Showing 30001 words to 33000 words out of 120027 words
Chapter 11 - Halysaah Book 3 By Khaleesat Haydar
sai ta zauna gidan nan? What if I have my reasons for taking her away?" Gimbiya Firdausi tace "Kin ji ko Hajja? Ai in bai yi fitsara ya nuna ba a isa da shi ba bazai ji dadi ba, reasons dinsa na banza da hofi, ita din nace er gidan uban wacece da bazata zauna nan ba? Mu da muke jinin sarauta bamu ce baza mu zauna da ita ba sai ita da ba kowan kowa ba kowar wake? Who the hell is she? Wallahi kar ka bari in yi mugun saɓa maka a kasar nan idan kace zaka kawo min iskanci Ahmad, ni ba sauran iyayenka da ka raina bace yanxun nan zan gyara maka zama wallahi, kuma ka sanar mana er gidan uban wacece yarinyar da tafi karfin zama cikin mutane...." Ajay ya kalli Hajja yace "Saboda wata al'ada can idan ina bukatar matata sai in ki tafiya inda zan tafi da ita kenan? Al'adar ce ta haramta in kebe da ita if the need of that arise?" Kallonsa su Aunty suka dinga yi da mugun mamaki jin kalamansa, duk kowa yayi shiru a dakin kamar anyi ruwa an dauke, can Hajja ta gyara zama tace "To kun dai ji bukatar ta yake, yana bukatar matarsa a kusa da shi don haka sai ku hakura da mita kuma haka tun da ya bada uxurin sa, kin ga ba reason din banza da hofi bane kamar yanda kika ce ke Firdausi, yi tafiyar ka sai da safe Junaid, ga abinci nan ba ci zan yi ba sai ka tafi maku da shi, Allah ya tashe mu lafiya" Yace "Ameen, sai da safe" Mikewa yayi without looking at anybody ya dau warmer din abincin ya nufi kofa ya fita daga dakin, Hajja tace "Tun da bukatar ta yake kun ga ko ai baza a tauyesa ba saboda wani dalili mara tushe, ku bar su kawai su yi zaman su a can, yaran yanxu ba kunya gare su ba kun dai ga kansa tsaye ya bada uxurin sa, yana kuma da gaskiya, shi yasa nace da ba a gaya ma Sarki ba, gashi nan dai kun ga yafi mu gaskiya...." Gimbiya Firdausi tace "Da yake shi fitsararre ne mara kunya ba, ya kamata ya kalle mu ya gaya mana wannan magana idan ba raini ba? Idan Jawwad ne yaushe zai yi haka?" Hajiya A'isha tace "Ai Jawwad bazai ma taɓa dauke matarsa idan ana sha'ani ba balle ya kawo mana zancen rashin kunya" Gimbiya Firdausi tace "Da yake shi ya koshi da tarbiyya ba, kin taɓa ganin yana musu da na gaba da shi ko kuma ace yayi abu yace bazai yi ba shi ga yanda zai yi?" Hajja ta hade rai don no matter what ta tsani a dinga maganganu kan Ajay, tace "Don yace yana bukatar matarsa sai kuma ya zama abun magana? Haramun ya aikata? Babu warce tafi sa gaskiya akan wannan batu duk inda za aje kuwa, laifi ne don ya fadi uxurinsa da za ku dinga hadasa da Jawwad? Naga dai halinsu ba daya ba, in Jawwad ne ko uxurin zai kashesa bazai yi magana ba, shi kuma Junaid bai yarda ya cuci kansa ba, he speaks for himself always, don haka bana son in kara jin maganar Yarima ya dauke matarsa a gidan nan" Babu wanda ya sake cewa komai a dakin ko wacce ranta babu dadi tsabar takaici da bakin ciki, can Gimbiya Firdausi ta mike ta fice daga dakin, Aunty dai takaici sai da ya saukar mata da wani mugun migraine headache nan take a wajen, kalmomin Ajay sai yawo suke mata a kai, wai yana bukatar matarsa, abun har ya girmama haka bayan duk shige shigen da take a can Nigeria, sosai hankalinta yayi matukar tashi a wajen... Ajay na sauka downstairs ya tarar babu kowa parlor duk yan matan gidan na Bedroom a sama, kitchen ya nufa zai dau plate da spoon, shi ba cin abincin zai yi ba don ya sha shayi, Khaleesat zai kai ma idan taga zata ci duk da bai ma yi niyyar kai mata ba, yana shiga kitchen din ya tarar da Jay da Hadiyah makale da juna, within seconds suka yi separating, Ajay dai har ya juya ya fita daga kitchen din ya bar warmer din abincin a nan parlon tunda babu plate yayi tafiyarsa... After a while Aunty ta tashi ta fita daga dakin Hajja tana jin ciwon kanta na tsananta, dakin da Gimbiya Firdausi suke ciki ta nufa amma sai taji kamar suna magana da Hajiya Sumayya kasa kasa, har sai da ta kasa kunne jikin kofar dake bude slightly bayan ta tabbatar babu wanda ke tahowa daga downstairs sannan ta iya jin abinda suke cewa, Ta ji Gimbiya Firdausi na cewa "To ai naga alamar wankin hula na neman kai ni dare ne Sumayyah, ina ga a duk masarautar mu babu wanda ya kai ni ƙin auren yarinyar nan da Junaid, yau ace yarinyar nan tayi ciki ta haihu a masarautar nan shikenan magana ta kare kuma, kin ga idan Allah ya bata namiji Yarima ya samu Magaji kenan fa, wanda hakan na nufin wataran dole ɗan nan da zata haifa yayi sarauta, yaron da uwarsa ba kowa bace facce er matsiyata er talakawa mara asali, Sarki yaki fahimtar cewa yanzu ba a auro bare a shigo da ita gidan sarauta, an dena wannan gangancin, ga 'ya yan 'yan uwa kaca kaca da ya kamata ace ya aura ma Junaid daya kamar yanda Jawwad ya auri Hadiyah, sannan yarinyar nan fa Bazawara ce ba budurwa ba babban abun takaicin, Sumayyah har yanxu fa ban hakura batun sai Junaid ya auri Shahuda ba, yau ace Shahuda ta auri Junaid kin ga dai saurauta kara kusanto mu yayi ba nisa yayi mana ba...." Hajiya Sumayyah tace "Kwarai kuwa Gimbiya zancen ki hakkun, yanxu kamata yayi a tado da batun Shahuda gadan gadan idan mun koma gida, kin san dai kina daya daga mutanen da sarki ke jin maganar su, amma ki bari mu koma Nigeria sai mu tsara yanda za mu yi cikin tsanake, nasan kilishi ma baza ta rasa abinda zata ce ba akan lamarin nan don ita ma tana bakin ciki da wannan aure, nasan ita kanta zata kawo solution din matsalar nan" Gimbiya Firdausi tace "Haka ne, Allah ya maida mu gida lafiya" Hajiya Sumayyah tace "Ameen, ana wani cewa ai shi ma Junaid din bai san da auren ba sai bayan da aka daura, a yanxu kam na ƙaryata hakan, bana jin zanyi kaffara idan na rantse cewar Yarima na sane da shirin Sarki, sarai ya san da auren kuma alamu sun nuna yana son yarinyar shi ma, banda haka ki ga fa shigar yarinyar na yau, komai na jikinta designers ne tana er matsiyata da ita, kuma ba wai kayan cikin lefe ba, don kaf lefenta babu irin wannan kaya masu zunzurutun kudi haka, duk designers ne jikinta fa Gimbiya, da nayi estimating kudin shigar nan da tayi yau sai da nayi takaici, wallahi duk yanda za muyi ma dole mu yi a kawo karshenta a gidan nan don bata da ce da zama matar ɗan sarki me jiran Gado ba, Shahuda ce tayi deserving wannan matsayin ba ita ba" Gimbiya firdausi ta sauke wani nauyayyen ajiyar zuciya tace "Allah ya maida mu gida lafiya Sumayyah" Aunty tayi wani makirin murmushi bayan duk ta gama jin conversation dinsu tana gyada kai a hankali, a ranta kuwa tace "Sai dai in ni Hafsah bana numfashi ne za ku aiwatar da wannan nufi naku, amma baku isa ku wargaza min nawa shirin ba wallahi, Shahudar banza, ban gama da dayan nan dake gabana ba ku ke neman karo masa daya, gwara da aka yi akan kunne na, mu zuba da ku..." Juyawa Aunty tayi da sauri jin Footsteps, ta hango Jay yana haurowa sama hakan yasa ta bar bakin kofar da sauri, ta karasa har wajen stairs din kamar sauka zata yi, cikin nutsuwa tace "Jawwad yau ɗan uwanka ya shayar da mu ruwan mamaki" Jay dai kallonta yake yana haurowa don yasan Ajay take nufi, Aunty tace "Muna ta fadan bai kamata ya dauke matarsa ba bayan ba haka al'adar mu yake ba ya kamata ace ita ma tana gidan nan ayi komai da ita, buden bakinsa sai cewa yayi shi yana bukatar kebewa da ita ne shi yasa ya tafi da ita saboda uxurinsa, bai ji kunyan idanuwanmu ba ya fadi haka kansa tsaye, Hajja kuwa ta hadasa da Warmer din abinci tace sae da safe, is this proper Jawwad?" Jay dai bai ce komai ba yana tafiya slowly bayan yaji abinda Aunty tace.....
*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah, ur evidence 07087865788*
HALYSAAH PAGE 115
Khaleesat na zaune gefen gado Ajay ya shigo dakin Hotel din ta daga kai ta ɗan kallesa sai kuma ta sunkuyar da kanta tana ci gaba da danna wayarta alamar she is chatting, Ajay ya ajiye ledan abincin hannunsa ya nufi gaban madubin dakin ya tsaya yana cire wrist watch din hannunsa yana kallonta ta madubin, dai dai nan ta daga kai ta kallesa ganin he is backing her, hada ido suka yi ta madubin which she never expect don bata san yana kallonta ba, ta sauke idonta a hankali sai kuma tace "Good evening" Banza yayi mata kamar bai ji ba, ita dai ta ci gaba da danna wayarta bata sake dago kanta ba, ya ajiye agogon ya shiga bandaki, ta taɓe baki ta sauka daga kan gadon ta duba ledan da ya ajiye taga takeaway din abinci ne, dama yunwa take ji rabonta da abinci tun wanda ta ci around 11am na safe, kan kujeran dakin ta zauna tana bude abincin bayan ta ajiye bottle water da Gwangwanin lemon dake cikin ledan akan table, har ya idar da sallah bata gama cin abincin ba cause ta raba hankalinta tana cin abincin tana danna wayarta, daga karshe ta ajiye sauran abincin don ta koshi, ta saci kallon bangaren da yake dai dai sanda ya kashe wutan dakin yayi kwanciyarsa a kasa, hararansa ta dinga yi cikin duhun duk da ba ganinsa take ba, kawai zai kashe wuta bayan yaga bata gama abinda take ba, can ta taɓe baki ta hau saman gadon ta kwanta, da second bedsheet din kan gadon ta rufe har kanta ta ci gaba da Chatting dinta, babu haske kwata kwata a dakin sai na screen din wayarta da ta saka cikin bedsheet, bayan kusan awa daya ta ajiye wayar ta gyara kwanciyarta ta lumshe ido.... Can wajen karfe biyun dare ta farka ta fara laluban wayarta a inda ta ajiye kusa da ita zata je bandaki tayi fitsari, amma bata ga wayar ba, ta mike zaune tana laluba beside drawer nan ma bata ji alamar waya ba, sauka tayi daga kan gadon tana tafiya a hankali ta zaga ta inda switch din wutan dakin yake, being careful kar taje ta buge da wani abu, tumble ta kusa yi kansa yana zaune kan darduma ya turata daga gabansa, tana komawa baya a hankali kamar zata yi kuka tace "Ni switch din wuta zan kunna fa" Jin bai tanka ta ba ta mike tsaye, a haka ta laluba ta kunna wutan dakin ta juya ta kallesa, sai kuma ta kalli kan gado, mamakin yanda wayarta ya dawo tsakiyar gado ta fara yi bayan tasan kusa da ita ta ajiye kafin tayi bacci, taga ya mike ya ci gaba da sallan sa, ta fi minti daya tsaye tana kallon wayar, can ta shiga bandaki, tana fitowa ta hau saman gadon ta dau wayar ta bude Password din don akwai password jiki ta duba abinda zata duba sannan tayi kwanciyarta wondering how the phone changed position, juyawa tayi ta kallesa taga he is still praying, idan ma shi ya dauka ba accessing wayar zai iya yi ba because of the password, a haka bacci ya dauketa. Da asuba Khaleesat tayi mika ta bude idonta dai dai lokacin da take tashi yin Sallah, tsaye taga Ajay gaban mirror wearing just short yana goge gashin kansa alamar wanka yayi, hada ido suka yi ta madubin tayi saurin mayar da idonta ta rufe kamar warce taga mugun abu, kamar munafuka ta ja duvet din jikinta ta rufe har kanta da shi ta wani turo baki, she wish she can unsee that muscular body of his, har karfe shidda da yan mintuna bata yarda ta cire duvet din da ta rufe kanta ba gashi tana son tashi tayi sallah don tasan lokaci ya wuce amma ta kasa, ji tayi kamar ya bude kofar dakin hotel din, cikin dubara ta ɗan bude fuskarta tana lekowa ta duvet din taga fita yayi daga dakin, da sauri ta mike zaune ta cire duvet din jikinta ta sauka daga kan gadon ta daure gashinta sannan ta saka hularta ta wuce bandaki, ta idar da sallah tana cikin yin azkar dinta sai gashi ya shigo dakin, ita dai bata yarda ta daga kanta ba har ya wuce ta ya tafi ya zauna kan daya daga kujerun dake dakin ya dau wayarsa yana dubawa, ta idar da azkar dinta ta mike ta linke pray mat din ta ajiye sannan ta zauna gefen gado ba tare da ta cire Hijab din jikinta ba, satan kallonsa tayi tace "Ina kwana" Danna wayarsa kawai yake bai dago kansa ba balle ya amsa, ta turo baki ta kwanta edge din gadon ta juya masa ba, sai a sannan ya kalleta, dai dai nan aka yi knocking kofar dakin ya mike ya nufi kofar ya bude, ya amshi tray din Hot coffee da Croissant daga hannun daya daga ma'aikatan hotel din sannan ya kulle kofar ya koma inda yake zaune ya zauna ya ajiye tray din kan table. Cikin minti ashirin Khaleesat ta gama shirin da take ta dau jakarta bayan ta saka takalmi ta tsaya gaban madubi tana kallon kanta, sai taga kamar kayan ma yafi na jiya kyau, yau ma dai she look expensively beautiful, kamar dai jiya yau din ma designers ne kaf jikinta, kayan yayi mata mugun kyau ba kadan ba, juyawa tayi ta nufi kofa ta fita daga dakin hotel din, yana tsaye jikin Taxi yana jiranta ta fito, tun da suka hada ido ta sauke nata idon ta bude motar ta shiga, after some seconds ya dauke idonsa daga kanta ya bude gaban motar ya shiga, Drivern taxi din ya ja motar suka bar wajen, tun da Khaleesat ta lura da inda za su je gabanta ke faduwa don sarai ta gane unguwan, Taxi din na parking gaban apartment din Ajay ya bude motar ya sauka, a hankali ita ma ta bude motar ta sauka ta bi bayansa walking slowly, bell ya danna don kofar a kulle yake, Iklima ce ta bude kofar ganinsu ta koma gefe without much attention tace "Sannu da zuwa yaya" Bai ce mata komai ba ya shiga parlon, Khaleesat ta bi bayansa ba tare da ta yarda ta hada ido da Iklima da ta bi ta da ido tana kare ma dressing dinta kallo ba, juyawa yayi yana kallon Iklima fuska daure yace "Ke baki iya gaisuwa bane don uwarki?" Tayi yake tana sosai kai tace "Lahh yaya nace fa sannu da zuwa" Sai kuma ta kalli Khaleesat tace "Ohh sannu da zuwa" Khaleesat dai bata kalleta ba tace "Yauwa nagode" Cire takalmanta tayi ta bi bayan Ajay tana tafiya a hankali har suka karasa cikin parlon, Iklima ta bi ta da wani shegen kallo, Gimbiya Firdausi ce zaune parlon da Yayar mahaifin Hadiyah Hajiya Shema'u sai Hajiya Sumayya, Ajay ya gaishesu gaba daya, Hajiya Shema'u ce kadai ta amsa masa da kyau, Khaleesat ma ta gaishesu nan ma ita kadai ce ta bata attention dinta, Hajiyah Shema'u na kallon Ajay tace "Ita ce matar taka, da yake jiya bana jin dadi da wuri na bar Convocation arena din bamu hadu da ku a can ba" Ajay yace "Ya jikin yanxu?" Tace "Na ji sauki Alhamdulillah" Kallon Khaleesat tayi tace "Maa sha Allah amarya, Allah Ubangiji ya baku zaman lafiya, ki zauna lafiya da mijin ki kin ji, yi kin yi bari kin bari kin ji, kuma ki zama mai hakuri da kauda kai, Allah Ubangiji ya zaunar da ku lafiya ya baku zuri'a dayyaba" Khaleesat dai ta sunkuyar da kanta without saying a word tana wasa da veil dinta, Hajiya Sumayya kuwa sai kallon kayan jikinta take da jakar hannunta, Ajay ya kalli Hajiya Shema'u yace "Za mu je wajen Hajja a sama" Hajiya Shema'u tace "Toh sai kun sakko" Mikewa yayi ya bar parlon, Khaleesat na ganin haka ita ma ta tashi ta bi bayansa suka nufi stairs, Gimbiya Firdausi ta bi su da kallon gefen ido har suka haura sama, Ajay ya bude kofar dakin da Hajja ke ciki ya shiga Khaleesat na biye da shi, Hajja na zaune dakin tare da Hadiyah da duk yan matan gidan sai Hajiya A'isha, Khaleesat ta zauna kasan carpet kanta a kasa, Ajay ya zauna kan kujera ya gaida Hajja da Hajiya A'isha, sauran yan matan duk suka gaishesa ya amsa masu a takaice, Hajja ce kadai ta amsa gaisuwar Khaleesat a dakin, sannan ta kalli yan matan dakin tace "Ba ku ga matar yayanku bane?" Dukansu suka kalli Khaleesat kamar sun ga bola, shi dai Ajay daya bayan daya yake bin su da kallo, a walakance duk suka gaisheta banda Hadiyah da ta hade rai tun shigowar Khaleesat barin da taga handbag din dake hannunta da rigar jikinta, Shahuda kuwa danna wayarta kawai take kamar bata san Allah yayi ruwan Khaleesat a dakin ba, Khaleesat dai ta amsa gaisuwar su Khadijah tana ɗan murmushi jikinta a sanyaye, ita kanta tasan ba karamin gata Ajay yayi mata ba na dauketa a gidan nan, she felt really grateful da hakan da yayi mata, don kilan da bai dauketa ba tsaf zata samu heart attack kafin su bar kasar, sam bata ga alamar mutunci da daraja a gun yan matan gaba dayansu ba, as if they have grudges against her from anywhere, daga su har iyayensu ita kam