BA NI DA GATA

Chapter 14 of 45

hud'u duk su na aikatau. Mazan ne k'anana ke gaba na su ma kuma duk na saka su sana'a. Ita ma Binty ganin ta kawo girma ne, nan da shekaru biyu za ki ha manema sun fito. Shiyasa na turo ta nan domin ta yi aiki mu samu mu tattala kud'in ai mata kayan d'aki da su. Wayyo Binty marainiyar Allah". Kandala ta k'arisa maganar ta re da rushewa da kuka.
Sosai Hajiya Na'ima ta ji tausayi ya ka ma ta. Yanzu
"Kenan yanzu wannan yarinya ba dan Allah ya turo ta nan ba, da yanzu nan da wasu shekaru biyu masu zuwa aure za'a mata kenan da duhun jahilci a kan ta. Gaskiya dole ma yarinyar nan ta dawo waje na". Fad'in Anna cikin zuciyar ta, a zahiri kuma ce wa ta yi,
"Allah sarki! Allah ya jik'an mahaifan ta da kuma mijin ki. Allah ya k'ara maku hak'urin rashi. Amma tabbas ku abin tausayi ne. Idan har za ki amince min, ina son Binty ta kasance a waje na. Sannan saboda marayun da ke gaban ki, na k'ara miki hamsin akan kud'in da zan ba ki duk wata sun zama dubu d'ari sai ki kula da sauran marayun da ke gaban ki, ki kuma sa ka su a makarantar islamiya da na boko. Don zama da jahilci bai yi ba".
"Wallahi Hajiya in dai Binty ce na bar miki ita halak, malak. Wallahi na ba ki. Ai nasan gidan mutunci na kawo ta. Hajiya nagode, nagode Allah ya sa ka miki da alkhairi ya k'ara girma".
"Ba bu komai Kandala, ai yi wa kai ne. Sannan duk wani abu da ki ke buk'ata ki min magana ka da ki ji kunya. Yanzu idan za ki tafi, zan had'a ki da kayan abinci, sai driver ya kai ki. Bintyn bacci ta ke yi, shiyasa ba ta zo kun gaisa ba".
"Ai babu komai Hajiya, idan na sa ke zuwa ma gaisa ai". Fad'in Kandala cike da farin cikin riba biyu da ta sa mu.

Kamar yarda Hajiya ta ma ta alk'awari, da za ta tafi ta had'a ta da babban buhun shinkafa foreign buhu hud'u, buhun semo guda hud'u, couscous katon biyu, taliya da macaroni katan uku-uku. Baban gwangwanin madara guda hudu, suger loka ashirin, mangyad'a rabin abod, manja ma haka. Sai maggi star katon biyu ta re da k'arin dubu d'ari. Haka aka loda mata a mota.
Sosai Kandala ta b'arke da kuka harda fyace-fyacen majina. Ba kukan komai ta ke yi ba face na dad'i. Ta tabbatar wa kanta Binty sa'ar da alkhairin ta ce.
"Dan Allah ki bar kukan nan Kandala. Duk wani abunda ki ke buk'ata ki ma ni magana". Fad'in Anna.
"Nagode sosai Hajiya. Allah k'ara girma". Fad'in Kandala ta re da shiga mota driver ya ja ta re da kai ta har k'ofar gidan Datu aminiyarta.
Ganin irin uban kayan abincin da ake ta shigowa da shi ne ya sa Datu fitowa k'ofar gidan don ganin waye zai bud'e shago sai idanuwan ta ya sauka akan Kandala ta na baiwa yaran da ke shigar mata da kaya umarni.
Ai k'arisa fitowa Datu aka cigaba da shigar da kaya ta re da ita. Sai bayan sun shigar da komai d'akin Datun ka na Datun ta kalli Kandala ta re da fad'in,
"K'awas ya na gan ki da sha tara haka?".
"K'awa ai ni kaka ta ta yanke sak'a wallahi". Tu ni Kandala ta zayyane wa Datu duk yadda su kai da Hajiya Na'ima da kuma irin k'aryar da ta shatata wa Hajiyan. Sai dai ba ta fad'a ma ta ainahin yawan kud'in da Hajiya Na'ima ta ce za ta rik'a ba ta duk wata ba.
"Kin ga abunda na ke fad'a miki ko? Da kin ma kan kin salalar tsiya wallahi. Ah gaskiya Kande kin shigo Habuja da k'afar da ma. Yanzun ya za ki yi da wad'annan uban kayan abincin?". Fad'in Datu.
"Sayar da su zan yi, amma zan aje mana wanda za mu rik'a ci ai". Fad'in Kandala.
"To ni kuma miye nawa kason a cikin dubu arba'in d'in da za ki rik'a karb'a duk wata?". Datu ta fad'a.
"Zan rik'a ba ki dubu goma duk wata. Sannan zan rik'a ajiye dubu biyar duk wata na haya. Daga yanzu na d'auke miki biyan kud'in haya". Kandala ta fad'a.
"Kai shiyasa na ke k'aunar ki k'awata. Hanzarta maza in raka ki ki sai do da kayan, kin san na fi ki sanin kan kasuwa. Kin san ni ai". Fad'in Datu.
"Aiko dai bari in ta shi". Kandala ta fad'a.



..........Bayan Alhaji Usman ya dawo da daddare, Hajiya Na'ima ta shaida masa duk yadda su ka yi da Kandala. Shi kan shi sai da ya tausaya masu, kuma ya umarci Hajiya Na'ima akan duk wata idan ta zo karb'an kud'i, to a had'a mata har da kayan abinci ma'ishi.
Sosai hakan ya yi wa Hajiya Na'ima dad'i.

Tun daga wannan ranar Anna ta d'auki d'ammarar kula da Binty. Da kan ta ta ke koya ma ta wasu abubuwa na addini. Idan malam ya d'aura mata karatu, kullum Anna sai ta tsare ta ta yi ma ta karatun da malam d'in ya masu.
Gyefe guda kuma, kullum da daddare dai sun yi bitan yaran fulatanci ita da Fanan. Kuma da ya ke Allah ya mata kwakwalwa, nan da nan ta ke d'auke abun.
Gaba d'aya satin ta d'aya da zuwa, amma ta haddace suratul fatiha kuma babu kuskure. Ga ta da zak'in murya.
Anna kuwa ko k'ofar parlour ba ta ba ri ta je balle ta fita waje Suhaila ko mahaifiyar sa su gan ta.
Maganar boko kuwa, Anna ta ce sai first term, shekara mai zuwa kenan. Don so ta ke ta d'auko lesson teachern da zai koya mata karatu kwakwalwar ta ya bud'e tukun.
Fanan ba ta ji dad'in haka ba, amma haka nan ta hak'ura.
Anna ba'a nan ta tsaya ba, kasancewar gwana ce wajan girki, duk lokacin da za ta had'awa Alhaji Usman girki, da Binty ta ke zuwa ta yi ko mai a gabanta duk da dai ba ta tab'a ba ta wani abun ta yi ba. Don ranar da ta fara shiga kitchen da ita ta kunna gas. Binty rud'ewa ta yi ta re da fasa ihuu ta fita daga kitchen d'in da gudun. Ba k'aramin tsoro gas d'in ya ba ta ba. Da kyar ta yadda ta soma tsayawa a gaban gas d'in amma ta na d'ari-d'ari.
Kasancewar ta na da tambaya, duk abunda ta ga Anna ta yi sai ta yi tambaya a kai, hakan ya sa ta ke sanin wasu abubuwa sosai ga me da girki. Don ko ruwa Anna ta k'ara a girki ko ta saka ingredients sai Binty ta tambaye ta miye dalili. Anna kuwa ba ta gajiya da ba ta amsa.
Tuni har Anna ta samo mata lesson teacher mai su na Mashkur.
Daga k'arfe 10-12 su ke karatun boko. Na islamiya kuwa k'arfe uku don sai Fanan ta dawo daga school saboda ta re ake ma su karatun kuma ana parlourn k'asa.
Tuni Binty ta sa ki jikin ta kamar dama y'ar gidan ce.
Fasila kuwa duk duniya ji ta ke babu wacce ta tsana kamar Bintyn. Don gani ta ke ita da ta d'au shekaru a gidan ba'a mata irin wannan gatan ba sai ita da ta zo jiya-jiya. Wannan dalilin ne ya sa ta ke jin haushin ta.


..........Zaune su ke a parlourn k'asa akan center carpet, Fanan na koya mata letter sound. Kasancewar tu ni ta iya ABCD har zuwa Z, yanzu letter sound ake koya mata. Sun kai letter p, sai dai Bintyn ba ta bambamce P sound da F sound. Fanan ta ce
"Look Binty, kalli bakina, ki kalli yadda zan yi da ba ki ne. Shi F sound haka za ki yi ffffff kamar ki na hura abinci idan akwai zafi. Yanzu ki yi imaging, ina nufin ki d'auka kamar abinci ne a hannun ki, kuma akwai zafi, to hura abinci mu gani". Fad'in Fanan ta na kallon bakin Bintyn.
Binty ta yi kamar yadda ta ce ta re da fitar da sautin,
"Ffffffffff!". Ta na kallon Fanan d'in ko ta yi dai-dai.
"Great! Haka ake fitar da sound d'in F. Kamar idan za ki ce flower, wanna sound d'in za ki sa a farko ba na P ba. Fffflower. Kin ga ne?". Fanan ta fad'a ta re da jann harafin F d'in
"Fflower. Hakane ko?". Binty ta fad'a.
"Yauwa Binty na. Haka ne. Sai kuma P sound. Shi kuma kamar za ki hure candle haka za ki yi, 'puff' haka. Kin ga ne. Ba ri na ba ki misali da pencil. Pa fencil ake cewa ba, pp pencil. Yan zu kin ga ne bambamcin?".
"Eh nagane Fanan. P, pencil, sai Ffff flower". Fad'in Binty.
Rungumeta Fanan ta yi ta re da fad'in,
"Wallahi za ki yi k'ok'ari sosai. Ki na da saurin fahimta".
Anna da ke zaune can gyefan su ta na jin su, kuma ita ma ta lura Binty na da saurin fahimta, tun da ko wajan girki yanzu ta na barin ta ta dafa indomie da kuma white rice, duk da ta na gyefe ta na kallon ta saboda sharrin gas. Kuma alhamdulillah ta iya. Tun ta na shinkafar ta na cab'ewa, har ta iya sosai. Ta ma fi Fanan shiga kitchen saboda ita ta na gida ba makaranta ta ke zuwa ba, shiyasa su ke samun ishashshan lokacin da Anna.
Barrister Fu'ad ne ya yi sallama ta re da knocking, Fanan ce ta bud'e ta je ta bud'e masa k'ofa. Ta na ganin sa ta rungume sa. Ita ma Binty ta ta so da gudu ta je ta masa oyoyo........





















*SORRY IDAN KIN GA TYPING ERROR, MATSALAR KEYBOARD NE KUMA BA NA EDITING*🙏🏻



*PAID BOOK 08128755583*

🌹 *27-28*🌹

Rungume su ya yi su duka ta re da manna ma su kiss a goshi. Ka na ya rik'o hannunsu ta re da k'arasowa wajan da Anna ta ke ya ce,
"Anna ina wuni?". Ya fad'a ya na zama a k'asa.
"Lafiya k'alau. Yau ba aiki ina ka je?". Anna ta fad'a.
"Wallahi na je wajan Muhammad. Ya na ta min tsiya wai ban tab'a zuwa gidan sa ba. Kin san fa ba dani aka kai sa ba. To shine na je yau". Fad'in Fu'ad.
"Ma sha Allah, to ya ka baro su?". Anna ta san ke tambaya.
"Duk su na lafiya". Fu'ad ya fad'a ta re da kwanciya akan center carpet.
"Ya barrister alk'awari na fa?". Fad'in Fanan ta na kallon Fu'ad cike da shagwab'a.
"Kin fa ra ko? Alk'awarin mai na miki kuma?". Fu'ad ya fad'a ta re da k'ara gyara kwanciyar sa.
"Yaya ba kai ka ce za ka kai ni shopping during weekend ba. Kuma yau Saturday". Fad'in Fanan.
"Aikuwa ya Fu'ad haka ka ce ina wajan. Ni ma kuma ka ce idan har na iya nasi babu kuskure za ka siya min irin rigunan Fanan da cak'ulet". Fad'in Binty.
"Ke dallah chocolate ake ce wa ba cak'ukate ba. Kar ki fara ba ni haushi mana". Fad'in Fanan ta na hararar ta.
"Eh to shi, haka ka ce wallahi". Binty ta fad'a.
"Ohhh Allah! Wai mi ya sa ba ku da mantuwa ne? To yanzu ya kuke so a yi?".
"Ai kawai ka tashi mu tafi yanzu". Fad'in Fanan.
"To uwar san yawo, to ba bu inda za ku". Anna ta fad'a.
"Anna dan girman Allah ki yi hak'uri. Ya Fu'ad ka sa ka ba ki". Fanan ta fad'a ta na rik'o hannun Fu'ad d'in kamar za ta yi kuka.
Shi kuwa Barrister Fu'ad har wani k'ara kwanciya ya yi ta re da lumshe idanu don da ma ba son fitar ya ke yi ba.
Muryanta ya ji dai-dai cikin kunnan sa ta na fad'in,
"Ya... Bar...rister, please ka sa ba ki".
A hankali ya bud'e idanunsa ta re da saukewa a cikin na ta da ita ma ta zuba masa fararar idanuwan ta da su ke kamar zaiba a marairaice.
"Har da ke Binty? Ba kya so Yayan ki ya huta ko?". Fu'ad ya fad'a shima a shagwab'e.
"Yaya dan Allah". Fanan ta sa ke fad'i.
Kamar had'in baki a ta re su ka kama hannun shi su na jijjigawa su na fad'in,
"Yaya dan Allah, yaya dan Allah, yaya dan Allah". Sai su ka mai da abun kamar wak'a.
Kallon Anna ya yi ta re sa fad'in,
"Anna please ki yi hak'uri mu je, idan ba haka ba wad'annan yaran ba za su bar ni na huta ba, a can k'orafin mutane su ishe ni, anan kuma na su ya ishe ni".
Kallon shi Anna ta yi ta re da fad'in,
"Sai kun dawo, amma ka da Ku dad'e. Sannan ka tabbatar ka dawo min da su har cikin d'akin nan".
"In sha Allah Anna. Sai Ku ta shi Ku je ku shirya mu ta fi". Ya k'arisa maganar ta re da mai da duban sa izuwa ga Binty da Fanan.
Cike da farin ciki su ka kwasa zuwa sama. Dama sun yi wanka. Fanan ta yi wa Binty kwalliya ita ma ta yi wa kan ta. Ba k'aramin kyau su ka yi ba, musamman ma Binty da ke sanye da doguwar riga english wears kalar purple da tatsin fari. Sai ta ba ta farin takalmi mai d'an tudu ta re da farin baby hijjab bayan ta nad'e mata gashin ta a tsakiyar kan ta. Ita kuwa pink riga da wando ta saka. Sun yi kyau sosai.
A ta re su ka sauko. Gaba d'aya idanun Fu'ad ya koma kan Binty ya na yaba irin kyawun da Allah ya yi mata.
"Anna sai mun dawo". Fad'in su Binty ya yin da su ka nufi k'ofa.
"To iyayanta zumud'i Ku dawo nan. Shi ko mik'ewa bai yi ba, amma kun saka kai za Ku fita. In ga wata ta saka k'afa a waje in karya k'afar". Fad'in Anna ta re da mai da duban ta izuwa ga Fu'ad ta ce,
"Yarda za ku fita tare, haka na ke so ku dawo cikin d'akin nan ta re. Ka ji ni ko".
"Yes Anna". Fad'in Fu'ad ta re da mik'ewa y kama hannun Fanan da Bintyn su ka fito.

Kicibis su ka yi da Suhail as usual sanye da 3quarter da arm less, wuyan shi kuma wata shegiyar sark'a ce har ciki kamar kare. Ga uban gashin nan da ya tara tsaf mace za ta kitse shi. Shi kan shi 3quartern an zazzago shi k'asan d'uwawu sai wa ni tafiya ya ke yi yan bouncing.
Cak ya tsaya ya na k'arewa Binty kallo. Binty kuwa ta na had'a idanuwa da shi ta koma bayan Fu'ad ta ri'ke masa rigar sa jikinta har ya soma rawa.
Zagayo da ita gaban shi ya yi ta re da fad'in,
"Kwantar da hankalin ki, ina wajan ai. Babu abunda ya isa ya miki".

"Sai dai idan ban yi niyya ba". Fad'in Suhail ciki-ciki yadda Fu'ad d'in ba zai ji ba.

"Gidan uban wa za ka je kamar d'an arna?". Fu'ad ya fad'a a fusace.
"Ahhhh, ni fa ba mace ba qur'an ba bu wanda ya isa ya takuran. Ai ba gadi na aka baiwa mutum ba. Kowa ya yi rayuwar sa. Ba ruwan ka da ni". Suhail ya fad'a cike da gungunai.
"Uban mai ka ke cewa dan uban ka?". Fad'in Fu'ad ya na zazzaro masa idanuwa.
Shafa k'eyarsa ya yi ta re da juya idanuwan sa gyefe.
"Idan ka ce kai d'an iska ne, to in dawo gidan nan ban sa me ka ba. Ni kuma sai na nuna maka d'an guguwa ne ni. Dan iska kawai". Fu'ad ya fad'a ta re kama hannun Fanan da duk ita ma a firgice ta ke su kai parking load.

Dai-dai lokacin motar Mansura mahaifiyar Suhail ta danno kai, k'awarta na gyefan ta. A parking space d'in su ka yi parking.
K'awar ta ta ce ta soma fitowa, idanuwan su ka sauka akan na Binty da ke yi wa Fanan magana ta na dariya. Kyawun ta ya bayyana sosai, ga lob'awar da kumatun ta da su ka yi duka biyun. Ga shi ta wani d'age girar ta d'aya.
"Ya subhanallah! Inna lillahi. Zan mutu yau ni Zuwairah! Wannan kyakkyawar yarinyar fa?" Fad'in k'awar Hajiya Mansura ta na k'ara k'arewa Binty kallo.
Hajiya Mansura ce ta fito daga motar ta na kallon inda Mansuran ta ke kallo. Cikin second 1 ta yi kicin-kicin da ranta ta re da watsawa Hajiya Zuwairah harara wacce ba ta ma San ta na yi ba, domin tuni ta mai da duban ta ga Binty da har ta shige mota.
Shi ma kuma Fu'ad dakatawa ya yi daga shiga mortar kasancewar ya ga Hajiya Mansuran da k'awarta. K'arasawa ya yi inda su ke ta re da fad'in,
"Sannu da zuwa Hajiya, ina wunin ku".
Yak'e Hajiya Mansura ta yi ta re da fad'in,
"Lafiya k'alau the great Barrister. Ya fama da jama'a?".
Murmushi ya yi ta re da fad'in,
"Alhamdulillah Hajiya". Fu'ad ya fad'a ta re da satar kallon k'awar Hajiya Mansurar da ko kallon shi ba ta yi ba saboda Binty da ta tafi da imanin ta.
Juyawa Fu'ad ya yi ta re da komawa wajan mota ya bud'e ya shiga ta re da reverse ya bar wajan.

Ajiyar zuciya Hajiya Zuwairah ta sauke ta re da fad'in,
"Mansura ina kuka samu kyakkyawar yarinya haka? Wallahi ta yi min. Ki shigo da ita harka mana. Wallahi zan biya ko nawa ne. Kuma zan iya sacrificing komai a kan ta wallahi. Kallon ta kawai da na yi, dai da zuciya ta ta buga da k'arfi. Wani irin mugun sha'awar ta na ke ji wallahi".
Wani harara Hajiya Mansuran ta jefe ta da shi ka na ta ce,
"Wallahi, kin san ko no wacece. Kin san abunda zan iya yi akan duk abunda na ke so. Saboda haka, ki fita harkan wancan yarinyar domin ta wa ce. Ina nan ina babban shiri a kan ta, don auran ta ma zan yi. Zan kula da ita, zan ba ta rayuwar da ba ta tab'a tunanin

Download complete TXT · Novel page