BA NI DA GATA

Chapter 12 of 45

sai pant. Da sand'a ta fito ta re da bud'e k'ofar a hankali don ganin ko ya fice daga part d'in ta gaba d'aya.
Shurun da ta ji ne ya sa ta koma d'aki ta re da d'aukar wayarta ta danna numbern Wasila da ke can d'akin ma'aikata mata.
Wasila na d'aga wayar Hajiya Mansura ta ce,
"Dawo maza-maza ya fice, kuma kar ki bari a gan ki". Ta na gama fad'in haka ta yanke wayar.


Daga nan d'akin matar shi ta biyu ya nufa, wato Hajiya Huriya (Business woman kenan).
Ita a parlourn k'asa ya same ta da uban kaya a gaban ta, gyefe guda kuma kud'ad'e ne sai uban lissafi ta ke yi. Ga uban y'an aiki a gabanta sai had'a mata kaya su ke yi su na saka wa a cikin wani kwali su na manne kwalin da salatep.
Alhaji Usman na sallama, gaba d'aya y'an aikin nan su ka mik'e su na kwasan gaisuwa ta re da k'ok'ak'in barin parlourn.
Dakatar da su ya yi ta re da fad'in ku yi zaman ku. Ni ma wuce wa zan yi yanzu".
Komawa su kai su ka zauna su na kallon Hajiya Huriya da ko kallon Alhaji Usman d'in ba ta yi ba, sai faman lissafi ta ke yi.
Murmushi Alhaji Usman d'in ya yi ta re da fad'in,
"Barka hajiya y'ar kasuwa".
Sai a lokacin ta d'ago da kan ta ta re da fad'in,
"Ohhh sorry Alhaji, na bar ka tsaye ina ta faman lissafi. Kaya ne nai ordern su, shi ne su ka iso yau na ke dubawa".
"Masha Allah! Allah ya kawo kasuwa. Babu wani matsala ko?". Fad'in Alhaji Usman d'in.
"Babu". Ta fad'i ba ta re da ta kalle shi ba.
"To sai da safe. Amma dan Allah ki d'an sallami bayin Allahn nan su ma su samu su huta. Dare mahutan bawa. Tun safe su ke aiki".
"In sha Allah yanzu za mu gama su tafi su kwanta". Fad'in Hajiya Huriya.
"Mu kwana lafiya". Fad'in Alhaji Usman ta re da ficewa daga d'akin ya nufi part d'in Suhail. Sallah ya tarar da shi ya na yi. Ja masa k'ofar ya yi ta re da furta Alhamdulillah cikin zuciyar sa. Daga nan kuma ya nufi in da ya ke wato d'akin Hajiya Na'ima.

Ya na tura k'ofar wani k'amshi ya daki hancinsa sai da ya lumshe idanunsa.
"Alhamdulillah, masha Allah". Fad'in Alhaji Usman ta re da k'ara bud'e k'ofofin hanci ya na shak'ar daddad'an k'amshin da ke fesowa daga cikin d'akin.
Tsit d'akin ya ke. Babu kowa a parlourn k'asa. Kasancewar tu ni Hajiya Na'ima ta sallami y'an aikin ta. Saboda ba komai ta ke bari su ke mata ba. Musamman girki, har yanzu ita ta ke abunta da kan ta. Kuma babu girkin da ba ta iya ba. Daga na zamani har na gargajiyan.

Sama ya nufa, nan ma sai da ya lumshe idanunsa saboda k'amshin ya fi wanda yaji a parlourn k'asa. Kallon dining ya yi da ke jere da kulolin abunci da kuma fruit.
"Ke ta musamman ce Na'ima". Fad'in Alhaji Usman ya na nufar dining d'in.










*BA NI DA GATA ISN'T FREE, PAY #500 THROUGH THIS ACCOUNT NUMBER 0592412800, SAID ZULFAU GTBANK. SCREENSHOT YOUR EVIDENCE AND SEND IT TO THIS NUMBER 08128755583👆*



*MRS SAYYADEE*✍🏻
🌹 *23-24*🌹

Bud'e kular farko ya yi, ya yi arba da favourite d'insa wato mashed potato da ya ji bushashshan kifi sai zuba k'amshi ya ke yi. Duk da daddare abinci light ya ke ci, sai da miyan shi ya tsinke da ganin mashed potato d'in nan. D'ayan kulan kuma zallar bushashshan kifin ne ta masa farfesun sa. Ko kad'an ba k'arni kasancewar gona ce wajan gyara kifi. Ga yankakkun fruits nan a k'aton tire dangin su apple, banana, pineapple, watermelon, grapes da sauran su.
Grapes d'in ya d'auka ta re da sakawa a bakin sa ta re da lumshe idanuwa. Dai-dai lokacin Hajiya Na'ima ta fito daga d'akin su Fanan domin du ba su.
Da murmushi ta k'ariso wajan ta re da fad'in,
"Barka da dawowa Abu Julaibib. Ya gajiyan hanya?". Hajiya Na'ima ta fad'a ta re da k'ariso ta tsiyayi ruwa a dispensers ta mik'a masa har da d'an duk'awa.
Karb'a ya yi ta re da fad'in,
"Alhamdulillah Ummu Julaibib. Allah ya sa ka miki da alkhairi ya k'ara shirya miki zuri'ar ki baki d'aya".
"Ameen". Ta fad'a ta re da jawo masa kujera ya zauna, ka na ita ma ta ja ta zauna ta re da soma serving d'in shi. Favourite d'in sa ta zuba masa ta re da mik'ewa ta kai har gabansa, ka na ta dawo wajan zamanta ta na kallon sa.
Aje cup d'in ruwan da ke hannunsa ya yi, ta re jan kujera baya ya mik'ewa.
Kallon shi ta yi ta re da fad'in,
"Abu Julaibib lafiya ka tashi?".
"Zan je na wanke hannu na ne. I preferred using my hand than spoon. Abunci ma ya fi dad'i wallahi". Alhaji Usman ya fad'a.
"Please come back and sit. Ba ri na kawo maka bowl ka wanke hannun a ciki". Fad'in Hajiya Na'ima ta re da mik'ewa.
Dawowa ya yi ta re da zama kamar yadda ta buk'ata. Ita kuma ta kawo masa bowl d'in ya wanke hannunsa ta re da yin bismillah ya soma ci.
Ko loma hud'u bai ba, Barrister Fu'ad ya yi sallama a k'ofar parlour. Sai da Anna ta ba shi izinin shigowa ka na ya shigo shi ma ya ja kujera ya zauna ta re da fad'in,
"Dad ina wuni? Ka dawo lafiya?".
"Lafiya k'alau Barrister. Ya aikin?". Fad'in Alhaji Usman.
"Alhamdulillah daddy. Anna ina wuni?". Fu'ad ya fad'a ta re da mai da duban sa ga Anna.
"Lafiya k'alau. Have eating?". Hajiya Na'ima ta amsa ta re da tambayan sa.
Shafa cikin sa ya yi ta re da fad'in,
"I eat nothing since afternoon".
Dariya Alhaji Usman ya yi ta re fad'in,
"You better find a wife before your momma stop giving you her food".
"Ohooooo, you better tell him". Fad'in Anna ta na dariya.
"Hmm! Anna, I don't wanna rush my self. Women, now adays. Hmm sai dai alhamdulillah".
"Son pray, in Allah, Allah will here you and give you a better one". Fad'in Alhaji Usman.
"Ameen". Fad'in Fu'ad ta re da jawo plate ya zuba mashed potato ta re da bismillah ya soma ci.
"Hmm, ana maganar Fu'ad, to ina ki ka bar shugaban gwagwaran Africa? Baban boko. Boko mu ka zo yi duniya. Muna nan da ke, ya na dawo wa, zai kuma cewa wani degree d'in zai sa ke yi a wani fannin daban. Degree biyar fa gare shi". Fad'in Alhaji Usman ya na kai farfesun kishi baki.
"Hmmm, I'm tired of that boy, ina ga auran dole zan mishi. Tun da na ke ban tab'a ji ko a mafarki an ce ga budurwansa ba. Ina ga hatta Zaid da Suhail sai sun riga shi aure. Sai an Kai hotunan sa masallaci ka min ya samu matar aure. Don ma ya ci sa'a bai da jiki da fuskan tsufa ko kad'an. Wasu ma cewa su ke Fu'ad ne yaya".
"Anna na gan ku a rana ke da Yaya bibi. Ke da ki ke backing d'in sa amma yau har da ke ake masa haka". Fad'in Fu'ad.
"Na yi d'in. In dai a kan aure ne, mun dunga kenan. Mutun sai k'ara shekaru ya ke yi, amma ya zauna sai ya ga k'arshan biro. Mongol pack ma dai ya mutu ya bar boko, shi da ya k'irk'iri dictionary".
Daga Alhaji Usman har Fu'ad dariya su ka saka.
"Yauwa Anna, dan wannan y'ar kyakkyawar yarinya ta d'azu, d'iyar wacece?".
"Y'ar aiki ce. Kandala ta ka wo ta d'azu da safe". Fad'in Anna.
Shak'ewa Fu'ad ya yi ta re da jero tarurruka sai da Alhaji Usman ya ba shi ruwa ya sha. Tuni har idanuwan sa sun kad'a sun yi jazur saboda shak'ewar da ya yi.
"Anna, y'ar aiki fa ki ka ce? Wannan y'ar yarinyar kuma wani aiki za a kawo ta yi? Ai kamata ya yi ta na gaban iyayanta ta na karatu. Wai meyasa wasu mutanan dai kamar dabbobi su ke ne? Dan Allah Anna ku dai na k'arban k'ananan yara idan an kawo maku su a matsayin y'an aiki. Wallahi wannan child abuse ne. Idan human right su ka ji wannan, Allah abun kai k'ara kotu ne a nai mo mata hakkin ta a wajan wad'and'a su ke kawo su. Kuma wallahi wasun su mostly iyayan su ba su sani ba". Fad'in Barrister Fu'ad kamar zai yi kuka.
"Hmm, maganar da na ke son in yi da mahaifin ka kenan. Na yanke shawarar yarinyar za ta zauna da ni har ta kammala karatun ta ba bu wani maganar aiki. Domin akwai ciwon jahilci a kwakwalwar yarinyar da ma k'auyan su baki d'aya. Domin da kana nan d'azu ta ke min wasu irin tambayoyi, wallahi sai ka yi kuka. Sam ba su san addini ba, balle akai ga zancan boko. Alhaji idan ka amince min, zan yi magana da baabar ta wacce ta kawo ta aiki, a tambayan min iyayanta idan sun yarda zan rik'e ta har ta samu miji ta yi aure bayan ta yi karatu. Don wallahi yarinyar ta shiga rai na ba kad'an ba". Fad'in Anna ta na kallon Alhaji Usman.
"In dai wannan ne ai ba matsala Na'ima. Haka nake so in ga kuna taimakon mabuk'ata. Allah dai ya sa ka mi ki da alkhairi. Ni kuma idan har iyayanta sun amince, zan biya duk wani abunda za ta yi har tai aure. Ita ma ta zama d'aya daga cikin family na ba y'ar aikin gida na ba". Fad'in Alhaji Usman.
"Allah ya saka da alkhairi ya k'ara bud'i". Fad'in Anna da Fu'ad.
"Ameen". Ya fad'a ta re da goge bakinsa da hannun sa da tissue ka na ya wanke hannun ya wuce bedroom d'in sa.
"Idan ka gama ka tabbatar ka rufe min k'ofa". Fad'in Anna ta re da mik'ewa ta yi hanyar bedroom d'in ta domin ta kimtsa ta je wajan mijin ta.
Bayan mahaifiyar sa na sa ya yi da idanuwa ya na jin wani soyayyarta na k'ara huda zuciyar sa.
"Mummy like no other" Fu'ad ya fad'a ta re da goge hannunsa da tissue ya bud'e goran ruwa ya sha ta re da fita daga parlourn ya kullo k'ofar, haka ma main parlour ka na yai part d'in sa da ke gaban na Suhail.
Sai da ya fara lek'a d'akin Suhail d'in ta window. Duk da ya kashe wuta, amma haske waje da ya haska windown sa, sai da ya sa ya gane shaye-shaye ya ke yi saboda hayak'in da ke fitowa. Girgiza kai ya yi ta re da shigewa side d'in sa ya kullo k'ofa.
Wanka ya yi ta re da gabatar da shafa'i da wuturi, ka na ya hau gado ta re da kunna data ya hau WhatsApp ya d'an yi chatting kad'an saboda baccin da yaji ya soma cika masa idanuwa. Addu'a ya yi tare da kwanciya ya ja bargo.


*WASHA GARI*
Da asubar fari Anna ta je ta ta so su Fanan da Binty ta re da umartar su da su yi wanka ta re da d'aura alwala su gabatar da sallah.
Binty kuwa a tsayin rayuwarta bata tab'a baccin mai dad'i irin wannan da ta yi ba a katifa mai laushi ga sanyin AC har yawo yaso ya mata don sai da ta ja bargo har kanta.
Fanan d'in ce ta soma wanka ta re da d'auro alwala, ka na Binty ita ma ta je ta yi.
Ta re su kai sallar, duk abunda Fanan ta yi, haka Binty ke yin. Sai wannan karan, wus wus wus, ta ke ta fad'i kasancewar ta ji sautin fitar karatun Fanan d'in sai ta yi tunanin haka ake cewa.
Bayan sun idar, Fanan ta d'auko su ka shafa. Ka na Fanan d'in ta d'auko gogaggun uniform d'in ta, ta saka. Skirts d'in ta saka, ka na ta saka vest sannan ta saka rigar sama mai dogon hannu. Ka na ta d'aura suite d'in a sama ta re da b'ame botur. Ba k'aramin kyau kayan su ke ma jikinta ba. Ta je gashinta ta yi ta re parking d'in sa a tsakiya kamar yadda ta saba idan za ta school, ka na ta saka hula ta re da baby hijjab.
"Fanan kin yi kyau a cikin wannan kayan". Binty ta fad'a ta na k'ara kallon kayan jikinta.
"Ke ma kin kusa sa ka su very soon". Fad'in Fanan ta na saka white socks a k'afarta.
"Dan Allah dagaske ni ma zan sa ka? Zan rik'a zuwa makarantar ku?". Fad'in Binty out of exited.
"Sosai ma kuwa. Na yi wa Anna magana kuma ta ce za ta saka ki". Fad'in Fanan d'in ta na saka workbook d'in da ta yi assignment jiya a cikin Jakarta.
"Na ji dad'i sosai. Ni ma zan shiga makaranta in rik'a yaren da ku ke yi da Anna".
"Ke wannan yaran Anna ne ai. Fulatanci ne. Ku ma ke ma idan mu na yi a gaban ki a hankali za ki iya".
"To ku rik'a yi dan Allah, ni ma na koya. Ko kuma idan za mu yi bacci, ki rik'a ko ya min". Fad'in Binty.
"To shikenan, za mu fara daga yau idan na dawo school. Yanzu tashi mu je mu gaida Anna da Daddy". Fad'in Fanan ta re da yin hanyar k'ofa Binty ta mara ma ra baya.
Part d'in daddy da ke sama su ka nufa. Kusan zan iya cewa parlourn sa ya fi duka parlourn da ke part d'in kyau da kuma tsaruwa.
Zaune ya ke akan 1sitter ya na kallon BBC news, hannun shi rik'e d'an karamin cup irin na buzaye, amma na shi na glass ne mai kyau ya na sipping shayin da ya ji kayan k'amshi. A gaban shi a kan centre table flasks ne mai d'auke da shayi a ciki. Sai kwalin sugar cube a gyefe.
Sallama su ka yi ta re da tsayawa a ba su izini tukun. Don k'a'idar Alhaji Usman ne sai ya ba ka izini ka min na shigo masa d'aki.
Amsa sallamar ya yi ta re da ba su izinin shigowa.
Fanan ta kama hannun Binty su ka shiga. Duk'awa Fanan ta yi, Bintyn ma ta duk'a kamar yadda Fanan d'in ta yi a gaban daddy da ke kallon su ya na murmushi.
"Ina kwana dad?".
Binty ma ta kalli daddyn ta re da fad'in abunda Fanan ta ce.
Kallon Bintyn ya yi, domin yana nazartar ta. Domin jiya kusan raba dare su kai shi da Hajiya Na'ima su na magana a kan ta.
"Lafiya k'alau daughters. Har kin yi shirin makaranta Fanan?".
"Eh dad. Da 7:00am ya yi zan wuce. Breakfast kawai zan yi".
"Masha Allah!". Daddy ya fad'a ta re da mai da kallon sa izuwa ga Binty ya ce,
"Binty ya sabon waje? Hope kin ji dad'in zuwan ki gidan nan?".
Kasancewar sauran maganar da Hausa ya yi, shiyasa ta fahimci mai ya ke nufi. Ta ba shi amsa da,
"Eh dard (Dad). Na ji dad'i sosai. Mutanan gidan su na da kirki. Har da ya Fu'ad ba". Fad'in Binty ci ke da farin ciki.
"In sha Allah za mu yi magana da wacce ta kawo ki nan, ta yi wa iyayanki magana KI dawo nan gaba d'aya da zama sai mu saki a makaranta ke ma ki yi karatu kamar yadda kowace yarinya mai gata ta ke yi. Ke ma ki samu wannan gatan. Kin ji".
"Nagode dard (dad)". Fad'in Binty kamar ta taka rawa.
Fanan kuwa sai k'umshe dariyar ta ke yi saboda yadda Binty ke pronouncing dad.
"Ku ta shi ku je ku karya ka da ki yi latti. Seven d'in ta kusa". Fad'in dad ta re da sipping tea d'in shi.

Tashi su kai yi ta re da fita su kai part d'in Anna. Gadon ta su ka taras ta na gyarawa. Don ita sam ba ta yadda y'ar aiki ta gyara mata d'aki ba. Babu y'ar aikin ma da za ta iya cewa ta san kalar d'akin. Da kan ta ta ke gyara d'akin ta. Sai idan weekend ne sai ta saka Fanan d'in ta wanke mata bayi da kuma gyara d'akin. Duk da kuwa kasancewar Hajiya Na'ima d'iyar k'anin Sarkin Gombe. Hakan bai sa ta d'auki d'abi'ar nan na komai baiwa ta yi maka ba. Kuma hakan koyarwa mahaifiyar su ce. Lokacin auran ta ma sai da aka gad'o ta da kuyangu kusan bakwai, amma ta ce ita ba ta so, bautan ubangiji ta zo ba zama a mata hidima ba.

"Anna sannu da aiki. Ba ri na k'arisa gyaran gadon". Fad'in Fanan ta na k'arisawa wajan Annan d'in.
"No bar shi ai na gama". Anna ta fad'a ta na shimfid'a bargo a gyefan gado.
"Ina kwana Anna?". Fanan ta fad'a.
Ka min Anna ta amsa, Binty ma ta ce,
"Anna ina kwana?".
"Lafiya k'alau yara na. Kun dai yi sallah ko?".
"Tun da ki ka tashe mu ai ba mu ko ma ba. Mun yi sallah. Kuma yau ta re mu ka yi. Duk abunda na yi, shi ta yi ita ma. Yau ba daga sujada ta fara sallah ba".
"Alhamdulillah! Ki yi ko ya mata, za ta iya a hankali. Yanzu mu je ku yi breakfast ki wuce makaranta, kar ki yi latti".
"To Anna". Fad'in Fanan.
"Anna dan Allah wanene kwana da yinin da kullum safe da rana sai in ji mutane da yawa su na nai man shi?". Fad'in Binty ta na kallon Anna.
"Ban ga ne ba Binty, a ina ki ka ji a na nai man na su?". Fad'in Anna ta na kallon Bintyn.
"To Anna d'azu munje wajan dard mun ce masa ina kwana. Yanzu ma mun zo mun ce miki. Kuma duk lafiya ku ke cewa. To shi kwanan ya na ina? Ba'a ganin shi sai dai ai ta nai man shi".
Dariya ce ta kufcewa Anna da Fanan suka kuwa da ra sosai. Anna ta ce,
"Rai dai Binty. In sha Allah idan Allah ya ara

Download complete TXT · Novel page