Showing 3001 words to 6000 words out of 162658 words

Chapter 2 - BA NI DA GATA COMPLETE HAUSA NOVEL

29 Jan 2025

42910

"Dan iyayan ki mata ba na hanaki zuwa wajan nan ba. Shegiya yarinyar kawai mai d'an banzan nacin tsiya. Ni anya ma yarinyar nan ba aljana ba ce? Shegiyar yarinya tun ta na da shekara uku ta ke rayuwa ita kad'ai a saman bola kuma ta rayu har izuwa yanzu. Ni wallahi tsoro ma ta ke ba ni yarinyar. Sai shegen kyau kamar ita tai kanta".
"Kai kuwa d'an Liti ai Allah shi ke rayawa kuma shi ke kashewa. Ba abun mamaki ba ne dan ta rayu ita kad'ai a saman bola. Kai dai idan zaka taimaketa ka ba ta buredi da shayi ka ba ta, ba ka tsaya kana wani surutan banza a wajan ba". Fa'din wani mutum da ke cin taliyar 'yan yara (Indomie).
"To bazan ba da ba. Idan kuma kai ka basheni jalin, sai ka d'iba ka bata". Fa'din D'an Liti.
"Yo to ai abunda za ka ce kenan. Ke yarinya zo ungo wannan sauran taliyar ki cinye duk da dai kad'an ya rage". Fa'din mutumin nan.
"Idan wanga d'iya ta ci taliyar nan a cikin robata Allah gwada maka yai. Sai dai ka juye mata a cikin leda". Fa'din d'an Liti.
"Haka ka ce d'an Liti?". Fa'din bawan Allah nan.
"Awo wallah". D'an Liti ya fa'da ya na buga cinya irin na y'an daudu.
Girgiza kai bawan Allah ya yi tare da d'aukar ledar da aka b'are indomie ya juye mata a ciki tare da mik'a mata. Da uban sauri Binty ta karb'i ledan. Nan wajan a tsaye tai loma biyu ta cinye tass tare da zubawa wannan bawan Allah idanu alamar nai man k'ari. Da gudu 'dan Liti ya biyo ta tare da fa'din,
"Bar nan ko in halako ki walleh".
Gudu ta yi sosai, duk da D'an Liti ya dai na bin ta ba ta zai na gudu ba. Sai da ta ga ta yi nisa sosai sannan ta tsaya ta na mai da numfashi.
Haka tai ta gararanba a cikin anguwanni. Duk in da ta je kyamatar ta ake yi. Musamman wajan ma su sai da abinci. Idan Allah ya ba ta sa'a wani ya ci ya rage tai wuf da shi ta cinye. Idan kuma aka kamata ta sha kirb'a. Haka tai ta yawo ga rana kuma ba takalmi da d'ankwali a kan ta. Hatta kayan da ke jikin ta ma ba na kirki ba ne. Sai da rana ta fa'di ka na Binty ta dawo wajan bolan nan ta zauna ta na sauke numfashi. Bakin ta duk ya bushe. Sosai ta ke jin k'ishirwan ruwa. Kallon himilin bolan nan ta yi tare da fad'in,
"Mama yau ban samu abinci sosai ba. Yunwa na ke ji. Ina jin k'ishi sosai".
Daga bayan ta taji an saka hannu an rufe mata idanu. Wani farin ciki ne ya lullub'e ta tare da fad'in,
"Hadaan, kai ne ko? Nasan kai ne. Ai kai kad'ai ne kawai ke zuwa waje na".
Zagayowa yai ta tare da fad'in,
"Yau ma kin je yawo ko? Ai tun d'azu na ke ta nai man ki, na kawo miki abinci ki ci ban gan ki ba na bawa kare ya cinye".
Kwal-kwal ta yi da idanu tare da fad'in,
"Hadaan yunwa na ke ji, dan Allah ka ba ni abinci, yau na yi bara ban sa mu ba. Ina jin k'ishi sosai zan mutu".
Sosai tausayin ta ya kamashi, ji ya ke dama zai iya convincing mummy ta yadda Beauty ta dawo gidan su da zama. Amma ya san ko mutuwa zai yi hakan ba zai faru ba.
Juyawa ya yi tare da d'auko wani d'an basket da ya zo da shi sai ya boye a bayan wani bulo tare da ajewa a tsakiyar ta. Cikin sauri ta soma kiciniyar bu'de abunda ke cikin basket 'din. Rik'e hannun ta ya yi tare da girgiza kan sa ya na fad'in,
"You've already know the rules. Wash your hands before eating".
A cikin maganganun sa, kalmar wash kawai ta rik'e, shiyasa da ya yi dogon turancin sa idan ta ji the word `wash` ta san mai ya ke nufi. Wato ta wanke hannun ta. Mi'ka masa hannuwan ta yi alamar ya zuba mata abunda ya saba zuba matan idan zata wanke hannunta. Zazzaga mata detergent ya yi tare da ruwa sannan ta soma mitstsike hannun. Sai da ta wanke sau goma. Har ta k'osa ka na ya fiddo plate tare da bu'de kula ya zuba mata lafiyayyan fried rice da ya ji kayan lambu ga mi da hanta. Aikuwa ko kallon cokalin da ya ke mik'a mata ba tai ba ta zunduma hannu ta soma ci. Kasancewar shi ko da cokali za ta ci abinci ba ruwan shi sai ta wanke hannun ta. Cikin abunda bai fi mintuna uku ba har ta lamushe ta na kuma buk'atar k'ari. Sauran na cikin kulan ya juye mata tare da cinyar kaza da baya. Aikuwa ta cinye tas har da tauna k'ashi murus ta kuma d'ad'd'ake goran ruwan faro ta saki gyatsa tare da jingina da bangon kangon ta na mayar da numfashi.
Shikuwa Hamdam tun ya na jin mamakin irin cin abincin da Binty ke yi har ya dai na. Don shi ko kashe shi za'ayi ba zai iya cin ko kwata ba.
Wani wawan mari yaji an sauke masa a kan fuskan sa wanda k'arar marin ya saka Binty firgita daga baccin da ya soma d'aukar ta. Don ita haka take da cikin ta ya d'auka za ta soma gyangyad'i.
"D'an uban baban ka ba na hanaka zuwa wajan nan ba? D'an iskan yaro ya na so ya jawo mana fitina. Wani d'an iskan ne ka ga ya na zuwa inda ta ke idan ba kai ba. To yau sai na ci uban ka, kuma wallahi dole ba bi su kulsum ku wuce Abuja. Bazan iya da iskancin ka ba. Ke kuma idan ma wani abun ki ka wa d'ana aniyar ki ta bi ki, ba bu abunda zan miki balle anjima da daddare a turo min bak'ak'en aljanu su ga baya na. D'ana kuma daga yau ba za ki k'ara ganin sa ba. Shegiya". Hajiya Saratu mahaifiyar Hamdan ke fad'in haka tare da jan hannunsa, 'dayan hannun ta kuma na kan hancin ta. Uncle Sauban da ke can gyefe tsaye sai aikawa Binty da harara ya ke yi. Shi kuwa Hamdan sai ihu ya ke ya na fad'in shi bazai koma abuja ba. Daga nan wajan bolan mota aka jefa Hamdan 'din, dama already an saka kayan sa cikin mota. Binty fitowa tai da gudu ta na kallon abunda ke faruwa ta na kuka. Ta na hango Hamdan daga cikin mota ya na dukan glass ya na kallon ta ya na hawaye. Da gudu ta shiga bin motar ta na kuka ta na 'daga masa hannu, shi ma kuma ya na kallonta ta glass 'din baya yana mata waving. Ba ta dai na bin motar da gudu ba sai da motar ya b'ace mata da gani. Haka ta dawo cikin kangon bolan nan ta na kuka sosai.


*ᗩᗷᑌᒍᗩ*

Wata kyakkyawar yarinya ce da ba za ta wuce ten years ba, sanye da wando pencil sai wata riga mai matu'kar kyau iya guiwarta. Gashinta tai parking d'in shi a tsakiyar kan ta wanda ya kasance jajaja, maroon-maroon. Kyakkyawa ce sosai kuma fara ce. Fuskan nan na ta ya ci make-up kamar wata babbar budurwa. Hannun ta kuwa tasha zanan lalli. Kallon wata kyakkyar mace ta yi da ke zaune akan 1sitter ta na yanke farcenta. Kallon ta yi ta re da fa'din,
"First love ya ki na ganin?".
Wacce ta kira da first love 'din ko kallon ta ba ta yi ba, a yadda kanta ke k'asa ta ce,
"Looking good!".
Sautin kuka yarinyar ta ji ya kara'de d'akin. Cikin sauri matar ta d'ago ta kalle ta tare da fad'in,
"Sabrin mai ya same ki?".
Sosai Sabrin ke kuka tare da fad'in,
"Mom ko kallo na fa ba ki yi ba balle ki ce na yi kyau kuma na fi kowacce mace kyau a duniyar nan. Sai cewa kawai ki ka yi Wai looking good".
Baki bu'de Hajiya Sakna ke kallon autar tata tare da fad'in,
"Me ke damun ki ne Sabrin? Ta yaya zan miki k'arya in ce kin fi kowace mace kyau a duniya. Ke ma kin san k'arya ki ke yi. Ki na da kyau Sabrin sosai, amma ba ki fi kowa kyau ba. Akwai wanda su ka fiki sosai".
"No way! Everyone in school said that I'm the Queen of the country. We have wealth, Education, beauty and rest. And I am also the Queen of our school. Duk makarantar mu ba bu Wanda ya kai ni kyau, duk ajin mu na fi kowa k'ok'ari. Daddy na ya fi daddyn kowa kud'i a makarantar. Ba na son kowa ya fi ni, ina so in ga na iya komai ta yadda babu kamar ni in the whole world".
"Sabrin, whole word?". Mom ta fa'da cike da tashin hankali da mamaki. Domin kuwa sosai halin Sabrin ke ba ta tsoro. Ta na da wani irn kishi da ya wuce misali. Ita burinta ta kasance ta fi kowa, babu Wanda zai fita. Idan kuwa ko cikin k'awayanta ta ga wa ta ta fi ta da wani abu, to fa zaman lafiya da kwanciyar hankali ya k'are har sai ta fi wannan da ta fita za ta sa mu natsuwa. Sosai Sabrin ke da mugun hali. Hatta mom d'in ta kishi ta ke da ita. Ko wani abu daddyn ta ya siyawa mom in dai ya fi abubda aka sai mata to babu zaman lafiya sai ita ma an sayo mata. Kuma daddyn ta ya d'aure mata gindi wanda hakan na matu'kar k'ona ran mom don ta tabbata idan Sabrin ta ta shi da wannan halin zata sha wuya a rayuwa don gidan wani zata.
"Of course mom. Babu wanda zai fi ni a cikin duniyar na. Ko mai nawa ne ni kad'ai. Nagode miki da kika haife ni mai kyau.".
Mom ta kasa cewa komai, don har ga Allah sosai lamarin Sabrin ke ba ta tsoro.
Juyawa Sabrin 'din ta yi tare da fad'in bari na je side d'in aunty, nasan ita za ta min maganar da zan ji da'di. Ta fi ki sona". Ta na gama fad'in haka tai side 'din kishiyar mahaifiyar ta da ke k'ara dulmiyar da ita.

*ASSALAMU ALAIKUM READERS, GA NI NA ZO MA KU DA SABON LITTAFI NA MAI SUNA A SAMA, WANDA YA ZO DA ZAFI-ZAFIN SA, KUMA NA TABBATA ZA KU JI DAD'IN SA. BA ZAN CI KA KU DA SURUTU BA, KAWAI KU BI NI A FREE PAGES, KU DA KAN KU ZA KU GA NE BOOK D'IN NA DABAN NE. KAWAI KU NU NA MIN ONE LOVE WAJAN SIYAN BOOK D'IN AKAN FARASHI AKAN FARASHI MAI RAHUSA KAMAR HAKA:*




*Normal group shine mutum zai bi ya 500 idan ka ti ne, idan kuma ta account ne 300.*

*VIP kuma 1000 ne idan kati ne. Idan kuma ta account ne 700.*

*MUTANAN NIGER KUMA ZA SU BI YA KAMAR HAKA*:


*Normal group shine mutum zai bi ya 500F idan ka ti ne, idan kuma ta account ne 300F.*

*VIP kuma 1000F ne idan kati ne. Idan kuma ta account ne 700F.*
*ʜᴀʙɪʙᴀᴛɪᴇꜱ ᴅᴀɴ ɢɪʀᴍᴀɴ ᴀʟʟᴀʜ ᴋᴜ ɴᴜ ɴᴀ ᴍɪɴ ʟᴏᴠᴇ ᴡᴀᴊᴀɴ ꜱʜᴀʀɪɴɢ*
🌼 🌹 🌹 🌼
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹 *BA NI DA GATA*🌹
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌼. 🌼
🌹
🌹 🌹
🌹 🌹


*ᴘᴀɪᴅ ʙᴏᴏᴋ*

*NARRATED & WRITTEN BY*
*ZULFA'U SA'EED IBRAHIM*
( *_MATAR SAYYADEE_*)


☀️ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION*☀️💪
( *Home of quality and trusted writer's of the nation*)💪🏻


*DEDICATED TO THE MOST BEAUTIFUL WOMAN IN THE WHOLE WORLD (MY MOTHER). ALLAH YA JIK'AN KI DA ℝ𝔸ℍ𝔸𝕄𝔸*



*________________*
*FREE PAGE 5&6*
*________________*

.............."Ohhh my gosh! Queen kin ganki kuwa? Looking more and more beautiful dear. Wa ne Barbie. Ai ko ita ta gan ki sai 'kishi ya kama ta. Daughter zan fa ci kud'i a nan. Gaskiya wanda za ki aura sai ya kasance classic guy ne. Irin kyakkyawan nan, mai kud'i na nunawa sa'a. Amma fa duk kyan shi ba zai kai ki had'uwa ba domin daga ke aka rufe babin kyawawan mata". Fa'din aunty Junaina, kishiya a wajan mahaifiyar Sabrin. Da ita da Alhaji Saifullahi su ne musabbabin k'ara tab'arb'arewar Sabrin d'in. Domin duk abunda ta yi nuna mata suke ta na kan gaskiya. Rungumeta Sabrin ta yi tare da fad'in,
"Ohh sweet aunty. That why I love you soon much. Dan Allah aunty kullum ki ri'ka fad'amin irin wannan maganar. Allah ji na ke kai na na k'ara girma".
"Do you know what dear? I'm not saying all this to impress you, I'm saying the fact. You're soo adorable my Queen".
Wani irin duk'awa Sabrin ta yi tare da kamo hannun aunty Junainan irin yadda akewa princess ko Queen idan ana son rawa da su. Ta ce,
"I love you soo much my aunty. Me kike so in yi miki?".
"Abu d'aya kawai na ke so ki yi min. Kawai ki yi ta kyau ki na k'ara kyau a cikin kyau". Fad'in aunty Junaina.
"Ohhh ba ki da wannan matsalar. Yau na ji gidan shuru, ina sauran y'an matan gidan su ke?".
Sosai dariya ya kusa kufcewa aunty Junainan. Wai y'an mata. Duk sa'o'in ta ne y'an shekaru goma. Aunty Junaina na da 'yan mata guda biyu Wanda su ka kasance 'yan biyu kuma lokaci guda aka haife su da Sabrin, sai dai ta girme su da sati biyu. Wannan dalilin ne ya sa ta ke d'aga masu kai. A cewar ta, ta fisu kyau da komai ma. Kamar yadda ta ke auta, suma autan ne a wajan aunty Junaina.
"Sun je wanke kai kin san gobe Monday". Fa'din aunty Junaina.
Ta'be ba ki ta yi tare da fa'din,
"Ni ba ko wa ni beauty saloon na ke zuwa ba. Sai after zuhur prayer zan sa driver ya kai ni. Don ba ni son rana". Yadda Sabrin ta ke wasu manyancan, wallahi za ka d'auka wata k'atuwar budurwa ce.



*BINTY*
Gaba 'daya duniyar ji ta ke tai mata zafi. Ko kyankyaso ta ga ni ya wuce, sai ta ce dama Allah ya mai da ni kyankyaso in huta. Ranar da daddare ko nai man abinci ba tai ba. Ita ce har sha biyu idanunta biyu ta kasa bacci.
Wasu samari ne guda biyu a bige su ka zo wucewa ta wannan bolar da ko da kud'i aka had'a ka bazaka zauna a wajan da rana ba balle da daddare. Haskata su kai da torch light. D'ayan da bai bugu sosai ba ya ta'ba d'an uwansa tare da fa'din,
"Babaa! Ni fa wancan yarinyar da ke rayuwar bolan can zan rufar mata in rage yawa. Dan naga ehh, ba yawa ta na da garin jiki, zan yi maleji a hakan. Dan ka fa san ehhh, kwana biyu Safara yawa ta ke min don ban da kud'i. Kawai dan rannan na d'an yi ehhh, ban ba ta ko sisi ba shine ta dai na duba min. Kawai zan farwa yarinyar can in rage yawa. Ni wallahi babaa idan har tai min ma zan iya d'auke ta in raine ta tunda dai ba ta da ehhh, ina nufin iyaye". Ya na maganar ne irin yadda y'an daba su ke yi d'in nan.
"Sata kawai babaa, zan jira ka a nan. Idan ka gama kai min fito ni ma inzo inyi ehhh, irin in samu nawa share d'in nan".
"Ba ka da case ba ri na je". Ya na gama fad'in haka yai wajan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login