Showing 24001 words to 27000 words out of 120027 words

Chapter 9 - Halysaah Book 3 By Khaleesat Haydar

fita waje ta bi bayansa, tuni dama Ajay ya bar gidan bayan da Baby ta raka Khaleesat sama, Baby na kallon Jay bayan ta bi sa waje tace "Gani yaya" Yace "Hope you gave her a separate room?" ta gyada masa kai yace "Ohk akwai abinci a gidan ai?" Ta ɗan karyar da kai tace "Akwai, fried rice Ummi suka dafa mana da chicken and Salad, very delicious" Yace "Ok now ki je ki xuba abincin ki kai mata da ruwa" Buga kafa tayi ta rungume hannu kamar zata yi kuka tace "Yaya na gaji da hawa stairs fa, sai ni ce kawai za ayi ta aika a gidan nan" Yace "C'mon Baby, be a good gal and do what I ask you" Ta langwabe kai a hankali tace "Ohk" Daga haka ta juya ta koma cikin gidan, shi kuma daga nan yayi tafiyarsa gidan da ya sauka which isn't far from this House kuma duk gidajensu ne, Gimbiya Firdausi da Hajiya Sumayya ma can suke kwana da yayar mahaifin Hadiyah, Baby tayi yanda Jay yace mata ta kai ma Khaleesat abinci da ruwa sannan ta koma wajen uwarta ta kwanta jikinta, hira su Aunty suke amma gaba daya hankalin Aunty na kan Khaleesat da aka kai sama, abincin da Baby ta kai sama ma bata san ita zata kai ma ba ta zata yayyinta ne suka sa ta debo masu abinci da baza a kai ba, ita dai Khaleesat ko taɓa abincin da Baby ta kawo mata bata yi ba saboda bakin ciki gashi ta kasa daina kuka, she was so hurt da abinda suka yi mata, daga karshe haka ta tashi ta shiga bandakin da ta gani kusa da dakin ta dauro alwala ta dawo ta bude akwatinta ta dau hijab ta saka ta tada sallah.... Baby ta fito waje saboda kiran da Ajay yayi mata ta nufesa a inda yake tsaye tace "Gani yaya" ya mika mata ledan hannunsa yace "Take this food to her" Baby ta wara ido tace "Sau nawa za a kai mata abinci, Bayan ya Jawwad ya sa na kai mata abinci da ruwa daxu" Ajay yayi shiru jin abinda tace, can yace "Ohk, but still ki kai mata wannan ma" Tace "To ni ina nawa fa?" Ya hade rai yana kallonta yace "Ina wasa da ke ne?" Tayi yake tace "No Yaya" sannan ta amshi ledan ta juya ta koma cikin gidan, shi kuma yayi tafiyarsa can daya gidan, Baby na shiga parlor da abincin Aunty ta kirata ganin leda a hannunta, ta tafi har kusa da Aunty tace "Ga ni Momy" Aunty tace "Meye wannan a hannun ki?" Baby tace "Ya Ajay ne ya bani abinci in kai ma wife dinsa" Aunty ta karɓe ledan ta ajiye kusa da ita tace "Tafi ki ban waje" Juyawa Baby tayi ta tafi ta zauna ta dau wayarta ta ci gaba da kallon Cartoon din da take. Khaleesat na kwance saman Carpet bayan ta idar da sallah da kusan minti talatin har sannan ta kasa daina hawaye, ko kallon abincin da Baby ta ajiye mata bata yi ba, text message ne ya shigo wayarta ta dau wayar tana dubawa taga Ajay ne ya turo mata message yace "You need anything?" Taji wani sabon hawayen ya zubo idonta, reply ta mayar masa tace "Eh" Sai ga wani message din nasa yace "What?" Ajiye wayar tayi tana goge hawayen dake zuba idonta bata mayar masa reply ba, bayan minti biyar sai ga kiransa ya shigo wayar, Sai da ya kusa katsewa tayi picking ta kai kunne tayi shiru, yace "Ke kika saka min katin zaki yi shiru? What is that you need?" Shesshekan kuka ta fara yi ta kasa ce masa komai, Calmly yace "What happened?" Ta ma rasa me zata ce masa kawai ta fashe da kuka, shiru yayi yana sauraronta for few seconds, can yace "Come outside" Bata ce komai ba, calmly yace "Kin ji me nace maki?" A hankali tace "Uhm" Daga haka ya katse wayar, goge idonta ta dinga yi duk da hawayen yaki tsayawa, after some minutes ta mike ta tafi bandaki ta wanke fuskarta ta fito, tana tafiya a hankali ta sauka downstairs, kanta a kasa ta nufi kofar fita waje ba tare da ta yarda ta kalli inda su Aunty suke ba, su Aunty da Mami da sauran matan dake parlon duk suka bi ta da kallo har ta fita ta kullo kofar, waige waige ta dinga yi a neighbourhood din ganin bata gansa ba, after almost 2 minute ta hangosa walking toward her, ta sunkuyar da kanta har ya iso inda take tsaye sannan ta daga kai tana kallonsa, yana kallon kwayar idonta da yayi ja yace "Me ya faru?" Ta girgiza masa kai sai ga hawaye na silalowa daga idonta, bai sake cewa komai ba yana kallon wani direction din, bayan few seconds ya nuna mata wani roadside chair yace "Zauna can" Ba musu ta tafi ta zauna wajen da yace, ya karasa cikin apartment din, kallo daya yayi ma su Aunty ya wuce sama without saying anything to them, Aunty dake cin abincin da ya ba Baby ta kai ma Khaleesat ta bi sa da wani kallo, haka ma Ummi da Mami, dakin da su Hadiyah ke ciki Ajay ya bude, gaba daya suka juya suna kallon kofar, one by one suka dinga gaishesa ganin shi ya bude kofar, duk yayi masu kallo daya ya fice daga dakin without bordering to answer their greetings, ya bude wani dakin yaga Hajja tana bacci sai Hajiya A'isha dake dakin, gaisheta yayi bayan ta amsa ya kullo dakin, ya bude last room din yaga box din Khaleesat da handbag dinta sai wayarta, shiga ciki yayi ya dau akwatin da handbag din ya saka mata wayar cikin handbag sannan ya fita daga dakin, tun da ya sauko downstairs su Aunty suka bi sa da kallon mamaki har ya fice daga parlon without looking at them, duk suka kalli juna irin kallon mamaki, Ummi ta gyada kai tace "Tabdi, dauketa zai yi a gidan yake nufi ko me?" Gimbiya Firdausi dai tayi shiru tana kada kafa a hankali fuskarta dauke da wani expression ita ma na mamaki, Aunty ta rike haɓa tace "Kun ga wani ikon Allah kuma" Ummi tace "To ku ka san me ta kintsa masa?" Gimbiya Firdausi tace "Ku kyaleni da shi" Ita dai Mami bata tofa nata ba don bai shafeta ba, Ajay na komawa inda Khaleesat take zaune ta bude ido sosai tana kallonsa da mamaki, ya ajiye mata akwatin ta da handbag ya zauna leaving much distance between them, sosai jikinta ya kara sanyi ta dinga kallonsa babu ko kiftawa, wani bakin jinin yake son kara ja mata gun danginsu, wayarsa ya ciro yana duba hotel din da zai yi reserving, after a while ya gama making reservation din hotel din da yayi selecting ya biya kudi sannan yayi order din Indrive that will take them there, da kyar Khaleesat tace "Amma bai kamata ka dauko akwatina daga cikin gidan ba....." Wani kallo ya jefa mata yace "I will give you a dirty slap" a hankali ta sauke idonta bata sake cewa komai ba, after waiting for almost 15 mins sai ga Indrive din ya karaso, Mikewa yayi ya dau handbag dinta ya ajiye mata kusa da ita ya dau akwatin ya kai Ride din, ta bi sa da kallo sai kuma ta mike jiki a sanyaye ta nufi motar ita ma, Front seat Ajay ya shiga bayan drivern motar ya saka akwatin a booth din motar, ita kuma ta bude back seat ta shiga, bayan tafiyar kusan minti talatin suka isa hotel din da yayi booking, without much wasting of time in the hotel reception tunda ya riga yayi reservation online suka yi lodging din hotel room din, gefen gado Khaleesat ta zauna a dakin har lokacin jikinta a sanyaye yake bata taɓa tunanin abinda zai yi ba kenan, ya shiga bandakin dake cikin dakin ya dauro alwala ya fito don lokacin la'asar har ya wuce, mikewa tayi ita ma ta tafi ta dauro alwala, ko da ta fito har ya tada sallah, ta dau wani hijab din nata a box ta saka ta tafi bayansa ta tsaya zata bi sa sallan.....

*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah, ur evidence via 07087865788*
HALYSAAH PAGE 113

Da daddare Khaleesat ta fito wanka kenan taji ana knocking kofar dakin hotel din, tun bayan da Ajay ya fita wajen karfe biyar ya kawo mata abinci ya sake tafiya take ta zaune ita kadai a hotel room din har yanxu da karfe tara da rabi yayi, hijab dinta ta saka har kasa don towel kadai ne daure jikinta ta nufi kofar ta bude tana kallonsa, kallo daya yayi mata ya shiga cikin dakin, ta juya ta bi bayansa still looking at him, ya ajiye ledan hannunsa kan Centre table din dakin, da tsadadden darduman da ya dauko daga gida sannan ya cire Jacket din jikinsa, a hankali ta dau doguwar rigar da zata saka na bacci dake gefen gado ta nufi bandaki, bayan few minutes ta fito daga bandakin ta ajiye hijab dinta da ta linke, ta ɗan kallesa ta gefen ido taga duk hankalinsa na kan abinda yake yi a wayarsa yana zaune kan kujeran dakin, gun ledan da ya ajiye ta tafi ta dauka don ledan restaurant ne, bata ci abincin da yawa ba ta sha drink din ta ajiye sauran abincin ta zauna gefen gado ta jingina da furniture din gadon ta fada duniyar tunani, ta kusa 30 mins zaune maganganun su Hadiyah na dawo mata da irin tarban walakancin da su Aunty suka yi mata a parlor, that not being enough Jay ma yaki ko da kallon inda take shi ma da ya ganta, gaisuwanta ma without much concentration ya amsa mata, duk cikin abubuwan da aka yi mata yau wannan ne yafi yi mata ciwo har cikin ranta, she felt really hurt and pained, hannu ta kai ta goge hawayen da taji na silalowa daga idonta a hankali, don kar ma ta fashe da kukan dake cin ta kawai ta jawo wayarta ta kunna data ko zai yi distracting dinta from what is making her wants to cry, bata expecting ko wani important WhatsApp message da ya wuce na Ummanta sai Sophie sai ko Aunty Farida, sosai gabanta ya fadi bayan ta ci karo da message din Jay, babu ko kiftawa ta dinga kallon message din da ya rubuto mata kamar haka "An maki wani abu ne a gidan?" And he is even online at the moment, cikin sanyin jiki ta masa reply tace "A'a" After few minutes sai ga wani message din nasa yace "Then why did you leave the House?" Wasu sabbin hawaye taji na taruwa idonta ta tura masa "Ba komai" Sai ga message dinsa yace "Alright, take care" har cikin ranta take jin kaman kaso tamanin daga cikin abinda ke damunta a ranta ya ragu, baƙin cikin da take ciki yau taji kamar an yaye mata shi lokaci daya, kallon message din nasa na karshe ta dinga yi babu ko kiftawa, cikin sanyin jiki ta sake masa message tace "Plss me yasa idan nayi maka message kake ignoring? I want to speak to you plss" Without waste of time sai ga shi yayi reply kamar haka "Hum! About?" Ta goge hawayen dake zuba idonta tace "Many things" Ya sake cewa "Hmm, Like?" Tace "Plss spare me even if it's just a little of ur time ka saurareni don Allah" Yace "Kina ina yanxu?" Ta dinga kallon tambayar da yayi mata zuciyarta na bugawa, a hankali ta juya suka hada ido da Ajay, ta sauke idonta sai kuma ta dauke kai daga direction dinsa, tana kallon message din da Jay yayi mata ta mayar masa da reply tace "Nima ban san wajen ba" after few seconds Jay yayi mata reply yace "Forward ur location" Khaleesat ta kusa minti daya tana tunanin ta tura din ko kar ta tura, don tana tura masa location din hotel zai gani, a hankali ta juya ta kalli Ajay taga idonsa na kan wayarsa, kawai ta tura ma Jay location din nata ta WhatsApp, ta fi minti talatin zaune tana jiran reply dinsa amma bai yi ba kuma yana online, daga karshe tayi masa message tace "Kayi shiru" Nan ma dai har bayan minti ashirin bai mayar mata reply ba ta ga ya ma sauka, hawaye ya cika idonta ta kashe data dinta ta ajiye wayar ta kwanta ta rufe jikinta da farin duvet din kan gadon, bata san sanda bacci ya dauketa ba wajen karfe sha biyu bayan ta gama zubda hawayenta. Biyu da yan mintuna na dare Khaleesat ta farka ta dalilin mafarkin da tayi about Jay, ta mike zaune ta dinga bin dakin da kallo don wuta ne mara haske a kunne, she was wondering if ita kadai ce a dakin, tafi minti goma zaune bata motsa daga inda take ba, can dai ta koma daya side din gadon tana leka kasa a hankali, Ajay ta gani kwance kan darduman da ya shigo da shi daxu yana sanye da jacket ya saka eye mask for sleep alamar baya son haske, dakin yayi sanyi sosai saboda Ac dake kunne, gashi dama tun da suka zo kasar ta lura yafi America sanyi, duvet din jikinta ta cire ta rufa masa ta koma ta kwanta tayi using second bedsheet din kan gadon ta rufa da shi. Da asuba ko da Khaleesat ta tashi taga duvet din a jikinta, ta mike zaune ta juya tana kallon inda yake tsaye yana sallah, sauka tayi daga saman gadon tana gyara hularta ta shiga bandaki. Khaleesat na idar da sallah bayan ta gama azkar dinta abu na farko da tayi shine kunna data din wayarta ko Jay yayi mata reply din message dinta, amma taga har sannan bai mata reply ba kuma ya hau not long ago, sosai taji zuciyarta ya karaya, ta ajiye wayar cikin sanyin jiki lkci daya idonta ya kada, kamar ance ta daga kai taga Ajay yana kallonta, sunkuyar da kanta tayi, babu yabo babu fallasa taji yace "What is it?" Without looking at him tace "Nothing" Gaishesa tayi ya dauke kai bai amsa ba, ta mike ta tafi edge din gado ta kwanta ba tare da ta cire hijab din jikinta ba, ji take kamar an kwaso mata damuwar da taji ya tafi jiya an maido mata kayanta, lumshe ido tayi after sometime bacci ya dauketa..... Ajay ne ya shigo dakin hotel din fuska daure yace "Baki da hankali ne zaki bar ni zaune a mota tun daxu are you okay?" Khaleesat ta gama daure gashinta da take yi ta juya tana kallonsa bata dai ce komai ba, bai sake ce mata komai ba ya dauke idonsa ya juya ya fita daga dakin, ta dau veil din kayan jikinta tayi rolling dinsa sannan ta dau handbag dinta ta saka takalmi ta nufi kofar dakin hotel din ta fita, walking slowly ta nufi Indrive din dake jiranta outside of the hotel, sau daya Ajay ya kalleta ta madubin motar da yake ciki ya dauke ido kamar bai ganta ba, har ta iso ta bude back seat ta shiga ta kulle. Da gangan Ajay ya bari suka je Venue din convocation din Hadiyah extremely late, don har an gama taron ana ta hotuna ne suka isa wajen, ita dai Khaleesat tana biye da shi a baya gabanta sai faduwa yake, front dinsa ya nuna mata hakan yasa ta shiga gaba yana biye da ita, tun daga nisa take kallon yanda familyn suke ta hotuna cikin farin ciki da annashuwa ba iyayen ba ba 'ya yan su ba, Hajja kuwa na zaune daga gefe cike da izza ga fruits an ajiye mata gabanta, Hadiyah sai makale ma Jay da yayi mata side hug take kamar zata shige jikinsa su zama daya ko kunya babu ana masu hoto, kana ganinta kasan tana cikin farin ciki mara misaltuwa, Khaleesat dai ta sauke idonta daga kallonsu tana tafiya a hankali, lokaci daya duk aka yi noticing Ajay da Khaleesat that were walking toward the scene, gaba daya aka maida attention kansu barin ma Khaleesat, Ba iya su Hadiyah da cousins din ta ba, hatta iyayensu kowa kallon Khaleesat yake barin Aunty, cause whatttt?? she look expensively beautiful, gaba daya dressing dinta ya doke duk na yan matan wajen har me convocation, komai na jikinta is screaming nothing but pure luxury gashi tayi wani nutsattsen kyau duk da babu make up fuskarta pink lips dinta kuwa sai sheki yake, tsadadden kayan jikinta ya kara haska farin fatar ta, Walid ya dinga kallonta kamar zai cinyeta, Khaleesat was only feigning smile ganin all eyes were on her hakan yasa beauty point dinta ya dinga lotsawa ciki, amma tsabar yanda duk ta rikice da yanda suke kallonta sai da ta harde kafa wajen tafiya wanda hakan yasa kirkis ya rage ta fadi banda Ajay da yayi saurin tarota, yana facing dinta speaking calmly yace "Are you a bush gal?" Kamar wanda ya tuna abu sai kuma ya saketa within few seconds suka ci gaba da tafiya, this time around he let them walk together ba kamar daxu da take gaba yana bin ta ba, Aunty taji wani abu ya tokareta a kirji ta juya ta kalli Hajiya Nafisah, Hajiya Nafisah tace "Uhum" irin na takaicin nan, Ummi Mahaifiyar Hadiyah kuwa hade rai tayi sosai ta ci gaba da harkar gabanta a wajen, Mami dai ko bin ta kan Khaleesat bata yi ba tana ta kokarin sallamar wasu ɓakin ta da za su tafi, Hadiyah ta dinga kallon designer bag din hannun Khaleesat da rings din fingers dinta sai kuma ta dauke kai tana jawo wasu frnds dinta da suma suka tsaya kallon Khaleesat, ta kira me hoto yayi masu hoto duk don ta kawar da attention dinta daga kan Khaleesat, Tun da Jay ya kalli Khaleesat sau daya ya dauke kai daga direction din, Shahuda kuwa sai kallon doguwar rigar jikin Khaleesat take with sheer jealousy, sauran yan matan ma dai kowacce zaka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login