Showing 39001 words to 42000 words out of 120027 words
Chapter 14 - Halysaah Book 3 By Khaleesat Haydar
saboda kayan baccinta, bandakinsa ta shiga tana kallon farin towel dinsa da ta shanya, can ta dauka ta fito, duk da yanda gabanta ke faduwa haka ta dora towel din a kirjinta tana tafiya kamar mara gaskiya ta fita parlor, da mamaki Ajay ya bi ta da kallo babu ko kiftawa ganin yanda ta maida masa daki public room, ita kuwa taki yarda ta kallesa ta nufi kofar fita daga parlon da sauri gabanta na faduwa, a haka har ta fice daga parlon, tana isa corridor ta hango legend downstairs yana zarya a parlor, duk da bai ganta ba haka ta kwasa a dari da sittin kamar mahaukaciya ta koma part din Ajay tana shiga parlon ta nufesa da gudu ta zauna kusa da shi cikin gigicewa tace "Wallahi i saw it" Sai kuma ta fashe da kuka kamar er yarinya tana kallonsa, shi dai kallo daya yayi mata ya dauke kai don ba tare da towel din ta dawo parlon ba, ita kanta bata san ta gantalar da towel din a wajen gudu ba, ganin yaki kulata ta mike zata wuce dakinsa ya bi ta da kallo, within few seconds ya dauke idonsa ya maida wani direction daban after seeing what he wasn't prepared to see, Sai da Khaleesat ta koma cikin dakinsa ta hango kanta ta madubi ta zaro ido with shock ganin babu towel a jikinta, ta tafi edge din gado ta zauna da sauri tana zumburo baki, after 10 mins ya bude kofar dakin ya jefa mata hijab din hannunsa without looking at her ya juya ya bar wajen.... Bayan ta idar da sallah ta gama azkar dinta sannan ta kalli wayarsa dake ajiye kan bedside drawer, mikewa tayi ta tafi ta dau wayar da sauri ta duba taga babu Password jiki ta koma kan darduma ta zauna ta bude wayar ta shiga call logs dinsa, kallon yanda yayi saving numberta ta dinga yi babu ko kiftawa, can ta wani tura baki ta fara scrolling taga uban miss calls din da tayi masa and it is not as if baya picking sauran calls dinsa, nata ne kawai baya picking, ta hade rai ta shiga WhatsApp dinsa, taga last messages da aka turo masa was from yesterday night alamar rabonsa da bude data tun jiya da daddare, tayi searching contact dinta sai gashi ya fito, ta shiga ciki, babu ko kiftawa ta dinga kallon screen din wayar ganin blocking dinta yayi ta WhatsApp din ashe, after some seconds ta kunna data dinsa messages dinsa duk suka shigo, wani number da taga anyi saving da Pinky ta bude message din da aka turo tun karfe biyun dare taga an rubuto "Good Morning Aristocrat, hope u slept well, jiya nayi bacci sanda ka kira, idan na dawo school zan kira direct call, have a nice day, bye" Khaleesat ta maimaita message din a zuciyarta yayi sau uku, ta kalli WhatsApp call da yayi ma number wajen karfe takwas na daren jiya, scrolling chat dinsu ta dinga yi tana karantawa, har sai da ta kai dai dai inda aka turo masa hotunan Birthday tana duba hoton taga Inteesar ce, ta dinga kallon hoton for almost a minute, sai kuma ta ci gaba da scrolling chat din nasu, bude kofar dakin aka yi tayi saurin cusa wayar cikin hijab dinta tayi keeping straight face tana kallon wani wajen daban, ko kallonta bai yi ba ya tafi zai dau wayarsa inda ya ajiye amma yaga babu wayar a nan, tana ganin haka tayi dubara ta cusa wayar a kirjinta don rigar baccin jikinta na da tight-fitting daga chest dinta, Yana ta tsaye for like 15 seconds yana kallon wajen da yasan ya ajiye wayarsa, can ya kalli other side din nan ma bai ga wayar ba, ita dai Khaleesat taki yarda ta kallesa fuskarta a daure, ya juya ya fita daga dakin zai duba parlor duk da shi dai yasan wayar a bedroom dinsa ya bar sa, amma ya gama duba parlon gaba daya bai ga wayar ba, har kasa sai da ya sauka yana duba wayar, can dai ya dau other phone dinsa yayi dialing number wayar, Khaleesat na jin vibration din wayar a kirjinta don ma it's very low amma bata fito da wayar ba, bayan minti goma sai gashi ya dawo dakin yana mata wani kallo yace "Bani wayata kar in sa ki kuka yanxun nan" Tayi kamar bata san da ita yake ba don ko kallon inda yake tsaye taki yi, bude kofar dakin yayi sosai yana kallon parlor ya ɗaga murya yace "Hey Legend" Wani uban tsalle ta doka sai ga ta kusa da shi tana zaro ido a tsorace tace "Don girman Allah kayi hakuri, wallahi zan baka" Ya daure fuska yace "Bani" Sai ga Legend ya shigo parlon da gudu wai har yaji kiran da yayi masa, Khaleesat ta kurma ihu ta makale gefen Ajay tana rirrikesa cikin rawan jiki tace "Don girman Allah kace ya tafi wallahi zan baka, send it away plsss" Ajay ya tura kofar dakin slightly, ya juya yana kallonta yace "Where is it?" Ɗaga hijab dinta tayi da sauri tana zaro ido zata ciro wayar ya dinga kallon kirjin nata, tana ganin haka ta hade rai ta sake hijab din ta juya masa baya taki ciro wayar, bata ankara ba sai ji tayi ya fara fixge hijab din ta bayanta, ta rike da sauri tana zaro ido taki bari ya cire tana cewa "Nooo, don Allah ka tsaya zan baka wallahi" Kokuwa ta fara yi da shi taki yarda ya cire mata hijab din ganin da gaske cirewa zai yi, Legend ya ɗan leko dakin saboda noise din da yake ji, Khaleesat na ganinsa da karfi tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Ajay ya ɗagata sama da hannu daya ya tafi yayi dumbing dinta kan gado ta kwanta tana jawo duvet dinsa da sauri zata rufa da shi, kwace duvet din yayi sannan ya fixge hijab din gaba daya daga jikinta yana kallon chest dinta da ta cusa wayarsa, dama tana ganin Legend a bakin kofa ko yunkurin hanasa cire hijab din bata sake yi ba sai ma jawosa da take yi cikin tsoro tana son ya boye ta tana cewa "Plss send it away, shigowa zai yi, don Allah ka koresa" tsit tayi ganin ya fado kanta kawai daga jawosa, ta kasa kwakkwaran motsi don ji tayi kamar duk weight dinsa ya sakar mata, nan ta fara turasa da kyar tana zaro ido don ko magana ta kasa, amma kamar tana tura Rock don ko gezau, da wata irin muryar da bata san sa da shi ba yana kallonta directly in the eyes yace "Me kika yi da wayata?" Tana numfashi da kyar tace "Wallahi ba komai, ka duba ka gani" kawai ji tayi ya zura hannunsa ta kasan rigar jikinta a hankali, ta zaro ido cikin gigicewa bata san sanda ta kankamesa ba don sai taji kamar an hadata da naked electric wire cikin rawan murya tace "Na shiga uku, ba ta nan yake ba wallahi yaya, ka tsaya in ciro da kaina plss" ashe all this while ba duk weight dinsa ya sakar mata ba don tana kankamesa yayi collapsing gaba daya a kanta, hakan kuma bai hanasa kutsa hannunsa dake cikin rigarta har zuwa saman kirjinta ba, she couldn't even react any more tsabar wani irin shock da taji a ko wani gaɓa na jikinta jin hannunsa a plain chest dinta yana fondling dinsa gently, tuni salon numfashinsa ya canza taji lips dinsa na bin wuyanta yana sauke wani ajiyar zuciya, bakinta; na rawa ta hade laps dinta tace "Plsss i want to use the restroom, ga wayarka na cire maka wallahi, i want to pee plsss" abubuwa da yawa suka yi mugun tsorata Khaleesat a wannan lokacin don ko Abdul bata ji masa irin wannan tsoron ba, cikin rikicewa take ta ce masa zata je tayi fitsari duk tunaninta baya jin ta ne, cikin wata muryar da bata san sa da shi ba me kama da rada taji yace "Yi a nan"
HALYSAAH PAGE 119
Mikewa Hadiyah tayi ta nufi kofa ta fita daga dakin Hajja fuskarta babu walwala kwata kwata, Ajay ya bi ta da kallon gefen ido, dakin da Umminta take ta tafi, ta sameta ita kadai tana waya da Abbanta, zaunawa tayi har Ummi ta gama wayar tana kallonta da damuwa tace "Ya aka yi daughter? An maki wani abu ne?" Hadiyah ta kalleta fuskarta a daure tace "Ummi ta yaya wannan er iskar zata zo Convocation dina ta dinga yawo da designers? Jakan hannunta na yau ma fa designer ne haka ma na jiya, sai da na gaya ma Ya Jawwad shekaranjiya mu je inyi shopping jaka da takalmi for my Convocation kamar nasan abinda zai faru kenan amma yace min wai ya gaji i should use the one of my lefe bayan an gama Convocation din sai mu je ya siya mun wanda nake so, yanxu gashi wannan matsiyaciyar ta zo sai flaunting designers take making me look miserable ni da occasion dina, 3 of my friends fa sai da suka kirani daxu da safe wai they wants to be friends with her don Allah in hadasu da ita, basu san er talakawa bace matsiyaciya luck ne kawai ya kawota gidan sarauta, ni ko nace masu nima ban san daga inda take ba, uninvited guess ce" Ummi dake ta kallon Hadiyah cikin bacin rai tace "To ke da yace ya gaji baza ki takura masa ba, banda iskanci ma me yayi na gajiya sai kace wanda yayi dako? Baki ji nima yanda raina ya ɓaci ba jiya da na ga yarinyar, dama ashe ita Jawwad din yace sai ya aura?" Hadiyah ta hade rai tace "Don Allah ki dena cewa haka Ummi, wannan ai ya zama past tense, bana ma son Ina tunawa, my problem now is the type of bags and shoes and even clothe she is wearing, hatta jewelries dinta fa me tsada ne sosai Ummi, me yasa shigarta zai fi nawa?" Ummi ta daure fuska tace "Ki kirasa yanxu kice masa ke lallai lallai yau kike son ku je ku yi shopping din nan, go and dress up and call him immediately, tana matsiyaciyarta uban me zata nuna maki? abinda ma gidan da uwarta da Ubanta ke ciki Jawwad din ne ya siya, daga baya bayan nan kuma muke samun labarin hatta kudin makarantar ta da kudin hayan gidan da take a Amurka Jawwad ke biya ashe" Hadiyah ta bude baki tana kallon uwarta with shock tace "Don Allah da gaske Ummi? Is this how poor and wretched they are?" Ummi tace "Ba shi yasa Mami ta gigice ba ta fita hayyacinta sai da tasan yanda ta bi ta rusa auren sannan hankalinta ya kwanta, nima kuma daga bangarena ban zauna ba ina ta yin nawa abun na ganin auren bai yiwu ba, shi ne don tsiya shi kuma Mai martaba ya maida aure kan Junaid, Oho dai shi ya sani, amma Allah ya sani ni har yau da Junaid na so ki ba Jawwad ba cause Junaid is the Heir to the throne not Jawwad, I want nothing but the best for you, kema ki gaji kakarki ki zama Sarauniya watarana, amma hakan bai yiwu ba" Hadiyah ta wani kalli Ummi tace "To ni me zan yi da wanda yace baya so na Ummi, beside i love Ya Jawwad soo Much, ni shi nake so ba Junaid ba" Ummi ta taɓe baki tace "Amma dai ai ba haka aka so ba wai kanin miji yafi miji, Gobe za mu je Sheffield tare da Hajiya Shema'u wajen yarinyar ta Basira kinsan bata da lafiya, yanxu yaushe Jawwad din yace za ku koma Nigeria?" Hadiyah ta girgiza kai tace "Bai gaya min sanda za mu koma ba" Ummi tayi kasa da murya tace "Toh ban san kwana nawa za mu yi a can Sheffield din ba, ita kuma Fulani Hafsat naji tana cewa za su je America ban san me zata yi a can ba, kinga kenan duk watsewa za mu yi, to yanxu zan baki sakon da nace zan baki in case bamu hadu ba kun tafi Nigeria" Mikewa Ummi tayi ta kulle kofar dakin da makulli ta tafi gun akwatinta ta bude ta fito da kayanta daya bayan daya daga cikin akwatin sannan ta ciro wani zani da ta nannade wata leda a ciki, sai kuma wani babban ledan daban shi ma ta ciro a akwatin ta dawo kusa da Hadiyah ta zauna ta bude ledan farko ta fara ciro kullin magunguna da wasu kwalabe kanana, sai kuma tayi kasa da murya tace "Da kin san uban kudaden da na kashe kan su wallahi baza ki yi wasa wajen yin amfani da su ba Hadiyah, and it's for ur own good not mine, idan kika yi shashanci wajen amfani da su wallahi kanki za ki yi ma, jajircewa za ki yi kiyi duk yanda aka ce...." Hadiyah tace "Me zai hana ni amfani da su Ummi" Ummi tace "Ko wanne da takarda a ciki na rubuta yanda zaki yi amfani da shi" Hadiyah tace "To, kin ma san me Ummi komai sai ya ce Maminsa abun nan ya fara bani haushi wallahi, why always her? gashi ita ma bini bini ta kirasa a waya ko muna tare, she always have one or two things to speak to him about ni kuma na tsani haka, ko kuma idan yaje bangarenta sai ya dade bai fito ba wani lokacin har minti ashirin yana yi wallahi, kafin fa mu zo convocation din nan har na dena zuwa bangarenta in gaisheta nayi pretending bani da lafiya don haushi take bani wallahi yanxu, ko wani abun dadi ya siyo min ita ma sai ya siyo mata ya kai mata fa kamar wata kishiyata" Ummi ta hade rai tace "To ke uban me yasa zaki dora ma kanki dinga zuwa bangarenta gaisheta? Wa yace maki ana wannan haukan? To kuna komawa gida kiyi cutting din zuwa wannan gaisuwan in kun hadu cikin gida ki gaisheta amma kar ki sake zuwa part dinta, ita sanda aka aurota ko da yaushe take zuwa gaida Hajja ba sai ta ga dama ba?? sannan ki kwantar da hankalin ki wataran in ance yace Mamin ma haushi zai ji, kar ki wani damu, yanxu dai ki bi wannan magungunan step by step babu mistake, shi yasa ma duk na rubuta maki a takarda kuma wallahi ba karamin kudi na kashe ba use them wisely" Hadiyah na murmushi tace "In sha Allahu zan yi using dinsu yanda aka ce Ummi" Ummi tace "Kwanaki kika ce ma yarinyar kanwar babanki you are in pain always during intimacy, har yanxu hakan ne?" Shiru Hadiyah tayi, sai kuma ta sauke kanta, Ummi ta hade rai tace "In zaki bude baki ki min magana ki bude baki, kunyar me zaki ji, ko kina da wata uwar bayan ni ne? Duk wani abu da ya dameki talk to me, ba sai ma kin je kina magana da kowa ba kina tona asirin kanki, I know you are confuse shi yasa kika ma Marwana magana, but I am always there for you my sweetheart, Kar ki ji komai koma menene ki dinga gaya min, I am ur mother and also ur best friend, isn't this how I brought u up?" Hadiyah da ke ta tunanin irin azaban da ta sha during those period duk da ita ce tayi ta shige masa lokacin har komai ya faru, after that kuma yaki daga mata kafa, ta girgiza kai a hankali tace "A'a na dena ji yanxu Ummi" Ummi tace "Good, dama it's just for a while, it's always like that for every woman" Daya ledan Ummi ta jawo wanda ke dauke da authentic magungunan mata masu kudin gaske, nan ta dinga nuna mata su da yanda zata yi using dinsu daya bayan daya, bayan ta gama nuna mata ta ajiye ledan tace "To ita Mamin na zuwa bangaren ki ne?" Hadiyah ta taɓe baki tace "A'a, kawai sanda na dena zuwa gaisheta ne da yace mata bani da lafiya shine ta ke shigowa ta dubani kuma pretending kawai nake yi don lafiyata qlau, ko fita zata yi fa wani lokacin sai tace ya kai ta sai kace wani driver dinta, so annoying, wani lokacin sai ki ga ta sa shi yayi transferring huge amount of money for her businesses, kuma ko musu baya yi mata" Ummi tace "Don't worry, all that nonsense will come to and end soon, yayi resuming aiki asibiti ne?" Hadiyah tace "A'a sai mun koma zai yi resuming fully" Ummi tace "To yanxu ina zaki boye kayan nan kar wani ya gani?" Hadiyah tace "Cikin kayana mana Ummi" Ummi tace "Bazai ce zai bude maki akwatin ba?" Hadiyah tace "A'a, can kasan akwatin zan ajiyesa babu wanda zai gani" Ummi ta sake nannade mata ledan da zaninta, kayan matan ma ta kulle ledansa da kyau ta nannadesa da wani zanin sannan tace "A haka za ki saka su a karkashin akwatin, sannan ki kirasa kice ke shopping kawai zai kai ki, and you make sure duk abinda zaki dauka ya zamto designer ne a wajen" Hadiyah tace "Toh Ummi" Ummi tace "Amma dai je ki dauko akwatin naki, kar kije can dakin gantalallun ya matan can su saka maki ido" Hadiyah tace "Eh haka ma zai fi" Mikewa tayi ta nufi kofa ta bude ta tafi dakin da suke ita da cousins dinta ta dau akwatin ta zata fita, Iklima na kallonta tace "Can apartment din zaki koma ne Hadiyah?" Hadiyah ta yatsine fuska tace "A'a gyara kayan zan yi kawai" Daga haka ta fita ta koma dakin da uwarta take da akwatin nata. Khaleesat ta ɗaga kai ta kalli Baby da ta shigo dakin Hajja, Baby ta wara ido ta nufeta tace "Waow, kin yi kyau yau ma Aunty, I love your handbag, it's soo cute" Tana fadin haka ta dauki jakar tana jujjuyawa with admiration, Khaleesat ta ɗan yi murmushi tace "Kina so ne?" Baby tace "Sure ina son irin sa" Khaleesat