Sarautar Mata

Chapter 17 of 94

fita daga zargi inda tabar kubura din tana darzan kukan ta ita kadai a daki sai da tai mai isar ta tagaji don kan ta ta share hawayen ta,
Mama Saude wace duk abinda take hankalin ta a tashe yake,sai faman tunane take ko daga ina aka samu matsala da yarta,
Shin da abokiyar zaman ta ne ko da maigidan nasu ne take da,matsala,
Mama Saude ta koma dakin a lokaci yar nata ta dan samu natsuwa daga kukan da takeyi
Jin shigowar mahaifiyar ta yasa ta dan dago kai tana sauke sanyayar ajiyar zuciya,
Mama Saude ta samu guri ta zauna don ta ji may ke faruwa da yar nata alfaharin ta,
Ki natsu Kubura ki min bayanin may ke faruwa,ne wai daga ina kuma matsala ta,fito maki, tafa a cikin dan tausa murya,
Cikin dan sauta murya take cewa wallahi mama daga Nura din ne amma don kwata kwata tun ranan da na,shiga gidan ban da wani matsayi mai muhinmanci a gare shi,
Sai kiramin yake wai muncuce shi mun zalunce shi mun mai munafunci,
Da,sauri mama tace mata a kan may kuma Kubura ?
Mama nima ban sani ba wallahi abinda dai yake yawan fadamin ke nan a duk ranan da muka kasance a tare dashi,
Kubura ko kin taba sanin wani da namiji ne a,waje kafin kiyi aure, ?
Da sauri Kubura ta dago kai a cikin hawaye tace wa uwar nata ,a,a mama, wallahi ban taba kwaci da kowa a waje ba,
To idan ko har hakane shiga tsakanin ku akayi ke nan ?
Kubura tana kokarin tsayar da hawayen ta take fadin nima wallahi mama tunanen da nakeyi ke nan ,
Don wallahi matar nan tashi ba karamar munafuka bace don nuna min take wai ita ta Allah ce a fili gata abin tausayi amma,sherin ta yai yawa,
In kin ga yadda yake wani nan nan da ita da yaran ta a gidan sai abin ya baki mamaki kamar ba gurguwa bace,
Mama Saude tace ai nasan irin su ko bagani dasu ba,a gida badon ina tsaye ba agidan nan da ai yanzu sai tarihi na ko,
Don haka ya zama dole mu dauki mataki akan ta zata san da cewa dani take, ai,,,
Haka kubura tai yini daga baya tadan sake jiki tafito waje inda suka dan taba hira da matan gidan nasu sama sama,
Har take tambayan Ummi labarin Aisha Ummi bata bata amsa ba amma Atika ke fada mata cewa ai Hamza ya koma makaran ta sokoto karo ilimi,
Kubura tace wata sabuwa kuma,

****** ********** ******
Abinda ya daure min kai yanzu shine tun tafiyan Hamza makaranta na rage yawan aiyukan da,nake a gidan Umma Rabi,
Yanzu a tsakani na da ita sai wani haba haba take min, ba tsangwama ba,takura,,
Idan ina daki itace zata kwada min kira tace nazo ko nafito mu sha iska a,waje,
Akan shigo da,waya wani lokaci daga waje wurin abokan shi sai mu gaisa da shi, daya bayan dayan ,
Sai dai hiran da shi da Umma yafi daukan lokaci don bata bari na dauki lokaci muna hira, balle ma ni may zance mai,
A wani safiyane muka tashi da labarin cewa motar yan zuwa kasuwar kauye ta,yi accident,
Hakan yasa hankalin mu tashi don mun san cewa akwai mutanen uguwar mu masu zuwa don da farko har da Ibrahim za ai wanan tafiyan amma sai daga baya yace bazai samu zuwa ba don rana yayi a lokacin,
Amma Baba Mudi yana a cikin motor cewa Ibrahim wanda yazo yana fada muna,wanan labarin na tashin hankali,
Hakalin mutane duk a tashe yake a lokacin kafin aji labarin halin da suke ciki,
Sai zuwa dan rana akasamun labarin cewa al,amari da sauki sai dai sunji ciwo daga cikin su akwai masu kariya wasu kuma basu ji ciwo ba ma sosai,
Shi Baba Mudi yadan samu gwaucewa a kafadar shi hakane yasa bayan an ja mai akadawo dashi gida daga asibiti,
Yan uwa da abokan arziki sai shiga suke don zuwa duba lafiyan Baba mudi wanda a zahiri yake jin jiki,
Duk yaran shi masu aure a lokacin suna gida gurin ganin jikin mahaifin ns su,,
Ganin hakane yasa Ibrahim wanda ke zaune waje yana ganin mutane na ta shiga yashigo gidan ,
Yana kwada min kira a kwance nake lokacin dakina kadaici yana damuna,
Sai nake jin kiran daga sama na taso zuwa waje don naji may yake kirana dashi haka ,
Ina daga labulen dakin nawa na hango shi a tsaye zai shiga dakin Umma yana fadin ki shirya ki shiga gidan ku ki gaida Baba don naga duk yan uwan ki sun shigo gidan, don duban jikin malam din,
Kinga ke gaki a kusa ke ce yadace ace kin fara shiga, amma baki shiga ba har yanzu ,
Yadda ya fahinci fuskana yasa shi gane cewa umurni nake jira daga gurin Umma,
Ibrahim yace kai tsaye jeki shirya ki shiga ki duba lafiyan shi, ki dan zauna har zuwa lokacin da zaku watse,
Umma ce tafito daga bandaki hannun ta dauke da tsohuwar butar ta duk ta mokade take cewa,
Tau rasa kunya kaine ma mai bata umurnin fita ke nan ko,?
To dakata kaji ko mijin da ya ajeta bai isa yace tafitaba kai tsaye ina cikin gidan nan,
Ibrahim yace Umma yanzu may ye rashin kunya aciki mahaifin su ne fa ya auna arziki duk yan uwanta dake nesa sun shigo sai ita dake nan manne dasu ne za,a ce har zuwa yanzu bata shiga ba,
Umma wanan ai sai ki sa mutane su zarge mu akan yarinyar nan, wallahi dama gashi an fara fadin cewa kece ke takurawa yarinyar nan,
Kin ga za,a ce ai fon bashi ya haife ta ba yasa bata shiga gaida,shi ba,
Umma ta aje butan dake a hannun ta tana cewa cikin salati tare da tafa hannun ta,
Ibrahim bai bari ta furta komai ba yake cewa, yanzu dai Umma,don Allah ki bari ta tafi kawai koma maye daga baya zamuyi maganan,
Ya shige dakin ta don ya dauki abincin shi a ciki yayin da yabar Umma a waje tana ta faman sababi dashi,
Daki na koma na gyara jikina na canza tufafin jikina tare da sake hijjab dina,
Na samu Umma a bakin randar ruwan ta tana zuba ruwa a wani kwano mai fadi,
Nake ce mata a,sanyayye Umma zan tafi sai na dawo, ki gayar min dashi don dazun da,aka dawo dashi na,shiga don ina waje suka dawo,

****** ********** ******
Baba yana kwance a saman katuwar tabarman roba a barandar kofan turakan shi Atika tana daga gefe tana mai fitara a hankali,
Nashigo gidan da,sallama na idanuwa na akan baba wanda ke cije labben shi ya na gyara kwanciyar shi a hankali,
Direct inda yake na nufa ina mai gashe shi tare da mashi sannu da jiki da auna arziki,
Daga nan nagaisa da,su mama Saude da Ummi na, dake daga cikin kitchen tana aiki,
A hankali na mike inda na kwabe hijjab dina na rataye a saman kofan dakin Ummina na shiga kitchen din muka karasa aikin a tare,
Su Kubura suna dakin mama Saude suna tahira a cikin kyalkyala darita kamar ba mahaifin su suka shigo dubiya,ba,
A tare Ummi ta,saka muna abinci dasu acikin wani katon ture duk da naci abinci a gida amma Ummi tace naje mu hada hannu dasu,
Anty Sa,a ce kece min bayan nadan samu guri a can gefe na zauna,
Yar Agwai ke dai ba,ruwan ki da zuwa gurin kowa kin yanke zumunci da kowa ko ?
Nai murmushi ina cewa anty ai zan zo sai yadawo gari zan shigo in gaida ku,
Kubura ta tabe baki tana cewa idan ma baki shigo ba ba sai ki ta zama cikin wanan rubaben gidan naku ba,
Anty Sa,a tace haba Kubura wanan wani irin zance ne kuma haka sai kace ba yar uwar ki ba,
Yar Agwai din ?
Tawani dan tabe baki can gefe sai uwale ce ta canza topic din hiran a,daidai lokacin da za,a fara cin abincin dana kawo,
Wai ya zancen wanan abin da kikace zaki aiko min dashi ne ranan?
Nan suka fara hiran irin kayan matan da suke amfani dashi,
Da kuma irin yadda abubuwa ke gudana a tsakanin su da mazajen su,
Wani irin mamaki ne ya rufe a urin bayanan da,suke tun dai Kubura da yarta,
Nan suke musulta abinda ya dace mace ta soma yiwa namiji wanda zai sa macen shiga cikin rayuwan namiji har abada,
Tsit nayi zakace ai bani gurin sai sauraren zancen su nake yayin da idan sun fadi wani magana nakan ji shi a matsayin rashin kunya ne,
Don tayaya za,a ce mace ta zage tanawa namijin irin bayananan da,suke ta fadi a fili,
Ganin hiran nasu bazai kare ba na mike zuwa gurin kara gaida Baba sai a lokacin na shiga daki gurin mahaifiyata,
Tana zaune da yaranta suna cin abinci wanda nake gani tashin su ke nan daga barci take basu abinci
Bayan na zauna ne Ummi ke ce min to yaya labarin mijin naki ?
A kunyace na amsa mata da fadar lafiya kalau ,
Tau ki daiyi ta hakkuri don duk matar da mijinta yake karatu sai tayi hakkuri,
Hakama zama da sararkuwa sai ki yi hakkuri k8n kai zuciya nesa,
Don koda yake naga ai zaman naku ba,wani tsangwama sosai,
Aiki dai ne kuma kin riga da kin iya su ko tun a nan gida don haka ki ta hakkuri, kin dai san irin halin da nake ciki a gidan nan ni duk abinda muti
Um zai yi na kan barshi da,Allah don Allah bai barci ,
Na amsa a hankali da fadan To Ummi nagode insha Allahu zan kula kamar yadda kike fada min kullun,


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU



👑 SARAUTAR MATA 👑
1⃣5⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA


Na kamla duk wani aikin da zanyi a,wanan safiyan don yanzu ba,wani aiki mai yawa nakeyi ba,
Don sau daya,muke dada abinci tinda Yaya Hamza baya gari,
Abinci dare kawai nake dafawa inda da rana zamu gyara sauran tuwo ko yan cima muci sai dare kuma za,a ci mai zafi
Hakan yasani yau yanke shawaran na tafi vidan zarah nakai mata,ziyara kamar yadda,nai mata alkawari kwanakin baya,
Zama babu wani abinyi a gidan zaman haka kawai ya fara isata, banda yadda zanyi don tun tafiyan Hamza sai komai na gidan ya tsaya muna cif, ba wani motsi a gidan kamar baya,
Yau dai na yanke shawara a raina zan cewa zan tambayi Umma zance zuwa gurin Anty Zahar kamar yadda nai alkawari zuwa a gaban ta,
Da,daddare kuwa suna zaune gaba daya diyan Umma suna a tsakar gida zaune a,saman tabarma suna cin abinci,,
A can daga karshen tabarman kadan nazsune sai dai zaman tankar a takure nake a gurin ,
A hankali na kira sunsn Umma tare da dan sunkuyar da kaina a kasa a hankali,
Abinda duk yadawo da hankalin su a gare ni ke nan lokaci guda,
A cikin ladabi na fara mata magana da cewa Umma dama ina son na tambaya ne ina son zuwa gidan anty Zahar ne kamar yadda nai mata alkawari ranan ,
Nakarashe zancen a cikin dan kara dukar da kaina kasa a hankali,
Yar nan wai wanan futar da kike yawan yi haka na may nene ?
Don kinga mijinki baya gari shike nan wani son fita yawo yazo maki a,rayuwa,
To bazaki ba shin gidan Zarah yin ma ma wai kawai don son zuwa ganin may ?
Wani iri naji a raina tare da kokarin hade yawun da suka taru min a bakina masu daci,
Kafin na karasa hade su sai naji muryan Ibrahim yana cewa Umma yaushe Aisha tafita gidan nan banda labari,
Shiru Umma tayi tai banza dashi tankar bata jishi ba yace ko fitan da tayi zuwa gaida baban su shine fita Umma,?
Asmau tace ni wallahi Umma, Aisha dai ce amma ina zan iya ta zama gida haka ko da yaushe cabdi gaskiya nikan zanta zuwa gida kuna ganina koda yaushe,
Amma gaskiya Umma k8 barta dan Allah dai ta tafi gidan Anty don bata taba fitaba fa,
Jibrin yace wanan ai ta zama kifin rijiya bakauya kawai koda yaushe tana gida gurin umma kamar wata tsohuwa can,
Umma tace tooo wooo ke nan kuna zugata ta fara kirkiro fita zuwa uguwa nan da can,
Umma, kofa kitso da kumshi Aisha bata fita zuwa sai dai kullun itace mai jagwalgwalawa kanta haba don Allah dai Umma a sasauta mata wanan abin haka man,
Umma ta juya inda nake zaune a marairaice tana cewa, kinji ai sun yardan maki saiki shirya idan kun tashi zuwa ku tafi,
Ni dama bawani abu bane ban son wanan irin yawan fitan na matan zamani yarinya da kurciyar ta kin ganta nan yau gobe ki gan ta can kamar ba aure take ba,
Aisha kan ba zatai haka ba Umma wace tun tana gidan su fita bai damay ta ba, ma,
Hira,sosai ake a gurin na rayuwan duniya wanda akasarin firan ya koma a can gurin yan uwan su wa yanda zance tun shigowa ni banga suna wani mu,amula dasu yadda ya dace ba,
Washe gari tunda safe na shirya don zuwa gidan anty Zahar yini,
Na fito a,cikin shirina na nufi kofan dakin Umma don in mata sallama da kuma kiran yar rakiyata Asmau don mu tafi,
Nace a sanyaye Umma na, shirya zamu wuce ta miko min wani leda tana cewa gashi ku kaiwa zarah kunce ina gaida ita,
Asmau tafito a cikin shirin ta inda na dauki ledan da Umma taba sako mukai mata sai mun dawo muka bar gidan,

****** ********* ******
Karatu sosai yake ba kama hannun yaro don shi dama mutum ne mai kwazo a,rayuwan shi,
Dan lokaci kalilan sunan shi yai fice a gurin dalibai da malamai a makaranta inda suka bashi classrep, na su,
Mutane suna mashi kallon sauri ne matashin wanda baida ko budurwa balle matar aure a gida,
Hakan yasa yan ajin nasu yan mata suke kawo mai hari don son kutsa rayuwan su gare shi,
Amma da yake shi mutum ne mai bahagon rayuwa sai ya,nuna masu tankat bai fahince su ba bai gane nufin su ba a kan shi,
Wani lokaci zai zauna yana tunanen gida Umma Aisha yan uwan shi, sai kuma shagon shi ,
Ga damana ta sauko yanzu hankalin shi ya koma ga noma tuburan hakan ne yasa shi yanke shawara cewa karshen wata zai dan je ya ziyarci gida kafin su fara texts da exam yadawo,
Sabon Abokin harkokin shi na makarata mai suna Nazifi, shine ya hango shi a zaune daga gurin da yake yana ta faman tunanen gida,
Nazifi ya karaso gaban shi inda ya dafa kafadar shi ya zama yake fadin mutumina yaya akayine na hango ka tun can zaune ka,shiga vabration, haka,
Hamza ya dan sauke ajiyan zuciya tare da gyara zaman shi yana cewa bari kai dai mutumin
Wallahi hankalina ya koma gida ne ina tunanen iyali na ne?
Dariya sosai nazifi yayi tare da dan tafa hannayen shi yana fadin wallahi har ka bani dariya sosai,
Wai iyalina sai kace wani magidanci wanda yabar mata a gida ,
Murmushi kawai hamza yaiwa Nazifi tare da mikewa tsaye yana fadin to da kai may kake nufi ne wai, ?
Yaro kai ke nan muje hostel mu samu abinda zamuci Nazifi yace da dai yafi maka wanan fargab dajin da kakeyi,
Maganar abokiin shi na,gida,ne ya fado mai a,rai inda dazai zo yake ce mai yasamu yar waya yasaya yabar daya koda yar nokia ce a,gida dayan kuma ya rike a hannun shi,
Sai yanzu yagane hikimar yin hakan da abokin nashi ya,bashi shawaran yayi kafin ya bar gida,
Don gashi yana,son sanin halin da yar mutane take a gida da ya barta tare da,Umma da yan uwan shi,
Yana gidan ma yaya,suka kwashe da,Umma, balle yanzu da bai kusa dasu
Duk da ga mata,nan wayayyu yan birni yana gani bila,adadi, amna sam hankalin shi bai taba,raya mai ya,shiga cikin so ko kaunar wata har sha,awa,yashiga ba shi kawai idan ma,wani abu yadan bijiro mai yakan dan tuna,da,yar matar shi da yabaro a gida duk da karama,ce amma,tafi mashi wa yanda ba halal din shi bane,

****** ********* ******
Mun shiga gidan sukuburan da,sallama sai yan kalle kalle nake tun a kofar shiga gidan, don wanan ne karo na farko da zan shiga gidan, nasu,
Gidane mai tarin iyali mata da yara a cikin sa don tun a kwanan shiga cikin gida zaka fara jin hayaniyar mata da yara yana tashi,
Parts, parts na mata biyu biyu suna,fuskantar junan su,
Anty Zarah tana tsakar gida tana shanya wankin da tayi mukai sallama inda ta tare mu da murna tana fadin, a,a yau matar yaya ne a gidan namu lalai yau ana ruwa a garin nan,
Ina yar dariya yayin da nakewa sauran matan da suka sako muna idanuwa don su kalleni da kyau,
Cikin yar siririyar muryata nake masu ina kwana tare da dan karasawa gurin su,
Matar da na ke zaton itace uwargidan su na,shedata don kwanaki da ta zo ta biyo bayan Zarah din yasa na gane ta,
Mun shiga dakin zarah duk da bawai takai sauran yan uwanta kayan daki bane amma dakin nata fes fes gwanin ban sha,awa,
Mun zauna tafita zuwa can sai gata da goran kunun zaki mai sanyi da ruwan leda a cikin wani dan madaidaicin ture,
Muna zaune muka fara,gaisawa da ita tana min wasan kaunar miji saidai ban iya mayar mata da,amsa don nauyin ta nake ji sosai,
Mun bata sakon Umma inda tabude ledan sai naga tadan tabe baki tana cewa ita mama kullun tana kashe kudin ta,a gurin wanan abin,
Ga wanda ta aiko min dashi last banyi komai dashi ba,
Aisha ki dauka,mana idan kina so kiyi amfani dashi,
Anty na maye fa ?
Da sauri ta juyo inda nake tana cewa ke kayan matane fa kuma masu kyau na rasa a ina Umma ke samo su haka masu kyau wallahi,
Tace bari wanan tabar nan nai maki

Download complete TXT · Novel page