Sarautar Mata

Chapter 15 of 94

tun kafin na,amsa take cewa yau baza,a girka muna abinci a gidan bane Aisha,
Abinda yasani saurin mikewa ke nan na fito daga dakin da,sauri, inda Umma ta hau yi min fadan cewa zan barsu da yunwa ita da diyan ta na shige daki na kwanta,
Shigowan Hamza din ke nan a lokacin yake kokarin gaida Umma din yake cewa batare da ta amsa ba,
Yarinya ta shige daki abinta zata barmu mu yini da yunwa don kiyya, irin ta matan yau,
Yace ke ina waken da na saki gyara sauran na koma dakin don na dauko wanken inda Umma tabi da fadan tana cewa ai inda sanyi jikine irin na Aisha yanzun haka bata gyara ba,
Nafito dauke da waken cike a wani roba nawa mai fadi ,
Abinda ya san sasauta fadan Umma din ke nan tace kai shi kumq wanan irin a ina aka samo shi haka,?
Hamza yace wanan dai namu din ne Aishan take gyara tunda safe dana barta dashi,
Hannu Umma din takai cikin waken tana dan juyawa a hankali,
Sai ta juyo inda Hamza din yake tana cewa amma Allah yasawa wanan wake ido,da kwari wallahi kamar bashi ba ya samu gyara sosai,
To ai saiki ce min ba kwance kike ba aiki kike a dakin amma kuma a zauna ba,aci bane,
A lokacin har na share gurin murhu ina kokari tura ittace don tuwon gatin masara ne tace zamuyi da miyar busassan kubewa ,
Suna hiran su ina,aikina,sai dai kallo guda,mutum zai min ya fahinci cewa na ramay don nadan fada,sosai,
Asmau tashigo gidan inda take cewa tun kafin ta kai zaune wallahi yunwa nake ji may kika dafa muna ne, yar Agwai,
A cikin wani irin zafin nama Hamza din ya dago kai yace mata cikin dakiya kada na karajin wanan sunan a gidan nan,
Tace a cikin yar shagwaba to ai sunar ta ke nan ko,
Umma tace tunda yace baya son kina kira mai mata da wanan sunan to ki bari kin dai san halin yayan ki, ba ruwana,
Hamza yace Umma bai dace wanan sunar da yan gidan can ke kiranta dashi muma anan mu kirata dashi ba tunda ba,sunan alheri bane,
Tau kaji mai mata fa nine zaka fadawa cewa ga,abinda ya dace da matar ka a gidan nan,
Yana kokarin daukan roban waken dake a gaban shi ne Umma ke cewa yanzu kana ganin cewa zasu barka kayi wanan gwajin da dan wanan,
Yace Umma ki samu na albarka acikin al,amarin don shi muke nema,
Umma tace Allah yasa mu dace Allah ya sanya alherin sa ya amsa da amin tare da kokarin wucewa da roban inda na fito dashi,
Da,sauri na karaso na karbi robar daga hannun shi ina niyar mayar wa dakina,
Umma tace kai shi can dakina ki aje gefen gado kada ya kuma samu matsala,
Ba mussu najuya da roban nakai dakin ta kamar yadda ta umurce ni dayi,
Na gama abinci da wanan uwar ranan narabawa kowa sai dai da yake garin baida yawa abincin bai kai ba,
Gab da Hamza zai shigo gidane yaji Umma tana cewa sai na juyewa Ibrahim nawa abincin nazo ta yanka min nata,
Ya karaso cikin gidan yana cewa haba Umma ita da ta dafa ba,a bata taci mai isar taba sai Ibrahim wanda ke waje yana samun abu yana ci za,a ce ta ajewa kason ta,
Ya juya inda nake yana cewa na dauki nashi kason zai fita ya samu abin da yaci a waje shi,
Umma bataso hakan ba sai cewa tayi na bar ma Ibrahim na Hamza din naci nawa,
Ibrahim din ya,shigo gida nan ya zauna zai ci a binci ganin kayan abincin dan uwan shine yake cewa shi Yaya Hamza mai zaici dana ga anbani abincin shi,
Nan Umma ke cewa shi yasani don matarshi bata samu rabo ba,shine yai fushin zuciya yace abar mata nashi,
Da sauri Ibrahim din ya,dago kai yana cewa amma, gaskiya Umma bai dace ace matar yaya,bata samu abinci ba itace ta girka ba,
Kai kama min bakin ka kafin na bata maka rai waya fadama bata,samu ba,
Wai don suwa nake zaune a haka da kowan ki zai dinga ganin laifina haka,
Ibrahim wanda yakai loma a bakin shi yace Umma ai itace wai naga ya kamata ace taci tunda amana take a gurin ki,
Kadan yaci da,alamar a koshe yake nan ya mike ya kwaso kayan abincin yana ce min gashi ki kara kin ji Aisha,
Ina zaune inda na idar da,sallah nadago kai acikin murmushi nake cewa dadai kakai wa dan uwanka don shine bai samu abincin ba,

****** ********* ******
Motocine kala kala ke yawo a,cikin garin inda jamian tsaro suka cika ko wani lungu da,sako na garin da tsaro,
Wanan dalilin yasa mutane zuwa kama guraren nuna show din nasu da,wuri kafin guri ya cika,
Yan kauye dama makwabtan gari duk sun halaro gurin wanan taron mai dibin tarihi a,rayuwa,
A gurin zakaga manyan namun daji wanda akadade ba,a gan su ba da kuma dabbobi da ake kiwo a gida sunci sun koshi don samun kiwo na kwarai,
Taro yai taro inda har da turawa da, sauran mutanen kasar waje suka shigo don kallon wanan taron,
Hamza ma ba,a barshi a baya ba gurin zuwa da nashi kayan show din amma yana ganin irin abubuwan da wasu suka kawo duk sai jikin shi yai sanyi sosai,
Yana ji a,rayuwan shi kawai ya koma gida saboda babu wanda zai ko san cewa yana gurin balle ya kalle shi,
Zuwan manya naki na kasa yasa gurin ya kara rikicewa gaba daya inda akafara bude taro da,addua tare da fatan samun sa,a gama su nasara,
Layin masu gwajin amfanin gona daban inda haka ma layin masu gwajin dabbobin gida dana daji daban su ke,
Ga masu wasan gargajiya suna wasa kowani kabila da kalar tasu shigar a gurin,
Tafe suke inda duk gurin da wanan shugaban ya tsaya za,a bawa,mai wanan amfanin gonar nomba ta kyauta,
Tafe suke tawaga takai tawaga ta manyar ma mutane masu bada zabi ga jami an tsaro nata,bin su bayan su,
Gaskiya kaya sunyi kyau sunga abinci masu amfani yadda yakamata don basuyi tsanmanin samun abinci masu inganci irin haka ba a kasar, nan,
Wani manomi ne ya baza kayan amfanin gonar shi mutane sun taru sai kallo akeyi yadda,sukayi kyau sosai,
Maigirma babban bako ya juya don zuwa kallon wanan shagon na,wanan babban manomin,
Abokin tafiyan wanan bakon wanda yazo daga kasar waje don ganin abinda ke guda na,
Wani dan saurayi matashi mai karamin shekaru ya hango can nesa kadan da,wanan rufan ,
Yana tsaye da kayan da yazo gwaji a cikin wasu kananen roba, guda uku,
Kawai sai yaga burgewan wanan matashin da kwazon shi har ya kai ga yazo nuna nashi kayan amfanin ba tare da, jin komai ba ,
A hankali ya tako zuwa gurin wanan saurayin wanda duk yai zufa ga,rana tana kudar shi ga yunwa,
A hankali mutmin yaduka ya debo wanan wake dake a cikin roba kursa kursa dasu, yana dan jujuyawa a hankali,
Sai daga baya abokan tafiyan shi suka luracewa bai tare dasu don haka suka shiga neman shi inda suka hango shi a tsugune gaban wanan yaron mai kaya,
Sauran jama,an suka yo a kansu suna kallon su a cikin mamaki don babu wani abin azo a gani a gaban yaron amma gashi maigirma babban bako ya zo gurin yaron,
Shima,shugaban na wanan kasar diban wanke yayi yana dan juyawa yayin da,sauran yan tawagan suka shiga diba suna kallon
Kowa sai yabawa da kyau da,girman waken sukeyi gwanin ban sha,awa,,,
Nan ya jawo irin dawan da Hamza ya shigo dashi filin shima yana dubawa a hanakali,
U
Idanuwan jamaa yoyyy a kasu don su azaton su laifi hamza din yayi,
Sun dauki lokaci a tare da,Hamza suna,mashi yan tambayoyi ya ba basu amsa sai cewa,suke interested,
Daga karshe dai aka,rubuta sunan hamza din daga,cikin wa yan da za,a bawa kyauta a gurin,
Nan aka karbi sunan shi aka juye wanan kayan a cikin wasu robobi na gwajin kayan agric din da aka zaba,
Hamza ya koma gefe guda ya na sauraren su kamar yadda suka umurce shi da yayi,
An dauki lokaci mai tsawo kafina agama wanan gasar gwajin kayan amfanin gonan da,akeyi,
Nan aka soma kiran sunayen mutane ana fadin iri abinda mutum ya,burge bakin dashi daga fanin abinci dabbobi da kuma kayan ruwa,
Can kamar a mafarki Hamza yaji ana kiran sunan shi inda ya,fara ratsa taro don zuwa inda ake kiran sunan shi,
Nan wanan baturen ya daga hannun hamza yana fadin cewa Hamza matashin da yazo na,daya gurin nuna dogaro da kai har ya kawo amfanin gonan shi da,full confidence,
Ga kuma waken da yakawo gwaunati tanq bukayar wanqn irin don wani gwaji da zatayi a kan shi don haka gwauti ta,sayi wanan waken akan gudu naira,,,,,,,
Haba guri ya rude da,sowa da ihu da kuma tafe daga yan kallon da,sukazo na,sassa daban daban na kashen Africa,,
Inda wanan bature ya nemi hamza da ya bashi full address din shi da in da yake da zama,
Haba aikuwa hamza yana karba,sai kawai ya,saka kabbaraza fili da cikin zuciyar shi,

****** ********* ******
Ina zaune gurin dana idar da sallah na daga hannaye na biyu sama ina rokan Allahya rufa muna asiri duniya da lahira,
Ina gab da zan sauke hannaye na ji murya Umma a cikin murna tana cewa o, o Allah nagode ma,Allah mun godema bisa wanan baiwar da kai muna ,
Ina kuke yaran nan kufito kuji abin arzikin da ya,samay mu a gidan,
Jin abinda ta fada yasani saurin mikewa zuwa kofan daki do ganin may Umma kewa farinci haka,
Babu kowa agurin na dai fito sai naji tana cewa yau kan Allah ya nufa Hamza ya samu yar ga Allah yasa shi cikin zabbabu,
Yar fara wace ina ga ban taba yinta ba tun zuwa na gidan nasake ina cewa masha Allah ashe yaya Hamza Allah ya karba addun mu,,
Uguwa baki daya zance ya karade ko ina kowa da abinda yake fadi a bakin shi,
Wasu har dakari sukeyi wai har da mota aka bashi wasu suce ai mashin ne aka,bashi,
Ga yan murna sun fara shigo muna gida gashi shi mai abin arzikin bai dawo gida ba har wanan lokacin,
Saboda farin ciki Umma taje ta,auno muna shimkafa a,makwabta mudu daya tace nayi tuwo da,miyar sobarodo da busashen kifi,
Ina aiki ina Allah Allah kafin na gama kafin yashi nayi wanka na dan kimtsa irin da naga mata sunayiwa maza jen su idan sun fita gurin neman kudi,


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU👑SARAUTAR MATA👑
1⃣3⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA


RABBI HAB LI MIN AL-SALIHIN,,,,

YA UBANGIJINA KABANI ABOKAN ZAMA DAGA BAYINKA SALIHAN,,,


Washegari Kubura ta farka gari ya waye tangararam haske ko ina,
Tamike tanufi bandakin dake a cikin dakin ta tagyara jikin ta tsab ta dauro alwala tafito,
Saidai sam zuciyar ta ba dadi har lokacin don na ta gabatar da,sallah asuba tare da jero addu,oi,
Kubura ta na zuwa islamiya don haka tasan abinda ya kamata nadaga addini,
Matsala guda shine addu,a idan har babu tsabtatacen zuciya ba lalai ne ta karbu ba, ga Allah
Domin Allah yana amfani ne da zuciyoyin mu,
Yunwa take ji don haka tadan gyara jiki irin na,amare ta nufi cikin gidan don samun abinda zataci,
Saboda rabon ta da abinci tun da rana jiya da,mama,saude ta tsare ta dan ci kadan saboda jamma,a
Kamshin soye soye ke tashi a gidan ta nufi kitchen inda take jin motsi
Yar aiki ce ke ta faman aikin kayan break fast ita kadai a gidan,
Motsin yara taji daga bayan ta wanda batai zaton cewa Nura din yana da yara har uku ba haka ?
Basu bi ta kanta,suke magana da yar aikin su cewa tayi ta basu abinci kada su makara zuwa islamiya, don yau ba ranan zuwa boko bane,
A hankali ta juya don jin abinda yara suke cewa baba oyoyo,
Nura ne tsaye daga bayan ta , yana,wa yaran shi murmushi a cikin fara,a,
Sai ga Uwargidan mai suna Jamila tafito cikin jefa dan kafa gudan ta take tafiyan ta, tasha kwaliyanta ba laifi don kyauta ya fito sosai, matsalar ta guda shine kafa,
Ganin Kubura a tsaye waje yasa ta kago murmushi a fuskan ta tana cewa a,a amarya kece a nan ,
Yanzu nake cewa na laikoki naga ko kin tashi ai kifito mu karya,
Fuska a daure kubura ta amsa mata da cewa eh na tashi, ai,
Sai dai idanuwan ta yana a kan Nura din wanda hankalin shi ke gurin yaran shi,
Jamila tace Allah sarki to karaso mu isa dinning table sai mu karya gaba daya don ga Angon naki ya iso ai,
Kubura wace maganar Jamila din ke bugun ta kamar saukar guduma a kai,
Kubura tace ba a nan zanci ba asalima ni ba nawa tsarin ke nan ba ai,
To inji Jamila wace amsa yazo wa banbarakwai, don ita a zaton ta tasamu abokiyar zaman kwarai zasu zauna su hade kan su su zauna lafiya,
Jamila tace to ai shike nan idan kin tashi ga abin kari a table kya karya ai,,
Sai a lokacin Nura ya bar yaran shi ya nufota yana fadin,
Kizo a karya gaba daya haka muke karyawa a gidan nan mu a tare,
Cikin kwarin gwiwa Kubura tace bata tashi karyawa ba asalima ita ba,a tare da kwamacalan iyalin shi zata karya ba,
Wata uwar harara ya jefa mata wanda yasa ta shiga hankalin ta don tun a waje tasan halin Nura bai daukan raini ga mace,
Kawai dai kwadayin duniya ce yasa ta yarda ta cusa kanta a gidan shi a matsayin matar auren shi,
Juyawa tayi zuwa dakin ta duk da yunwar da take ji amma ta dage sai tajawa kanta aji a gidan ,
Don ita matar soyayyace ba matar cushe bace wace aka bashi a matsayin kyauta,

****** ********** ******
Ina, zaune a bakin magudanar ruwan gidan ina wankin yan kayan wankin mu don da,safe nake wanki saboda gudun kada rana yai min,
Babu kowa a wajen gidan sai ni kadai dake ta faman sintiri a tsakar gidan,
Ganin mutum nayi tafado gidan babu ko sallama har saida nadan razana,
Zahar ce duk fuskanta a kumbure yake da alamar dai babu lafiya ,
Nai mata,sannu da,zuwa duk da batai min sallama ba da zata shigo gidan,
Ban tsanmaci ta amsa min ba nikan naci gaba da aikina kawai,
Daga gurin da nake zaune nake iya jiyo muryan zahar a cikin kuka tana mayar wa mahaifiyar ta,abinda yafaru,
Ban damu da wai sai na saurare su ba don ba matsalata bace sai har kokina nakeyi ina jin muryan Umma har kunne, take kwarar makogwaron ta,
Sai surfawa kishiyoyin Zahara zagi take tana cewa wallahi basu isa ba,
Sai dai maigidan yasan yadda zaiyi da yar nata amma bazata yarda ana cusawa yar ta sunnu ba,agida don an ganta yar karama za,a ce duk wani aiki a gidan itace zatayi shi wai don tana karama,
Hamzane ya shigo gidan da,sallama a bakin shi tun daga kofa yakai idon shi a kaina ina kokarin shanya kayan dana wanke a giyar shanyi duk da igiyar yafi karfin tsayi na,
Tausayin yadda banda hutu ko kadan agidan yake, wanki, shara, girki, da duk sauran aiyukan gida yanzu nice mai yin su,
Kuma babu nuna gajiya ko kadan a tare dani idan ina aikin, sam ban d time din kaina ko kadan,
Sanni da zuwa nai mashi yayin da ya karba yana min sannu da,aiki idanuwan shi nabin yawan kayan da,na wanke tun da farar safiyan nan,
Dakin Umma y nufa don can ake nemar shi inda tun a kofa yake iya jin muryan Umma din,
Yashigo da,sallama idanuwan shi na akan zarah da yaga tana kuka wiwi da hawayenta shabe shabe a fuskan ta,
Yana kaiwa a tsugunne yake cewa Zarah lafiya dai ko tun da,safen nan gashi kuma kina kuka haka ?
Injin dai lafiya dai ko ?
Umma ce ta cabe zancen da,cewa ina fa lafiya munafukqn kishiyoyin ta,sun hana min yarinya zaman lafiya a dakin ta,
Umma may yafaru yake tambaya a cikin son kaguwa da jin abinda yasa yar uwar shi take kuka haka da safen nan,
Wanan karon ma Umma ce takara magana da cewa wai kamar zarah za,a ce itace zatayi duk wani aiki a gidan su,
Yacw Umma ban fahinta ba aiki kamarya za a ce itace zatai komai a gidan ita kadai,
Yanzu mai ya kawo matsalane wai take wanan kukan haka ?
Hamza ke tambayan uwar cikin dan kaguwar son yaji may faru,
A,hasale Umma tace gashi ko na fada maka abinda yafaru ,
Wai sai tadafa masu abinci tunda safen nan tunda,basu da abin da,zasu dama kunu kowa yasha,
Inda Zarah take zaune ya ke duban ta acikin mamaki yace yanzu don dafa abinci kawai ka zo gida da,safen nan zarah,
Ina idan mace tai aure duk wani aikin gida ya,wajaba a kanta ke nan,
Kamar ya ?
Umma ce ta jefo mai wanan tambayan a gagauce,
Yace Umma yanzu ina ga Aisha can tun asuban farko take wajen nan bata huta ba,
Ita ce komai na gidan nan hatta abinda ya kamata ace Asma,u ko Amina sunyi a gidan dasu jibrin duk itace yanzu maiyi,
Waya taba jin tun shigowar ta gidan nan tayi korafi ko wani nata yace wani abu, akai,
Umma ta cabe zancen da cewa oho don Aisha tana aiki a gidan nan sai akace Zarah ma taje tayi ko ?
To bazan dauka ba gida kamar gidan Bukar za,ace Zarah ce mai girka abinci safiya da marance aci,
Hamza ya dan kallo Umma yai murmushi yace Umma wanan abin ina ba bakon abu bane ga diya mace kamar yadda kikace ,
Duk yarinyar da tai aure tasan cewa akwai irin eanan a gidan aure don haka takoma dakin ta tayi hakkuri kamar yadda kowa ma keyi,
Tabari idan wani abin ya hadata da mutanen gidan ko mijinta ba akan girki ko aikin gida da yake

Download complete TXT · Novel page