi ɗan murmushi ta wurga manyan idanunta tace "kin shekara ba'a gyara miki ɗaki kin kwanta ba, ki shiga kitchen a store akwai broom da packer da Mop ki gyara abinki Khausar, idan kuma hka zaki kwana ba gyaran saiki rubuɗa a ƙura..", Hajar na gama faɗin haka ta haura sama abinta, direct kuma turakar mijinta ta shige, haka dai Khausar ta ɗauki kayan shara taje ta gyara ɗakin fess. Washe gari as usual bayan Hajar ta idar da sallar asuba ta fito ta gyara gidanta, ta bulala masa turaren wuta mai mugun ƙamshi, ynxu samm ba tada case a fannin ƙamshi don Oum Sulthan makwabciyarta sana'ar siyar da turaruka take na gida da kuma jiki, turarenta kam ba'a cewa komai sbd ƙamshi, har na Sudan India da sauran ƙasashe da suka san turare tana siyarwa. Hajar na gama gyaran gidan ta shiga kitchen ta shirya lafiyayyen breakfast, dining ta kai ta ajiye snn ta wuce room dinta ta fesa wnka, daga hka ta wuce ɓangarensa don taimaka masa wajen shiri tinda yau zai fita aiki, tare suka sauko downstairs tana riƙe da briefcase ta cokala hularsa a kanta, dining suka zauna ta zuba masu Irish a plate ɗaya, sai kuma ta ɗauki bowl ta zuba masu Offals pepper soup, da haka ta ja kujera ta zauna, yace "Heartbeat ina Khausar..?", tace "ina jin bata tashi ba..", yace "Ohk", tace "Na ajiye mata nata a kitchen..", yace "Thank you..", tayi murmushi tace "Eat alot", ta ƙarƙashin table din ya zura hannu ya shafa tummy dinta yace "you too, baby love ma yaci da yawa", ta juya idanunta ba tace komai ba, jin footsteps alamar ana saukowa daga stairs ta fara ƙoƙarin cire hannunsa daga tummy dinta, Khausar ta ƙarasa saukowa ta ɗanyi bowing tace "Good morning Yaya", yace "Morning how was your night..?", tace "great Alhmdllh", ita dai Hajar abincin ta kawai take ci, juyawa Khausar tayi zata koma saman Nurain yace "come join us..", walking gently Khausar ta isa dining din taja kujera ta zauna, sai a lokacin Hajar ta ɗago kanta ta ɗan kalli Khausar tace "kin tashi lfy..?", a takaice Khausar "Eh lfy..", Nurain ya tura mata warmers din abincin gabanta, Khausar ta buɗe ƙaramar warmern tana kallon farfesun da yake fitar da wani ƙamshi mai daɗi, tini yawunta ya tsinke amma saita yamutsa fuska ta rufe, warmer din Irish da kwai ta buɗe itama ta rufe, cup ta ɗauka ta haɗa shayi ta fara sha, Khausar ta ringa satar kallon Hajar don har ynxu hularsa ce a kanta, ganin Khausar na shan shayi bata zuba abincin ba Nurain yace "ki zuba abinci fa..", ta girgiza kai tace "Amm bana cin offals..", ya gyaɗa kai yace "Ohk then, you should cook something else karki zauna da yunwa...", tace "No am okay with the tea", bai sake cewa komai ba suka cigaba da cin abincinsu, Hajar ce ta fara gamawa don haka ta jirasa har ya gama, miƙewa yayi ya riƙo hannun Hajar itama ta miƙe, ya kalli Khausar yace "saina dawo sai muyi karatun ko..?", tace "Toh a dawo lfy..", tabi hannunsu dake riƙe cikin na juna da kallo kafin ta cigaba da shan shayinta, suna fita balcony ya rage tsaho ta ciro hularsa dake kanta ta kafa masa, hannunta dake cikin nasa ya murza yace "stay safe wife..", ta matsa gaff dashi ta sunkuyar da kanta, a hankali ya sunkuyo yayi pecking forehead dinta, yace "Then your turn..", tace "What..?", ya taɓa lips dinsa yace "Peck", ɗaya daga cikin kujerun dake balcony din ta taka ydda zata kamo tsahonsa, murmushi tayi ganin yacca ya wni lumshe ido wato yana jira, saida ta goga karan hancinta a nasa snn ta basa light peck a lips, da uban gudu har dasu tuntuɓe Khausar dake maƙale jikin ƙofa ta koma ta zauna kan sofa, Hajar ta shigo da murmushi a fuskarta, kallo ɗaya ta yiwa Khausar ta haura upstairs tana humming song. Hajar ba ta sake sakkowa ba sai sha ɗaya da rabi, kasaƙe tayi tana kallon palour, an wurgo da kaf throw pillows din kujeru kan carpet, ga ɓawon Abaya da seeds din Apple kaca kaca a ƙasa, Khausar ce zaune kan doguwar kujera ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, ga Orange nan a gefenta tana sha ta tara ɓawon akan hannun kujerar, ko a jikinta kawai typing dinta take a jikin laptop, Hajar tafi 50secs tana kallonta kafin ta juya ta shiga kitchen, turus tayi a bakin kitchen din ganinsa kamar anyi yaƙin badar, gaba ɗaya cupboard a buɗe suke, ga uban kayan wanke wanke da suka cika sink, everywhere was untidy, 30mins ta ɗauka tana gyara kitchen din, toh wai hka ake girki ko kuma dai wulaƙanci ne, gaba ɗaya an ƙone tukwanen da akay girkin, da tazo mopping kam saida tayi da gaske don wni uban vegetables oil ne malale kan tiles, saida ta gama gyaran kitchen din snn ta ɗora lunch, snow rice din da tayi draining ta mayar kan wuta don tayi steaming, fita tayi daga kitchen din, at that time Khausar bata nan, Hajar ta girgiza kai tana kallon palourn lokaci guda ta duƙa tayi picking ɓawon Ayabar ta kai dustbin, throw pillows din kuma ta mayar dasu kan kujera, room dinta ta koma tayi sallar Azahar, downstairs ta sauko don tasan shinkafar ta gama steaming, Khausar ta tarar A palour still dai Laptop take operating, sukay ido huɗu, Khausar ta ɗauke kanta kamar bata ganta ba, itama Hajar din bata kulata ba ta wuce kitchen, sosai tayi mamaki da taji kitchen din ya cika da ƙauri, gani tayi an ƙure wutar gas din bayan kuma ta rage sosai, da sauri ta isa gaban gas din ta kashe wutar a bit confuse, sama sama ta yaɗe shinkafar wcca bata ƙone ba ta juye a warmer, Allah yaso ba tayi ƙauri ba. Wajen karfe uku Khausar taji ƙarar bell, tsallake throw pillows din da ta sake wurgowa ƙasa tayi ta nufi door ta buɗe, murmushi tayi ta koma gefe tace "Yaya sannu da zuwa", ya amsa kafin ya shigo yana ƙarewa palourn kallo, wnn shine karo na farko da ya shigo gidansa ya tarar da hka, sai ya fara neman matarsa a palourn don ya saba idan ya dawo ta taho da gudu ta rumgumesa tana masa snnu da zuwa, tini ya nufi stairs yana cewa "Baby wife.. Sweet pie.. Honey" da haka ya haura saman. Tinda ya dawo Khausar take zuba ido taga ya sauko don suyi karatun amma shiru, ai kam sai wajen sallar la'asar ya sauko shima kuma mosque zai fita, da kansa yace ta jira idan ya dawo zai duba mata, bbu jimawa Hajar ma ta sauko ta haura sama da kayan abinci, sake saukowa tayi ta ɗauki ruwa da lemo daga nan bata sake dawowa ba. Da daddare Hajar na naɗe jikinsa tana kallon stuff dinta, A hankali yake shafa lallausan gashinta yace "Baby wife wai su duk kamarsu ɗaya wadan nan mutanen..?", tayi ƴar dariya tace "A'a fa kowa da kamarsa", kallon Tv yayi yace "Ga wni can kamar Mr Lee", ta ɗaga kai ta kallesa tace "Wanne..?", yace "the one in black and red..", tace "Chab ai shine boss..", yace "Ohh toh a bani spoiler so that i can catch up..", zaune ta miƙe ta fara surfa masa bayani, shi dai kawai kallonta yake yana nodding head don ba fahimta yake ba, shi dai kawai daɗin kallonta yake ji a haka, ya shafa kansa yace "Mene ne ma kika ce sunan actor din..?", ta gaya masa, tuntsirewa yayi da dariya harda jingina da kujera yace "wnn wane irin suna ne sai kace za'a zura da gudu..", dariya tayi ta kwanta a ƙirjinsa listening to his heart beat tace "kaga fa sunansa da daɗi..", yayi wrapping dinta sosai yace "wollah ba daɗi", a hankali ta ɗagasa ta kalli Tv, yace "ita kuma Actress din fa..?", ta maƙe shoulder tace "dariya zakamin wllh..", yace "Toh idan ban san sunansu ba taya zan gane series din", sai da tayi gyaran murya snn ta gaya masa, pointed nose dinsa ya ja ya gyaɗa kai sai kuma ya zuƙe