Sarautar Mata

Chapter 21 of 94

amsa ba tafito dauke da,wani bukitin roba a hannun ta tana kokarin budewa,
Duk wanda ta bude sai ta,lasa ta min bayani ta,daure ,
Tana dariya tace kin san fa mu mata ne sai da dan gyara dole don dan guntun lokaci gare mu a,rayuwa,
Amma fa,sai kin hada da ladabi da biyayya da kwarkwasa ,
Duk da,a,gida guda kuke da uwar mijin ki rufe idon ki ki kama mijin ki ki mashi abinda ya,dace kafin wata tazo tana mai kina kallo,
Don mu matan hausawa kin san bamu da tabbacin cewa ba,ai muna kishiya,
Kada ma kiyi mamaki idan anyo wata sai ya nuna,aike baki taba mashi komaiba duk zaman ki dashi,
Don kin a wanan zamanin maza suna son suga ana kula,su ana tarairaya idan ba hakaba,sai suje su aro wacce suka ga zata iya kula dasu yadda suke so duk da wahalan da akasha dake a baya sai a fita batun ki ki zama hoto a gefe,
Tace Aisha wallahi ai hakan ma yafi faruwa yanzu ka,wahala da namiji idan dadi yazo yace aike baki iya ci ba,
Don Allah Aisha ki cire kunya ki kama mijin ki ki kula da abinki kin ji gaki yarinya karama,
Wanan abin da zan baki kiyi amfani dasu zasu taimaka maki sosai sai wasu kwalabe da ta bani guda biyu ruwane kamar turare a ciki tafada min yadda,zan yi amfani dadu,
Sai a lokacin na nuta da wanda gwagona ta taba bani a baya lokacin ina amarya,
Inata mata godiya tana jin dadi yadda nake ta bata girma
Ta hada min da bed shet sabo da kuma room fresh masu kamshi da man kitso dana,wanke gashi,
Sai yamma lis yazo muka tafi gida da ledana fam shake da kayan tsaraba inda ta,rufewa Umma baki shine sabulai da man shafa babba vasilen tace nabawa umma don yanzu sarakai kyauymta,suke so,
Muka,rabu muna ji tankar kada mu rabu da juna don dan sabon da mukayi da ita da,sararkuwar ta mai kirki tabani turaren wuta da yan abubuwan amfani,

****** ********* ******
Tunda muka dawo umma tadan fara shan kamshi amma ina bata tsaraba tare da,fada mata sakon Hindatu cewa zata shigo su gaisa sai ta shiga washe baki,
Tana cewa yar albarka ke nan ince yaron dai ya samu sauki,
Nace to da dama dai za,ace tace ai zance Hamza ya kaini na dubo shi kafin ya tafi,
Na,shiga dakina na,samu guri na boye tsarabata yadda ba mai gani inda,suke,
Umma tana min tayin abinci nace mata na koshi munci abinci acan,
Tace yar nema anciwo dadi ke nan yau ba,a yayin talen umma ko ?
Tun a ranan nafara amfani da abinda anty Hindatu tabani inda take ce min na daina yawan karban abinda Anty Zarah take bani don ko banza matar dan uwanane don duk yadda akayi zatafu son dan uwanta dani,
Wata rana ma Uwar ta zata iya bata wani abu a cuta min ta wanan ha yan don haka nai taka tsantsan da dangin miji don ba abin yarda bane sunfi son dan uwan su da matar dan uwan su,
Ranan Hamza ya kasa daurewa sai da ya nuna min iya zakuwar shi a kaina sai zance yake sakewa yana tambayana wai may ke faruwa ne haka da yawa yaga fa gaba daya na canza mai sallo da tako wanda bai sanni dasu ada can baya,
Kwanan su hudu da mansur suka kwasa suka koma ba tare da ransu yasobba kamar yadda duk wani dan makaranta mai iyali ke komawa yabar matar shi cikin rashi son barin ta

****** ********* ******

Dama ta sauka mai albarka inda mutane sai gona suke kaida kawon zuwa saboda lokaci ne na noma yanzu,
Kudin da Hamza ya bani ajiya ya karbi rabin rabi daga ciki ya nufi harka noma dashi,
Idan yana makaranta Ibrahim ne mai kula,da harkan noman shi da,sauran abubuwan gida
Inda sukan kwashi yan kallo da da Umma su hau sama su fado amma ibrahim yace shi sam bazai yarda ba,
Saukin ta sai idan Hamza ya shigo gari takkan dan samu irin yadda take so a gare shi,
Shuka sunyi lab lab dasu acikin daji tankar an shimfida Carpet ne a fili, gwanin ban sha,awa dasu,
Mutane suka zance a kan noman hamza din inda suke mamakin wanan hikamata karamin yaro kama shi har zai yi irin wana shukan babban gona haka,,
Baba Mudi yana daga cikin masu farin ciki da irin wanan ci gaban da karamin yaro kamar hamza ya samu akan amfanin gona,
Sun shiga hutun dogon zango inda dalibai su kan dade a gida suna shan hutu kowa da irin abinda yake a wanan lokaci,
Wani ranan asabar da hantsi ina sauri na kamala aikin abincin masu zuwa gona,
Wanda duk yawan shi babu daya daga cikin yan matan Umma dasuke tayani wanan aikin mai wahala,
Ganin yadda nakw ta faman aiki ni daya Ibrahim yake tambayan ina,su Asmau su taya ni,
Umma da ke daga daki take cewa to dan na iya bazasu fito ba ina aikin mijinta takeyi ita,
Ibrahim yace su kuma aikin yayan su ko do duk abinda aka,samu aidasu ake ci,
Hamza din yana daga kofa yana jin zancen da akeyi amma bai ce masu uffan ba don tsakanin Umma da,Ibrahim ba a shiga tsakanin, su,
Hakana Umma ta rufe shi da fada ta inda take shiga bata nan take fita take cewa taga kamar ana son a shiga tsakanin ta da diyan ta a raba ta adasu abinda bazata taba yarda da shiba ke nan a rayuwan ta,
A karshe Hamza ne ya shiga bata hakkuri inda da kyat ya samu tai shiru a kan zancen,
Daga haka Hamza din ya samu ya ja Ibrahim suka fita zuwa gona don gudun kada ya kara jawo wani zance,
Suna hanya ne a,saman yar tsohuwar babur din da Hamza ya,saya mazu don rage zirga zirga ata haya,
Hamza yake cewa ina son kafin na karasa karatun nan Aisha ta koma makaranta itama ta karasa nata karatu ,
Sai dai Umma taki yarda da hakan ban san may isa bata son zancen Aisha ba a rayuwan ta,
Ibrahim yace idan har kana,ra ayin haka kada ka,fada mata,sai ka kan mala komi yadda ya,dace sai ka sanar da ita zance tafiyan kawai shine fatin ka ka kuma fada mata a lokacin da nake a gurin,
Sosai Hamza ya ji dadin wanan zancen na dan uwan shi inda ya,sa aran shi cewa da zaran ya koma zai fara nema min gurbin karatu a inda ya dace,

****** ********* ******
Yanzu ace duk yawan ku yaran nan kun kasa ko da rabin aikin da yaran gi
dan Rabi mai gyada suke,
Yanzu ku diba kusan mu goma sha amm gona daya karama ta gagare mu nomawa,
Audine ke cewa Baba su ba, tun suna yara kanana suke wanan noman a gidan su,
Mu tayaya ma,zamu iya wanan aiki da Hamza yake shi da yan uwan shi, su da,suka tashi tun suna yara suke aikin karfi,
Rayuwan Baba mudi ya baci inda yai masu kaca kaca akan su dage su tashi tasaye su nemi na kansu don in shine yau gobe ba,shi bane,
Ganin yadda rayuwan shi ya baci dasu yasa suka fahinci cewa fada ne yake masu na kwarai a lokacin,
Boka ya bata matasa yanzu har takai basu iya,sana,ar hannu ko kadan ,
Abinda sauran diyan yan kudu sukafi matasan arewa dashi kenan,
Don su basu dogara da boko ba kawai ace sai aikin gwaunati,
A na son duk uba ko uwar da ya san kan shi yadan koya wa danshi sana,ar hannu ko ta karfi wanda zai iya tallafawa rayunwan shi ,
Domin mutum in shine yau tau bashine gobe ba saboda mutuwa,a koda yaushe zata iya daukan bawa tabar iyalin shi inda idan ba mataimaka,masu karfi sai zama liability ga,sauran dangi,


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
👑 SARAUTAR MATA 👑
1⃣8⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA


Gurbin karatun da,aka,samo min zanyi heka ka dawo ne ba a,can zan zauna ba,
Umma tai masifa tai jidali, tayi jinini amma Ibrahim yace sai ta barni natafi tun da mijina yana,ra,ayi haka,
Shekara uku zan dauka ina karatun a makarantar koyon aikin ungwazo ma dake a cikin garin Jega ta jahar kebbi,
Wanan karatun da zanyi ya jawo surutu sosai ga mutanen uguwar mu yan daukan wa kai nauyi,
Inda duk Umma tafita,a can sukr zugata cewa yanzu ace mutum da auren ta bazata zauna a gida ba,sai tai tafita wai zuwa wani makaran ta can,
Da,surutun shiya ya ishi Ummi na,sai ta,bukaci ganina gidan amma bata tsawala,min ba don cewa tayi anytime na,dan samu daman zuwa tana magana dani,
Aiken ta,da kwana,biyu ranan Asabar na fadawa Umma cewa ina,son na,shiga gidan mu nagai dasu,
Allah ya bani sa,an ta na samu ta barni na tafi don Hamza ya fada mata cewa idan har gidan mu zan shiga ko zan tafi gurin yan uwan shi a barni na tafi koda baya gari
Don haka ba bata lokaci na,shirya tsab dani na,shiga gidan na mu,
Suna a tsakar gida kamar kullun kowa tana aiyukan gaban ta,nai masu sallama,
Inda na bisu daya bayan daya ina gaida su a cikin ladabi kai ba,sai anfada maka cewa irin kallon da mama Saude da Atika suke min na hassada ne ba,
A cikin rashi sakin fuska kamar kullun suke amsa min gaisuwan nawa sai dai tankar ban fahince su ba,
Atika ce dan ta tsinkani take cewa, ke Aisha kullun da hijjab guda kike fitane, wai ?
Nai murmushi tare da dan kara kallon hijjab din nawa nake cewa, ai wanan sabone mama don baki sanni dashi cikin wanda yaya ya,saya min ne da zai tafi din nan don shiga makaranta,
Sai na gan shi kamar kullun dashi kike shigowa gidan nan ai idan zaki zo,
Dakin mahaifiyata na nufa inda na,samau ta a dakin ta tana jiran karasowa na,
Zaune take a bakin gadon ta tana nade kayan wanki da na samu tana kwasa dana shigo, gidan,
Har kasa nakai ina cewa Ummi ina wuni a cikin ladabi da girmamawa,,
Nace Ummi yaya,su yaya yusuf da su yan biyu take cewa,duk suna lafiya cikin dan ci gaba da abinda takeyi, batare da ta dakatar ba,
Na ce Umma an fada min sakon ki shine yau nace bari na, shigo naji,
Ta dan dago kanta kadan tare da dan kallo na cikin dan kura min idanuwan ta nadan wani lokaci sai kuma taci gaba da abinda takeyi,
Sai take cewa dama kiran ki nayi don naji gaskiyan zancen karatun nan da akace wai kin matsawa yaron nan sai ya mayar dake karatu,
Nan da nan naji wani bacin rai idanuwa na suka ciciko da hawaye inda Ummi takecewa Atika tashigo muna da zancen da,bai muna dadi ba,a gidan nan don haka nace kizo naji daga gare ki,
Idan har wanan karatun ba,dole bane kiyi hakkuri ki zamn ki a dakin ki shi ya fiye maki, daraja,
Don kin ga,surutu yai yawa ga wanan zancen karatun naki
Uwar mijin ki tana yada magana wanda ni dai da, wasu ma mun san cewa ba gaskiya bane,
Don haka ni dai ba,wai na yarda bane don nasan halinki nasan ko ke wacece,
Amma idan ita Umma Rabin yanzu tafadi zance a kanki mutane zasu dauka ne su zaci da gaske ne tunda ita ce ke zama da ke, yanzu,
Take naji jikina yai sanyi da jin maganganu Ummina da ake fadi a kaina cikin uguwa,
Hawaye yadan fara silalowa,daga idanuwa tace min dakata mana don kuka bazai fishe mu ba ki fada min gaskiya shin ke ce kika matsawa mijinki cewa sai ya mayar dake makaranta ko kuwa ra,ayin shi ne hakan,
A hankali na dan girgiza kaina ina ce mata ina wallahi ban san komai a kan zancen karatun nan ba asalima dai ni shine yazo min da zancen,
Ummi ki san halina kin san abinda zan iya da,wanda ba,zan iya yin sa ba,
Tsawon lokaci Ummi tana min nasiha tare da kara lurar dani zaman duniya da mutanen ta,
A karshe take ce min kada ki biyewa halin sararkuwar ki ki ci gaba da hakuri da kowa yadda kika saba yi,
Don haka in har kika bi magan ganun da na fada maki zaki samu rayuwa ingan tace a karshen rayuwan ki don zaman lafiya da mutane shine azikin bawa a,duniya,
Ganin yadda yau muka samu dan lokaci da mahaifiyata yasa na,dan fada mata kadan daga cikin halin Umma da nake fama dashi har diyan nata ma,
Amma,sai Ummi ta katse ni da cewa ko yaya halinta yake mahaifiyar mijiki ce don haka sai ki bita da halinta ku zauna lafiya
Hakan kuma zai kara maki daraja da marta a idon mijinki koda taushe don yasan hakkurin da kike yi a gidan ai tunda a gaban shi ake komai,
Jeki idan kina,da abinyi a gida don kada, na tsayar dake da surutu kiyi laifi,
Zan daga take cewa mijinki ya kawo muna,amfanin gonan da ya,samu a gidan nan duk da dai ance ya rabawa mutanen uguwa da,dama,
Sai a lokacin nai dan murmushi ina cewa ai ina ga kamar zakka ne ya rabawa mutane,
Muryan mama Saude ce daga kofa take cewa matar sarkin noma sai ga sako daga maigidanki gudan mai yawa haka,
Murmushi nayi kawai banyi magana,ba,fon kawaici wa iyayye,
Ance kin matsawa mijinki wai sai ya mayar dake makaranta Yar Agwai,?
Atika ce ta,dago labulen dakin Ummi na tana tsaye daga bayan mama Saude wace ta rigata shigowa daga ciki kadan,
Haba Atika wai may yasa kike magana itin haka ne,
Ke yanzu ko wani kikaji yana fadan wanan maganan a gabanki bazaki tare zancen ba akan sanin halin yarinyar nan da kikayi,
Ni bani son irin haka gaskiya mama saude ce ke magana a dan hasale ta juya batare da kara fadan wani abuba,
Itama Atika ta mara mata baya suka bar kofan dakin ummi din,
Shiru mukayi a,dakin Ummi tace min tashi kije rayuwa ce wata rana sai labari ke dai ki ta hakkuri kinji,
Har na mike nake cewa Ummi don Allah gobe lahadi ki turo min su yan biyu suyi min yini muyi hira dasu,
Ba,wai ban son zuwan su gurin ki bane Uwar mijinki ce nake gudun anyi ance din ta a uguwa,
Ummi har da yan uwana sai tace kuma kada su zo gurina haba dai Ummi don Allah ki bari su zo din kinji Ummi,
Tace cikin dan guntun murmushi Allah ya kaimu gobe din zasu zo,

****** ********* ******
A makarantar da nake zuwa hijjab nake sakawa har kasa idan zan fita da nikaf, sai zan shiga get din school nake cirewa,
Ban yarda nayi kawaye irin na zamani ba kamar yadda Ummi na tai min gargadi ga yin haka,
Tace min yin kawayen da,suka fi karfin a jina zai iya jawo min matsalar rayuwa,
Mussaman idan ina kallon irin rayuwan da wasu keyi yau da,gobe zance na dauka,
Amma idan har naci gaba da normal life dina batare da yawan mu,amula da kawayen zamani ba zanci gaba da,rayuwa a cikin dadin rai babu kunci a cikin sa,
Wanan magan na Ummi ne ya tsaya min a,rai nake ta taka tsantsan da komai da nakeyi a makarantan daga gurin lecture sai masallaci sai na,fito zuwa gida,
Duk wanda,aka fadawa cewa ni matar aure ce sai kuji mutane suna mussawa cewa wai yar karama dani za,ace nai aure,
Da yake Allah ya taimakeni tun ina primary three akai promotion dina zuwa primary five kan wani devet da mukayi da wani makaranta nai sanadiyar cin wanan gasar a makarantar mu,
Shine dalilin gama karatuna dawuri ina da karamin shekaru a lokacin
Da,nadawo karfe biyar zan dora girkin abincin gida da,nakeyi kullun,
Wanda karatu bai kawo sauyi akan duk wani aiki da nake a,gidan ba a baya,
Kowa zai kwanta ya barni ina aiki a cikin dare don gudun makara da,safe zuwa makaranta na,
Dalilin da yasa Umma ta kasa samun wani dalili ko hujjan da zata kawo suka na akan fita na zuwa makaranta da bata so,
Don ina matukar yin taka tsatsan da halin Umma din don gudun abinda za,a jimu da ita,

Sai da sati ya,zagayo ne su yan biyu suka zo min wuni kamar yadsa Ummi tai min alkawarin zuwan su din,
Don wancan satin basu samu zuwa din ba saboda hassan ya,tashi da gudawa, a ranan,
Nai murna kwarai da zuwan yan kannen nawa wanda yar gurin Atika ce yar matashiya takawo min su,
Ko da yaran suka zo Umma bata a gida tafita uguwa zuwa buga bugan ta na yau da kullun don yanzu har da dan dillanci take hadawa,
Sun samu daman ina girki na gama na zubs a kwano tare da,su muka shiga daga cikin dakina muna ci muna hira ina dariya wanda mutum zai iya cewa tun shigowa na gidan ba,a taba jin dariyana irin haka ba,
Umma,wace dawowan ta ke nan daga uguwar da ta tafi,
Take jin dariya na da,surutun mu mamaki take yau may ke faruwa yayin da take dan kara karasowa cikin gidan zuwa kofan dakina,
Sai da,tazo gab da kofa tai sallama tare da dan tsayawa kamar mai shigowa,
Ganin ta yasani cewa,a,aUmma sannu da,dawowa ina,mikewa yayin da nake nufar kofar don karban ledar dake a hannun ta,
Idanuwan Umna kyam a,cikin kwanon da nake cin abinci da yan uwa na da,sukajo har yar gurin Atika,din,
Au yaran gidan malam Mudine suka, shigo ashe gaske nake jin muryan ki tun a kofan gida,
Murmushi nayi tare da karban ledan hanu bibiyu take cewa su yan biyu kyautar Allah,
Abinci kowa an zuba mai mai isarsa, ko don kada wani yace min bai koshi ba, daga baya,
Nai mamakin jin tambayan da Umma din tai min kan abinci don haka nake cewa, Umma kowa ya,samu,
Bude kwanon abincin nata tayi tana dan dubawa komay ta gani sai ta,rufe tana cewa Allah ya kyauta,
Na koma gurin yan uwa muna ta shirmay mu a daki sai dai yawan kiran da Umma take min ya,fara isat, aamma haka na daure i ta ta

Download complete TXT · Novel page