Showing 6001 words to 9000 words out of 162658 words

Chapter 3 - BA NI DA GATA COMPLETE HAUSA NOVEL

29 Jan 2025

42909

kangon da Binty ta ke.
Ita kuwa Binty ta kasa bacci, ta na nan zaune ta ha'da kai da guiwa ta na kuka. Sai ji muryan mutum a tsawace tai a kan ta ya ce,
"Ke mik'e!".
Sosai ta firgita tare da mik'ewa ta na raba idanuwa. Shikuwa d'an iskan sai lashe baki ya ke yi kamar yaga cikakkiyar budurwa. Hannu ya kai ya fincikota tare da matseta a jikinsa sosai. Ita kuma Binty duk ta gama rikicewa jikinta sai rawa ya ke yi. Wannan ce rana ta farko da wani namiji ya mata haka idan aka cire kaka.
Matsar da ita gyefe ya yi tare zuge zip 'din wandon sa ya sauka a kan k'afafunsa.
"Ke dan uban ki kama min nan. Matsa min maza ko in yanka wuyarki ki mutu, da safe sai dai aga gawarki". 'Dan iskan nan ya fad'a.
Ita kuwa Binty ta k'i yin yadda ya ce sai gwalalo idanuwa ta ke yi a cikin duhu.
Ji ya yi an cafke masa mazantakarsa da k'arfi kamar za'a cire. Wani irin ihu ya yi tare da fad'in,
"Ke dan uwar uban ki ba da k'arfi ba a hankali za ki yi. Sa ke min abu na ko in ci uwarki ana wajan". Ya fad'a cike da wahala don har ya soma hawaye.
Ita kuwa Binty da ke gaban shi a tsaye sai mamaki ya kama ta. Don ita dai ta san ba ta kama masa komai ba amma yake ta ihu wai ta sakar masa abunsa. Ko mi ye abun nasa oho".
Wani gigitaccan mari yaji an sakar masa hagu da dama a fuskar sa wanda ya saka sai da ya yi k'undun bala akan bolan da ke zubowa k'asa. A matu'kar hargitse ya mik'e ya na waige-waige. Binty dai na nan tsaye ko motsawa ba ta yi ba. Tu ni tsoro ya dabaibaye shi, hankalin shi ya ta shi. Wani duka yaji an kai masa a k'eyarsa sai da ya yi taga taga zai fa'di. Saurin juyawa yai bai ga kowa ba. Can kuma sai ya soma jin k'arar kofato ya na yowa in da ya ke a tsaye. Ai bai san sadda ya cire wadon da ya ke hard'e shi a k'afa ba, ga shi ko boxer ba mu a jikinsa, yai wurgi da shi ya soma gudu ya na fad'in,
"Marados ka gudu wallahi mun shigo sansanin aljanai. Wallahi maganar da mutane su ke fad'i akan yar bolan ce gaskiya ne. Tabbas aljana ce. Ka gudu ka ceci kan ka". Ya na fa'din haka ne ya na falla gudu gashi babu wando Allah ya so shi dare ne. Shi kuwa wanda a ka kira Marados da ya soma 'dan gyangyad'awa a firgice ya mik'e shi ma ya shiga gudu. Gaba d'ayan su kuma su na jin takun kofaton nan kamar ana tseran doki. Marados ne yaji an d'aga shi cak, aikuwa ya shiga sakin fitsari tare da fad'in
"Wa innahu min sulaiman, wa'innahu bismillahi rahmanir rahim. Ku kuke ganin mu ba mu muke ganin ku ba. Bawan Allah aljani, dan rahamar ubangiji kai min rai. Wallahi ko ta layin nan idan na k'ara bi ka kashe ni. Dan girman Allah yallab'ai aljani".
Shikuwa d'ayan da akai nasarar cafko shi, zawo ya yi ta saki kamar farar kura. Daga sama suka ji an ha'dasu waje d'aya ka na aka sake su timmm a k'asa. Sannan su ka ji wata murya abun tsoratarwa ya na fad'in,
"Duk ranar da na sake ganin ku wajan bolan nan, kashe ku zan yi. Kuma ko ba binty ba, ku ka k'ara k'ok'arin yi wa wata yarinyar fyad'e to sai na kashe ku. Daga yau na fara bibiyar al'amuran ku kenan. Ku bar nan ko kuma in yanke mazantakar ku".
Ai a sittin suka arce. Ba su suka tsaya ba sai da su ka isa rumfar fale falen da su ke kwana su na ta sakin ajiyar zuciya.


*ᴡᴀꜱʜᴀ ɢᴀʀɪ*
Binty haka ta ta shi sukuku. Gaba d'aya kewar Hadaan ta ke yi. Musamman da ba ta ga pure water da MacLean da brush d'in da ya saba ajiye mata ba. Hawaye ta ji su na sauko mata daga idanunta.
"Kaka, ka na ina". Binty ta fa'da can cikin zuciyar ta. Mi'kewa ta yi ta haye can saman bolan. Bolan na da tsini sosai, domin bene ya yi, amma sam bai mata wuyan hawa. Sai da ta kai k'arshe ka na ta duk'a a kan gwiwowinta ta na hawaye ta re da fad'in,
"Ni ma zan tafi wata duniyar daban ba nan ba. Babu abunda na ke samu a nan. Nan ba duniya ta ba ce. Wanda ya ke so na d'in ma ya tafi ya barni. Ni ma zan tafi. Ba zan sake dawowa ba. Idan kin ki kewa ta ki ne me ni a wata bolar na wani duniya da ban". Binty na kuka ta ke fad'in hakan. Mik'ewa ta yi tare da soma saukowa. Sai da ta sauko gaba d'aya ka na ta d'aga kanta ta kalli bolan ko za ta ga kaka, sai dai wayam babu kowa a wajan.
Share hawayanta ta yi ta soma tafiya ta na waigen bolan. Tafiya ta yi mai tsayi har ta shigo wani unguwa. Unguwan tsit ya ke, irin unguwan nin masu kud'in nan. Zama ta yi a dandamalin wani tanfatsetsan gida tare da tsinko wasu furannin da aka shuka a k'ofar gidan ta na gutsirawa tare da jefawa a cikin kwata.
Wata jibgegiyar mota ce tai parking dab da gidan. Wani jibgegen mutum ne a cikin motar. Tumbinsa har tab'a steering ya ke yi. Bak'i ne sosai har wani shinning ya ke yi. Akwai hak'orin maka golden colour a bakin sa. Wayar sa da ke ringing ya 'dauka a gefan sa tare da kara wayar a kunnensa. Ka min yai magana Wanda ya kira shin ya soma fad'in,
"Sammani ka na wasa da k'ungiya wallahi. Saboda kai sabon shiga ne shi ya sa har su ke d'aga maka k'afa. Yau kimanin shekaru biyu ke nan ana fama da kai ka samo yarinya yar shekaru goma ka sadaukar da budurcinta da jininta wa dodon tsafi amma sai wasa da hankalin su ka ke. To ka bud'e kunnan ka ka ji da kyau. Saboda yadda mu ke da kai ne shi ya sa ma zan fad'a maka. Wallahi kwana uku aka ba ka idan baka kawo abunda aka buk'ace ka da shi ba, Durdus da kan shi zai aika Dobak'o ya d'auko masa matarka da babban d'anka a yanka su a kuma shanye jinin su a gaban ka kuma harda kai, idan kuma kak'i sha kai ma a sha jinin ka. Saboda haka ya rage gareka. Kuma ka da ka manta akwai meeting yau k'arfe biyu zuwa asuba, ka da ka sake kai fashi. Don Durdus na nan ya na k'irga fashin ka".
Kamin sammani yai magana idanuwansa su ka sauka akan Binty da ke wasa da flower. Wani farin cikin ne ya lullub'eshi tare da fad'in,
"Mai nasara yau zan kawo yarinyar nan ba sai jibi ba. Yanzu haka ma ga ta a gaba na".
"Na ta ya ka murna. Kuma ka rufawa kan ka asiri". Fad'in Mai nasara tare da yanke waya.
Shikuwa Alhaji Sammani bud'e murfin mota ya yi tare da fitowa ya nufi in da Binty ta ke a zaune.



*𝘼𝙎𝙎𝘼𝙇𝘼𝙈𝙐 𝘼𝙇𝘼𝙄𝙆𝙐𝙈 𝙍𝙀𝘼𝘿𝙀𝙍S, 𝙂𝘼 𝙉𝙄 𝙉𝘼 𝙕𝙊 𝙈𝘼 𝙆𝙐 𝘿𝘼 𝙎𝘼𝘽𝙊𝙉 𝙇𝙄𝙏𝙏𝘼𝙁𝙄 𝙉𝘼 𝙈𝘼𝙄 𝙎𝙐𝙉𝘼 𝘼
*ASSALAMU ALAIKUM READERS, GA NI NA ZO MA KU DA SABON LITTAFI NA MAI SUNA A SAMA, WANDA YA ZO DA ZAFI-ZAFIN SA, KUMA NA TABBATA ZA KU JI DAD'IN SA. BA ZAN CI KA KU DA SURUTU BA, KAWAI KU BI NI A FREE PAGES, KU DA KAN KU ZA KU GA NE BOOK D'IN NA DABAN NE. KAWAI KU NU NA MIN ONE LOVE WAJAN SIYAN BOOK D'IN AKAN FARASHI AKAN FARASHI MAI RAHUSA KAMAR HAKA:*




*Normal group shine mutum zai bi ya 500 idan ka ti ne, idan kuma ta account ne 300.*

*VIP kuma 1000 ne idan kati ne. Idan kuma ta account ne 700.*

*MUTANAN NIGER KUMA ZA SU BI YA KAMAR HAKA*:


*Normal group shine mutum zai bi ya 500F idan ka ti ne, idan kuma ta account ne 300F.*

*VIP kuma 1000F ne idan kati ne. Idan kuma ta account ne 700F.*
🌼 🌹 🌹 🌼
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹 BA NI DA GATA*🌹
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌼. 🌼
🌹
🌹 🌹
🌹 🌹


*ᴘᴀɪᴅ ʙᴏᴏᴋ*

*NARRATED & WRITTEN BY*
*ZULFA'U SA'EED IBRAHIM*
( *_MATAR SAYYADEE_*)


☀️ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION*☀️💪
( *Home of quality and trusted writer's of the nation*)💪🏻


*DEDICATED TO THE MOST BEAUTIFUL WOMAN IN THE WHOLE WORLD (MY MOTHER). ALLAH YA JIK'AN KI DA ℝ𝔸ℍ𝔸𝕄𝔸*



*________________*
*FREE PAGE 7&8*
*________________*

............"Yarinya ya sunan ki? Alhaji Sammani ya fad'a yayin da ya ke tsaye a gaban ta yana mata murmushi.
D'agowa ta yi tare da zuba masa idanuwanta da suke kamar madara tare da fad'in,
"Sunana Binty. Binty y'ar bola". Ta fad'a tare da cigaba da jefe flowers a cikin kwata.
"Binty 'yar bola kuma? To ina iyayen ki su ke? Ina ne gidan ku?". Alhaji Sammani ya fad'a ta re da zama kusa da ita.
"Ni ba mu da gida. A bola mu ke zama. Kuma mamana ce bolan, ita ta haife ni. A can na tashi".
Wani farin ciki ya dabaibaye zuciyar Alhaji Sammani, domin ya ga ne d'aukar Binty ba zai masa wuya ba.
"To yanzu me ki ke yi a nan wajen ke d'aya?". Alhaji Sammani ya sa ke jeho mata tambaya.
"Ni ma ban sa ni ba, amma bazan sa ke ko ma wa bolan mu ba. Ban san wancan duniyar, kowa bai so na a can. Ina so in je duniyar da kowa zai so ni, kuma in rik'a samun abinci ina ci sau uku a rana. Ni ba dole sai na yi wanka ba. Amma ina son in canza wannan wandon na jiki na. Kalla duk ya yage. Ka san wa ya ba ni? Wallahi Hadaan ne ya kawo min, kuma maman shi ta d'auke min shi ta kai shi wani waje mai ni sa". Ta fad'i haka ne hawaye na zubowa daga idanunta.
"Ayyaah kin ban tausayi. Amma ki kwantar da hankalin ki, zan kai ki in da za ki samu duk abunda ki ke so, za ki je duniyar da kowa zai k'aunace ki kin ji y'ar yarinya". Alhaji Sammani ya fad'a ta re da rik'o hannunta.
"Dagaske? Har wajan Hadaan d'ina za ka kai ni?". Binty ta fad'a out of excited.
"Sosai ma kuwa, muje ga motata can ki shiga mu tafi". Alhaji Sammani ya fad'a tare da kama hannunta su ka yi wajan mota. D'aga kan da Binty za ta yi ta hango Kaka a kan wani katanga ya na girgiza mata kai sannan kuma ya na maganar da ita kad'ai ke jin abunda ya ke fad'i.
"Ka da ki bi shi Binty. Za ki halaka idan ki ka bi shi. Ki dawo ki koma ki zauna a in da ki ke. Shine alkhairi a gare ki. Za ki fad'a wani hannu daban da zaki sha wahalar rayuwa. Za ki kira k'addarar ki da kan ki Binty".
Girgiza kai Binty ta yi ta re da fad'in,
"Ni sai na bi shi, bayan wajan Hadaan zai kai ni. Ni ba ruwa na da kai, ai kai ma guduwa ka ke yi ka na bari na babu abunci". Binty ta fad'a ta na murgud'a baki.
Kasancewar Alhaji Sammani ya d'an yi gaba kad'an shiyasa bai ji abunda Binty ke fad'i ba.
"Binty kar ki bi sa". Kaka ya sa ke fad'i ya na girgiza kan shi.
"Sai na je". Binty ta fa'da ta re da isa wajan motar.
"Ke da wa ki ke magana Binty?" Alhaji Sammani ya fad'a ya na mai waiwaigawa don ganin da wa Binty ke magana.
Ita kuwa Binty ba ta ba shi amsa ba ta shiga k'ok'arin shiga gaban motar da ya sha tinted, amma ta ka sa saboda ya mata tsayi.
'Dagata Alhaji Sammani ya yi ta re da d'aura ta a kan kujera shi kuma ya zagaya ya shiga mazaunin driver ta re da yin reverse ya ko ma ya hau highway zuwa garin Abuja babban birni, don a can ne su ke gudanar da tsafin su.
A cikin wani katafaren hotel Alhaji Sammani ya yi parking tare da fita ya kulle Binty a ciki da ke ta bacci. Domin tunda aka haife ta bata tab'a irin wannan doguwar tafiya haka ba. In fact in her whole life ba ta tab'a shiga mota ba sai yau.
Reception ya shiga tare da biyan kud'in d'aki na kwana d'aya kawai. Ka na ya karb'i key ta re da fitowa ya dawo cikin mota ya kunna ya yi reverse ya bar cikin hotel 'din. A wani katafaran saloon ya tsaya ta re da bubbuga Binty da ke bacci ta na mafarkin kaka na mata kashedi akan ta gudu ka da ta bi wannan mutumin da ta ke ta re da shi.
Farkawa ta yi ta re da fa'din,
"Ni sai na bi shi, bazan gudu ba kaka. Ka dai na tab'a ni. Shi ba mugu ba ne. Ya saya min kayan dad'i a hanya. Kuma wajan Hadaan d'ina zai kai ni". Idanuwa Alhaji Sammani ya zuba mata, Can kuma ya k'ara bugunta a hankali. Wannan karan gaba d'aya ta bu'de idanunta ta zuba masa ta re da fad'in,
"Mun kawo in da za ka kai ni wajan Hadaan d'ina ne?"
"A'a beauty ba mu kawo ba, nan mun zo in da za'a gyara ki ne ai miki wanka a gyara miki gashin ki, saboda in da zan kai ki ba su son k'azamin mutum, kuma ba za su yarda ki ga Hadaan d'in ki ba a haka".
"Kai kai kai.. Hadaan ne ya fad'a maka yadda ya ke kiran suna na? Allah ni ban san wanka, amma tunda za ka kai ni wajan Hadaan zan yarda a min wankan". Binty ta fad'a cike da farin ciki a fuskan ta.
"Yauwa to jira ni a cikin mota ina zuwa". Alhaji Sammani ya fad'a ta re da fita ya shiga cikin wannan dank'areran Saloon 'din.
Mintuna goma su ka fito shi da wata kyakkyawan siririyar mata su na dariya ita da Alhaji Sammani. Wajan motar su ka yo, Alhaji Sammani ya bud'e ta re da sauko da Binty daga cikin mota ka na ya kalli wannan kyakkyawar matar da ta saki hanci da baki ta na kallon tsananin kyawun Binty.
"Precious Lord in heaven! What a beautiful girl. Alhaji ina ka samo wannan kyakkyawar yarinya haka? Oh my God, dan Allah ka ba ni ita mana".
"A'a ni ba za a ba ki ni ba, wajan Hadaan d'ina zai kai ni". Binty ta fad'a ta re da mak'e kafad'ar ta, ta kuma koma bayan alhaji Sammani ta b'uya.
Kaka ta ga ni a bayan wannan kyakkyawar matar ya na girgiza ma ta kai ta re da fad'in,
"Binty ki bi ta, idan ki ka bi ta ba za ki halaka ba. In har ki na son k'ara ganin Hadaan ki bi ta". Ita kad'ai ta ji maganar. Zaro idanuwa ta yi ta re da fad'in
"Kaka nan ma sai da ka bi yo ni? Ni Allah ba zan bi ta ba. Wannan zan bi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login