BA NI DA GATA

Chapter 9 of 45

d'akin.

Ka mo hannun Binty Fanan ta yi ta re da fad'in,
"Menene sunan ki? Ni suna na Fanan Usman Mai Rabo. Ke fa?".
"Suna na Binty ummmm, ummm Binty.... Binty.... Yauwa, Binty Hashimu mai goro". Binty ta fad'a ta na mai jin dad'in tuno sunan da Kandala ta fad'a mata a kan duk wanda ya tambaye ta sunan mahaifin ta.
"Nice name. Amma sunan ki kenan Binty ko kuwa Nick name d'in ki ne?". Fad'in Fanan.
"Nee name? Menene nee name kuma?".
Dariya ce ta zo wa Fanan d'in, ai kuwa ta sake shi har towel d'in jikin ya kusan za me wa.
"Ba ki tab'a zuwa boko ba ne?". Fad'in Fanan.
"Ni ban tab'a zuwa ba. Hadaan ne kawai ke zuwa". Fad'in Binty.
"Wa ye kuma Hadaan?". Fanan ta tambaya.
"Ba ki san shi ba". Binty ta ba ta amsa ta re da sa ke fad'in,
"Fitsari na ke ji sosai".
"Oh sorry, ta so mu je in nu na mi ki yadda za ki yi amfani da bayin". Fanan ta fad'a ta re da nufar bayin Binty na bin ta a ba ya.
Kai hannu Fanan ta yi kan wani kyakkyawan panfo sai ga ruwa shaaa. Wani irin tsalle Binty ta yi ta re da ficewa daga bayin da gudu jikinta na rawa.
Da gudu ita ma Fanan ta bi bayanta ta re da fad'in,
"Lafiya Binty? Mai ya faru?'.
"Hannu na ga kin kai a jikin irin wannan abun mai kama da panfo kawai sai na ga ruwa ya zubo. To Allah akwai dodo a cikin bayin nan".
Dariya Fanan ta yi ta re da ka ma hannun Bintyn su ka ko ma ba yin.
"Ki kwantar da hankalin ki babu wani dodo a cikin ba yi. Zan ko ya miki yadda a ke amfani da komai a cikin nan wajan".
Sai da Fanan ta ko ya mata yadda ake amfani da komai, kasancewar Binty ta na da saurin fahimta da d'auke abu a kai, ta fahimci yadda ake amfani da bayin. Don Fanan ba ta fita ba sai da Binty ta gwada amfani da wa su abun tukun ta fita.
Ko da Binty ta fito tu ni har Fanan ta gama shiryawa cikin wando pink da riga white, sai tai parking gashin ta a gyefe da pink d'in ribom, kasancewar ita d'in y'ar kwalliya ce kuma ita ma ta na da gashi ba laifi don ya zubo a kafad'arta.
"Yauwa kin yi alwala?". Fanan ta tambayi Binty.
"A'a ban yi ba". Binty ta ba ta amsa.
"To ko ma ki je ki yi, lokacin sallah na ta wuce wa. Ba kyau wasa da sallah". Fad'in Fanan.
Komawa cikin bayin ta yi ta re da d'auro alwala ko in ce shirme ka na ta dawo da'kin. Tu ni har Fanan ta fiddo ma ta da wani riga da skirt y'an kanti kalar pink da ratsin purple a jiki. Don Fanan gaba d'aya kayanta da wuya ka ga babu pink colour a jiki. Don ko a school sunan ta pinky.
"Na yi alwalar". Binty ta fad'a.
"Yauwa goge jikin ki sai ki shafa wannan mai d'in ki saka wad'annan kayan ki sai ki sallah ga praying mat nan na shimfid'a miki".
Kallon mai d'in ta din ga yi ta re da fad'in,
"To Fanan ya ake shafawa? Ban iya ba".
Cike da mamaki Fanan d'in ke kallonta ta re da fad'in,
"Na tab'a so d'aya, amma ba ni na shafa ba, wata ce ta shafa min".
"Lord in heaven". Fad'in Fanan ta re da rik'e goshin ta.
"Mai ki ka ce?". Binty ta fad'a ta na kallon Fanan d'in.
"Ohhh nothing. Ban ce komai ba. Yanzu dai kalli ki ga yadda ake shafawa". Fanan ta fad'a ta re da matso lotion d'in ta shafa a jikin. Ita ma Binty ta yi kamar yadda ta ga Fanan d'in ta yi.
Powders Fanan ta d'auko ta shafa mata ta re da taje mata gashin kan ta da ya zubo har tsakiyar bayanta ta kuma ka ma mata shi da ribom ta bar jelar ba ta re da ta nad'e ba.
"Ki na da gashi Binty". Fad'in Fanan d'in.
"Ke ma ki na da shi Fanan. Na ki ba b'aki ba ne irin na wa, ya fi na wa kyau".
"Ke! Allah na ki ya fi kyau, du ba fa, ga cika da tsawo ga shi bak'i sosai. Yanzu dai ta shi ki yi sallah sai mu je parlour". Fad'in Fanan ta re da mik'a mata hijjab.
Kayan da Fanan d'in ta fito mata da shi ta saka ta re da hijjab d'in ka na ta hau kan darduman.
Kai tsaye ba wani tada ik'ama bare a kai ga karatun sallah ta tafi sujada.
Waro idanuwa Fanan ta yi ta na kallon Bintyn ci ke da tsoro da kuma tsan-tsan mamaki.
Ita kuwa Binty bayan ta d'ago daga Sujadar sai ta yi ruku'u ta kuma k'ara yin sujadar. Ha ka ta din ga yi har sai da ta yi raka'a takwas ka na ta ce,
"Assalammaa alaiku". sau biyar ta re da mik'ewa ta kalli Fanan ta re da fad'in,
"Fanan na gama".
Ba ki sake Fanan ta ce,
"Yanzu wannan sallah ce ki ka yi? Haka ake sallan?".
"Eh haka naga a na yi a garin mu".
"Lallai! Wallahi to duk y'an garin ku ba su iya sallah ba. Ku ma muje wajan Anna ki je". Fad'in Fanan ta re da yin hanyar parlour Bintyn na bi ye da ita a baya.
A parlour su ka samu Anna d'in ta na kallan tashar Arewa 24 su na haska shirin mata a yau.
"Anna, wallahi i`matsala. Onni owawa julde. Owi b'e gari rimab'b'e, nihib'b'e julirta. (Anna akwai matsala. Wannan yarinya ba ta iya sallah ba. Kuma ta ce y'an garin su duk haka su ke sallar)".
Kallon ta Anna ta yi ta re da fad'in,
"Innoye ojulurta? (Yaya ta ke salar)".
"Daga sujjada ohud'd'i julde. Ko jande julde uwatta. (Daga sujada ta ke fara sallar. Ko karatun sallah ba ta yi)".
"Gaskiya i`matsala. Unangai yaki jande to modibbo mud'un ware. (Gaskiya akwai matsala. Za ku rik'a zuwa karatu ta re idan malamin ku ya zo). Amma nan ga ka, ekki tukimo i hankali. (Ke ma ki rik'a koya mata a hankali)".
"To Anna, mi'ekki taimu jande". Fad'in Fanan.
"To yahun yama abinci". Fad'in Anna ta re da mai da duban ta ga TV, amma sam hankalin ta ya bar TVn ya ko ma tunanin Binty gaba d'aya.
"Lallai yarinyar nan ta na buk'atar taimako". Fad'in Anna cikin zuciyar ta.

Fanan kuwa Dining d'in da ke parlourn ta nu fa ta re da zama ta zuba farfesun Kaza da kuma sinasir, ka na ta zuba wa Bintyn.
Da kyar Fanan ta iya cinye rabin sinasir ta re da cinyar kaza ta tura plate d'in gaba. Ita ma Bintyn kasancewar ta k'oshi rabin sinasir d'in taci. Kazan ne dai ta k'ara cin cinya da wani tsokar nama har ta lalata gaban rigar ta da roman farfesun Kazan nan.
"Oh my God! Du bi yadda ki ka lalata gaban rigar ki, ga shi malam ya ku sa zuwa ku ma ta re za mu je mu ko yi karatu a wajan shi. Mu je in ba ki wata rigar ki canza". Fad'in Fanan ta re da mik'ewa.
Ita ma Bintyn mik'ewa ta yi ta re da bin bayan Fanan zuwa d'akin ta.




*_________*
Tsaye ya ke gaban katotan plasma da ke manne a jikin bango d'akin. Hanu ya kai ta re da k'aro volume d'in home theatern, ka na ya canza music ta cikin wayar da ke hannun sa kasancewar da AUX ya ke amfani. Wakar D'banj ya saka fall in love ya shi ga bin wak'ar kamar haka.


🎻 _I'm D'banj or skibanj like my Jamaica friends call me_
_When the koko master fall in love_
_You know say water water don pass garri_
_Hmmmmn_
_I'm in love, are you in love?_
_Omo you don make me fall in love (you don make me)_
_Fall in love oh, fall in love(you don make me)_ _We suppose marry, 'cause you don make me fall in love (you don make me)_
_Fall in love (you don make me)_
_Fall in love_ (you don make me)
_My sweet potato_
_I wanna tell you my mind, wanna tell you my mind oh_
_I no understand oh_ _'Cause I dey see well-well but them say love is blind oh_
_You see as you dey so_
_you are the love of my life, you are the love of my life oh_
_I cannot deny woo_
_I wanna make you my wife, make you my wife ohh_
_see, I never though that I'll find someone like you_
_That will capture my heart, and there's nothing I can do_
_But since I set my eyes on you_
_Omo you don make me fall in love(you don make me)_
_Fall in love(you don make me)_
_Fall in love(you don make me)_
_We suppose marry, 'cause yo don make me fall in love oh (you don make me)_
_Fall in love(you don make me)_
_Fall in love(you don make me)_
_Fall in love oh_ 🎻

A matuk'ar fusace ta banko k'ofar ta re da shigowa tta kashe home theater ta re da buga wayar da bango ka na ta juyo ta kalle shi idanuwan sun kad'a saboda b'acin rai ta ce,
"Abu Sufyan ba za ku kashe ni ba wallahi sai lokaci na ya yi. Yanzu da girman ka saboda kai sha-sha-sha ne ba ka san in da ke ma ka ciwo za ka cika min part d'ina da hayaniyar wak'e wak'en banzan ka. To wallahi ka ki ya ye ni. Da ku manya zan ji ko kuma da k'anwar ku Sabrin da ke nai man saka min hawan jini mahaifin ku na d'aure mata gindi? Ko rantsuwa na yi ba zan yi kaffara ba, Abu Sufyan ba kai sallar asubha ba. Mai makon ku da Ku ke maza ku ma manya ku tsaya min a kan k'anwar ku da ke nai man fin k'arfi na, amma ku kan ku nai ma Ku ke ku hauka ta ni. Haba Abu, kun yi min adalci kenan? Ana zuga ku kuna k'ara tab'arb'arewa ku a naku tunanin k'aunar ku a ke yi ko? To wallahi idan za ka natsu, ka natsu. Shekara uku kamar yau ne a wajan ubangiji. Ai Babban wan na Ku zai dawo". Hajiya Sakna na gama fad'in hakan ta juya ta fice ta na jin wani k'una a k'asa zuciyar ta.
Ta na fita Abu Sufyan ya ta'be baki ta re da fad'in,
"Mom wallahi ki na da matsala. Dad'in aunty Junaina ke nan, ba ruwan ta da sakawa mutum idanu". Ya fad'i hakane ta re da kunna home theatern ya rage volume d'in ta re da cigaba da miming ya na rawa.

"Ya Allah ka na kallon komai. Ka taimaka min ga me da lamarin y'ay'ana".
"Sannu wacce duk duniyar nan ita d'aya ke da y'ay'a. Ni fa wallahi akan takurawa y'ay'ana wallahi za mu samu mugun sab'ani da ke Sakina. Ke ba za ki koyi da Junaina ba? Ba ki ganin yadda ta ke yi da y'ay'an ta har da ma na ki y'ay'an kamar k'awayan ta. Ta na barin su suyi duk abunda su ke so in dai ba zai cutar da su ba".
"Cutarwa ke ce Alhaji? Cutarwa ku ma na nawa? Ai Junaina da kai kun dad'e ku na cutar min da y'ay'a wajan d'aura su a hanya mara b'illewa barin ma Sabrin da Ku ka riga ku ka halakar da ita. Kuma wallahi tallahi sai Allah ya tambaye ku a kan hakan da Ku ke yi. Kun sa Sabrin ta fi k'arfi na. Yanzu haka ka duba agogo almost to 4 amma yarinyar nan ba ta dawo daga makaranta ba bayan an tashi tun 2:00pm. Kuma na aika driver ya ce makarantar a kulle ba ta can. Na ma ka magana ka ce min ai tasan garin ba b'acewa za ta yi ba. Haba! Haba!! Haba!!! Alhaji. Kai ka na ganin hakan dai dai ne? Ina ta ke zuwa? Da izinin wa ta ke fita? Yadda yanzu kidnapping ya yi yawa a gari. Idan aka sace ta fa?".
Duk maganganun da Hajiya Sakna ta yi bai shige sa ba, sai maganar sace Sabrin d'in da ta yi ne ya girgiza shi. Wayar sa ya zaro daga cikin aljihu ta re da fita da sauri ya yi wajan mota ya na kwalawa driver kira.
Da gudu driver ya zo ta re da duk'awa a gaban Alhaji Saifullahi.
Wawan mari Alhaji Saifullahi ya d'auke Shafi'u driver da shi sai da ya kifa k'asa. Ka na ya nu na masa hannu ta re da fad'in,
"Wallahi duk ranar da ka k'ara shigowa gidan nan ba ta re da Sabrin ba, a bakin aikin ka kuma sai mun yi shari'a da kai. Kai wallahi ba zai yuwu ba. Bodyguard zan d'auko wa y'a ta". Kamar mahaukaci haka Alhaji Saifullahi ya bangaje Shafi'u ta re da shiga mota ya ja a guje ya bar gidan da tuni mai gadi ya bud'e don ya na ganin duk abunda ke faruwa ka da shi ma ya samu ba shi rabon.


Ta re su ka fito Binty na bi ye da ita a baya sanye da hijjab. Wani waje da aka zagaye da fararan kujeru su ka nufa in da Malam Abdulrazaq ya ke zaune ya na jiran su k'araso.
Sallama su ka yi ta re da zama ka na su ka gaishe sa.
Amsawa ya yi ya na kallon Binty kasancewar Hajiya Na'ima (Anna) ta kira sa ta masa bayani a kan Bintyn, ta kuma ce masa ya taimaka ya lura da ita ta iya duk abubuwan da ya kamata. Kuma ya yi mata alk'awarin in sha Allah zai yi hakan.
"Mai nene sunan sabuwar d'alibar tawa?". Malam ya fad'a ya na mai kallon Bintyn.
"Suna na Binty Hashimu Mai goro". Fad'in Binty.
"Masha Allah. Da fatan za ki natsu ki kuma ba ni hankalin ki saboda ki koya ta re da fahintar abunda zan koya miki?".
"Eh zan yi Malam". Fad'in Binty. Kasancewar sai da Anna tai ma ta fad'a sosai akan duk abunda Malam ya koya mata ta tabbatar ta iya shi. Domin idan har ba ta iya ba sai ta Zane mata jikinta.
"To Alhamdulillah, yanzu za mu fara da ummul kitab wato fatiha. Bud'e Qur'anin ki". Malam ya fad'a.
Upside down ta rik'e Qur'anin. Don iya tsayin rayuwar ta ma ba ta tab'a ganin shi ba. Karb'a Fanan ta yi ta re da nuna mata yadda ake rik'e Qur'anin.
Tun a wajan bismillah Malam ya san akwai babbar matsala. Domin ba ta iya ba. Sai dai in da hankalin shi ya kwanta, yadda Bintyn ta ke da saurin d'auke abu a kwakwalwarta.

Sanye ya ke da three quarter da riga armless, sai wani shegen glass da ya kwama a fuska. Hannun shi rik'e da goran fanta da yaji kayan maye a ciki. Zugan abokan sa da kuma 'yan matansa da na abokan ba shi a bayan shi cikin shiga na rashin d'a'a.
Cak ya tsaya ya na k'arewa wajan da su Binty su ke zaune malam na ko ya masu karatu. Takawa ya yi har in da su ke ta re da k'urawa Binty idanuwa ko kyaftawa ba ya yi.
Ita kuwa Fanan ganin wan na ta ya nufi wajan da su, tu ni jikinta ya d'au rawa. Don mawiyacin abu ne su had'u bai mata mummunar duka ba.
"Zo nan dan uwar kiii"




*_MATAR SAYYADEE_*
🌹 *19-20*🌹

Jikin Fanan na wani irin rawa ta mik'e ta soma takawa a hankali ta na tsoran irin dukan da zai yi mata.
Shi kuwa malam zubawa sarautar Allah idanu ya yi, domin ba wannan ba ce rana ta farko da Suhail d'in ya ke hakan idan su na karatu ba.
"Dan kutumar uwar ki, in ta tsayuwa ina jiran ki? Kin tsaya ki na wani tafiya simi-simi kamar macijiya. Wallahi na k'irga uku ba ki k'araso nan ba, sai na karya k'ashin k'afar ki". Fad'in Suhail ya na wani muzurai.
Da gudu-gudu Fanan ta k'arasa wajan sa ta re da fad'in,
"Ya Suhail ga ni. Wa ni abun zan yi maka". Ta fad'i hakan ne bakinta na rawa kamar wacce tai k'arya.
Sai da ya k'ara kallon in da Binty ta ke, ka na ya dawo da duban sa izuwa ga Fanan d'in ta re da fad'in,
"Wa cece wancan yarinyar?". Suhail ya fad'a ya na wani yamutsa fuskan shi.
Kallon Bintyn ta yi, ka na ta mai da du ban ta ga Suhail ta re da fad'in,
"Anna ta ce min y'ar aiki ce, za ta rik'a ta ya ni ayyukan gida".
"Y'ar aiki". Suhail ya maimaita cikin zuciyar sa ta re da k'ara mai da du ban sa ga Bintyn da ta mai da hankalin ta gaba ga karatun suratul Fatihan da malam ke koya mata.
"Kai! Malam ka ke ko malum-malum, sako yarinyar nan ta zo nan". Fad'in Suhail ya na wa malam d'in wani kallon k'ask'an ci.
Kamar malam zai ce wani abu, sai kuma ya kalli Binty ta re da fad'in,
"Je ki ana kiran ki". Ya fad'i hakan ne ta re da mai da duban sa a kan Qur'anin sa.
Binty kuwa mik'ewa ta yi ta re da nufo in da Fanan da ya Suhail su ke a tsaye. Ta na zuwa wajan ta tsaya k'ak'am ta na kallon fuskan Suhail da ke kallon ta from head to toes.
"Fanan mai ya sa ki ka tsaya a nan bayan malam na jiran mu zai mana karatu? Har na fara iyawa Allah. Malam ya ce zan yi k'ok'ari sosai".
"Ke biyo ni". Fad'in Suhail ta re da wucewa gaba.
Ita kuwa Binty ba ta san ma da ita ya ke yi ba. Ganin ya yi gaba ita ma ta juya za ta koma wajan malam domin ya cigaba da koya mata karatu.
Ruk'o hannunta Fanan ta yi ta re da fad'in,
"Binty Yaya Suhail

Download complete TXT · Novel page