Showing 42001 words to 45000 words out of 120027 words
Chapter 15 - Halysaah Book 3 By Khaleesat Haydar
ta amshi jakar daga hannunta ta bude ta ciro wayarta dake ciki sannan ta mayar mata tana murmushi tace "To na baki" Ajay ya daga kai ya kalleta, ita dai taki yarda ta kalli inda yake zaune, Shahuda da Maryam dake dakin su ma sai da suka daga kai suna kallon Khaleesat, Baby kuwa har da tsallenta bayan ta amshi jakar tayi ma Khaleesat side hug tace "Thank you so much" Sai kuma ta nufi Ajay ta zauna gefensa tana nuna masa jakar tace "Yaya look, she just dashed me the bag" Ajay yace "Kin gode" Hajja tace "Ke haka ake yi Baby? Baki ga wayarta bane a cikin jakar?" Baby ta tura baki tana kallon Hajja tace "Ai dai tace ta bani kuma kin ji" Daga haka ta mike ta fita daga dakin looking so happy, Shahuda ta mike ta fice daga dakin, Hajja ta kalli Khaleesat tace "Ke kuma ai ba haka ake ba Jiddah ya za ki zo da abu tace tana so ke kuma ki dauka ki bata bayan kema amfani da shi kike, kamata yayi in ma zaki bata sai ko a gida amma ba a nan ba, kar ki sake yin haka" Khaleesat dai murmushi kawai tayi bata ce komai ba tana wasa da fingers dinta, Maryam ta tashi ita ma ta fita daga dakin cike da mamakin Khaleesat, wato ita ga ta isassa saboda ta nuna masu designers ba komai bane a wajenta idan tana son wani ma Ajay zai siya mata shi yasa ta kyautar da jakar a gabansu su gani, a stairs Baby ta hadu da Jay cikin farin ciki tana nuna masa jakar tace "Ya Jawwad look, matar ya Ajay ta bani jakar nan kyauta" Jay ya kalli jakar yace "Ohk... kin gode, is Hajja sleeping?" Ta girgiza kai tace "A'a tana zaune" Dakin ya nufa ita kuma ta sauka downstairs zata je nuna ma uwarta, Jay na shiga dakin suka hada ido da Ajay, shi ya fara dauke kansa ya karasa cikin dakin ya zauna, Khaleesat dai sai kallonsa take, Jay ya gaida Hajja, Hajja ta amsa tace "Duk yau baka shigo ba Jawwad ko kana can kana sana'ar" Calmly Jay yace "Eh bacci nayi" Hajja tace "Dama na fada, tunda naga baka shigo ba nace kana can kana ba bacci hakkinsa, to ka dai ci abinci ko?" Yace "Na ci" Mikewa Ajay yayi ya nufi kofa ya fita daga dakin, Hajja ta bi sa da kallo.
*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah, ur evidence via 07087865788*
HALYSAAH PAGE 120...
Wajen karfe shidda da yan mintuna na yamma Ajay ya shigo dakin Hajja, har sannan Khaleesat na zaune dakin tana danna wayarta ko nan da can bata fita ba, inda Allah ya taimaketa Hajja na dakin all through ita ma ba fita take ba, wannan yasa Hadiyah da cousins dinta sai dai su shigo su harareta su fita babu me ce mata uffan sai kallon banza, Walid ma yayi shigowa yafi goma zuwa dakin amma duk ya shigo zai tarar da Hajja zaune sai dai yayi ma Khaleesat kallon kasa kasa ya fita daga dakin, su Aunty da Gimbiya Firdausi kuwa sun ma ki shigowa dakin tun zuwan Khaleesat gidan, duk da ba hira Khaleesat suke da Hajja ba amma she prefer it that way akan a bar ta da su Hadiyah ko su Aunty ko Walid don kam ba karamin taimako rashin fitan Hajja daga dakin yayi mata ba, a yanda ta lura duk yan matan gidan cike suke da ita kuma akwai magana a bakinsu amma ba dama saboda Hajja, jifa jifa Baby ke shigowa dakin da duk wani abu na dadi in dai ta ci to sai ta kawo ma Khaleesat tunda ta bata kyautan Handbag, in kuma ta shigo dakin sai ta cikata da surutu kafin ta fita, tun da Ajay ya shigo dakin Hajja ke bin sa da kallo tana jin ranta babu dadi, gashi sam baka gane inda ya dosa da mood dinsa, kullum a haka yake baza kace yau yana cikin farin ciki ba ko kuma akasin haka, baka gane walwalarsa da rashin walwalarsa, baka gane damuwarsa da akasin hakan, if you are lucky to see him laughing or vibing probably you met him sitted together with Jay back then, Khaleesat dai taki kallon inda yake sai danna wayarta take, yana kallon Hajja daga inda yake tsaye yace "Sai da safe Hajja, I am leaving" Hajja ta sauke boyayyen ajiyar zuciya tace "A tsaye zaka min sallaman kuma Ahmad?" Bai dai ce mata komai ba, after some seconds ya karasa cikin parlon ya zauna, tace "To abinci fa Junaid? Me zaka ci?" Yace "Ke komai abinci, to na koshi" Hajja tace "To ai shikenan, Allah ya tashe mu lafiya" Yace "Probably zan koma Maryland gobe in sha Allah" Hajja tace "Gobe kuma? Ai nayi tunanin kuna nan har weekend" Ajay yace "In zauna inyi me a England har weekend" Hajja tace "Daxu naji Hafsat na cewa za su je can Maryland din ita da Gimbiya Firdausi, ban san me za su je yi can din ba" Ajay dai kallon Hajja kawai yake jin abinda tace, Can ya mike yace "Alright, Good night" Hajja tace "To Allah ya tashe mu lafiya, amma dai ba sallaman kenan ba ko, ya kamata goben ku zo ku yi ma iyayenka sallama tunda basu san za ku tafi ba" Ajay yace "Ohk" Hajja ta kalli Khaleesat tace "Toh sai da safe Jiddah, a baki abincin ki tafi da shi ne?" Duk da yunwa Khaleesat ke ji don bata wani ci abincin daxu da Hajja ta zuba mata ba amma ta girgiza kai kawai tana ɗan murmushi tace "A'a na koshi Hajja, Nagode" Hajja tace "To Allah ya tashe mu" Tuni Ajay ya fita daga dakin Hajja, Khaleesat tayi ma Hajja sallama sannan ta bi bayansa tana tafiya a hankali cikin sanyin jiki, Hajja ta bi ta da kallo har ta fita, babu abinda Hajja tace mata akan yanda suka samesu ita da Jawwad daxu don tasan shi ya kamata tayi ma magana tunda ya fita hankali not her, sam bata ji Khaleesat ta kwanta mata a rai ba har yanxu amma kuma bazata iya walakanta ta ba... Tun da Khaleesat taji Hajja tace su Aunty za su je Maryland jikinta yayi sanyi sosai ba kadan ba, har cikin ranta tsoron Aunty take ita kam, ga ita ma Gimbiya Firdausin taga idan ta gaisheta bata amsa mata gaisuwarta, infact tsoron duk family din ma take ita, da kyar take jan kafa tana biye da Ajay har suka isa parlor, babu kowa a parlon har ma da gidan baki daya don Hajiya A'isha da Ummi da Mami sun tafi daya apartment din wajen Hajiya Shema'u Yayar Baban Hadiyah, Gimbiya Firdausi da Aunty kuwa sun fita zuwa gidan wata kawar Gimbiya Firdausi dake England ita ma, Hajiya Nafisah a safiyar yau ta koma Nigeria saboda wani uxurin ta, ita dai Khaleesat na biye da Ajay suka fita daga apartment din, ko juyawa bai yi ba balle yasan tana biye da shi ko akasin haka, ya bude gaban taxi din dake gaban apartment din ya shiga, a hankali ta bude back seat din motar ta shiga ita ma, driver ya ja motar suka bar wajen. Tun da suka shigo hotel room din Khaleesat ke zaune gefen gado tana danna wayarta, tana kallo ya shiga banɗaki ya dauro alwala ya fito don lokacin Magrib yayi, hakan yasa ta ajiye wayarta taje tayi alwalan ita ma ta fito, kamar yasan abinda zata yi bai tada sallah ba har ta fito, tana dauko pray mat zata shimfida a bayansa ya juya ya kalleta fuska daure yace "Fita a bayana" Kallonsa ta tsaya yi, cikin tawa yace "Ko baki ji abinda nace ba?" Juyawa tayi ta bar wajen, ya tada sallahn sa, ta turo baki ta tafi ta zauna gefen gado tana hararansa, yana idar da sallahn bayan kusan minti goma ya mike daga saman darduman alamar ya gama azkar ya fice daga dakin, sai a sannan ta mike ta tada nata sallan, ko da ta idar kayan baccinta ta dauka ta shiga bandaki tayi wanka ta canza kayan a ciki sannan ta fito taga bai dawo dakin ba har lkcn, a haka lokacin sallan isha'i yayi ta mike don yin sallan, har karfe goma Ajay bai shigo dakin ba gashi yunwa take ji, tana kwance edge din gado suna chatting da Sophie da yarinyar Hajiya Zaliha ya shigo dakin, ita dai bata daga kai ta kallesa ba har sai da ya wuce ta sannan ta bi sa da kallo taga ya canza kaya, which shows daga gida yake kenan, kashe wutan dakin taga yayi sannan yayi kwanciyarsa a inda yake kwantawa, ta kalli direction dinsa cikin duhun duk da ba ganinsa take yi ba, tura baki tayi tace "To ni bazan ci abinci ba?" Taji yayi mata banza, after some minutes kamar zata yi kuka tace "Ka ji...." Nan ma bai kulata ba, kawai ta ci gaba da danna wayarta, bayan kusan minti sha biyar ta kashe data din ta ajiye wayar ta hau kan gadon ta rarrafa can daya side dinsa tana kallon ƙasa duk da ba wani ganinsa take sosai ba, kamar zata yi kuka a hankali tace "Ni fa yunwa nake ji wallahi" Still dai bai kulata ba, ta ɗan duka closer to him tana kallonsa cikin duhun tace "Ka ji mana" Cikin kakkausar murya yace "I will give you a dirty slap idan ba ki dena damuna zan yi bacci ba, uban me ya hanaki amsan abincin a can gida" Shiru tayi don sai da ya bata tsoro da intonation din da yayi using, bata ma san sa da irin tone din ba, after a while ta koma inda take kwanciya a hankali ta kwanta ta rufe kanta da duvet tana goge hawayen da ya kawo idonta, after almost 30 mins ta gama juye juyenta bacci ya dauketa. Cikin bacci Khaleesat taji an sauke duvet din da ta rufe kanta da shi, firgita tayi sosai ba kadan ba ta fara kokarin mikewa zaune tana komawa baya tace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un...." Tun da Walid yayi mata haka to tana jin an taɓa duvet dinta komin nauyin baccin da take sai ta firgita don scenario din ne ke dawo mata, kunna wutan dakin yayi yana kallonta, ta sunkuyar da kanta kamar zata yi kuka ta dau hularta tana cusa gashinta ciki a hankali tace "Tsoro na ji" Ya mata wani kallo yace "Tunda baki da gaskiya dama me yasa baza ki ji tsoro ba" Yana fadin haka ya juya ya bar wajen ta bi sa da kallo, Sleeping mask dinsa taga ya dauka, ta juya tana kallon paper bag dake ajiye bedside drawer kusa da ita saboda aroma din abinci da taji, wayarta ta jawo ta duba agogo taga karfe sha biyu saura few minutes, ta ajiye wayar ta bude paper bag din taga takeaway din abinci ne ya siyo mata da ruwa, turo baki tayi ta juya ta kalli direction dinsa taga har ya kwanta, sai kuma a hankali tace "Thank you" Dama bata sa ran zai amsa ba don kuwa banza yayi mata, ta dau abincinta ta fara ci, tana gama ci ta shiga bandaki don wanke bakinta, bayan ta fito ta tafi ta kashe wutan dakin sannan ta koma saman gado ta kwanta ta rufa da duvet. Washegari da safe Khaleesat ta gama rufe akwatinta ta mike tana kallon Ajay dake zaune dakin yana danna wayarsa fuskarsa daure, tashi yayi ya nufi kofa ya fita daga dakin, ta turo baki sannan ta dau handbag dinta ta bi bayansa, can gida suka tafi zai je yi ma wa enda Hajja tace sai yayi ma sallama kafin su tafi, ya sami Aunty da Gimbiya Firdausi da Hajiya A'isha zaune parlor, ya zauna kan kujera ya gaishesu gaba daya, Khaleesat ma ta zauna kasan Carpet ta gaishesu cikin sanyin murya, Ajay bai jira sae sun amsa gaisuwar ba yace "Za mu koma America yau" Gimbiya Firdausi da Hajiya A'isha ne kawai suka ce "Allah ya tsare" without giving much attention, Aunty kuwa kara wayarta tayi a kunne tana answering call, Ajay ya mike ya nufi sama, tuni Khaleesat ta tashi ta bi bayansa da sauri gashi taki yarda ta hada ido da su, duk suka bi ta da kallo don yau ma tsadadden Black Abaya ne jikinta da yayi mugun amsan fatar jikinta, tayi kyau sosai ba kadan ba kamar balarabiya, dakin Hajja Ajay ya tafi ita ma zai yi mata sallama, Hajja na kallonsu bayan sun gaisa tace "Flight din karfe nawa ne?" Ajay yace "Karfe daya in sha Allah" Hajja ta dau wayarta tana duba agogo taga karfe sha daya da rabi, tace "Lokacin ma ai ya kusa, toh Allah Ubangiji ya kai ku lafiya, amma kaje can apartment din kayi ma Hajiya Shema'u sallama, ita ma Asiya da Ummi suna can, duk ku sallame su" Ajay dai bai ce komai ba, Hajja ta juya tana kallon Khaleesat, ita kanta a ranta sai da tayi admitting kyan Halysaah, amma damuwarta jikokinta da suka samu matsala ta dalilinta shi yasa ma bata jin ta kwata kwata a ranta, Khaleesat ta sauke kanta kasa ganin kallonta Hajja take, Hajja ta sauke boyayyen ajiyar zuciya tace "Kun karya ne Jiddah?" Gyada mata kai Khaleesat tayi tace "Eh Hajja" Ajay ya mike, Hajja na kallonsa tace "To Allah ya kai ku lafiya Ahmad, we will speak on phone idan kun isa" Ajay yace "In sha Allah" Khaleesat ta yi mata sallama ita ma sannan ta mike ta bi bayan Ajay da har ya fita daga dakin, ji yake kamar ya gansa a Maryland yanxu. Apartment din da su Mami suke Ajay ya karasa don it's just few houses away, Khaleesat dae na biye da shi har suka isa gidan, Hadiyah ce ta bude masu kofa bayan Ajay ya danna bell, daga sama har kasa take kallon Khaleesat tana kare ma kayan jikinta da jakar hannunta kallo, can ta koma gefe fuskarta babu walwala, kamar warce ake tilasta ma tace "Ina kwana Yaya" Ba tare da Ajay ya kalleta ba yace "Lafiya" Tuni ta juya ta bar bakin kofar ta koma cikin parlon tana cika tana batsewa, a karo na farko tun fitowarsu Ajay ya juya ya ɗan kalli Khaleesat da ta rakube jikin kofa kamar munafuka, juyawa yayi zai karasa parlon suka hada ido da Jay dake saukowa stairs dake opposite din kofar parlon, Ajay ya dauke idonsa ya karasa cikin parlon ya zauna ya gaida su Mami da Hajiya Shema'u, duk suka amsa masa, da fara'a Hajiya Shema'u tace "Fatan kun tashi lafiya?" Yace "Alhamdulillah" Khaleesat ta karaso ta zauna kan Carpet jikinta a sanyaye bayan da ta hada ido da Jay zai sauka downstairs amma ganinsu ya juya ya koma sama, cikin sanyin murya ta gaida Hajiya Shema'u da su Mami da Ummi, duk suka amsa a takaice, Hajiya Shema'u kadai ce ta bata attention, Hadiyah dai na zaune parlon fuskarta daure tana danna wayarta, Ummi kuwa sai satan kallon kayan jikin Khaleesat take, Ajay yace "Za mu koma America ne dama" Hajiya Shema'u tace "Allah sarki, nima gobe in sha Allahu zan koma Nigeria, kace sallama ku ka zo yi mana kenan" Ajay yace "Ehh haka ne" Hajiya Shema'u tace "To Allah ya kai ku lafiya" A takaice Ummi da Hajiya A'isha suka ce "Allah ya tsare" Ajay yace "Ameen" Khaleesat ta ɗan daga kanta ta kalli sama ko zata kara ganin Jay amma taga ba kowa wajen, Ajay ya mike yace "Jirgin nan da awa daya ne, za mu tafi airport..." Hajiya Shema'u tace "To Ahmad din ne zai kai ku Airport din? Ni duk yau ma ban gansa ba" Ajay yace "A'a nayi booking ride" Hajiya Shema'u ta kalli Hadiyah tace "Ke Hadiyah ina mijin naki?" Hadiyah na danna wayarta tace "Ya fita baya nan" Khaleesat ta daga kai a karo na farko ta kalli Hadiyah suka hada ido, wani matsiyacin kallo Hadiyah ta watsa mata akan idon Ajay, Khaleesat ta sake kallon sama sannan ta sunkuyar da kanta, Hajiya Shema'u na kallon Ajay tace "Ko kun yi sallama ne da ɗan uwan naka?" Ajay yace "Eh mun yi sallama" Hajiya Shema'u tace "Toh Allah Ubangiji ya sauke ku lafiya, Allah ya kara ɗankon zumunci" Ajay yace "Ameen mun gode" Ajay ya mike ya sake yi ma Mami sallama tace "Allah ya tsare" Sannan ya juya ya nufi kofa Ummi ta bi sa da harara ta taɓe baki, Khaleesat ma tayi masu sallama sannan ta mike ta bi bayan Ajay tana tafiya a sanyaye, Hajiya Shema'u ta bi su da fatan alkhairi tana sa masu albarka, sai kuma ta kalli Hadiyah tace "Ji shashashar yarinya, baza ki tashi ki raka su ba" Hadiyah ta kara hade rai sai kuma ta mike ta bi bayan Khaleesat, Khaleesat na isa kofa bayan ta saka takalminta sai da ta kara kallon upstairs tana jin hawaye na taruwa idonta kawai ta juya ta fita daga parlon, Hadiyah dake mata wani tsinannen harara ta kulle kofar parlon da karfi..... Har suka koma hotel Khaleesat taki yarda ta kalli inda Ajay yake, sai daure fuska take tana cika tana batsewa kamar warce ke jiran kiris ta fashe da kuka, bata san shi ma bata ishesa kallo ba don ko bin ta kanta bai yi ba balle ya kalli inda take yasan halin da take ciki, ya dau Charger dinsa da Hand luggage ya fice ya bar ta a dakin don Taxi din da zai kai su Airport din har ya iso, ta bi sa da wani harara sai kuma ta goge hawayen da ya fara taruwa idonta, daga karshe ta dau akwatinta da Handbag after making sure she is forgetting nothing in the hotel room sannan ita ma ta fita daga dakin.... Da daddare karfe takwas da rabi suka sauka Baltimore, nan ma dai ya bar ta da akwatin ta yayi gaba, bayan sun shiga mota she was expecting zai sa driver ya tsaya a restaurant ya siya mata abinci don babu abinda