Showing 39001 words to 42000 words out of 299981 words
zo ya,dauketa su fita yakuma dawo da ita,
Duk a gaban idon Hamza wanda shagon shi yake kallon kofan gidan nasu,
Tsakani Hamza da ita yanzu ko gaisuwa babu sai ma yar harara da take yawan watso mai idan sun hada ido,
Malam Mudi tun yana ji har yagani da idon shi ranan yai masu masifa sosai ita da uwar ta
Yace yaba sati biyu in har aurenta yake son yi to ta fada mai ya fito ya wanke ta yahuta don shi bazai aje yarinya haka a gida ba,suna gwada sa,a da uwar ta,
Hakan yasa ta fadawa Alhaji Nura sakon Baba din da farko yaso ya,doje mata amma kuma ko may ya tuna sai yake ce mata, zai zo yaga mahaifin nata akan zancen,
Zuwan Alhaji Nura gurin Baba ya,saka mahaifiyana a,wani sabon kuncin bakin ciki a gidan mu don irin gori da habaicin da suke mata,
Amma mama Rahana taba Ummi shawaran cewa tayi tankar bata fahince su ba,
Ta zage ta shige cikin su tanuna farin cikin takoda kuwa,suna basar wanne taa nuna tafisu farin ciki da hakan
Hakan ko akayi don duk da nuna matan da suke basu ra,ayinta a cikin su tana nuna zakewar ta a zancen Kubura din don dai a zauna lafiya kawai, ,
Ance idan kana son shanmatar uwa to karike dan ta ganin haka a sannu sannu har mama saude tadan fara rage tsangwamar da takewa Ummi da yarran ta suka dan koma daidai sai dai sama sama don na ciki na ciki,
Sai dai su su a ganin cewa ai dai nagaba yai gaba don sun tserewa Ummi din da komai tun da yar ta a gidan wahala take rayuwan ta ai,
Su ko zasu tafi inda kowa nasu zai huta har su shafa ma,wani arziki,
Arziki kan ana gwadawa kubura din shi don yanzu har takai bata iya cin abincin gidan mahaifin nata sai dai a sayo mata ko ta girka abinda ran ta yake son ci taci,
****** ********** ******
Bayan fitar iyayyena daga dakin ina zaune ni kadai a dakin ba wanda ya leko dakin,
Sai dai ina jin hayaniyar mutanen gidan daga dakin su acan naji Zarah tana masu sai da safe inda tadan leko dakin nawa tashigo da yar fara,ar ts tana cewa,
Tau amaryan mu ni zan tafi sai da safe nasan cewa ba lalai bane Alhaji ya barii na fito gobe amma insha Allahu idan an kwana biyu zan shigo na duba ku,,
Ga amanan yayana nan nabar maki kin san yayana salihin mutun ne idan munga ya canza ke ce,
Damm naji don zance mama Hanne ne ya fado min a rai na cewa sai nayi taka tsantsan don su da alamar nasu suka sani,
A hankali na dan bude baki nace Anty Zarah sai anjima nagode a gaida gida ,
Tace ke waya fada maki cewa ni antyn ki ce yanzu ai kin zama matar yayana don haka ni kaunarki ce,
Nace cikin dan jin kunya ainima yayanane ko kin mata cewa ni din kaunar ku ce,
Tadan dafani tace hakane Aisha Allah yabaku hakkurin zama kinji sai kiyi hakkuri da kowa a gidan nan,
Tai min sallah ma ta,tafi na kara komawa ni kadai a cikin dakin, bakowa a tare dani,
Sai zuwa dare ina zaune a gefen dan gadon katakona mai cin mutum biyu wanda yasha shimfida da zannuwan gado,
Naji Asma,u ta,shigo dakin tana rataye da hijjab din ta da wani zani take cewa Umma tace wai nazo na taya ki kwana,
Cikin dan murmushi da,sakin fuska na ke ce mata, to ga wuri ki kwanta don haka na mike tare da jawo kofan dakin nadan rage kayan jikina na,dauki butana wanda yake cike da ruwa nafita zuwa babdakin gidan don nasan dashi,
Nai sarki saidai naga an dan gyara bandaki ba kamar yadda na,san shi ba,
Ina tsugune na,fara alwala naga shigowan Hamza gidan dauke da,wani bakin leda bag karama a hannun shi,
Ganin nice naje alwala a tsanake yadan sashi shan jinin jikin shi kamar zai min magana ssai mukaji muryan Umma Rabi tana cewa kai Hamza zo nan,
Ya juya zuwa gurinta nidaii nai alwalana nashige daki na rufo abina inda na tada sallah,
Nakai wani lokaci a gurin da nai sallah a zaune ina jero addu,io neman tsari daga Allah ga,wanan sabuwar rayuwan da na,fara fuskan ta a,sabon mazauni na,
Na koma can dan nesa kadan da Asmau na kwata inda ina jinta sai nasarin ta take hankali kwance abinta,
Washegari asabar na tashi don kiraye kirayen sallah da,akeyi na, dauro alawala ,
Ana,sallamay sallah nafito na,gyara tsakar gidan nan gaba,dayan shi don dama nasan kan gidan,
Har ban daki na tsabtace muna koda gari zai haska ko ina na gidan na gyara tsab har zuwa lokacin banji Umma Rabi tafito daga dakin ta ba,
Na nufi gurin da,suke ahe icce na debo na hassa wuta a murfu tare da dora ruwan zafi duk da ban san may za a girka a matsayin abin karya kumallo ba,,
Na hada kwanuka zan wanke sai dai babu clean din da zan wake a fili,
A lokacin naji motsin Umma ta bude kofan ta abinda yadan sani sauri dan dago kaina ke nan na nufi kofan nata don in gaishe ta,
Yayin da take bin gidan da kallon mamakin yadda na gyara shi haka tun da farar safiya,
Sai idon ta ya sauka a murhu naji tana cewa ke Aisha wanan irin icce da kika zumbuda a murhu ai yau kawai zaki kashe muna dan jarin namu damuke maneji dashi,
Hamza ne yashigo gida a lokacin inaga daga masallaci yake don naga casbaha a hannun shi,
Inda murhun yake yake kallon sai naji yace Umma sai naga kamar kwara biyar ne tasa kawai,
Kaina na,sada a kasa inda naji Umma tace tau mara kunya zaka hana na nuna mata yadda ake tattali ke nan ko ?
Yace a,a wane ni kawai dai na zaci ai baki gani bane dakyau,,
Yace mata ina kwana Umma an tashi lafiya ya gajiyan baki,
Nima,sai a lokacin na tuna cewa bamu gaisa,ba,shi nazo yi ta tareni da wani magana,
Nazube kasa a gaban ta gwiwa bibiyu ina cewa acikin yar murya ta,siririya Umma ina kwana,
Tace Lafiya kalau ya kuka kwana nace cikin dan jin kunya Alhamdullahi,
Ashe har kun tashi kinyi wanan aikin haka ni barci ya kara kwasana ai ban sani ba,
Gefen da yake a tsaye nadan kalla still ina,a,tsugunne nace ina kwana yaya Hamza,
Ya amsa min a,wani yanayi da cewa lafiya ya gajiyan jama,a,
Idon Umma,Rabi kyam a kan mu kamar wacce ke,son gano wani abu a kan mu,
Nace Umma nasa ruwa ban san may za,ayi da safen nan ba,
Akwai saura kamun koko yana nan shi zamu dama, aiko,
Hamza yace ko na,turo da madara ne ku dan hada tea ko ?
A,a kada ka fara min shi ranan da babu tea din fa kariga da ka,saba mata dashi,
Na mike a,sanyaye nabar gurin ban tsaya jin may zasu ce ba,
Ina bada baya naji tana cewa kawai zaka kwashi dan jarinka a ciye bayan ko yar irin gara,din nan da ake kawo wa Ango banga an kawo muna,ba mu,
Hamza wanda ya,danjin gina jikin shi a bayan bangon dakin Umma din ya dan ce a hankali haba Umma wani gara kuma bayan kin san yadda akai wanan auren ba,shiri,
Ta,watsa mai harara tana cewa da yake basu san kunya,ba za,sy kawo muna ya hakana ,
Na dawo nake cewa tabani Omo na wanke kwanoni sai ce min tayi ai kayan basu yi wani dauda,ba na wanke hakanan kawai,
Fita naga yayi sai gashi da clean yake cewa idan na gama,saina ahe sauran a gurina lokacin Umma ta daki ita da kanin Hamza din wanda ya,fito yana shirin zuwa makaran tan boko,
Kamar yadda Imma tace kunnun na dama inda batazo ta,gani ba amma take ce min wai nadama kunu da,ruwa ruwa kuma,bai dahu ba
Yarinyar ce taahigo da robar kosai tana cewa ance a cire na dari wai a raba,abawa kowa nashi,
Na karbi ledan na kaiwa Umma kosai din na juya don na bar dakin naji tace min karbi naki kafin ki fita,
kosai ne kwara biyu tamiko min na karba gwiwa bibibyu nake mata godiya,
.
***** *********** ******
Yan uwa na,suka shigo da kayan garar da Ummi tafa min gori a kanshi ,
Shikafa garin masara, gero sai kayan miya su mangyda ,albasa, maggi gishiri, kifi da,sauran su,,
Sai kuma bahohi dakeda guguru cincin da sauran su,,
Haba nan Umma ta,shiga waahe baki tana cewa au a she kuna tafe dama ,
Nan tafara dan cewa Allah sarki wanan irin dawai niya haka yan uwa,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABUN KU
👑 SARAUTAR MATA 👑
1⃣0⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
A,kofan dakin Umma Rabi aka jibge kagan gara inda suke ce mata ta karba d hakkuri don bukin yazo ba,shiri,
Su ka kaimin wanda zanyi amfani dashi a dakina,,
Ina,zaune tare dasu a,daki ne Gwagona take kara min nasiha irin wanda iyayye kewa diyan su,
Hawaye ne ki tsiyayo min a idanuwa na, gwago tace, kamar yadda na fada maki jiya yau sji din ne,rayuwa takai a,wani guri kuma na,daban,
Yanzu halinki mai kyau ne kadai zai maki jagora a zamantakewar ki da,su,
Kada kiyi sakaci da ibadan ki hakkuri da kuma kunya,
Idan harkin iya tsare wa yan nan tau kingama tsara rayuwar ki ke nan,
Sister din Ummi dake daga gefe tana gyara,min kaya,tace a,kuma hada da tsabta,
Don kin san mazan yanzu mai tsabta suke yayi idan mace tace ita yar son jiki ne zaki ga komai nata sai a,slow,
Gwago na tace min karbi wanan a cikin dabara na karba kamar mai rada tace wanan farin gorar naso nabaki tunjiya, kisha duk dai ko yanzu bai baci ba,
Amma anso kafin miji ya,shigo gurin ka kadan goga kadan a goshin ka zuwa kirjin ki da,marar ki,
Abin kurciya sai cewa nayi ai baishigo dakin ba tun jiya, har suna hads baki a tare da mama hanne,
Gurin cewa to a ina yakwana shi ?
ke nan ke kadai kika kwana, ?
Nace tare da Asmau kaunar shi mama tace mu kwana tare
Sai naga sun dan kalli junar sai kuma suka,ce lalai da akwai matsala amma Allah ya gyara kawai kiyi ta hakkuri kinji,
Tafiyan yan uwa na Umma ta,shiga kasafin kayan cicin da aka kawo mata,
Sai muryan ta kake ji yana tashi sama ita da yarsn ta da masu shigowa don ganin amarya,
Tun tafiyan yan uwa ina zaune a dakina nayi tagumi sai famsn tuna ne inda matsalar da naji suna kira zai shigo min,
Shigowan Hamza sau biyu gida baiga giccin Aisha ba a tsakar gidan, yana son shiga ya duba yana tsoron idon Umman shi,
Ganin hankalin Umma yana gurin kayan dake gaban ta ya sashi dan satan shiga gurin da nake,
Ina zaune a kasa saman tabar roban da aka shinfida a kasan dakin wanda su Gwago suka tashi a saman shi,
Ban san da shigowasar ba sai ganin shi nayi a tsaye yana cewa
Aisha ke kadaine a dakin abinda yasani saurin dan dago kaina ke nan sai kuma nai saurin dukar da kaina,a kasa,
Ya matso inda nake a zaune ya dan tsuguna gap dani kadan yana cewa kin kuwa karya Aisha, ?
A cikin natsuwa da kulawa yake tambayan nawa, ?
Na dan dago kaina a hankali nake cewa eh na karya yaya,
Hmmm naji yana cewa kiyi duk abinda Umma take so don ku daidaita da ita,
Cikin sauri na dago kai na dan kalle shi yayin da idanuwa na,da,basu raina hawaye har sun ciko ko,
Yace idan har kin kiyaye abinda take so to zaki ji dadin zama da ita sosai,
Don tafi da son duk abinda tacewa mutum to mutum ya to kawai shine zaman lafiya
Yace don haka Aisha kamar yadda na,sanki da hali irin na kirki don Allah ki cigaba dz halinki da hakkuri,
Duk abinda ta hane ki ko umurce ki dayi ki yishiba lokaci don bata son mussu da tauri kai nace tau a hankali,
Nasan baki saba da yadda muke karyawa ba,agidan nan da irin cimar da muke yi amma ina rokon ki daki daure ki ci ko yayane don samun salama kawai,
Muna ciki haka mukaji muryan yaro yana cewa wai ana sallama da Hamza a waje,
Umma tace ai yana nan shagon ka barshi a ciki yaron ya kara fadi cewa baya shago yashigo ciki yanzu
Take naga rudewa a idanun shi kaman wanda yayi wani iri laifi maigirma duk dan rude a hankali yadaga labulen dakin yai waje simi simi dashi yana cewa gani nan ai yanzu nashigo gida,
Banga giccin yarinyar nan bane tundazi shine na dubata don naga ko lafiya take,
Wani uwar harara Umma ta sakar mai sai ya sadda kan shi kasa da sauri tace baka dai jin magana ke nan ko ?
Umma yanzun nashiga don na dubata kawai ba wani abin ba,
Har zatai magana ko may ta tuna kuma sai tai shiru kawai ta kuta ya bishi da harara bayan shi inda yafita kofan gida gurin da ake neman shi,
Tun daga wanan lokacin ban kara ganin Yaya Hamza a dakina ba sai dai idan ya shigo naji muryan shi a tsakar gida daga nesa,
Kwana biyu ke nan ina zaune a gidan duk wani aiki nice ke yin shi batare da najira ko kuma ance ba,
Idan na dafa abinci Ummace ke rabawa da kan ta, don sai dai na dauko na kawo mata a gaban ts ta raraba,
Umma bata jin kunya ko nauyi gurin cika wa Asmau da dan ta karami Ibrahim tana cewa wai yarane, bari a zuba masu da yawa alhalin sa,ar mu guda da ita Asmau din,
Ba ruwan Yaya Hamza da al,amari na nima din haka iyakata dashi idan ya shigo nai mashi ina kwana da safe,
****** ********** ******
Kubura yanzu zancen ta da wanan Hamza din dan uguwar sabon gari ya kan kama don kowa yanzu yasan cewa shine zai aure ta,
Take mutane suka,soma magana a kan zance kowa na kawo suka daban daban,
Idon mama Saude ya rufe sai cewa take hassada ga mai rabo ai taki ne,
Don haka kowa ya cirewa yar ta ido ga,al,amarinta da mai baki da goro da mai baki da taba da mai baki da kuka duk suka kwaso zancen su sai suce wai Kubura to ita hakan ya sheta don haka zata daura kafan wando guda dasu ne,
Hakan ne yasa mutane suka ja bakin su sukai shiru suna kallon aikin karya, a cikin uguwa,
Ranan da safe babu yaron da zata aika ya sayo mata idomie a shagon hamza,
Hakan yasa ta yafa dan yalalon gyalen ta akai na just to cover ta fita zuwa sayowa,
Yun bayan cin mutuncin da taiwa Hamza wanan ne karo na farko da zasu gana,
Yana daga cikin shago yana mikawa wani yaro kayan da yasaya yaji wani irin kamshi ya daki hancin shi,
Da sauri ya juyo don yaga ko waye mai wanan kamshin haka a lokacin yayi zufa zufa dashi,
Ba,sallama ba komai tace aban idomie na dari biyu kwai guda shidda,
Cikin dan murmusawa yace a, hajiya Kubura ce barka,da,dare ta,wani ya, mutsa fuska tace ka,ban indomie nace,
Murmushi kawai yai mata inda a zuciyar shi yake jin ke jin wani radadin abinda take nunawa a kan shi,
Abinda tazo saya ya,saka mata a leda ya mika mata ta miko mai naira dubu guda ya cire kudin shi yace jeki kawai kibar shi,
Tace look malam wakake ne ma dauki kudin ka kabani canji na don ban son hada abina da abin matsiyata mutum yace ka kashe mai shago kawai,
Yai tsaye sororo yana kallon ta a cikin mamaki yace Kubura nine kuma matsiyaci yau don nace ki bar kudin ki,
Dakata malam may kake so dani ne bari na fada ma ko wanan ganin da kai min a dalili na,zo inbashi banda lokacin tsayawa harka da yaku bayi irin haka masu zubarwa mutum da daraja,
Ta fige ledan ta tawuce tana zuba mai bakaken magan ganu daga bakin ta,
Binta HAMZA yayi da kallon mamaki yadda akaiyi idanuwanta suka bude haka aa lokaci guda,
Shi bawai da manufar da take nufi yabata wanan alheri ba kawai din mutuncin da ke a,tsakani na,sarrakuta yanzu,
Ta shiga gida tana ta masifa Atika ce ke cewa may yafaru ne haka kuma,?
Nan tana kokarin cire dan gyalen da ta yafa a kanta take fada mata a cikin daga murya,
Wanan matsiyacin mana Hamza ke so ya kawo min rainin wayyo wai na tafi saye indomie yake ce min na bar kudin,
Nace mai anfada mai cewa ni matsiyaciya ce ko may yake nufi yatafi can