Sarautar Mata

Chapter 16 of 94

bautan aure ba sai tazo ayi magana amma wanan ai kowa yasan dashi a gidan aure,
Shiru Umma tayi don bata da bakin cewa wani abin don ita da bakin ta furta mai hakan alokacin da yasamay ta akan zancen cewa,
Aiki yai wa Aisha yawa a dan rage mata wasu daga ciki arabawa Asmau da Amina su dinga taya ta,
Amma fir umma ta,rufe ido tace ai Aisha zaman aure ne yakawo ta dole tayi don suma idan sunyi aure zasu yi agidajen su,
Nan Umma ta shiga fadan karya tana fadin cewa ai ak8n ba,daya bane nan gidan har mutum nawa ne acikin sa da za a hada dana gidan da zarah take,
A karshe sai cewa Umma tayi Zarah bazata koma ko ina ba sai maigidan nata yazo sunyi mai iyaka don yarta ba boya bace, ai,

****** ********* ******
Ina zaune daki bayan na fito daga wanka ina shirin zuwa dora girkin rana,
Zahar ta,shigo dakin tana ce min bata ganni ba tun dazu gashi ta kasa barci, don ta dan kwanta ta huta amma barcin ya gagare ta,
Tace ai ina ce barci kike ke ma nace a,a cikin danbsakin fuska don bawai na saki jiki da ita bane tunda ban saba hakan ba ni,
Nake ce mata wankin kayan mu nayi yanzu nake batun fita na dora girkin rana kada na makara,
Tace kardai nace kece duk kikai wanan wanki dana gani a igiyar shanya waje,
Murmushi nai mata batare da na bata amsa ba ga tambayan ta,
Take cewa ina su Asmau ne wai naga basu gidan tun da na,shigo,?
Nan ma dai shiru nayi sai ce mata nayi naso nazo gidan ta amma banda time saboda aiki bai bari na fita ko ina,
Tace ke dai baki son zuwa ko ina aini nayi fushi wallahi ace wai har yau baki san dakina ba Aisha,
Nace ban fita ko ina saudaya na fita ko shi da darene na shiga gidan mu gurin yiwa Kubura murnan aure,
Ranan a tare da zarah mukai girki inda sai kallo na take da nazari na kawai,
Take ce min a lokavin da muke cin abinci a wani katon ture ,
Aisha idan yamma yayi Alhaji baizo ba komawa zanyi dakina,
Don maganan yayana yasa jikina yin sayi kuma na gane kuskure na,
Don dai kinga yanzu bawai muna zaman fitina bane da abokan zamana amma kinga kawai sai shedan ya rudeni nai masu rashin mutinci kan dan abinda baikai yakawo ba,
Ita kuma Umma maimakon tai min fada tunda ke ma anan tsaye kike kyam da,aiyukan gida wanda ko kwatan shi banayi amma wai sai ta goyi bayana,
Sai a lokacin nai magana nake cewa Anty zarah kiyi hakkuri duk abinda diya mace zata gani a gidan auren ta idan har ba mijintane ya kawo wani abin kaucewa addini ba to muddin tai hakkuri zata ga bayan abin in har akwai rayuwa,
Don kin ga ni karama ce amma na,dade da,sanin cewa hakkurine rayuwar aure,
Musanman ladabi da biyayya suke kawo zaman lafiya a aure, don wanan kawai ya ishi mutum zama makamin daki,
Don haka ki bar sauri zuwa gida kawo karan rayuwan auren ki wa iyayye,
Don sai ke kiyi hakkuri amma su gida bazasu matan ba karshe ma,sai su kama ganin bakin mijinki su dauke shi mai rashin adalci,
Cikin dan marairaice murya kamar wace zatai kuka taje cewa wallahi nayi nadamar wanan zuwan gida danayi matar yayana,
Kuma fa Alhaji baya ko gari yatafi kurmi kai kaya gashi ita uwar gidan mu bata son abinda zai bata rayuwana a gidan nan ko kadan,
Nace Gaskiya Anty Zarah kiyi maza ki koma dakin ki kafin Alhajin yadawo kiji kunya tace ai yanzu kuwa don duk abinda Umma zata ce sai dai ta fada, amma ni komawa zanyi dakina tunda ba fada nayi da kowa ba,
Tace bari a kira min yayana ya bani kudin mashin yanzu nakoma nace sai kuma kibawa mutanen gidan hakkuri tace bari kedai Aisha,
Yaya Hamza ta leka da kanta takirashi dakin mu suka shiga inda ta fada mashi kudirin ta na niyar komawa gidan mijinta,
Kirana yayi yana cewa nazo na bashi kudin daya bani ajiya jiya dadaren ,
Nadauko mai yacire duba daya daga ciki yabata yace taje tayi hakkuri a dakin ta,
Anan Allah ke son gani rayuwan ta don haka don Allah ta rika hakkuri don dai taga mijin ta yana sonta sosai kada tabari aji su dashi,
Sallama mukaji na wata mace, a tsakar gida Aisha naga tadafe kai tana cewa Lah wallahi yayace tazo da kanta,
Sallamar matan biyu ba, amsa mata ba sai nice nafito daga daki ina karba mata cikin sakin fuska nake mata iso da ta shigo zuwa dakin Umma,
But Umma din tafito daga waje tana cewa gani ai basai tashiga ba,
Murmushi matar tayi a,cikin fara,a take cewa ina dai fatan zarah tana gidan nan a daidai lokacin da nake shimfida mata tabarma don ta zauna,
But Zarah ta fito daga dakina tare da yayan ta tana cewa Lah yaya yanzu fa nake batun komawa gida sai kuma gaki,
Matar da,aka kira da yaya ta dan kaiwa zarah din harara tace shine kawai kikafito amarya babu sallama ko sai nadawo,
Tace ban zaci cewa zai kai har wanan lokacin agida ba shiyasa nafito,
Haba Amarya yanzu idan Alhaji yaji cewa kinfito ya kike son ku kwashe dashi,
Nima sai da na idar da azzakarah din da nakeyi ne naji shiru shine na tura danki ya,dubo min ke yake cewa,wai bakya nan kuma kin rufe kofa,
Shiru shiru zaki dawo bamu ganki ba,shine nake ce masu subari na biyo ki naji injin dai lafiya ko ?
Zarah wace ke ta faman shan harara gurin Umma take cew lafiya nazo duban matar yayanane gatanan,
Sai a lokacin matar ta kai kallonta gareni tana cewa au itace nan
Tubarkkalah masha Allahu, sam barka wallahi,
Allah ya bada zaman lafiya yabada kazantar daki da,wuri,
Umma kan baki ya mutu don haka taja bakinta tai shiru sai faman cika take tana batsewa don takaici,
Tana kallo Zarah da,abokiyar zamanta sukai muna Sallama suka tafi,,
Inda nai mats alkawarin cewa zan shigo mata wuni insha Allahu
****** ********* ******
Abin ya,daure wa Kubura kai sosai don tun daren farkon ta,dashi duk abu ya karkare jagule mata a gidan,
Gadai komai na arziki kamar yadda take son samu a rayuwanta amma abu yaci tura,
Don sam ko kallon arziki bata isheshi ba balle yasan da,wata amarya agidan har yai rawan kafa a kanta,
Dakinta yanzu ko kallon part din tanaji ma baiyi,a rayuwan shi kwatakwata,
Gashi ita tana bukatar kasancewa a,tare da mijin ta koda yaushe,
Irin rayuwan data shirya zasuyi idan sunyi aure dashi ko ita idan tayi aure zatayi da mijinta yanzu duk babu wanan a tare da ita,
Saidai ya shigo taji muryan shi yana hira da yaran shi ko kuma magana da yar gurguwar matar shi mai dangisawa,
Don haka yau a,shirye take da zaran taji muryan shi zata tunkare shi don taji inda matsalar yake mata,
Tana zaune zaman jiran shi don ta san lokacin dawowan shi gida zuwa yanzu, duk da bata samun kyakyawan kulawan shi,
Zaune duke falon gidan gaba,dayan su ana hira sai dai ita kubura bawai hiran ne takeyi ba,
Ya,shigo da,sallama hannun shi da ledoji guda biyu yau ba karatu duk yaran suna gida a lokacin,
Sannu da zuwa suke mai yana ta faman ansawa da fara,ar shi sai da tace mai sannu da zuwa kamar kowa a gurin
Sannan yasan da zaman ta a falon itama ledar dake hannun shi ya mikawa yaron shi guda yana cewa karbi wanan naku ne,
Dayan kuma ya mika,wa Uwargidan shi yana cewa ga naki ke kuma,
Daga haka yai shigewar shi dakin batare da ya amsa mata gaisuwan nata ba abainin iyalin shi,
Sai da akai kamar minti biyat zuwa goma hankali yan gidan yana ga tabon tsarabar da ya,shigo masu dashi,
Kubura ta mike a hankali tabi bayan shi zuwa dakin nashi sai dai gabanta sai faman faduwa yakeyi,
Tai sallama inda ta hango shi yana kokari balle aninin rigar sa baka dake jikin shi,
A cikin yar sakin fuska ya karba sallaman nata inda ta tako zuwa gare shi a hankali,
Ya zubo mata idanuwan har ta karaso gare shi inda ta zube a gaban shi tana mai marairaice muryan ta,
Don girman Allah Alh Nura ka fada min abinda nai maka kake wanan fushin dani haka ?
Wata irin tsawa da harara ya,daka mata a lokaci guda
Yana cewa amma kin raina min wayo da hankali Kubura,
Ni zakizo don baki da kunya kina tambaya na wai may kikai min,
Kina nufin ke nan ma baki san abinda kikai min ba,
Dake da uwar ki kuna nufin ni shasha nrme ban san may nakeyi ba ne ko ?
Oho so kike na zauna nace ke Kubura ga abinda kikai min
Kubura tace cikin sanyin murya amma yana dakyau daka fada min don nasan laifin da nai maka kaga sai na gyara ,ko,
Tsaki yaja mata tare da kara balla mata wani harara yana cewa look Kubura ki fice min daga daki kafin na kara hasala dake,
Rainin hankalinki yana,so yai yawa don har zaki iya,shigowa ki nuna min baki fahinci may nake nufi ba,
Bazan taba yarda da ke ba,a,rayuwata don kin bani mamaki sosai wallahi,
Kubura ta,dago kai idanuwan ta,da,suka cika da hawaye a lokacin tace a cikin raunin murya,
Alhaji shin dama ka,auroni ne don kazi ka,wullakantani kaci min mutunci yadda ranka yaso ko kuwa,
Kayiwa Allah Alhaji idan har da,wani manufa ka kawoni gidan nan dama ba,sona kakeyi ba ka sallamay ni na koma gidan mu yafi min wanan zaman a haka,
Ya kawo mata wani irin naushi a fuska da,sauri Kubura ta kauce ma naushin,
Yana cewa yar iskan banza kawai kin riga da kin gana zubar da mutuncinki duk a,waje shine zaku hada ksi da mahsifan ki ku cuce ni,
Don ina Nuran mahaukata zaku yi min rufa rufa ba zurfi azaton ku bazan gane ba ko may ?
Da,sauri Kubura ta,dago kai tana mai kallon shi a lokacin duk idanuwanta sun kawo ruwa yai tsuki yanufi hanyar bathroom din shi yana cewa idan nafito ma,samay ki a nan sai na,wullakan taki a gidan nan yau,
Kubura taga da gaske yake don haka tafice tabar mashi dakin tafito bata damu da mutanen dake falon ba tana kuka,



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
👑SARAUTAR MATA 👑
1⃣4⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA


YA ARRAHAMANI RAHIM, YA ZUL,ZALANI WAL, IKRAM,,,,


YAN UWA INA MAI MIKA GODIYANA A,GAREKU HAR KULLUN DA IRIN HADIN KAN DA KUKE BANI GURIN GANIN SAKON DA ZAMU ISAR A WANAN DAN LABARI ZAI AMFANE MU A RAYUWAR MU, ALLAHUMA AMEEN ALLAH YA BAMU IKON KARA RIKE AMNA AKAN ADANA MIN WANAN NOVEL DIN ANAN BATARE DA MUN FITAR DASHI WAJE BA,,,
NAGODE YAN UWA


Zancen karatun Hamza yan zu an kamala komai don haka,sai faman shiri yake na tafiya karatun shi,
Inda zai tafi ya barni da Umma Rabi da yan uwan shi a gida, tare zan zauna dasu sai dai yazo indan ya,samu dan chance,
Ummu ce mai shiri hatta kayan da zai tafi dasu a dakin Umma jakar tafiyan nashi yake,
Ni iyakata ace na dauko abu kaza daga cikin kayana na jeni na dauko,
Alokacin Umma tafi nuna matukar damuwar ta ga tafiyan na Hamza sosai,
Don har tadawo tana bani tausayi don dan motsi kadan zata daga hannu a sama tana cewa,
Ya Allah ga dan marayanka nan Hamza baida kowa a garin mutane Ya Allah ka,zama gatan wanan yaron ka,tsare muna shi,
Sai daren tafiyan nashine bayan ya kamala muna komai da ya kamata ace ya bar muna,
Kanin Ibrahim dayake shine babban yanzu bayan Hamza din zai zauna a,shagon dan uwar nashi,
A wanan daren ne Hamza ke kara jamin kunne akan na kara hakkuri da zama da mahaifiyar shi da yan uwan shi inda yake ce min na kuma dinga kokarin kula,da kaina musan man cin abincin da nake sakaci da ci a cikin lokaci,
Lokaci mai tsawo muka dauka dashi a ciki wani yanayi da ban taba sani ba, ,
Bayan ya samu natsuwar kan shi yake ce min Aisha wanan sauran kudin dake a gurin ki idan wani bukata ya taso zaki iya dan dauka daga ciki kina amfani dashi a,asirce,
Sai kuma yai shiru kamar mai nazari can yake cewa naso ace Umma ta barki ke ma kin dan ci gaba da karatun ki don hakan zai kara kawo min kwanciyar hankali a idan nake,
Wani irin abune naji a,raina wanda zan iya cewa kolon bakin cikine yadan tokare min a,wuya na,
Ya kare zancen shi da cewa ina fatan zan je nadawo batare da na,samu wani matsala daga gare ki ba,
Nai maza nace mai cikin dan karayar murya insha Allahu ba zaka,samau ni mai saba maka,ba,
Yace madallah
Sai naji yana sauke ajiyar zuciya a hankali tare da dan kifa cikin shi ina zaton tunane yakeyi,
Gari na,waye gaba dayan mu muna a kofar dakin Umma inda suke daga ciki suna kara kimtsa kayan nashi,
Bai dauki dogon lokaci ba ya fito rataye da wata bakar, jakar shi da,ya,sayo na tafiya,
Sallama yai damu a cikin wani yanayi, da bana dadin raiba ,
Umma har kofan gida inda zai hau mashi zuwa tasha ta bi bayan shi a cikin addua,
Daki na na juya acikin wani irin dacin rai wanda ban san dalilin shi ba, a lokacin,

****** ********* *******
Iyanzu Kubura abin duniya duk ya taru yai mata yawa a rai don a gurin Jamila matar Nura kawai take dan samun sassauci a gidan,
Ko shi ba wani can mai yawa ba saboda ta fahinci a kwai rashin mutunci a tare da Kubura din,
Gashi kimanin kwanaki takwas ke nan rabon da taga Nura a idon ta,
Kullun bata sani dawowan shi kuma bata sanin fitan shi gidan,
Sai da abinda take zato ko tsanmani shine, yana dawowa ne a cikin dare da,asuba yake kuma,barin gidan,
Jamila ce ta dan tako a inda take zaune tana cewa kauna ta wallahi yau naso naga mai gidan akan zancen kayan store din mu amma kuma lafins nane daban fada maki tun jiya ba ki fada mai, gashi yafita kuma ina ga mai ma na yau kawai ya rage,
Tace a cikin dan sakin fuska aiko da tun jiya naji da na fada mai ,gashi ya fita tun safe kamar yadda ya saba fita,
Jamila tace ai nace laifina ne amma kada ki damu zan dan yi dubara don baza rasa abin yi ba ai,
Ta mike dingis dingis ta yi hanyar fita waje ta kiran yar aikin su dake daga waje,
Kubura tabita da wani wawan kallo tana cewa gurguwar banza kawai sai na ture dan kafa gudan wata rana naga tsiyan botsewa ta bayan nan,
Har kwana goma,sha bata sake ganin Nuran ba sai a daren na sha biyar ne tana kwance a cikin dare taji motsin shigowar mutum dakin,
Dakyat ta bude nauyayan idanuwan ta dake cike da,barci a cikin su,
Ta gefen ta ya kwanta a hankali inda yaja bargo ya dan rufe su aciki a tare,
Batai tsanmanin cewa ya kai ga gamsawa da abinda yake so ba taji yaja tsaki,
Inda ya mike yakai wani lokaci a gurin window dakin a tsaye can taji yabar dakin a cikin bacin rai,
Gaban Kubura ya yanke ya fadi inda take cewa kar,dai ace shiga tsakanin su akayi da angon nata Nura,
Haka gari ya waye mata a cikin tunanen abinda ke faruwa a tsakanin su da mijin nata,
Sai dai tasha alwashin cewa zata ci gaba da boye sirinta bazata yarda har mazauna gidan su fahinci cewa akwai matsala a tsakani ta mijin nasu ba ,
Abinda bata sani ba shine Jamila ksllon ta kawai takeyi don ta,fahinci akwai matsala tun farko a tsakanin mijin nasu da amaryan shi Kubura,
Don ita fa Uwargida ce duk wani motsi na duk wanda ke acikin gidan yana a idanuwan ta,
Sai dai kawai ta nuna rashin ko in kula a fili tunda ba a tambaye ta komai ba a zance,
Idan mutum ya ga Kubura zai yi zaton cewa tana a tare da farin ciki saboda akwai ci da sha a gidan ga sutura na alfarma,
Abu guda yai mata nisa shine so da kauna mijin da take zaune a gidan shi a matsayin mijin aure,
Kubura karo na farko da tazo gida inda take matukar son hanin mahaifitar ta don duk fadin duniyan nan babu wanda zata iya fadawa matsalan ta,sai mahaifiyan nata,
Kubura wace ta,shigo gidan su da yar makalalan fara,a a fuskan ta,
Amma bai hana su Ummi da Atika su fahinci cewa akwai matsala a tare da ita,
Atika ce uwar shishigi take cewa da mai gidan naki kuke be ?
Kubura tai wani dan tabe fuska tana cewa yanzu ya ajeni ya tafi bazai samu shigowa ba sai yadawo,
Ummi ta dan karaso ida suke tana wa Kubura din yaya, gida da mutanen gidan ba,wai sun damu da sai ta,shigo ta gaida su ba,
Badon komai ba,sai don sani halinta da,sukayi na tsageranci tun a gida balle yanzu da take ganin cewa ita ma matar daki ce kamar kowa,
Daki mahaifiyan ta ta shiga inda mama Saude wace ke wanki a bakin kwatan gidan ta taso tabi yar nata daki wace ta shigo da,alamar a gajiye take,
Mama Saude na,shiga daki ta,samu Kubura kwance saman gado rigingine,
Tace a cikin yar fara,ar ta ashe kuna tafe shine bamu sani ba nadan maki tanadin wani abu,
Dagowa Kubura tayi daga kwancen da take tace cikin bata fuska mama barshi kawai ba wanan bane matsala,
Sai ga hawaye shar daga idanuwan Kubura tana fadin mama wallahi a kwai matsala sosai,
Kofa Mama ta,duba da,sauri idan babu mai shigowa dakin a lokacin,
Tace wa yar nata share hawayen ki kada wani yazo ya,ganki a haka kina kuna,
Juyawa mama tayi zuwa waje don ta dan saka mutana

Download complete TXT · Novel page