BA NI DA GATA

Chapter 8 of 45

ka fi ki guda hamsin su ka ba za su zurma ba ba re Ku ma ke y'ar tatsitsiya da ke. Dallah ta shi ki yi tafiya da k'afafun ki ka da ki ba da mu". Fad'in Fasila.
"Mai ke faruwa a wajan Fasila?". Hajiya Na'ima da fitowar ta kenan daga d'aki ta ji muryan Fasilan ta na b'ab'b'aka dariya.
Saurin natsuwa Fasila ta yi ta re da sunkuyar da kan ta, ka na ta ce,
"Wannan yarinyar ce ke rarrafe, wai tsoran ta ka wa ta ke yi".
Kallon Binty da ke tsugunne a k'asa Hajiya Na'ima ta yi ta re da k'arisawa in da ta ke ta ka mo ta su ka k'arisa hayewa.
"Har baabar ta ki ta wuce?". Hajiya ta fad'a ta na k'arewa Binty kallon. Ga dai rigar jikinta mai kyau da tsada sai dai duk ya yi butu-buti har da miya-miya a gaban rigar.
"Eh yan zun nan ta wuce ai". Binty ta fa'da ta re da ju ya wa ta na kallon stairs d'in da ta hauro.
"To mu je ki huta ki ci abinci, anjima zan fad'a mi ki abubuwan da za ki ri'ka yi".
"To. Da ma yunwa na ke ji sosai". Fad'in Binty.
Gaba Hajiya Na'ima ta yi, Binty na bi ye da ita a ba ya har zuwa wani tsararran k'aton parlourn da ke sama.
"Zauna a nan, ina zuwa". Hajiya Na'ima ta fad'a ta re da bin wani corridorn da zai sa da ta da bedroom d'in ta.
Za ma Binty ta yi a kan tamfatsetsan kujeran mai d'an karan laushi. Can ku ma ta mik'e ta na ta isa wajan labule ta na kallon su ta re da sha fa su.


"Ke Fasila shafa min dan Allah. Na ga wannan kyakkyawar yarinya da Kandala ta ka wo nan wajan Hajiya Babba ta bar ta. Ina ce Hajiyan tsakiya ce ta sa a can zo ta da Basira?". Fad'in Jummalo da ke ciro kaya a cikin washing machine.
"To uwar gulma, ni ma ban sa ni ba. Ki je ki tambaye ta mana, ai kin san hanyar d'akin nata ai". Fad'in Fasila ta re da maka mata harara.
Dafe k'irji Jummalo ta yi ta re da fad'in,
"In mutu maza su kai ni ba mata ba. Ko ke sai da ki ka kwashi shekaru bakwai ka min Hajiya Babba ta fara ba ri ki ka fara haurawa sama, shi ma iya kacin ki d'akin aje kayan wanki ki fito da su ki kawo su nan a wanke, balle ni da zuwan jiya-jiya. Ko fa shekara ban yi ba a gidan nan. Satin gaba dai zan cike shekara guda.
"Hmm to ai kuwa wannan kyakkyawar yarinya dai da sa'a ta zo, domin kuwa har babban parlourta ta shiga da ita. Zo ki ga yadda mamaki ya kusa kashe ni". Fad'in Fasila ta na kallon Jummalo da ta saki baki da hanci ta na kallon ta.
"Haba dai Fasila? Hajiyan ce ta kai ta har parlourn ta wanda daga Alhaji sai y'ay'anta ke shiga?".
"Yadda ki ka ji". Fad'in Fasila ta re da ficewa daga washing room d'in.
"Kan bura uban caaaan! Lallai wannan yarinya kin zo da sa'a, duk da ya ke Hajiya ta kirki ce, sai dai ta na da mugun rashin yarda ne. Ko in ce duka matan Alhaji ha ka su ke. To wai ma ni ina ruwa na". Fad'in Jummalo ta re da cigaba da kwashe kayan cikin washing machine d'in.


"Oga Solomon, watin happen? You no dey talk since dat fat human wey hold that pretty girl hand pass here.".
"Mtsww! Baba Haruna, Na something wey they kill me in this house. The thing way Alhaji son de so is no good, and his mother no everything way him de do. Yesternight if you see how he come back from club, ibi like say he wan kill me with his car. He horn like he wan remove my ear. He's drunk and na his baby who de drive the car. Mtsw no be that one de worry sef. Na that pretty girl who that stupid woman bring earlier, and she tell me say na madam se make she bring her to do work for that stupid child of her. I pitty for that cikili girl. I know that stupid he goat go spoil her, da boy na real ashawo. Every day him de bring three to four women to sleep with him. Imaging, this cikili pikin that is not up to twenty years. Chaiii! God they see everything". Oga Solomon ya fad'a cike da tausayi da jimami.
"Huh! Mtsw. No be only you that thing they worry. Even me sef, I they pity for that girl. I cannot count the maids who that stupid little brat rape in this house. Even the girl that was fire, what's that her name? I can't remember". Baban Haruna ya fad'a ya na kallon Oga Solomon.
"Sekina. Ohhh da girl is very cam". Oga Solomon ya fad'a.
"Yauwa, dat her name, Sakina. He impregnate her, thats the reason why Hajiya Mansura fired her".
"What? When did that happen". Oga Solomon ya fad'a da k'arfi.
"Hey, ni fa matsala ta da kai kenan. Ba ka iya magana a hankali ba, yanzu idan wa ni yaji fa? Ku ma kasan dai akwai munafukai y'an kai report".
Ajiyar zuciya Oga Solomon ya yi ta re da fad'in,
"Mtsw, I'm sorry baba Haruna, I was shoked that's why. But the thing way Hajiya Mansora de do is not fair atol. Alhaji no nothing about this".
Zaro idanuwa Baban Haruna ya yi ta re da fad'in,
"I swear him no no everything about this. Alhaji na goodman. I swear if he no wating his wife and his son de do him go furnish them, he will send Hajiya Mansura to her parent house".
"I pray may him come know everything way they happen in this house. I pray may hin send that old bitch to her parent house".
Tab'a shi da k'afa Baban Haruna ya yi ta re da nu na masa D'an kwairo da ke ta ho wa wajan su.
"An zauna ana sana'ar da aka saba kenan". Fad'in d'an kwairo ya na hararar su.
Ba bu wanda ya kula su a cikin su. Oga Solomon ne ya bud'e masa k'aramar k'ofa kasancewar fi ta zai yi".
"This dan kwero na original amebo". Fad'in Oga Solomon cikin rad'a.
"I never see amebo before like him". Fad'in Baban Haruna ya na dariya ta re da mik'awa Oga Solomon hannu su ka tafa.



Bubu abunda ka ke ga ni a d'akin sai hayak'in shi-sha da ya turnik'e d'akin kamar d'akin boko. Sai k'arar kid'an da ke ta shi kamar gidan casu.
Zuk'ar shi-shan ya ke yi cike da kwarewa ya na fesar da hayak'i. Y'an mata ne guda hud'u. D'aya ta na wajan kan sa ta na masa massage a kansa. D'aya kuma ta na shashshafa jikinsa. D'aya kuma ta na mammatsa masa k'afarsa. D'ayar ta karshe kuma ta na jujjuya jikinta a gaban sa.
Gyefe guda kuma cuncurundon abokansa ne su takwas ko wanne da shi-sha port da ya ji mix da kayan ma ye a ciki. Biyu daga cikin abokan sa kuma su na cikin d'aki d'aya da y'an matansu su na amfani da su.
"Hey Suhail, har yanzu fa ba'a kawo ma na abinci ba, ko y'an aikin gidan ku sun k'are ne?".
Wani bu'de idanu Suhail ya yi ta re da kulle su, ka na ya lallubi wayarsa da ke kan center table d'in gyefar kujeran da ya ke kai. Dialing Sweet mom ya yi ta re da karawa a kunnan sa.



"Ke saboda ke bak'ar annamimiya ce, munafuka shi ne ki ka kai mata y'ar aikin da na ce ki ka wo min ko? To ko ki je duk yadda za ki yi ki maido ta waje na, ko kuma wallahi zaman abuja ya ga gare ki wallahi". Fad'in Hajiya Mansura kamar za ta kwad'awa Kandala ma ri.
"Hajiya ki min rai dan girman uban giji, wallahi ke nai niyyar ka wo ma wa ita shine ta ce na bar mata ita ke kuma na sa mo ma ki wata. Dan Allah ki yi hak'uri ki ba no zuwa jibi wallahi zan sa mo mi ki wacce ta fi wannan girma da ko mai, wacce za ta iya duk ayyukan da za ki saka ta". Fad'in Kandala.
"Za ki rufan ba ki ko sai na kwad'a mi ki mari. Ita wancan yarinyar na ke so. Duk yadda za ki yi, ke ki ka sani".
Ka min Kandala ta k'ara magana, wayar Hajiya Mansura yai k'ara. D'aukar wayar ta yi a kan kujera, ganin mai kiran wayar ne ya sa Hajiya Mansura ta sallami Kandala da hannu ta re da d'aga kiran ta ce,
"Son ya aka yi? Wani abu ka ke buk'ata?".
Kasancewar Suhail ya tsumu da shaye-shaye, muryan sa har fashewa ta yi, idan yai magana za ka d'auka gardi ne d'an shekaru talatin, nan kuwa ko shekaru ashirin bai yi ba.
"Mom, we need food right now. Amma kar ki turo min wannan y'ar iskan yarinyar".
"Ka da ka damu son, ai tuni na kore ta yau d'in nan. Har na sa an kawo maka wata ma. Kyakkyawa da ita, wacce za ta iya duk aikin da ka saka ta. Ba ma za ta wuce shekaru goma ba. Sai dai fa wancan matar ta yi ma na overtaking".
Yamutsa fuska ya yi ta re da fad'in,
"Wacece wannan a cikin gidan nan da za ta mi ki overtaking ki na kallon ta kuma".
"Wacece kuwa ban da matar uban ka mai isa wai ita jinin sarauta".
"To ina ruwa na da jinin sarautar ta. Ko da a ce sarkin ne uban ta, ya min ba kyale shi zan ba. Don haka a karb'o yarinyar nan ko ta halin k'ak'a, ku ma a kawo min abinci in five minutes". Suhail na ga ma fad'in haka ya datse kiran ta re da kwantar da kan shi a jikin kujera. Don har hankalin shi ya tashi da ya ji an samu yarinyar y'ar shekaru goma. Lallai ashe zai more.


**********Hannun ta d'auke da faranti ta dawo parlourn. Murmushi ta yi saboda ganin Binty da ke wajan labule sai shafawa ta ke yi. Aje farantin ta yi a kan center carpet d'in da ke shimfid'e a parlour.
K'arar ajiye farantin ne ya dawo da hankalin Binty wajan Hajiya Na'ima da ke tsaye ta na kallon ta.
"Dawo nan ki zauna kici abinci". Fad'in Hajiya Na'ima ta re da nu na mata abincin.
K'arasowa ta yi ta re da zama a k'asa ka na ta bud'e plate d'in saman da aka rufe abincin. Zaro idanuwa Binty ta yi ta na kallon farfesun kaza da ya sha kayan lambu harda irish poteto a ciki ta re da fad'in,
"Duka wannan nawa ne?". Ta fad'i haka ne ta na kallon Hajiya Na'ima da ita ma kallon na ta ta ke yi.
"Eh duk na ki ne ke d'aya. Ciki sai ya ishe ki, idan ba ki k'oshi ba ki yi min magana zan k'aro mi ki". Fad'in Hajiya Na'ima.
"Kai amma nagode mi ki sosai. Gaskiya garin nan Ku na da kirki, ku na ba wa mutane abincin ma su dad'i sosai". Ta fad'i hakane ta re da d'aukar tsokar cinyar kaza ta yaga".
"Wayyiwooooo dad'i kashe ni. Wannan na ma da dad'i ya ke. Dan Allah ki rik'a ba ni kullum zan rik'a miki duk abunda ki ke so". Binty ta fad'a ta na karkad'a kan ta.
Girgiza kai Hajiya Na'ima ta yi ta re da murmushi ta yi hanyar da zai sa da ta da bedroom d'in ta.
Sai da Binty ta cinye farfesun rabin kazan nan da Irish d'in nan tas. Ka na ta kafa kai ta shanye roman ta re da sud'e hannunta ta d'auki goran ruwa ta kafa baki ta sha fiye da rabi, ka na ta ajiye ta re da sakin gyatsa ta jingina da kujeran. Cikin k'ank'anin lokaci bacci ya yi awon gaba da ita.







*DAN GIRMAN UBANGIJI KA DA KI FITAR MIN DA BOOK. IDAN KIN SAN ZA KI FITAR DAN ALLAH KI MIN MAGANA NA MAYAR MI KI DA KUD'IN KI*


*DAN ALLAH IDAN KIN GA NI BA KI SIYA BA KA DA KI KARANTA KU MA KAR KI YI SHARING, KI NAI MI NUMBER 08128755583 KI SI YA SABODA KI KARANTA DA GUMIN KI BA NA SATA BA*.

*_BA NA TYPING SATURDAY AND SUNDAY_*


*MATAR SAYYADEE*
🌹 *17-18*🌹

K'arfe biyu da rabi na rana wata y'ar budurwa wacce ba za ta wuce 13-14 years ba ta shigo d'akin sanye da uniform dark purple suit da skirt shi ma dark blue. Sai rigar ciki da ta kasance light purple. A jikin gaban suit d'in akwai logo na makaranta mai d'auke da tambarin makarantar da kuma logon su. Sai baby hijjab dai-dai wuyanta shi ma da ya kasance dark purple. Jakarta fashion mai kyau shi ma dark sagale a kafad'ar ta. Ba k'aramin kyau kayan su ka mata ba.
Tsaye ta yi a kan Binty da ke ta sharar bacci gaban rigar nan ya yi biji-biji da roman farfesun kazan da ta gama shi.
"What a beautiful creature!". Fad'in Fanan da ta d'an duk'o ta na shafa gashin kan Binty don ta tabbar shin na ta ne ko kuwa attachment a ka sa ka mata.
Murmushi Binty sabod mafarkin da ta ke yi ta re da mirginawa k'afarta ya sauka akan plate d'in da ta gama cin abincin.
Ita kuwa Fanan mutuwar tsaye ta yi saboda wa ni mugun kyau da murmushi nan ya k'ara fad'ad'a kyawun fuskanta sakamakon dimples d'in ta da ya lob'a.
Ko ma wa side d'in da ta juya Fanan ta yi ta re da tsugunnawa ta na kallon fuskan Binty.
"Ke kyakkyawa ce". Fanan d'in ta fad'a ta na tab'a kumatun ta in da ya lob'a.
"Idan kin ga ma k'are mata kallon, sai ki wuce ki je ki cire uniform ki yi wanka ki zo ki ci abinci". Fad'in Hajiya Na'ima da ta fito hannunta rik'e da waya ta na dannawa.
Ta shi Fanan ta yi ta re da isa wajan mahaifiyarta ta re da rungume ta ta ce,
"Anna I'm home". Fanan ta fad'a ta re da sakin Hajiya Na'ima ta mai da kallon ta izuwa ga Binty da har yanzu ke bacci ta ce,
"`D'un `b'ingum umoy'e? (Wa cece wancan?)".
"O inkesse mu'aiki. Unangai taimakima I aaki. (Sabuwar y'ar aiki ce, za ta rik'a taimaka maki da aiki.)".
"B'ingil gehil igillab'i. (Yarinyar kyakkyawa ce) muheb'b'i higo munangaimi labari imakko. (Na samu k'awar da za mu rik'a labari da ita). Anna gad'amu tu makaranta amin. Muhwalloimu to makaranta amil onni. (Anna ki saka ta a makarantar mu. Zan nu na wa y'an makarantar mu ita.)". Fad'in Fanan da harcan fulatanci.
"Ta wan nu muwad'aimu tu makaranta d'um, yahu itta ka ya ma d'a gara nyama abinci. (Kar ki da mu, zan sa ta a makaranta. Je ki can za ka ya ki zo ki ci abinci)". Fad'in Hajiya Na'ima da harshan fulatanci.
"Migodeki Anna imiyid'd'uma. (Nagode Anna ina son ki)".
"Mimma imiyid'd'uma Fanan. (Ni ma ina son ki Fanan)". Fad'in Hajiya Na'ima ta na murmushi ta re da jin k'aunar y'ar autar ta ta.
Ita kuma Fanan ta bi corridor ta wuce d'akin ta ta na jin dad'in sabuwar k'awa da aka kawo mata.
K'arisawa wajan da ta ke kwance Hajiya Na'ima ta yi ta re bubbuga k'afarta a hankali.
"Hadaan kai ne?". Binty ta fad'a ta re da bud'e idanuwanta a kan Hajiya Na'ima.
"Au ke ce? Ashe mafarki na ke yi". Fad'in Binty ta na mitsike idanuwan ta.
"Ki kira ni da Anna ba ke ba, kin ji?". Fad'in Hajiya Na'ima ta re da d'ago Bintyn ta tashi zaune.
"Anna fitsari na ke ji". Binty ta fad'a ta kamar za ta yi kuka.
"To ta shi mu je in kai ki d'akin Fanan sai ki yi a can har da wanka ta re da alwalama sai ki yi sallah kin ji". Hajiya Na'ima ta fad'i ta re da ruk'o hannun Binty su kai hanyar d'akin Fanan d'in.
Knocking Hajiya ta yi ta re da tura k'ofar ta shiga. Babu kowa a d'akin dai k'arar ruwa da ta ke ji daga bayin. Haka ne ya tabbar ma ta da Fanan d'in ta na ci ki ta fara wanka.
Binty kuwa sai bin d'akin ta ke da kallo da komai ya kasance baby pink. Ga hotunan Barbie nan a jikin bango da kuma manya manyan teddies nan a kan gad'on da shi kan shi pink colour ne har da zanin gad'on.
"Zauna a nan ki jira ta fito, sai ke ma ki Shiga ki yi wankan". Fad'in Hajiya Na'ima.
Ka min Binty ta ce wa ni abu Fanan ta bud'e k'ofar ta fito d'aure da towel a jikin ta. Zaro idanuwa Fanan ta yi cike da murna ta re da fad'in,
"Beauty kin tashi?". Ta fad'i hakane ta re da ka mo hannun Bintyn ta zaunar da ita a ba kin gado.
Binty kuwa mamaki ne ya kashe ta yadda kowa a nan garin ya san sunan ta.
"Hammu d'oho kullamu nu'uwatta amfani i`bayi, sai kukkama dirkaya ma d'a uwad'a. (Ga tanan ki koya mata yadda za ta yi amfani da ba yi. Sai ki ba ta daga cikin ka yan ki ta saka). Da ra mu had'a na mu gite o`juli. (Ki sa ka ma ta idanu tai sallah)". Fad'in Hajiya Na'ima cikin harshan fullanci.
"To Anna. Dussu du a`han, hunanga taka waliki? (D'aki na za ta rik'a kwana?)". Fanan ta fad'a ta na kallon Anna.
"Eh, d'an nangutun kawaliki tugu`u. (Eh a nan za ku rik'a kwana ta re)". Fad'in Hajiya Na'ima.
"Yauwa Anna, mihiggimmi. (Yauwa Anna haka na ke so)". Fad'in Fanan.
Har Hajiya Na'ima ta kai bakin k'ofa Fanan d'in ta sa ke cewa,
"Anna daga k'auye gard'a d'o? (Anna daga k'auye ta zo?)".
"Eh". Shi abunda Anna ta ce ta re da ficewa daga

Download complete TXT · Novel page