BA NI DA GATA

Chapter 10 of 45

fa da ke ya ke magana. Ya ce ki bishi. Kuma idan ya juyo ya ga ba ki bi sa ba, zan karya miki k'afa da duka wallahi".
Zaro idanuwa Binty ta yi ta re da fad'in,
"Da ni ya ke yi? Ai na d'auka da ke ya ke yi. To mai zan masa?".
"Oho ni ma ban sani ba, dan Allah ki je ka da ya juyo ya ga bai gan ki a bayan sa ba. Ku ma ya fara miki nisa fa". Fad'in Fanan.
Ai da gudu Binty ta bi bayan Suhail d'in har ta isa inda ta ke ta na haki don ya mata nisa. Ga gidan da shegen fad'i da tsayi.
"Ga ni Yaya, Fanan ta ce wai ka na kira na". Fad'in Binty ta na haki.
Juyowa ya yi ya kalle ta ta re da fad'in,
"Shiga mota". Ya fad'i hakane ta re da bud'e gaban mota, shikuma ya zagaya ya shiga mazaunin driver. Ya yin da uku daga cikin y'an matan shi su ka shiga gidan baya. Sauran abokan sa kuma su ka shiga na su motocin kasancewar sun zo da ita.
Har lokacin Binty na tsaye a wajan ba ta da niyyar shiga cikin mota.
"Ke dan uwar ki zan ta tsayawa ne ina jiran ki ba za ki shiga mota ba?". Suhail ya fad'a ya na zazzaro mata idanuwan sa da suka juye irin na masu shaye-shaye.
Saboda yadda ya yi maganar da k'arfi Binty ba ta san sadda ta shige gaban motan ba ta na zazzaro idanuwa.
Mik'owa hannunsa ya yi ta re da rufe motar ka na ya yi mata key ta re da reverse ka na ya fito daga parking load d'in.
Fanan kuwa wani ajiyar zuciya ta sauke ta re da nufar wajan malam.
Shi kuwa Malam tun sanda Binty ta ruga ta bi bayan Suhail gabansa ke bugawa don sarai ya san halin Suhail d'in ciki da bai. Yaron da a k'asar waje ya yi primary da secondary d'in sa. Lalacewar da ya so ma yi ne ya sa Alhaji Usman da kan shi ya dawo da shi gida Nigeria a wani zuwan bazata da ya yi masa ya tarar da abun asshan da ya ke yi da mata da kuma abokan sa turawa su ke yi. Babu irin kwayar da Suhail bai sha. Har safarar cocaine ya na yi ba ta re da sanin iyayansa ba. Mutum uku ya ke shakka a rayuwarsa, wato mahaifinsa da Hajiya Na'ima uwargidan mahaifin na sa. Duk rashin kunyar sa bai iya yin ta a gaban ta, sai kuma babba d'a ga Alhaji Usman da hajiya Na'ima, wato Julaibib Usman Mai rabo, wanda a yanzu haka ya na US ya na Masters degree d'in sa.

Malam ya kalli Fanan da ta zauna akan kujera ta na sakin ajiyar zuciya ta re da fad'in,
"Ina ki ka baro Bintyn?". Ya fad'i haka ne ya na kallon cikin idanuwan ta gaban sa na fad'uwa ka da Suhail d'in ya lalata y'ar mutane.
"Ya Suhail ya ce ta bi shi". Fad'in Fanan in I don't care manner, don ita Sam ba ta d'auka wani abun zai ma ta na cutarwa ba.
"Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Maza Fanan je ki fad'a Hajiya da sauri". Fad'in Malam.
"Malam mai ya faru?" Fad'in Fanan zuciyar ta na bugawa saboda yadda malam ya yi magana.
"Kar ki yi tambaya Fanan, ke dai yi sauri je ki fad'awa Hajiya Suhail ya ta fi da Binty". Fad'in malam.
Da sauri Binty ta mik'e ta re da yin part d'in Anna da gudu don zuwa fad'in abunda malam ya aiketa ta fad'i.


Kusada gate d'in k'arshe, wato gate d'in da Oga Solomon ke gadi Suhail ya rage gudun mota ta re da ciro sigari a cikin aljihun wandon sa ya saka a baki.

"Baba Haruna, see that stupid boy. He finish chop the girls, now he wan return them back to their houses". Fad'in Oga Solomon ya na tab'a k'afar Baban Haruna.
"Mtsww, I pray for da boy may him get HIV, may be he will stop following womens. Mtsee very bad pikin". Fad'in Baban Haruna.

Wani irin horn Suhail ke dannawa kamar zai cire kunnuwan Oga Solomon da Baban Haruna. Da gudu Oga Solomon d'in ya ta shi ta re da wangale gate d'in gidan.
Sai da Suhail ya zo gab da Oga Solomon d'in ka na ya sauke glass d'in motar ta re da turo kan sa waje ya saka sigari a baki ya na kallon Oga Solomon.
Oga Solomon ya soma lalube-lalube a jikin wandon shi ya Ciro lighter ta re da kunnawa Suhail d'in sigarin. Idanuwan sa ne su ka sauka a kan Binty da ke ta zare idanuwa. Gaban Oga Solomon ne ya buga da k'arfi ta re da fad'i cikin zuciyar sa,
"This girl don finish. Jesus helf her".

Da mugun gudu ya ja motar ta re da barin gidan.
Oga Solomon kuwa cikin hanzari ya kulle gate d'in ta re da dawowa wajan da Baban Haruna ya ke zaune ta re da fad'in,
"Heeeyyy! Baba Haruna dis girl don finish wallahe".
"Which girl?". Fad'in Baban Haruna ya na kallon Oga Solomon d'in.
"Da pretty girl way dat stupid old bitch bring dis money".
"Watin come happing to her?". Baban Haruna ya fad'a a firgice.
"I saw her with my eyes open in dat stupid boy car. I known he will go and rape that girl. Chaii! I pity for her". Oga Solomon ya fad'a kamar zai yi kuka.
"Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Allah dai ya tsinewa yaron nan. How did she even follow him? Kai Allah ya cece ki yarinya". Fad'in Baban Haruna ci ke da jimamai.


"Anna! Anna!! Anna!!! Ki na ina?". Fanan ta fad'a tun ta na hawa sama har ta k'arisa shiga parlourn saman.
Kicib'is su ka yi da Anna da ta fito a gigice.
"Lafiya Fanan ki ke min irin wannan kiran? Ina Binty?". Anna ta fad'a ta re da rik'o kafad'un ta.
"Yaya Suhail ya tafi da ita a mota". Fad'in Fanan.
"Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un3×". Hajiya Na'ima ta fad'a ta re da d'aukar wayar ta akan center table ta nufo stairs don saukowa parlourn k'asa Fanan bi ye da ita.
Wasu numbobi ta danna a wayarta ta re da kara wayar a kunnanta. Ringi d'aya cikin ba biyu wanda ta kira ya d'aga ta re da fad'in,
"Assalamu alaikum Anna....."
Katse shi ta yi ta re da fad'in,
"Wa'alaikumussalam. Fu'ad zo gida yanzu ina nai man ka. Ko kuma ka da ka zo gida, duk in da Suhail ya ke ka naimo shi ka dawo min da yarinyar da ya fita da ita. Za ka gan ta ba ta wuce Fanan ba. Dan Allah ka hanzarta yanzu ka naimo shi tun kamin ya lalata amanar da aka bar min".
"Yanzun nan kuwa Anna". Fad'in barrister Fu'ad ta re da katse wayar.
Wa ni number ya yi dialing bugu d'aya aka d'aga, ta re da fad'in,
"Sai Oga, da girman kujeran Barrister".
"Ka na ji na ko kacha, yanzan nan na ba ka minti biyar ka binciko min in da Suhail ya ke ka kira ni ka fad'a".
"An gama Barrister". Fad'in kacha ta re da katse kiran.
Barrister Fu'ad kuwa mik'ewa ya yi ta re da tattara files d'in da ke gaban shi ya jawo drawer ya saka ta re da d'aukar key d'in motar shi ya fito ya kulle office d'in shi ya fito zuwa wajan da motar shi ta ke ya shiga ta re da mata key ya bar High court d'in don cika umarnin mahaifiyar sa.


Cikin wani k'aton gidan gona ya yi parking. Makekan gidan gona ne in da ake kiwo kala-kala. Gyefe guda kuma wani rantsatstsan two bedroom ne. Shi kad'ai ya zo sai Binty da ke gaban mota ta yi tsamo-tsamo. Duk ya sallami sauran abokan sa da y'an matan sa da duk sun girme sa don gaba d'aya shekarunsa sha takwas ne, girman jiki ne Allah ya ba shi irin na mahaifiyar sa.
Bud'e motar ya yi ta re da fitowa ka na ya zagaya ya bud'ewa Binty k'ofa ta re da murtuke fuska ya ce,
"Sauko ki fito". Ya fad'a hakan da kausasshan muryan shi da shaye-shaye ya fasa.
Binty jiki na rawa ta fito daga motar nan ta re da rukub'ewa a jikin k'ofa ta na kallon sa da idanuwan ta da har ya cicciko da hawaye.
"Idan ki ka sa ke ki ka min kuka, kin ga dai girman gidan gonan nan ko, to daga ni sai ke ce a ciki. Zan iya yanka ki in bizne ki babu wanda ya sani, don haka kar ki sake ki min kuka. Duk abunda na ce ki yi kawai ki yi. Kin ji abunda na ce miki?".
Jijjiga kai Binty ta yi jikinta na k'ara tsuma musamman da ta ji maganar yanka da biznewa.
"Oya wuce muje". Fad'in Suhail ya na nuna mata hanya da hannun sa.
Simi-simi ta yi gaba k'afarta na hard'ewa. Tawowa ya yi ya wuce ta ta re da isa wajan k'ofar ya bud'e ka na ya nuna mata cikin d'akin da hannu.
Kallon shi ta yi idanuwan sun yi jazurr, hatta leb'anta rawa su ke yi kamar mai jin sanyi saboda tsabar yarda ta firgice. Shiga ta yi hawaye na zubowa daga idanunta tai saurin saka bayan hannunta ta goge.
"Oya cire wannan hijjab d'in". Suhail ya fad'a ya na tsare ta da idanuwa.
Hijjab d'in ta cire ta re da rik'e shi a hannun ta. Domin gaba d'aya ya firgitata, musamman muryan shi da ya ke kama da na rik'ak'k'un garada.
"Ke ban san iskanci. Aje hijjab d'in nan ko in zo wajan nan in taka miki wuya". Suhail ya fad'a ya na zazzaro mata idanuwan shi.
Saboda tsabar rud'ewan da ta yi, jifa ta yi da hijjab d'in a kan fridge d'in da ke d'akin ba ta re da ta sani ba.
Kallon ta ya shiga yi from head to toes ta re da fad'in,
"D'anya ce shataf, amma haka nan zan yi manaji a haka za ta girma musamman idan ta na jin taki".
Zame wandon jeans d'in jikinsa ya yi, ya rage da ga shi sai boxer. Rigar jikin shi da singlet ya cire ta re da zama a kan three sitter ka na ya ce,
"Zo nan". Ya fad'i hakan ne ya na shafa cikin sa.
Binty kuwa tsaye ta ke a wajan ta ki zuwan sai kallon shi da ta ke yi.
"Ba da ke na ke yi ba". Ya fad'a da k'arfi sai da ta firgita wanda ba ta san lokacin da ta isa gare shi ba.
Jawo ta ya yi ta re sa da zaunar da ita a saman cinyar sa ka na ya zame hulan da ke kan ta. Kyakkyawan gashin kan ta bayyana. Yayin da jelar gashin ke tab'a masa gwiwar k'afarsa.
"Wow!". Suhail ya fad'a ya na shafa kan tun daga tsakiyar kanta har k'arshan bindin gashin.
Hancinsa ya kai wuyarta ya na sunsuna ta re da lumshe idanu saboda daddad'an kamshin man shafawan Fanan da Bintyn ta shafa. Ga wani fitinannan k'amshi da gashin kan na ta ke yi saboda gyaran da mai saloon d'in nan ta ma ta da kuma wanda Fanan ta ma ta d'azu.
B'alle buturan rigar jikinta ya yi ta re da wurgi da rigar a kan tiles. Hannu ya kai ya na shafa ko ina a jikinta kamar ya na shafa jikin budurwa.
Ita kuwa Binty ji ta yi kamar ana watsa mata ruwan zafi mai mugun zafi a jikinta. Mik'ewa ta yi a razane ta na susan jikinta don wani irin rad'ad'i da ta ke ji.
"Ke ina wasa da ke ne? Waya ba ki izinin ta shi a kan jikina? Dawo ki zauna kuma duk abunda na mi ki ke ma ki min". Suhail ya fad'i ya na gwalalo mata idanuwa.
K'in zuwa Binty ta yi ta na soshe-soshen jiki ta re da hawaye.
Mik'ewa ya yi a zafafe ya d'auke ta da mari ta re hankad'ata ta fad'i k'asa.
Cire belt d'n wandon da ya yi ta re da zame shi ya fad'i k'asa ka na ya damk'o gashin kan ta har sai da ta saki ihu.
Ka yan jikinta ya cire kaf ka na ya kwantar da ita flat a kan 3three sitter ya Shiga k'ok'arin cire boxer d'in jikinsa. Dai dai lokacin Barrister Fu'ad ya banko k'ofar d'akin ya shigo.
Idanuwan sa ya sauka akan Suhail da ke nai man afkawa yarinya.
"Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Suhail kai wani irin d'an akuya ne? Dan uban ka wannan y'ar k'ank'anuwar yarinyar za kai rapping?" Barrister Fu'ad ya fad'a ta re da k'arasawa kusa da shi ya d'auke shi da maruka hagu da dama.
Shi kuwa Suhail jan boxer d'in sa da ya fara cirewa ya yi ta re da jaa baya ya na fad'in,
"Ni ai ba tilas nai ma ta ba, ita ta biyo ni".
'Kara d'auke shi da mari Barrister ya yi ta re da fad'in,
"Uban ka na ce, Suhail. Wannan yarinyar mai ta sani da Har za ta bi yo ka? Yarinya k'ank'anuwa da ko balaga ba ta yi ba, ita ka ke so ka b'ata. Yanzu idan Fanan ko Sunaina a kai wa haka za ka ji dad'i!".
"Oho! Idan su su ka kai kan su, to ni in ruwa na. Yanzu fa kowa fa abunda ya ga dama ya ke yi. Wa ya san kai me ka ke aikatawa". Suhail ya fad'a ya na wani ciccijewa kamar d'an daba.
Wanka masa mari ya sa ke yi ta re da nu na shi da yatsa ya ce,
"Dole ka ce oho tunda ba uwa d'aya ta haife ku da wad'anda na lissafo ba. Ku ma da ka ke cewa wa yasan abunda ni na ke aikatawa, an fad'a maka kowa d'an iska ne irin ka? To ba ri ka ji, wallahi, tallahi, duk ranar da ka sake attempting yi wa wata yarinya fyad'e, na rantse da girman Allah wannan a wannan karan ba zan saurari Anna da ta ke hanani ba. Ni ka d'ai na san hukuncin da zan d'auka. Ban key d'in gidan nan". Barrister Fu'ad ya fad'a ta re da mik'a masa hannun sa alamar ya sa ka masa key d'in a hannun sa.
Suhail sai wa ni cicciza ya ke yi kamar ba zai ba da key d'in ba. Can kuma ya mik'a masa.
Barrister ya kalli in da Binty ta ke jikin ta sai rawa ya ke yi ta re da fad'in,
"Sauko ki d'auko kayan ki kisa mu tafi wajan Anna".
Jikinta na rawa ta sauko daga kan kujerar ta re da d'aukar kayanta da ke yashe a k'asa. Saboda yadda jikinta ke rawa, sai ta kasa saka kayan. Barrister Fu'ad ya karb'i kayan ta re da saka mata, ka na ya kama hannunta ta re da kallon Suhail d'in ya ce,
"Fita ka d'au motarka, zan kulle gidan". Barrister Fu'ad ya fad'a ya na antaya masa harara.
Wa ni dogon tsaki ya ja ta re da fad'in,
"Kill joy". Kamar zai bangaje sa ya fice daga d'akin.
Barrister Fu'ad ma tsakin yaja ta re da yin kwafa ya ce,
"Zan yi maganin ka soon. D'an iskan yaro kawai". Ya fad'i hakan ne ta re fitowa hannun shi rik'e da hannun Binty. Kulle k'ofar ya yi lokacin tuni Suhail ya ja mota da uban k'arfi ya bar gidan.
Kasancewar mota Barrister na k'ofar gate. Kai tsaye fita su kai ya kulle gate d'in da key ya kuma saka kwad'o ta re da yin wajan mota ya bud'e gaban Binty ta shiga, shikuma ya zagaya ta re da shiga mazaunin driver ya kunna motar ta re da reverse.
Sai da su ka hau hanya, sannan Barrister Fu'ad ya juyo ya kalli Binty wacce har a lokacin gaban ta bai dai na fad'uwa ba.
"Me ya sa ki ka biyo sa". Barrister ya fad' ta re da mai da duban sa ga titi.
"Shi ya ce dole sai na shiga mota. Shine ya kawo ni nan". Fad'in Binty muryanta na rawa. Don har yanzu ba ta dai na jin jikinta kamar ana yayyafa mata ruwan zafi ba. Don har turiri-turiri ta ke ji jikin na mata.
"Daga yau ko ya kira ki ka da ki je. Ka da ma ki rik'a zuwa in da zai gan ki. Idan kuma kun had'u bi sa kuskure, ki yi gudo ki koma wajan Anna kin ji?". Barrister ya fad'a ya na kallon kyakkyawar fuskan da tsoran da ta ke ji ya k'ara bayyanar da kyawun fuskan ta.
"Yauwa Malam ne ke mana karatu, shine ya kira ni. Kuma Fanan ce ta ce idan ban je ba karya ni zai yi".
"Idan kuma ki ka je ya tab'a jikin ki, mutuwa za ki yi". Fad'in Barrister Fu'ad ya na kallon idanunta saboda ya ga reaction d'in ta.
Aikuwa ta zaro idanuwa ta re da fad'in
"Ba na so na mutu, Allah zan gudu idan na gan shi. Wajan Malam ma bazan k'ara zuwa ba". Fad'in Binty hawaye na silalo mata.
"Oho ni dai na fad'a miki, ba shi kad'ai ba ma, duk namijin da ki ka sa ke ji ka yadda ya na wasa da jikin ki, ko ya na tab'a miki jikin ki, ko ya ke ji tab'a na da jikin, to mutuwa za ki yi murus, saboda haka ba ruwan ki da wasa da maza, kin ji".
"Na ji, ba zan yi wasa da maza ba. Fanan kawai zan yi wasa da ita".
"Good girl. Menene sunan ki?". Barrister ya fad'a.
"Suna na Binty Hashimu mai goro. Kai kuma fa?". Binty ta fad'a ta na kallon shi.
"Yaya Fu'ad, ko ki ce Yaya Barrister. Sannan daga yau ba Binty Hashimu sunan ki. Tsoffi ke cewa Hashimu. Daga yau duk wanda ya tambayi sunan ki, ki ce Binty Hisham mai goro kin ji?".
"Binty Hisham mai goro". Binty ta maimaita ta na kallon shi.
"Eh daga yau haka za ki rik'a fad'i". Fad'in Barrister

Download complete TXT · Novel page