Murucin Kan Dutse
Chapter 127 of 146
kwanta ma.
Kin san ance kowa ya samu rana yai shayen sa wuri ta samu da tace kai yace sannu da tace kafa yana wayyo Allah na.
Sai ta bushe da dariya tace anya doctor ba kishi a ciki zamcen ki kuwa nace ba dole nai kishi ba tunda abinda take fama dashi shine nima nake fama dashi yanzu haka.
Ta sake bushewa da dariya tace to ai bashi ba doctor kece kika tsaya kina wani muku muku da naki cikin kamata yayi ace tasan kina dashi zakiga ta shiga hankalin ta ta daina duk wani sallo da yangan da take maku a gidan wai ita mai ciki.
Naja tsuki tare da cewa ai baki san halin ta bane ita fa kanta kawai ta sani a duniya bayan haka bata san komai ba haka rayuwan ta yake ko yaushe.
Mun dan dauki lokaci muna hira daga karshe muka juya kan maganan zuwa wani buki da zamuyi washe gari na auren diyar wata shugabar mu data gaiyyace mu.
Na biya na dauko yara daga school muka dawo gida a gajiye na iso ban tsaya ba na shiga wanka na fito daidai Aisha ta shigo ita ma a gidan.
Nan ta zauna ina shiryawa muna hira da ita tana bani labarin wai taga Raliya a hanya amma bata tsaya ta dauke taba.
Nace ina mikewa tsaye Aisha to may ye abin damu ba gaki kin dawo gidan ba zafin ki yake ji na sani ba yau ba duk wani wanda ke tare dani matar nan bata kaunar shi na ciki na ciki ne da ita.
Mun fito falo mun zauna sai fa Zulfa tafito tace ashe kun dawo ina barci daga barci kallo ya dauke ni a wurin .
Nai murmushi nace da ita ai dole ki dinga barci maganin da kike shane haka zai ta saki jin kasala kafin ya bi jikin ki da kyau.
Tace haba ni kan ai na manta cewa zai iya bani wani yanayi irin haka har nake ta mamakin may ke sa ina jin irin haka ne wai ko da yaushe yanzu ?
Abinci zamuci ta zauna take bani labarin wai dazun tunda safe an kwasa da maigidan da mahaifiyar hindatu a gidan.
Nace subbahanallahi may kuma ya faru haka ne wai take cewa dani nuna mai tayi kamar bai kula da yarta yadda ya dace shine shi kuma yau yai fushi ya fada mata magana son ran shi.
Ni tunda ma tashige ban sake gani giccinta ba tun safe nasan amsa daya bata ne bai mata dadi ba don ita kamar yar nata take kin sani.
Murmushi nayi kawai ban ce uffan ba a fili sai dai a cikin raina ina mamakin wanan irin rayuwa haka ace yarka ta dade gidan miji amma kullun kana mayar da ita karamar yarinya wai kaine may taya ta kishi.
A can kuma dakin hindatu uwar ce tsaye tana magana da cewa yanzu na kara tabbatar da cewa wanan yar kauyen yarinya ta dauki kanta wata tsiya.
Don tun zuwa na datazo tai min sannu da zuwa bata dawo ba gaida ni bance ke ma ki mutunta wani nata don itace ta fara.
Mammy haka Rahama take fa ke tama yaba da ke da har tazo tai maki sannu da zuwa har nan isan dai ba wani dalili mai kwari ba zaku iya shekara ma a gidan nan baku hadu da ita ba.
Don ko yaushe ita busy take har nan gida yanzu da aka gane ta biyota zakiga mata nayi da mazajen su tana duba su.
Tace kuko wawaye kuna zaune baku baki baku fari har yar kauye tazo ta fiku sanin kan ta duk cikin matan gidan nan ita zaka kalla ka san tana zaune a cikin daula da jin dadi ta bar ku jan gadin gida da haukan son miji a baki.
Kai haba mammy keda kan ki ke dadin wanan magana kuma har may Rahama tafini dashi da zaki fadi haka.
Tace tafi ku wayo da sani kai mana nayi nayi dake ki nemi aiki amma son jiki da kai ya hanaki nema kun kwanmace ku zauna a gida kuna kallon kishiyoyi suna fita nemawa kan su abin dogaro har yaushe ta shigo gidan da tai nisa haka ta haku tazara.
Kin san dai yau idan mijin ku ya fadi ya mutum wanan yar da kuke gani sai tafi kowan kason abin da ya bari.
Tace mama duk mun san da hakan ai bashiyasa kikaga ina son nima in tara ba Allah dai yasa namijin zan haifa nima.
Tace bakije an gwada ki ba ne ko may har yanzu?
Tace ranan nayi mashi magana yace min shi baya son wanan maganan ko may Allah ya bashi ai karuwa ne ba a rainawa.
Uwar tace ai dole ya fadi haka an cika mai gida da diya maza yana kallo yanzu bai damu da wai sai wani ya haifa mai su ba tunda ya riga da ya samu ko.
Kin san ance wai su yan kauyen nan akwai abinda suke sha wai don su haifi diya maza saboda su gaje gida ko suyi ta samun masu taimaka masu da noma.
Mammy wai da gaske ?
Uwar tace ke haki taba sanin haka bane ko may ?
Ai kibar bakauye inda kika gan su kin ga kishi da bakauye da bafillatana akwai wahala sosai a rayuwa.
Sai hindatu tace kin ko ga ita Rahama dama zubi biyu ne ita don wurin uwa bafillatana ce ai duk su ta kwaso don uwar ta sai mutuwar Saade ta taba zuwa gidan mu har muka gan ta.
Kice naku ya samay ku ashe ni ban ma taba sanin wanan maganan ba sai yau haba shiyasa muke aiki kullun kamar bamayi .
Nan dai sukaita suratan su har uwar nacewa ai sun hadu damu kin san su fa yaro bai zuwa aure haka kara zube sai sun shirya yaran su tsab.
Tace shiyasa dama nace a daurewa shegiya mahaifa kada ta kara haihuwa a gidan haka ya isa kowa ma ya samu tunda ba ita kadai bace mai cikin haihuwa.
Sun kai wani lokaci suna zancen su na shirka a tsakanin su inda suka sha alwashi cewa ba zan sake haihuwa ba agidan na tara yara maza bulbul dasu kamar kiyon agric a gida duk wanda ya gan su sai yaji sha awar su.
********* ********* *********
Washegari Jumma,ane daddy ya fita da yaran maza zuwa sallah kamar yadda a ko wani jumma, a yake fita dasu
Sun dawo akan idon mahaifiyar hindatu don sai ya zaga ko wani part dasu sun gaida kowa a gidan kafin su dawo inda muke.
Bayan fitan su ne mahaifiyar nata take cewa kin ga abinda nake fada maki kullyn ko ganin irin wanan ai takaici ne a gidan nan ba kunya yake fifita diyan shi maza akan kowa.
Jifa yadda ya tasa su a gaba ya fita dasu kamar mai nunawa duniya su ko shaddan jikin su iri daya da nasa kin ko san dai an sha kudi a wurin nan kan .
Yar tace ai tare yake masu dinkuna dashi lokaci da dama haka zai shigo da kaya yace wai nasu ne tare ya dinka masu dashi.
Da yamma muka shirya ni da yara zuwa wurin buki duk wanda yaga shigar mu sai ya kyasa muna a lokacin har mazan ban bari a gida ba tare zamu tafi dasu wurin dinner din.
Mun fito ashe hindatu da uwar ta na wajen gida a zaune suna shan iska suna hira fitowan mu yai daidai da shigowan Raliya gidan da yaranta itama.
Duk kallo suka bimu dashi nice nake cewa da Raliya kun dawo tace eh fita zakuyi ne haka tafi da gidan ka ke nan kuma yau zakuyi.
Nace eh zamu gun dinner ne ba dadewa zamuyi ba ai da yamma yayi zamu dawo don ban son tukin dare sosai.
Adawo lafiya tai muna ta shige don haka muka koma a fili zakace kalau ake zaune sai dai kowa na ciki na ciki kishin barki.
Ihisan ce ta na ganin mu take cewa mummy yau ina zaku nace inshan dinner zamu banganki ba tun dazu na dauka kina barci ne ai.
Tace mummy zan tafi sai kakan dake muna wani kallon sama da kasa, tace da jikan nata waya kasa dake balle ya kwashe.
Tace ni sai na tafi tace bazaki ba na fada maki sai yarinyar ta juya ta tafi nace Ihisan ki zauna ki bari wata rana mu tafi tare.
Ina ta shige ta tafi shiryawa nace da yara su shiga mota kafin ta fito aiko kakar na ganin haka ta mike ta shige ciki tabi bayan yarinyar murmushi nayi daga ina nake zaune a gaban motan.
Can ta samay ta ta hauta da fada tana cewa ai ga yacan mun shiga mota zamu tafi dama maganin ta ke nan ai.
Yarinyar tace mummy ba zata wuce ta barni ba tunda tasan na shigo na shirya don ni bats taba saba min alkawari ba irin mamana.
Rankwashi kakar takai mata akai tace da ita mara hankali da wayo kawai uwar wasu kike fifitawa akan naki don wayo bai ishe ki ba an riga da an shanye ki ko ?
Taci gaba da shirin ta kakar nata zagin ta har ta shirya tabiyo ta a baya tana fadin su kan ai yanzu sun kai inda zasu tafi ko don tun shigar ki gida suka shiga mota.
Sai dai suna fitowa tagan mu zaune a mota muna jiran fitowan ta daga ciki ina ganin ta fito na tayar da mota muka kama hanyan fita.
Nan muka barsu nasan dai zagine kwando kwando sai na sha shi gun mahaifiyar hindatu din don mace ce da bata iya boye kishin ta ita.
Mun samu wurin ya cika makil da Jamma, a na ja yarana muka dan tsaya daga baya na kira Fati take cewa na karaso daga ciki ga wuri ta aje muna.
Ciki muka karasa idon jamma, a a kan mu kamar dai yadda ake akowani buki idan kaga abinda zaka kalla.
Sai da naga duk yaran nawa sun zauna na zauna nima sai ga Fati tazo take cewa dani muje mu gaisa da mai bukin don tana cewa dama ba zan zo ba ai don tasan ni bana shiga jama, a sosai.
A can wani gun muka samay ta da yan uwan ta tana ganina ta taso ta rugumay ni tana fadin lalai yau sunana arziki tunda har kikazo wanan dinner din.
Tun a wurin tacewa yan uwan ta a ware muna gift din mu daban suke tambayana munawa nai murmushi nace ni tafi da gidan ka nayo don ban bar kowa ba a gida.
Antyn namu taji dadi sosai tace a samu abu a zuba mun da yawa naje na rabawa har abokan zamana nai godiya tare da bata envelop mai dauke da kudi a cikin sa muka fito muka dawo mazaunin mu.
Bayan fitan mune yan uwan ta suka bude envelope din suka shiga kirga kudin kamar yadda akeyi a kowani buki dayar tace anty 200 ne fa cif ta sako maki a ciki tace ai Rahama tafi da nan in dai itace.
Yarinyar nada kirki kwarai wallahi gashi bata da hayaniya baka sanin matan mai akwai ne sai wanda ya sani.
Buki ya kai buki aka shiga gudanar da event din bukin sai ga ta har table din mu tace ai muna photo da ita.
Nan mutane suka fahinci muma duk inda muka fito ba baya ba don manya basu hurdan banza haka da mutum a fili.
Sai tara na dare na kwaso yarana muka dawo gida tu fitar mu nabawa ihisan abin bukin ta ta wuce dashi part din su mun shiga mun samu daddy ya dawo gida a lokacin.
Yake cewa yau kan mummy da yaran ta tafi da gidan ka akayi ne nace na kai su ne suma suga gari sai Zulfa ke cewa shine kika fita da yar gwal zuwan mama biyu nan tana tambayan ku ai.
Nace tunda dai tagaban dawo da nawa yaran ba ai tasan muna tare ke nan dama tun fitan mu ai bata so ba ita.
Daddy yace ina ruwa ta da harkan iyalina nifa bana son abin raba daya biyun nan da ake son kawo min a gida idan bata biki ba ita wurta dawa take hurda balle ta san duniya.
Ni dai na shige abina ashe dattijuwar bata hakkura ba da safe yaje gaida sune take cewa dashi jiya ai na tafi neman ka baka dawo ba.
Yace lafiya dai ko mama ?
Tace a, a dama matarka ce ta fita da ihisan naga har dare basu dawo ba shine hankalina ya daga yace akan may hankalinki zai daga mama ?
Ita wacce ta fita dasu ba tare suke ba data dawo ai itama dole zakuga ta dawo gidan banga abin tayar da hankali ba tun da tare suka fita da uwarsu ai.
To amma ace an fita har dare ai ha dadi ko ?
Yace mama gidana ne fa kuma iyalina ne nasan halin ko waccen su Rahama ba zata kai su wurin banza ba tunda ba halin banza gare ta ba.
Shiru dakin yayi ya mike yana cewa shi ya tafi sai hindatun tace dashi wai daren jiya batai barci ba da dadi tana son ya kaita asibiti.
Hindatu nifa na fara gajiya da zancen asibitin nan cikin nan fa va kya kadai keda shi ba a gida nan yar uwar ki ni ko paracetamol bata taba min complain din shi ba kuma in ma wahala ne tafiki wahala da ciki amma take tsaye.
Kwance take amma sai da ta mike zaune da karfi tace ciki a gidan nan baya nawa wacece mai ciki gidan nan kuma ?
Yace ki lalaba ki gani ni dai na fada maki ya isheni hakana har ya juya ya fara tafiya sai ya juyo yace na manta mama ta shirya gobe zata koma gida munyi waya da Alhajin ku jiya.
Au korata ma kake a gidan ka ke nan to ni ba zaman kowa nazo yi ba yata nazo fakewa don halin da take ciki.
Ba koran ki nake ba gani nayi duk sauran na ciki amma suke iya kula da kan su haka na may ye amfanin mai aikin dake gareta da bata iya kula da ita sai wani yazo dubata ?
Shi Alhajin da aka bari a gida shi kadai ai yafi bukatan kulawa shida ba lafiya ya ishi jikin shiba ai.
Mamaki yabar uwar dashi takecewa bayan fitar shi daga dakin baby mijin ki fa yanzu ya fara baki dama baida kunya amma yanzu rashin kunyar nashi karuwa yayi don tun zuwa na gidan nan baiyi naam dani ba ina lura dashi.
Mama kema kin faye yawan magana ne kamar kece matar gidan ina ruwan ki da zancen wai ihisan tabi Rahama wurin buki da ta dawo da abin arziki ba tare kuka raba da ita ba kuma kin kai karanta gun ubanta.
Abu dai shirmay zalla haka suke gudanar da rayuwan nasu ba wani zancen tarbiya a cikin sa ko kwabo.
Ya barsu suna hasashen daga cikin mu wacece mai cikin da yake magana akai din sun rasa ganewa don kowan mu a tsaye take kyam ba mai alaman lolayi tare da ita balle su gane.
Hindatu tace kin san halin shi aiko don kada ya kaini zai iya fadan hakana don a zauna lafiya a gidan.
Munadukai ne kuma fa da naci abu kanza ko wacece yar bakin cikin da zatai ciki yanzu lokacin da sukai nasu ina kallo wani irin bakin ciki ne ban hadiya ba a lokacin.
Kedai yanzu a saka ido da kyau a gani ko za, a gane mai cikin sai mu san ta inda zamu bullo mata da shirin mu ba dai wata ta haihu ba a gida nan yanzu kuma don lokacina ne Allah ya gani.
Bata so wuce ba amma da yamma da ya dawo sai gashi ya hado mata tsaraba dole ta fara shirin komawa da safe don ba wasa ko jin kunya ga alamarin shi.
Ban san may ake shiryawa ba agidan na dai aikawa hindatun da sauran da abinda muka samo wurin dinner da muka tafi ne sai ga Amira ta dawo tana fada min taga hajiyan na shiri tana ganin zata koma ne.
Nace ruwa ya raka taki gona don nasan idan tana gidan nan na tsawon lokaci sai an kwasa da wani da ita.
Bamu fita ba ranan duk muna gida don weekend ne ina dakina kwance don ba abinda zan fito yi waje .
A bakin Zulfa ne da natashi nake jin wai ta tafi amma tana ta fada wai ta gane munafunci aka kulla yasa maigidan cewa ta koma gida to ga hindatu nan da ciki tabarta a hannun Allah ya tsare mata ita.
Nace kafin ta barta mu iyayyen mu da basu zo ba suka bari amana ai ba ita da ta kasa hakkuri tabar ma Allah alamarin shi ba.
Tun tafiyan ta komai na gidan ya koma normal don wani lokaci hindatun kan fito ta zauna a danyi hira da ita ranan har bugun cikin zulfa tayi don taji wake da ciki a gidan tace bayan ke akwai wata mai ciki ne kuma ?
Sai dai idan kina fatan ki samu mai tayaki daukan nauyi ne kuyi tare shine dai amma banga alaman ciki ga wata ba ita dai Raliya ban masa rai ga samun ciki gare ta don barikin ta bai bari tai ciki yanzu ai kuma.
Wanan maganan da sukayi ne ya kwantar mata da hankali har ta daina hasashen zancen ciki ga wata a gidan.
Bata san Allàh yayi ikon shi ba ko kowa kumshe yake da nauyin shi ya ja bakin shi ya kyale sai lokacin da aka gani.
Cikin jikin Raliya ta fara ganewa don irin tane mai raki itama don haka muna kallon su suna ta haukan su a tare.
Sai habaici da gori ake zubawa iri iri mu dai namu ido bukin kaunar Zarah ya tashi don haka yai min daidai da samun Leave din