Showing 18001 words to 21000 words out of 162658 words
ya k'ara d'agawa ta re da d'ago Binty da ke shimfid'e a k'asa. Mik'ewa ta yi k'ek'am ku ma still bacci ta ke yi ko motsi ba ta yi ba. Taho da yatsarsa ya ke yi, ita ma Binty ta na k'ara matsowa ku sa da shi. Sai da ta zo daf da shi ya tsayar da ita cak ta re da yin sama da yatsar shi. Ta ke fuskanka ta d'ago, shi ku ma ya sa ka idanunsa a kan na ta da ke rufe ta na bacci. Shafa idanuwan ta ya yi. Wani irin firgita ta yi ta re da bud'e idanuwanta ta sauke a kan Durdus.
*KU HANZAR TA FA, FREE PAGES 'DAYA YA RAGE. KUMA DAGA GOBE NE FA! KA KI JIRA NA SATA Y'AR UWA. D'ARI BIYAR D'IN KI ZAI BI YA MIKI BUK'ATA, SHI MA IDAN KATI NE ZA KI TURO. IDAN KUMA TA ACCOUNT NE. D'ARIN KI UKU YA ISHE KI*
Wani irin haske Durdus ya ga ni a cikin kwayar idanun Binty. Ja da baya Durdus ya yi wanda hakan ya firgita hancin gaba d'aya jama'ar wajan. Don yau ne rana ta farko da wani abu ya kid'ima Durdus har ya bayyana a jiki da fuskansa. Shi kuwa Alhaji Sammani zawo ne ya nai mi kwace masa. Hanjinsa kuwa kamar za su tsintsinke.
"Ka ji tsoro ne bak'in arne?". Binty ta fad'a da wani razananniyar muryan tsohuwa wacce za ta iya kaiwa shekaru saba'in a duniya.
"Wa cece ke? Mai ki ke buk'ata anan? Ni ban gayyace ki ba, ki fita a jikin wannan yarinyar jinin ta za mu sha kuma mu sadaukar da budurcinta ga Dodan tsafi.
"Karyan ka!". Fad'in Binty cikin muryan tsohuwan nan ta na wani irin mik'ewa ta na k'ara tsaho har sai da kan ta ya tab'o silin d'in k'aton hall d'in nan. Faratunan hannunta ya k'ara wani irin tsawo daga tsayan nan na ta har ya na tab'a k'asan d'akin taron nan.
Wani irin ihu Binty ta yi wanda ya saka ga ba d'aya kayan jikin mutanan wajan fita daga jikinsu har da shugaba Durdus. Wani ihun ta k'ara yi da ya kifo da Dodon tsafi nan da girman sa ya cika bango d'aya. Da ba din tashi saman da Durdus ya yi da sauri ba, sai Dodon na ya kashe shi. Duk da haka ma sai da ya kashe mutane saba'in.
Fa'duwa gabanta Durdus ya yi ta re da fad'in,
"Tuba na ke sarauniyar aljanu, ki min aikin gafara. Ku d'auki yarinyar nan ki tafi da ita ka da ki halakar da mu".
Gaba d'aya sauran mutanan su ma su ka kwanta flat su na rok'an Binty. Shi kuwa Alhaji Sammani ya san ta shi ta k'are. Don ya tabbata mutawa zai yi.
A hankali Binty ta so ma rage tsawonta har ta dawo dai dai tsayin ta ta re da fad'in,
"Ku azzalumai ku saurare ni, ban ga ma da ku ba, zan dawo a cikin shiri domin in ga ma da ku. Ba za Ku k'ara cutar da wa ni d'an Adam ba. Ku ma zan ta tafi, amma ta rezan ta fi da wannan azzalumin, da kai na na ke son in hukunta shi".
Alhaji Sammani kuwa da jin abunda Binty ta fad'a ya sa ki zawo ba adadi.
K'arasa Binty ta yi ta re da dafa Alhaji Sammani su ka b'ace ta re.
*ASSALAMU ALAIKUM READERS, GA NI NA ZO MA KU DA SABON LITTAFI NA MAI SUNA A SAMA, WANDA YA ZO DA ZAFI-ZAFIN SA, KUMA NA TABBATA ZA KU JI DAD'IN SA. BA ZAN CI KA KU DA SURUTU BA, KAWAI KU BI NI A FREE PAGES, KU DA KAN KU ZA KU GA NE BOOK D'IN NA DABAN NE. KAWAI KU NU NA MIN ONE LOVE WAJAN SIYAN BOOK D'IN AKAN FARASHI AKAN FARASHI MAI RAHUSA KAMAR HAKA:*
*Normal group shine mutum zai bi ya 500 idan ka ti ne, idan kuma ta account ne 300.*
*VIP kuma 1000 ne idan kati ne. Idan kuma ta account ne 700.*
*MUTANAN NIGER KUMA ZA SU BI YA KAMAR HAKA*:
*Normal group shine mutum zai bi ya 500F idan ka ti ne, idan kuma ta account ne 300F.*
*VIP kuma 1000F ne idan kati ne. Idan kuma ta account ne 700F.*
*EVIDENCE OF PAYMENT 08128755583*
🌼 🌹 🌹 🌼
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹 *BA NI DA GATA*🌹
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌼. 🌼
🌹
🌹 🌹
🌹 🌹
*PAID BOOK*
*NARRATED & WRITTEN BY*
*ZULFA'U SA'EED IBRAHIM*
( *_MATAR SAYYADEE_*)
☀️ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION*☀️💪
( *Home of quality and trusted writer's of the nation*)💪🏻
*DEDICATED TO THE MOST BEAUTIFUL WOMAN IN THE WHOLE WORLD (MY MOTHER). ALLAH YA JIK'AN KI DA RAHAMA*
*KU HANZAR TO KU HWARA PAYMENT, KA DA KU BA RI A BA KU LABARI. NORMAL GROUP, D'ARIN KI BIYAR #500 KACAL ZAI BI YA MI KI BUK'ATA, SHI MA IDAN KATI ZA KI TURO, IDAN KUMA TA ACCOUNT NE, D'ARIN KI UKU #300 YA ISHE KI. VIP KUMA #1000 IDAN KATI NE, IDAN KUMA TA ACCOUNT NE D'ARIN KI BAKWAI #700 ZAI BI YA MI KI BUK'ATAR KI. KI HAN ZAR TA KAR A BA KI LABARI. 0592412800, SAI KI TURO DA SHAIDAN BIYAN KI A WANNAN NUMBER 08128755583. SAYAN NA GARI, MAI DA KUD'I GIDA*
*____________________*
*FREE PAGE 13&14*
*LAST FREE PAGE*
*____________________*
.............Ko da Binty ta farka, gyefan wa ni unguwan ta tsin ce ta ya she a k'asa jikinta duk k'asa. Gashin nan da ya sha gyara duk ya b'aci da datti duk da dai bai kai ko kwatan lokacin da ta ke rayuwa a kan bola ba. Dube-dube ta fa ra yi, can Kuma ta mik'e ta re da fad'in,
"Ina ya ke kuma? Mai ya sa ya kawo ni nan? Shi ma ya gudu ya bar ni bai kai ni wajan Hadaan d'ina ba. Da ma na sa ni babu wanda ke so na". Ta fad'i maganar ne ta re da fashewa da ku ka sosai.
Daga can gyefe kuma wata mata ce ta ci ado sanye da atampa wacce ake kira da matso kalar maroon, sai gyalanta irin tsohon yayin nan mai sun tissue, kalar pink da takalminta flat shoe na roba kalar bak'i sai wata k'atuwar jaka da kafatin k'auyan su ba mai irin sa. Wata yarinya ce ke matsar kwalla a gyefanta. Ita kuwa matar nan sai faman fad'a ta ke yi kamar ta ari ba ki.
"Shegiya gantalalla y'ar Abun kwari, wacce ba ta san arziki ba. Yanzu ban da ke dak'ik'iya ce, wacece za ta yarda ta shiga gidan Alhaji Usman mai rabo a matsayin y'ar aikin su amma tai wa kanta sagegeduwa. Shegiya kawai kin cuceni kin cuci kan ki. Mu je wajan uwar ta ki, ita ma sai na mata ruwan rashin mutunci, kuma wallahi sai ta ba ni dubu goma na wahalar jigilar da nai ta yi da ke. Shegiya mai fuskan samudawa. Da na sani Bashira na d'auko ba ke lalatacciya ba. To in ban da lalaci ya za'ai in tura ki aiki ki je ki saki leb'e ki na bacci har d'an mai gidan ya buk'aci wani abu ai ta kiran ki shuru saboda ki na baccin asara. Wallahi sai na ci jakar Ubangi, y'ar k'undun uba kawai. Ga shi yau a kawai aka ba ni in samo wata y'ar aikin. Ni da garin mu ya ke Saminaka, Yaushe har na je yau na dawo. Ke dai wallahi anyi tsinanniyar y'a wallahi. Yanzu haka wata za su kira ta sa mo masu wata y'arkin, kin ga ni na rasa y'an karansin (currency) kenan. Wallahi Allah ya isa tsakanina da ke Basira". Kandala ta fad'i ta re da tura k'eyar y'ar yarinyar da ba za ta wuce shekara goma zuwa sha d'aya ba.
Yarinyar na hawaye ta kalli Kandala ta re da fad'in,
"Baaba Kande wallahi yaron gidan ne d'an iska. Kullum na je kai masa abunci sai ya rik'a tattab'a ni. Har wando ya ke cire min".
"Lahaula walak'uwata! Jama'a ku ji min y'ar iskar yarinya da sharri. Dan uwar ki duk y'an matan da ya ga ni a k'asar waje da kuma irin y'an matan da su ke bin sa, ya rasa wacce zai yi lalata da ita sai ke y'ar tatsitsiya da ke? Yau na batsula na ga sharri ganin idona. Shiyasa ke nan ki ka dai na kai masa abincin har cikin d'aki sai dai ki aje a kwar d'aki kamar kin ajewa kare ko mage. Shegiya mai zubin aladun zamanin da. Yanzu ke Basira ko da zan can da ki ka fad'a gaskiya ne, ai arziki ne ki bin ki amma da ya ke she d'in y'ar Abun kwari ce, sai ki ka k'i yarda ko? Wallahi na san da kin aminci a cikin wata d'ayan nan da ki ka yi, sai kin ta ra kud'i ya kai kusan rabin million d'an ba gidan matsiyata ki ke ba. Amma kin cuci kan ki Basira, yanzu ai a kawo wacce za ta amince ta ci arziki ta Kuma bar arziki a in da ya ke. Ni dai ga dukkan alamu watan rashin rabo na ne ya tsaya shiyasa na d'auko ki. Shegiyar yarinya mai k'ashin tsiya". Kandala ta fad'a ta na matsar hawayen asarar da Basira ta jawo mata.
Basira kuwa bata k'ara cewa ko mai ba, domin farin cikin da ta ke yi na barin ta gidan Alhaji Usman mai rabo. Don ita kad'ai ta san abunda ta ke ga ni na tantagaryar iskanci a wajan d'an sa na wajan matar gidan ta tsakiya. Don har sanin ta a matsayin y'a mace ya yi. Shiyasa yanzu ta ke jin dad'i da ta bar gidan.
Ita kuwa Kandala tsayawa ta yi cak lokacin da idanuwan ta su ka sauka akan Binty da ke kuka ta na waige-waige.
"Ki tsaya a nan ki jira ni ina zuwa". Fad'in Kandala ta re da nufar in da Binty ke a tsaye ta na kuka.
"Yarinya lafiya? B'ata ki ka yi ne? Ina iyayen ki su ke". Kandala ta jeho mata wad'annan tambayoyin ta re da zuba ma ta idanuwa.
"Ban gan shi ba, ya ce min zai kai ni wajan Hadaan d'i na kuma ya ka wo ni nan ya gudu ya bar ni". Binty ta fad'a ta na k'ara b'arkewa da kuka.
"Waye shi d'in wanda ya gudu ya bar ki d'in? Kuma ina ne gidan ku". Kandala ta sa ke watso mata tambaya.
"Ni ma ban san shi ba, amma ya min alk'awari zai kai ni wajan Hadaan, har kaya mai kyau ya siya min, ya kuma kai ni aka gyara min gashi na". Fad'in Binty ta na shashshek'ar kuka.
"To wai ke ina iyayen ki su ke?". Kandala ta sa ke tambayanta cike da k'osawa.
"Mamana ta na kan bola, ita ce ma bolan. Ba ni da kowa sai ita. Na gaji da zama a kan bolan ne saboda kowa bai so na shi ne na bar wajan don in koma wani wajan da kowa zai so ni. Shi ne wannan mutum d'in ya gan ni ya saka ni a motar shi ya ce min zai kai ni wajan Hadaan shi ne ya gudu ya bar ni ana". Binty ta fad'a ta na share kwallar da ke zubo mata.
Kallon ta Kandala ta yi daga sama har k'asa, ta na son ta tabbatarwa kan ta shin mahaukaciya ce a gaban ta ko kuwa. Ga yarinya dai kyakkyawa da ita.
"Ke nan ba ki da iyaye?". Kandala ta sa ke tambaya.
"Ni ba ni da kowa sai bola ta. Akan bola na ke rayuwa. Hadaan d'ina ke kawo min abincin da kaya. Shi ne maman shi ta d'auke min shi ta kai shi wani waje a mota. Wajan shi na ke so a kai ni amma babu wanda ya ke son kai ni". Ta k'arisa maganar ta re da fashewa da kuka.
"Alhamdulillah! Kandala a she ki na da rabo a duniya. Lallai idan na kai wannan zuk'ek'iyar yarinyar nan gidan Mai rabo na san sai sun ninka min kud'in da su ka saba ba ni. Kai Allah nagode maka". Fad'in Kandala a bayyane.
"Yarinya ki na ji na? ki kwantar da hankalin ki, ni nan Kandala shugabar dinlalan Saminaka zan kai ki wajan Hadin d'in ki".
"Ni ba Hadin na ce mi ki ba, Hadaan sunan sa. Kuma dagaske ki ke za ki kai ni wajan sa?".
"Eh kwarai dagaske. Na san shi ai, d'an makwafciya ta ce ai. Amma yanzu bai k'asar, ya je karatu wani k'asa. Idan har za ki yi duk abunda na ce ki yi, zan kai ki wajan shi da kai na".
"Zan yi, Allah zan yi. Mai zan yi? Mai ki ke so in yi yanzu?". Fad'in Binty.
"Zan kai ki wani gida, gidan da za ki huta. Ki ci abunci mai kyau sannan Ku ma a ba ki kud'i mai yawa ki sa yi duk abunda ki ke so".
Zaro idanuwa Binty ta yi ta re da fad'in,
"Dagaske? Zan bi ki Allah in dai za'a rik'a ba ni abincin sau uku kuma mai dad'i".
"Ai ko za'a ba ki, amma fa za ki rik'a masu aiki irin su wanke-wanke da gyaran d'aki".
"To ai ni ban iya ba". Fad'in Binty.
"Kar ki damu, za'a ko ya miki. Yanzu dai zo mu tafi ka da a kai wato". Kandala ta fad'a ta re da kamo hannun Binty su ka koma in da Basira ta ke tsaye.
"To annamimiya, ta Allah ba taki ba, ga shi na sa mo yarinyar da za ta maye gurbin ki. Mu je na aje ki gidan Datu na kai y'ar albarkan nan gidan Alhaji Usman Mai Rabo tun da ke ba ki san alkhairi ba. Shegiya mai kan kwankwalati". Kandala ta fad'a ta na tura k'eyar Basira gaba.
Cak Binty ta tsaya ta na kallon Kaka da ke gaban su shi ma ya na kallon cikin idanunta wanda ke cike da hawaye.
"Binty dan Allah! Dan Allah ka da ki bi ta, yanzu ba ni da ikon taimakon ki, Iyayah mahaifiya gare ni ta gina wa ni katanga tsakanin mu. Ba ni da ikon taimakon ki yanzu. Dan Allah ka da ki bi su ki bi yo ni na mai da asalin in da ki ka fara rayuwa wa to kan bola. Dan Allah Binty kar ki ce a'a". Kaka ya fad'i haka hawaye na ziraro masa.
Hakana Binty ta ji ita ma hawayan na zirarowa daga idanunta. Shafa fuskan kaka ta yi ta re da goge hawayan da ke zubowa daga idanun na sa ta ce,
"Ka yi hak'uri kaka, amma ba zan bi ka ba. Ban san ko ma wa wannan duniyar. Dan Allah kaka ka bar ni na bi ta. Ba na so na bi ka".
"Ba zan miki tilas ba Binty, amma idan so samu ne ki bi ni in kai ki wani duniyar da ban. Mutane ba su da tausayi, ba sa jin k'an way'anda su ke k'ark'ashin su. Maciya amana ne su. Dan ki yarda da wannan tsohon da ke gaban ki".
"A'a ni bazan bi ka ba, dan Allah ka matsa min a hanya. Zan bi ta, ita na ke son bi". Binty ta fad'a ta na kuka.
Kandala tsaye ta yi ta na kallon Binty ci ke da mamaki. Domin ba kin ta ne kawai ke motsi sai kuma hawayan da ke zubowa daga idanunta.
"Lafiya ke kuwa ki kai tsaye ki na ta kuka haka? Ko kin fasa bi na ne in kai ki wajan Hadin d'in na ki da ki