Sarautar Mata

Chapter 20 of 94

bari na,dauko ma kaci ko,?
Yace zan turo Aisha ta daukan min acan zanci don akwai abinda zanyi a dakin,
Kamar zatai magana amma kuma sai taja bakin ta tai shiru sai dai bataji dadin nisanta ta da danta da akeson yi mata ba,



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
👑 SARAUTAR MATA 👑
1⃣7⃣


ZAINAB IDRIS MAKAWA



Tun a cikin dare Yaya Hamza yace min washegari na shirya zamu tafi uguwa gidan wani, abokin karatun shi,
Naji wani iri a raina don nasan cewa wanan fitan namu zai iya jawo muna matsala ga Umma,
Amma banda halin mussawa don haka naja baki na nai shiru inga yadda zamu kwashe da ita,
Kamar kullun washegari na kamala yan aiyukan da ya dace nayi duk da Umma ta ban wanki nayi masu, amma sai na kammala da wuri kafin ya shigo gida,
Girki ma da, wuri na dora har Umma tana masifa wai don may zan dora girki da,wuri ya huce yai sanyi kafin a ci,
Hamza ya,dawo gida da dan saurin shi ya shigo inda ya samu nayi wanka ina shiryawa,
Wata farar atamfa mai adon gashin dawisu na saka tare da kara dan gyara fuska na da kyau,
Daga daki ina jin muryan Umma tana cewa Hamza wai may kake son komawa ne ne?
Yanzu don rashin kunya matar taka zaka dauka darana tsaka kufita kowa na ganin ku kana nunawa mutane ku gaku marasa ta ido ko ?
Hamza yace Umma ba hakana bane naga cewa shi wanan abokin nawa matar shi danta baida lafiya shiyasa mukazo tare dashi ya bani lift,
Kinga bai dace ace mun koma batare da taje taiwa yaron sannu ba,
Too,wooo sai kuma akace kuje da ranan nan kiri kiri kowa na ganin ku haka ko ?
Umma ba hakana bane kin san yanayin garin shi yasa zamu tafi yanzu ta dan yini masu,
O ashe ma,sai da ka gama ashirin ka shine kazo fada min kai ga mai mata ko ?
Umma kiyi hakkuri nayi kuskure bazamu kara ba ko yanzu don na riga na,aro mashin din Hadi ne da mun fasa to har na,zubawa mashin din mai ne,
Shiru tayi tana,dan kada kai tana nuna alamar cewa akwai magana gaskiya,
To ji nan idan zaku fita ka tabbatar da cewa kun bi ta baya da ita don ban son abin nuna rashi kunya,
Tau Umma mun gode sai mun dawo ai gidan ba nisane da namu ba can kasan layin suke gurin sabbin gidajen da akeyi,
Kai ka,sani kana,wani rawan kafa wai kai mai mata ko har ina matar take abu haka yar fayau da ita,
Wani iri Hamza yaji a rayuwan shi don dai shi a ganin shi wanan yarinyar bataci a dinga mata muzanci haka a gidan nan ba don ta taimaki rayuwan shi sosai yadda ita Umma din bata iya ganewa, sai shi kadai,
Daki ya,shigo ya,samay ni zaune, a bakin gado yanayin yadda ya samay yasa shi cewa may kuma ya faru duk da yasan cewa naji abinda Umma ke fadi,
Cikin dan marairaice murya nake cewa Yya idan har fitan zai sa ran Umma baci mu fasa mana,
Idan kin shirya ki tashi mu tafi kawai amsan da ya bani ke nan a takaice,
Namike tare da kokarin jawo dakina don awakin mutane da ke shigo muna,
Dakin Umma na nufa tana zaune ta mike kafafuwan ta don zafi ake ranan tana shan iska,
Nace a cikin sanyin murya irin nawa Umma zamu tafi a dakile tace min adawo lafiya,
Sai da muka fitane naga ashe a saman babur zamu yi tafiyan ya shiga shagon shi yafito da leda baka da abu a cikin shi yana mika min,
Ibrahim ya dan leko daga shago a lokacin na hau mashin din yake cewa yau ta daure an samu saki ke nan, adawo lafiya,
Nsi dan murmushi kawai don ban iya bashi amsa saboda ina ganin girman shi har yanzu kunyan su nake ji sosai,
Daida zamu dan sha kwana fita daga lungun mu mai mashi ya goyo Kubura wace ta bi mu da kallon kamar tana mamaki,

****** ********* ******
A kofan wani gida mai alamar dan hali a gidan dan ginan zamani muka tsaya da matshin din,
Yake ce min na,sauko daga bayan shi da nake zaunr ina,sauka ya gyara tsaguwar mashin din nasa da kyau yake min iso da cewa na,shiga nayi sallama na tambaya idan Mansur yana ciki ana mashi sallama ,
Gaba,na yana faduwa na shiga gidan inda nake jin wani iri a raina don ban saba shiga gida je ba,
Sallama nakeyi inda naga daki mai alamar akwai mutane a cikin sa don ga takalma a kofan dakin,
Sai dai karan tv yana tashi daga cikin dakin inda na kara dan matsawa ina daga murya na a,sallama,
Wata mata fara ce ta leko, daga dakin tana rike da yaro a kafadan ta da gani yar boko ce ta na min kallon mamaki,
Nace Ina wuni ta amsa da lafiya nace wai idan maigidan ya ciki ana mai sallama a waje,
Juyawa tayi hannunta yana rike da labule tana cewa kai akewa sallama,
Inda naji mijin yana tambayan waye ?
Tace wata yarinyace ban san ta ba ina gani ba yar shiyan nan bace,
Mijin yafito babu riga a jikin shi abinda yasani saurin kawar da kaina gefe ina cewa ina wuni ya amsa da lafiya nace wai ana ma sallama waje,
Rigar shi matar ta miko mai yana sawa inda yadan fito ni kuma ina tsaye a inda nake ya dan zo ya wuce ni ,
Ganin ina tsaye ban bi shi ba ya matar cikin dan kallon kallon da mukewa juna cewa shigo mana daga ciki,
Na shiga da sallamana dakine mai adon zamani TV, da DVD sai kayan kida ga kujeru manya set a,falon,,
Muka kara gausawa tana ce min ban ko gane ki ba na dan yi murmushi tare da dukar da kaina,
Muryan mijin ne ya shigo yana ce mata daga waje ashe matar Hamza ce fa,
Tace Hamza wani Hamza ke nan dear ?
Hamza course mate dina danake baki labari mun hadu a,school dashi,
Tacd OK wanan da kace tare kuka shigo dashi ke nan ?
Tambayan ta nayi da cewa Yaya maijikin da sauki ko tace gashi ai ya samu lafiya dama kyandace sai dai bata fito mai sosai ba ya samu lafiya sosai,
Na mika hannu na karbi yaron take cewa wanan dan kiwar ai ba zai zo ba don baida yarda, sam,
Yaron kuwa ya kara lafewa a jikin uwar shi tare da dan sako min idanuwan shi da yake lumshewa,
Hamza da maigidan suka shigo tare inda yai mai iso har cikin falon matar inda matar ta,shiga dakin ta soko riga don dama bata da riga a jikin ta,
Dariya suke yana cewa wallahi in ba yau dana gani ba banyarda cewa kana da mata ba,
Kai kai kai Hamza wanan ai sai ace kaunar kace ta rako ka,
Shima yaima matar ya yaro maijiki tare da mai fatan Allah ya,bashi lafiya ya tsare gaba,
Muna daga zaune nake jin magana irin ta manyan mata daga bayan tagar su ana cewa, baki kukayi ne,
Matar dakin ce ta bada amsa da cewa eh mama abokin karatun dear ne su kazo gaida Abba, da jiki, shi da matar shi
Tace Allah sarki sannun ku da zuwa kunji mun gode ai yaji sauki yanzu bisa ga shekaran jiya
Sosai naji mamaki a rai na yadda bata jin kunyan kiran mijin ta da,dear a cikin mutane haka,
Matar ce take ce mu na mama ce maman dear take gaishe ku jin haka na
Mikewa zuwa waje don in gaida matar da,akace mahaifiyar maigidan ce da muka zo,
Ina Fita Mansur ke cewa matarka karamar yarinya mai hankali ba irin yaran yanzu ba, yaushe kukai aure ne wai ?
Hanza ya ba da ansa da cewa almost eight months kenan
Kai ashe ma baku wani dade da ita ba,sosai, kace dai kai ango ne,
Matar,shi tace wallahi ta bani sha,awa sosai tana da kamun kai ba irin yaran yanzuba da sunyi aure sun fara rawan kai ke nan su ga matan aure,
Nadawo daki na bar yar dattijuwar a,waje tana ta,saka min albarka tare da muna fatan alheri,
Abinda yasani jin dadi dama ace nima haka nake zaune da umma danafi kowa jin dadi wallahi,
Yan mintina kadan Hamza ya mike yana cewa tau madam ni zan tafi zan barki da bakuwa sai anjima zan dawo na dauke ta,
Tace amma na gode kuwa sai ka dawo din a gaida gida,
Ya juya inda yake yana ce min tau zan tafi sai nadawo ke nan
Allah ya tsare nai mashi cikin dan sanyi magana
Suna fita take ce min wai yaya sunan ki ne ?
Nace mata a hankali Aisha,
Tace ni kuma suna na Hindatu nake amma anfi kirana da hindu, yara na biyu, ta farkon tana gurin mahaifiyata don ban yaye taba na,samu cikin Abba shine mahaifiyata ta dauke ta,
Allah sarki ita kuma mayne sunan ta,?
Tace Hadiza take ,
Tau,fa, sunan Anty nace na bata amsa da fadar hakan,
Muna zaune sai dan jana da hira take a hankali ina dan bata amsa a cikin hikima take dan fahinta a hankali duk da wai naga ina boye mata sirina,
Haba Abba kabari na dan tashi naje na wanke kanyan ka gasu can a jike tun da safe a ruwa,
Sai kuka yaron yake ta faman yi gwanin ban tausayi idan mutum na kallon sa,
Tace bari dai na kara ma magani nagani ko zaka samu barci kayi haka ta mike zuwa uwar dakin ta don dauko maganin,
Mikewa nayi na fita daga dakin zuwa waje inda famfon su yake ta jika kayan yaron a cikin baho mai dan fadi,
Na gyara hijab dina ba tare dana cire ba na,soma wanke kayan yaron da nata a hankali,
Har sai da na kusa kamalawa sai ga Hindatu tafito daga dakin goye da goyon yaron ta Abba a bayan shi
Lah Aisha yanzun ashe wankin kike yi ni ina ce kina nan zaune a,waje ke da mama,
Ashe kina nan kina wanki ne ke haba Aisha idan mijinki yazo ya,samay ki a haka fa,
Muryan mama ne daga bayan mu take cewa yar albarka ke nan,
Tarbiyan da ta samu daga gidan su ne haka in bashi ba ai da tun shigowar ta zaki gane,
Kyakyawan tarbiya wa da,gwada kan shi yake batare da mutum yasan Yana yi ba,
Mansur ne ya shigo gidan yake jin Hindatu nace na bari ta kara sauran da kanta,
Ikon Allah amaryan kece kuma ke wanki da kanki suke cewa ai shine ake magana a kai,
Mama tace ku barta halinta na alheri ne ke nuna kan sa,
Ledan kayan cefane ne yashigo dashi a hannun shi wanda inda Hindatu ta karbi ledan tana mashi sannu da zuwa,
Suna dan wasa da junan su a gaban mahaifiyar shi itako uwar sai murmushi takeyi tana nuna jin dadin ta a fili,
Mansur din ya,shiga daki yake cewa takai mai ruwa yai wanka,
Dakin su ta shiga da ruwan ina dan satan kallon su nace a raina kun huta da,sa ido duk da dai uwar mijin ba ruwan ta,
Amma ni wani lokacin ma Umma zata zo ta tsaya a bakin bayi da,asuba tace tana son kewayawa ne,,
Dole na fito a gagauce na bata guri tashiga tana bina da kallo,
Haka aikin girkin kusan nice na karasa wa Hindatun shi saboda yaron yaki yarda sai kuka yake hankalin uwar duk ya tashi,
A cikin wani turen silver ta zuba muna abinci a tare inda ta zuba nama da yawa duk ya rufe shikafan take ce min don Allah inci abinci in sake jikina don a gida nake ai,
Yaron ta ya samu barci don haka itama ta,samu ta dan shiga wanka ta gyara jikin ta tafito banci abincin ba duk da ina son ci amma kunya bai bari naci don kunya nake ji sosai,

****** ********** ******
Kubura tana ganin Hamza da Aisha taji wani irin haushi da takaici ya tokare mata zuciyan ts,
Tana shiga gida ta samu mutanen gidan duk a tsakar gida kowace tana aikin gaban ta,
Yanayinta kawai ya isar wa mutanen gidan cewa yau ba dadi sosai,
Lafiya ke kuwa Atikace ke wanan tambayan a cikin gwazai irin nata don ita ko yaushe nuna take bata,son Ummi ta rabu da Mama Saude,
Don kada a,samu alheri ace su raba tare da ita ko ta shigo tace zatafita iyawa,
Kin ganta da wani kamane na alamar rashin lafiya tarr da ita ?
Mama Saude ce ke tambayan Atika din cikin hasala,
A,a naga kamar baya da dain raine da ta shigo kawai shiyasa na tambaya inji Atika,
Daga inda Ummi take tadan murmusa don tasan cewa ramin karya kurara ce,
Ita dai badon wani abu take tare dasu ba duk da cewan da,suke diyan su na,aure a gidan wada ta da hutu,
To amma ina amfanin dukiya babu kwanciyan hakali a tare da yarinya,
Kubura tana zaune a saman kujera kanta sama tana kallon tsohon silin din dakin mahaifiyar na ta,
Mama Saude ta shigo dakin tana cewa yau ma kunyi tsiyan naku ko,
Wai may yasa baki daukan shawara ne Kubura kowa ya fada maki cewa kije kiyi hakkuri,
Kamar jira take uwar ta,shigo da zancen sai kuka ta fara acikin daga sautin maganan ta tana cewa,
Mama ni bazan kara komawa gidan wanan macucin mutumin ba,
Duk mai ganin laifina sai dai ya gani amma bazan koma gidan Nura ba na barshi har abada,
Cikintakaici uwar ke cewa yanzu da kike kukan nan haka so kike ataru muna a kai asan halin da kike ciki a gidan mijin ki har yaushe akai auren nan ne wai
Kubura ta kara sautin kukan ta batare da ta tsaya,sauraren uwar ta dake cewa ta tausa muryan ta ba,
Abin da yakara jawo hankalin mutanen gidan ke nan suka dan tsaya sauraren may ke faruwa a dakin,
Yanzu Kubura wanan abin da kike yi ai baidace ba yaushe akai wanan auren, dazaki zowa mutane da wanan zancen,
Atika ce kamar wace take a labe a kofan dakin tun farko ta fado masu daki,
Shekaran jiya fa mijinki yazo kofan gidan nan ya aikomuna da abin arzikin
Dago kai Kubura tayi tana kallon Atika cikin dakatar da kukan ta,
Tace kinji mugu ko azzalumi macuci kawai yana can yana gwada min boni yanzu yazo nan yana gyara kan shi,
Duk zancen da sukeyi Kubura bata saurare su sai magan ganu take fadi mara dadi a kan mijin ta,
Mama saude da ranta ya baci tafito waje inda ta samu Ummi tana aikin ta a hankali kwance,
Kubura na ta kuka tana tujara har lokacin da Ummi ta gama abinci ta zuba mata nata da kanta ta,shiga dakin Mama Saude dauke da abincin don ta kai mata,
Ummi tayi wankan ta kafin ya fara rabon abincin don ka,idar tane yin haka bata zama rabon abinci sai ta tsabtace jikin ta tukun na,
Kubura na kwance ta kifa ciki a saman gadon mahaifiyar ta inda Ummi ta shiga dakin da sallaman ta,
Haba Kubura maynene yai farko baiyo karshe ba yanzu kina ganin kin kyauta ke nan kizo kina tayarwa mahaifiyar ki da hankali haka,
Kusa da ita ta zauna tana mai kara dan bata hakuri a cikin tatausan lafazi mai kwantar da hankalin macen da,ranta ya baci
Dan tsakaita kukan ta takeyi can ta nisa tana cewa wallahi Ummi abin Nura ya isheni ne duk abinda kike tunanen zanyi mai na ban hakkuri nai mashi amma kamar kara tunzura shi nake yi ,
Hakuri zaki karayi Kubura kinji kinga ai kowa zaman hakuri yakeyi yanzu idan kince bazaki koma ba sai mutane su fara fadin abinda bashinr ba alhalin ke kikasan abinda ya hada ku dashi,
Kiyi hakkuri kiji Kubura mace bata gajiya da hakkuri wata rana shi da kan shi zai gane cewa bai kyauta maki a rayuwa,
Kiyi hakkuri kinji Kubura kitashi kici abinci ki watsa dan ruwa ko zaki dan watsake sai kiji zuciyan ki yai sanyi kikai wa Allah kukanki da kan ki Allah maiji rokon bawansa ne musan man ma bawan da ya roka da kan
Tashi kinji ki dan watsa ruwa kiji sanyin jikin ki sai kici abinci kinji, muje na zuba maki ruwa kiyi wanka,
Ga mamakin Ummi sai taga Kubura din ta mike zaune daga kwancen da take da farko,
Kiyi hakkuri kinji Kubura tashi muje kiyi wanka ki karasa hakkuri a zuciyar ki insha Allahu komai zai wuce,
Cikin wani sanyin murya kamar ba nata ba tace nagode Ummi nagode insha Allahu zanyi yadda kikace, din,
Mama Saude ta shigo dakin taji dadin ganin Ummi ta rarashi diyar nata ta daina kuka,
Tace wallahi Fatima yarinyar nan bata daukan shawara na fada mata ba yau ba inda bai son tane ai ba zai zauna da ita ba,
Abar zance kawai yaya tashi kijr kiyi wanka kin san mazan nan halin su ne sai hakkuri wallahi kinga kuma ita yarinya ce ba wai komaine yanzu zata iya shayewa ba,
Amma idan anbi abin a sannu zakiga komai ya wuce an manta,
Kubura ta mike tanufi waje Ummi tabita ta bata ruwan wanka tashiga,
A lokacin ne Ummi ke cewa yaya don Allah idan yaro yazo da zancen ce shi acikin taushin lafazi za,a bashi magana yadda zai fahinta tunda hankalin da saura,
Mama tace Fatima na gode don wallahi yau badon ke ban san ya zanyi da wanan yarinyar ba a gidan nan,
Ummi tace hakkuri za,ayi yayabita a,sannu har gano inda matsalar yake kinga sai a magance mata shi,

****** ********** ******
Kikan yi amfani da kayan mu na mata na baki Aisha,?
Muryan Hindatu ce daga uwar dakin take jefo mata tambayan nan,
Dan dariya nayi kawai bance komai ba tace to baki so ke nan,
Nace ina so mana tace to amma fa bana cusawa zan baki ba don shi yana wa mace illa sosai a jiki,
Nai shiru ban bata

Download complete TXT · Novel page