Showing 228001 words to 231000 words out of 252835 words
ka samu aiki..", Naseer yace "Wllh kam ai da offer dinsa ya fito", Umma tace "Masha Allah..", ya janyo ledar da ya shigo da ita yace "ga wasu kayan ma", Umma ta ja ledar kusa da ita tace "Alhmdllh Naseer ai ka kusa gama haɗa lefen ma", ya waro ido yace "bafa a siyi kayan shafa ba", tace "Toh ai anyi mai wuyar tinda an haɗa sutura da takalma da jakunkuna, kayan Shafa ba masu wni whala bane..", ya shafa kai yace "gani nake kamar kayan basu da yawa", Umma ta riƙe baki tace "Lalala siff dita ai ta zama kantin kwari, kaya kam ka haɗasu ba kaɗan ba Naseer, bari Hajar ta kawo mka abinci kaci saina fiddo mka kaga yawansu..", yace "A'a kar a fiddo in na gansu zan iya shagala", Umma tace "Toh shknn, ai kayi mai wuyar ma wllh, ka gama gini tass har an sakawa gida padlock, a marrar nan ka samu gidan kanka ai ba ƙaramin luɗifi bane", a lokacin Hajar ta shigo masa da abinci a plate da kuma jug din zoɓo mai sanyi. Biyar da ƴan mintina Nurain ya kira Hajar a waya yace mata yaxo, Hajar ta fita palour don da za tayi wayar ɗaki ta shiga, har lokacin Naseer bai tafi ba don dman idan yxo yana jimawa sbd sai ya daɗe baizo ba, tini Hajar ta gayawa Umma cewa zai shigo su gaisa, Umma tace "Toh kawomin hijab dina", Hajar ta koma ɗaki ta kawowa Umma hijab dinta snn ta fito, bbu jimawa suka shigo tare da Nurain, Nurain ya gaida Umma da ladabi, Umma ta amsa da sakakkiyar fuska, bayan sun gaisa da Umma ya juya ya miƙawa Naseer hannu sukay musabaha, Nurain ko minti biyu bai ƙara ba ya yiwa Umma sallama ya fita, Umma tace "marmaza ki shirya ku tafi karki barsa yana jira", Hajar ta shiga ɗaki ta ɗakko handbag dinta ta fito, tace "Umma na tafi, idan Sabrah ta dawo Islamiyya zan kira", Umma tace "Allah ya kaiku gida lfy, saura kuma na sake ganin ƙafarki nan kusa", Hajar ta turo baki tace "next week ma zanzo..", Umma tace "karma ki kuskura na gaya miki", Hajar ta dubi Naseer tace "Yaya ka gaida gida", yace "Aha, Allah ya kaiku gida lfy", tace "Ameen" da haka ta nufi tsakar gida ta fita, cikin mota ta tarar dashi don haka ta buɗe front seat ta shiga, kallonta kawai yake har ta rufe ƙofa ta gyara zamanta, ta ɗan kallesa sai kuma ta buɗa lulu eyes dinta tace "how was your day My Moon..?", yace "Totally dull without you by my side", ya kamo hannunta ya kissing deeply yace "I missed you", tayi murmushi ta sarƙe yatsunta cikin nasa tace "Same", Ai kam hka ya fara driving ba tare da ya saki hannunta ba, saida suka hau saman titi yace "bari mu tsaya mu sayi chocolates ba..?", tace "Ai basu ƙare ba", yace "yeah it is better mu ajiye extra kar ya yanke mna Princess ta mna rigima", tayi ƴar dariya tace "Ohk", A wani mall suka tsaya, tana gaba yana biye da ita suka shiga cikin mall din, direct Aisle din Chocolate da Crunchy biscuits suka tsaya, ya bata basket yace ta ɗebi wnda take so zai duba wni abu, Hajar ta fara dubawa tana ɗebar abinda take so tana sakawa a basket, kukan baby ta jiyo daga jikin Aisle din da take, ai kam da sauri ta zagaya, wata mata ta gani durƙushe a ƙasa tana kwashe kayan da suke zube tana zubawa a basket, babyn da yake hannunta sai tsanyara kuka yake tana ɗan jijjigasa, Hajar ta isa inda take ta ajiye basket din hannunta, matar ta ɗago ta kalli Hajar, Hajar tace "ya Baby yake kuka" da haka ta sunkuya ta amshi babyn ta fara jijjigasa, ai kam tini yayi shiru, Mamansa ta ƙarasa kwashe kayan ta miƙe tana kallon Hajar tace "ngd", Hajar tayi murmushi tace "mention not" sai kuma ta ciro babyn daga shoulder dinta zata miƙawa Mamansa, ba ta miƙa mata ba ta tsaya tana kallon fuskar babyn wcca ta mata kama da fuskar wni mutum da ta sani a rayuwa, muryan namiji suka ji ance "Habibty are you done..?", Matar ta juya gun wanda yayi mgnar tace "Eh Habiby..", Hajar ta ringa kallonsa still tana riƙe da babyn har ya ƙaraso, shima kallon nata yake bbu ko ƙiftawa, Hajar ta saukar da kanta sai kuma ta ɗan russuna tace "Ya Sayyadi ina yini", ya ringa kallonta yace "Hajar Adam Gini..?", Hajar ta gyaɗa kai, Nura ya kalli kyakkyawar matarsa Maryam yace "Ɗalibata ce", Maryam ta kalli Hajar tace "Allah sarki sannu ko", Hajar tace "Ashe matar Ya Sayyadi na kawowa temako..", Maryam tayi murmushi tace "Ai kuwa dai", har Nurain zai wuce Aisle din da suke ciki sai kuma ya dawo sbd ya hango Hajar, ya shigo Aisle din walking majestically, saida ya kusa zuwa kusa dasu snn yace "Baby wife..", Hajar ta juya tana ganinsa tayi wni kyakkyawan murmushi tace "My Moon", shima murmushin ya mata kafin ya ƙaraso ya dafa shoulder dinta yace "what are you doing here..?", tace "Ya Sayyadin Islamiyyarmu da mukay sauka a hannunsa ne..", Nurain ya kalli Nura for the first time yace "Okay" sai kuma ya miƙa masa hannu sukay musabaha, briefly suka gaisa, Nurain ya kalli Hajar yace "let go wife..", tace "sure" da haka ta miƙawa Maryam baby boy din tace "Allah ya raya", Maryam ta amshi babyn tace "Ameen ngd", Hajar ta sunkuya zata ɗauki basket din da ta ajiye amma tini Nurain ya rigata, ya riƙe hannunta suka bar wajen, shopping din suka ƙarasa snn suka bar mall din. Haka rayuwar ta cigaba da garawa Couple din cikin jin daɗi da annashuwa suna rainon unborn dinsu tare, kuma har zuwa wnn lokacin ba a duba gender din babyn ba kuma suma basu dena musu ba, kowa yana kan bakarsa, shi yace baby girl ita kuma tace boy, a haka cikin Hajar ya shiga wata tara, saida ya shiga wata na tara ne snn ta fara jin nauyin jikinta, ba ta iya wnn hawa da saukar kamar da amma dai ta kan sauka downstairs twice a day. Yau da wuri Hajar ta kwanta cause tin safe take jin slight pain sai ynxu ta samu ya lafa mata shine ta kwanta, tana kwance kan gado shi kuma Nurain yana zaune kan couch yana aiki jikin laptop, wajen ƙarfe sha ɗaya Hajar ta farka, ba tasan lokacin da ta kwaye duvet din jikinta ba tana so ta miƙe zaune amma ta kasa, ji take kamar bayanta zai ɓalle, ta shafa both side dinta wai ko za taji present din mijinta, tana jin wayam ta buɗe idonta tarwal tace "Moon", da sauri Nurain ya taso ya isa gaban gadon, ya ɗagota yace "Mene ne..?", ta shiga yarfe hannu don ciwon gaba gaba yake, kawai girgiza kai take sideways ta kasa cewa komai, hasken ɗakin ya kunna sosai, Hajar ta muskuta tayi kneeling kan gado sai kuma ta kwallara wata ƙara tace "Nurain..!!", da sauri ya dawo ya zauna, ta riƙe hannunsa da iya ƙarfinta tace "ka ciremin wnn cikin.. Princess ce ko Prince ni dae bana so na bar maka", habawa ai tini Nurain ya fahimci cewa labor ne, ya tashi ya fita daga ɗakin yana jin yacca take kwala masa kira, bai wni jima ba ya dawo, gani yayi har ta kifo daga kan gadon, ya duƙa gabanta ya fara ƙoƙarin cire mata rigarsa dake jikinta, kawai daurewa yake don har ya fara rikicewa, ita kam Hajar kawai cewa take Nurain ka cire Princess din na bar maka, da kyar yayi jarumtar saka mata ƴar shawalwalar rigarta da ya ɗakko mata, ya mayar da ita kan gado yana jera mata sannu, ƙoƙarin hantsilowa take yayi saurin riƙeta, ta fashe da kuka tace "wayyo na shiga uku na lalace nace ka ciremin", da kyar ya samu ya cire hannunsa a nata ya fita, box din da ya shirya 2weeks ago mai ɗauke da duk wani abu na baby da mother sbd zuwa asibiti ya ɗauka ya fita, bai wani jima ba ya dawo bayan ya kai box din mota, da bibbiyu ya haura stairs, a ƙasa ya sameta malala ta sake sakkowa daga gadon, da ita da turtsetsen cikin nata ya haɗa ya ɗauka, ko gidan ma bai iya rufewa ba ya ajiyeta gaban mota ya kwantar da seat din, gida biyu hankalin Nurain ya rabu, ɗaya yana kan tuƙin da yake ɗayan kuma yana kan Hajar da take cikin raɗaɗin ciwo, da haka suka isa private hospital din Dr Mansoor, tini Midwives suka amshi abarsu aka wuce da ita labor room, Nurain ya ringa shawagi tsakanin ƙofar labor room din, After 20mins wata Midwife ta fito, Nurain yace "how is my wife..?", Midwife din tace "Sir please go in your wife need you..", bai ƙarasa jin ta bakinta ba ya buɗe ƙofar labor room din ya shiga.......✍️
Read page 90 and 91
👇
https://chat.whatsapp.com/CjtDNv3iMzmFhMVE9jTZzW
💛 HAJAR 💛
{90..}
Nurain na shiga labor room din ya tarar da Hajar kwance kan gado, ya ƙarasa gaban gadon ya shafa fuskarta, ta buɗe idonta a hankali, duk gumi ya tsattsafo mata a goshi tana ajiye numfashi a hankali, ya kamo hannunta yana murzawa with care yace "Sorry wife", hawaye ne suka fara sauko mata tace "Nurain bana son nan wajen ka kaini wajen Ummana", ya shafa kanta yace 'Sorry, Allah ya saukeki lfy wife", lumshe idonta tayi ba ta sake cewa komai ba, wata Nurse ce ta shigo instead of Midwife tace "Amm za'a mayar da ita ward tinda labor din ya tsaya..", Nurain ya dan yi jim duk da cewa yaji abinda Nurse din ta faɗa, yace "idan laborn ya dawo sai kuma a dawo da ita nan..?", Nurse din tace "Sure", ya girgiza kai don bai yarda ba duk da yasan cewa hka tsarin hospital yake, gsky ba za a wahalar masa da mata ba a ringa wni walagigi da ita, yace "A barta a nan din har zuwa ta haihu mna..", Nurse din ta rausayar da kai tace "Ohk" sai kuma ta juya ta fita, Nurain ya janyo kujera ya zauna ya sake kamo hannunta ya riƙe, a haka bacci ya ɗan kwashe Hajar, shi kam yana zaune tunkurkur yana gadi don dman ya saba, ya ciro wayarsa ya duba lokaci yaga 12:30 na dare, yana nan tare da matarsa, duk bayan 20 to 30mins sai Midwife ko Nurse sun shigo to check on Hajar, ƙarfe huɗu da rabi lokacin asuba ta kunno kai toh a lokacin ne Hajar ta farka, kuma kai tsaye naƙudar ta taho mata gadan gadan, An sha gumurzu iya gumurzu, daf da sallar asuba Hajar ta silloɓo ƙatuwar baby girl dinta bayan ta leƙa lahira, gidan glass kam saida ta shigesa sbd girman ƴar, a duk wnn gumurzun Nurain na room din don hannunsa ta yiwa mummunar riƙo da haihuwar tazo, tini aka gyarata ita da baby dinta aka mayar dasu Amenity ward, bayan fitar Nurse da Midwife din da suka kula da ita Nurain ya taka gaban gadon, ya ɗaga fuskarta da tayi jajur, pecking forehead dinta yayi, ya ɗago yana sake kallonta yace "Thank you so much wife", ita dai ba tace masa komai ba sai aukin lumshe ido, yayi pecking hannunta deeply yace "Thank you for making me a Father..", ya sake pecking hannun yace "Thank you for giving birth to my child..", a kasale ta masa murmushi sai kuma ta lumshe idonta, sai a lokacin Nurain ya ɗauki babyn tasa dake kwance kan gadon jarirai, ya ringa kallon fuskar babyn wcca tke baccinta peacefully, kumatunta a cike ɓul ɓul ga kuma nauyi tubarkallah sai kace ba first born ba, rumgumeta yayi sosai a jikinsa for a while, bai mayar da ita kan gadon jariran ba ya kwantar da ita kusa da Mother dinta wcca baccin whala ya kwasheta, sai a lokacin Nurain ya samu chance din kiran Mami, ai kam bugu ɗaya ta ɗaga tinda asuba tayi, Mami kam da taga kiransa saida gabanta ya faɗi, tini ya sanar mata abin alkhairy da ya faru, ta tmbyesa suna gida ko asibiti yace asibitin Dr Mansoor daga hka suka katse wayar, Saida ya kira Nurse ta tsaya a room din tare da Hajar da babyn sa snn ya wuce mosque dake kusa da hospital din don yin sallah. Ƙarfe shida da minti sha biyar na safe Mami ta iso asibitin tare da Sakeena wcca a harabar asibitin suka haɗu itama tazo, Mai aikin Mami ta shigo da basket din abinci, Nurain ya tashi daga kan kujerar da yake zaune yana kallon Hajar da baby dinsa da suke bacci har lokacin yace "Mami snnu da zuwa", Mami tace "yawwa" sai kuma ta matsa gaban gadon tana kallon fuskar Hajar, Sakeena ta ƙarasa shigowa ta ɗauki Babyn ta zauna gefen gado tana kallonta, sai kuma ta kalli Nurain tace "Mace ko namiji..?", yace "Baby girl..", Sakeena tace "Masha Allah, Ya ilahi wllh kamarku ɗaya brother..", Mami ta juyo ta kalli Nurain tace "Tin yaushe take bacci..?", yace "Tin Asuba", Mami tace "Ohk", saida Mami ta zauna a position din da Nurain ya bata snn Sakeena ta kawo mata Baby, Mami ta ringa kallon Babyn snn tace "Tubarkallah Masha Allah..", Babyn kamarta ɗaya da ubanta bbu abinda ta bari, har thick eyebrows dinsa saida ta kwaso saidai ita komai nata na mace ne, even complexion na ubanta ta ɗakko saidai ynxu akwai hasken jinjirantaka shiyasa tayi haske, Sakeena ta tsaya daga gefen Mami tana cigaba da kallon Babyn, the baby is so cute, gata ƙatuwa masha Allah, duk da cikar fuskarta da cheeks amma hancinta bai nutsu ba, hancin ya fito sosai gashi ɗan ɗos masha Allah, wani motsi babyn tayi ta yamutsa fuska har saida dimple din da take dashi ya bayyana kansa for the first time, Sakeena tace "Woah Masha Allah har da dimple...", Mami tayi murmushi tana jin son yarinyar, Nurain dai ganin gaba ɗaya hankalinsu na kan Babyn kamar ma sun manta dashi ya duƙa ya gaida Mami, Mami ta kallesa da murmushi kwance fuskarta ta amsa snn tace "An samu ƙaruwa.. Toh Allah ya raya mna ita bisa sunnar manzo..", ya shafa kansa bai amsa ba, Sakeena ce tace "Ameen", After 30mins Hajar ta farka, Sakeena ta haɗa mata shayi mai kauri ta kai mata, ganin taƙi shan shayin Mami tace "ko ba kya son wnn dear..?", Hajar ta ɗago idonta da suke a kumbure tace "A'a", Sakeena tace "ko ya miki zafi ayi diluting..?", Mami tace "A'a da zafin sai yafi.. try and take it even small daughter..", a hankali Hajar ta fara shan shayin, har saida taji ɗuminsa a cikinta da take jin tamkar an yashe mata ƴar hanji, Nurain ne ya shigo ya ajiye ledar da ya shigo da ita, sosai yaji daɗi ganin ta farka, ya matsa gaban gadon yana tmbyrta how she is feeling, Mami tace "kira likita ya dubata", yace "sure", ya nufi door ya fita, bai jima ba ya dawo tare da Nurse da Dr, both the Mother and the Baby were fine haka likitan ya faɗa, snn yace nan da 12 idan an sake tabbatar da lfyrsu za a sallamesu. Kafin ƙarfe takwas su Umma suka zo tare da Anty da Hafsah, tini Sakeena ta miƙawa Anty babyn bayan sun gaisa, Hajar ta gaida Umma da Anty, Umma dai kawai kallon ƴarta ta take, Hafsah ta koma kusa da Hajar ta zauna tace "Sannu sister..", Hajar tayi murmushi kawai, daga kan su Umma bbu wnda ya sake zuwa, don duk wnda ya kira yace zaizo Mami take cewa ya wuce can gidan suma gasu nan dawowa, Hajjaju Hajiya ma can gidan Mami tasa aka wuce da ita, kamar yacca Dr ya faɗa hakan kuwa akay, 12 aka sallamesu bayan an tabbatar bbu wni matsala, gidan Mami aka wuce da Hajar snn aka bata ɗaki guda, kafin kace me ɗakin ya cika sai zuwa ake ganin baby da duba Hajar, Umma dai bata biyosu gidan ba ta wuce gida duk da cewa tana son kasancewa da ƴarta, taso ace an bata ƴarta ta tafi gida da ita amma kuma kawaici yasa tayi shiru, ai suma taga yacca suke taraiyar Hajar din suna bata kula ta musamman, ai soyayya ce ta jawo har suka tafi da ita, Hajar na zaune kan gadon ɗakin, Anty kuma na zaune kan kujerar room din, Hajiya ce ta shigo tana dogara sandarta, Anty ta tashi daga inda take tace "Hajiya ga waje..", Hajiya ta zauna kan kujerar tace "yewwa" sai kuma ta kalli Hajar tace "Sannu Hajaru.. haihuwar fari ki haifo wnn narkekiyar ƴa ai dole a miki sannu", Hajar dai ta saukar da kanta ba tace komai ba, Sakeena ce ta shigo da Babyn a hannunta wcca take tsanyara kuka don ta farka ne, Hajiya tace "A'a lfy..?", Sakeena na jijjiga babyn tace "Tashi tayi ne Hajiya", Hajiya tace "miƙata ga uwarta ta bata Nono", Sakeena ta miƙawa Hajar Babyn, Hajar bata amshi Babyn ba tayi kamar bata san ana miƙo mata ba, amma kuma har cikin ƙahon zuciyarta take jin kukan yarinyar, Sakeena ta ajiye mata ita akan laps tace "feed her", Hajar ta saukar da idanunta tana kallon babyn, tinda taxo duniya sai ynxu ta kalleta da kyau, wni gurmi ne taji ya buɗe a zuciyarta wnda wnn shine karo na farko da ya buɗe, ta ringa kallon jinjirar dake wutsil wutsil a cinyarta tana ƙishin ƙishin, lokaci guda ta fara kuka, ɗaukarta tayi ta sakata a shoulder ta ringa shafa bayanta, still dai babyn bata dena kuka ba, Anty ta zauna kan gadon tana kallon Hajar da kyau tace "ki bata mna", Hajar ta saukar da kanta tace "Ni me zan bata", Hajiya ta caɓe zancen tace "ki bata Nono ko saita shiɗe ne..", firr Hajar ta kasa feeding babyn a gaban mutane, yama za ai tayi feeding gaban mutane, Sakeena tayi murmushi don ta gane manufar Hajar, itama haka tayi wnn wautar a haihuwarta na fari, Sakeena ta amshi babyn daga hannunta, feeder dinta na