Showing 69001 words to 72000 words out of 299981 words
kai dubu biyar sai da na fitar da idanuwana waje tace kiyi kwalliyar buki dasu kitso kunshi da sauran su nai mata godiya sosai tace haba ba godiya a tsakanin mu don ke kaunata ce, yanzu,
Amma ki sai wani abu kici don kar ki zauna da yunwa don naga an karbi abincin ki,
Nai dan murmushi nace ai da,akwai kunu zan sha shiyasa na baxhi,
Tace idan lokaci yayi zandawo nakawo maki kati ko kuma naxo da kaina,
A tsakar gida muka samu su Umma ta ba Umma dubu daya zo kiji godiya a gurin Umma din nai mata rakiya tana ce min sai mun hadu akwai maganan da zamuyi insha Allahu nace tau Anty na gode idanuwsn Umma da yaran ta kar a kaina suna son ganin ko za,a bani wani abu,
Nake cewa Umma zasuyi buki a gidan su shine tazo fada muna,
Umma ta taso tana cewa Allah sarki mu gode kwarai da wanan karancin naki Allah ya nuna muna lokaci lafiya,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
👑 SARAUTAR MATA 👑
1⃣9⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
FATAN ALHERI DA GAMAWA DA DUNIYA LAFIYA GARE KU DUKKAN MASOYYANA NA GAISHE KU AKAN KOKARI DA KAUNAR DA KUKE NUNA MIN A KULLUN,,,
Rayuwan zamana agidan aure ya kasance na yau dadi gobe daci wanda duk akasarin rayuwa a haka yake yanzu,
Yau da gobe yasa na fara fahintar duniya a rayuwa yadda yake,
Uwar mijina na dan fahinci kadan daga halaiyar ta wanda shine bata kaunar taga danta ko kadan yana nuna kulawan shi a kaina,
Amma ita zata iya gwada min da kanta inda muna mu kadai a gidan,
Da,zaran kuma ya,shigo sai zance yadan canza a tsakanin mu,
Wanda na,fahinci ba wai kishin shi take ba bata dai kaunan ya nuna min zakewan shine a kaina,
Wanda ita a ganin ta idan ya soni zai guje mata tare da yan uwan shi ya koma komai sani kamar yadda matan yanzu sukeyi su raba mijin su da yanuwa har iyayye ma,
Su kuma yan uwan shi matsalar mu gudane dasu shine su tambaye abu ban basu ba yanzu zakiji manyan magan ganu suna tashi, a gidan,
Hakan ne dana fahinta na dauka ma kaina mataki gare su gaba daya,
Ita Umma dai na,sawa raina bazan yarda na nuna afili yadda zamana da mijina yake ba,
Duk yadda Hamza yaso ya nuna yadda ko soyayya a,gaban Umma koda a cikin magana ne ban yarda na nuna a fili,
Haka su ma yan uwan Hamza din watau dangin miji duk abinda suka bukata a guri na koda shi ke nan a gareni zan basu na huta,
Kusan zance rayuwa a yanzu haka yake, yau dadi gobe babu a ko ina mutum yake,
Na kasance mai kokarin ganin na hade duk wani bacin rai da zan iya gani daga rayuwan aure na a gidan,
Haka Fan,nin ka ratuna yake samun ci gaba acikin nasaran ubangiji na don bawai da Alkah yai min ya taimaka min kwarai da gaske, a school din,
Duk da ban shiga har kan mutane amma,su suna kokarin shiga nawa don dai nayi hurda dasu,
Yau ma kamar kullun mun fito daga dakin lecture lokacin sallah azahar ya yayi direct massalaci na nufa don sauke farali,,
Sam ni ban yarda da zuwa hostel dakunan mutane yin sallah ba,sai dai naje mosque din school nayi,
A hankali nake zare sock din dake kafana tare da cire dan agogon da na daura a hannuna, don diban time saboda gujewa fitinar Umma Rabi,
Butar dana dauka babu ruwa a cikin sa mai yawa dan waige waige na fara yi inda zan samu ruwan sallah can na hango wata mata baka mai dan kaurin jiki tana cin abinci ga ledan ruwa har guda uku daga gefen ta,
Na karasa,gurin da take zaune da sallama a,bakina ina mai gashe da ita da cewa sannu sister,
Ta dan dago kai fuskan ta round face ne da dan diple manne gareshi,
Don Allah sister ruwa nake son ki dai taimaka min da shi nayi alwala yau ba ruwa a famfo ,
Ta mike min leda daya na ruwa tana cewa wanan zai ishe ki ko ?
Na karba ina godiya na juya zan wuce take cewa bissimillah muci abinci ko,?
Alhamdullahi na bata amsa a,takaice na wuce zuwa sallah ,
Kamshin abinci na tashi gashi ya ji mai dagani miyan tumatir ne zai yi dadin da gardi a,baki don kamshin shi kawai dake tashi ya isar wa mutum da sakon hakan,
Gurinbda,na idar da,sallah a nan na zauna ina lazimi kafin time din komawa na lectures yayi,
Wanan matar da,ta,bani ruwa itace ta,shigo cikin mosque din da,alwalan ta,zatai sallah,
Har ta idar ina zaune a gurin ina,adduoi batare da,na kalle ta,ba,
A,kofar fita muka hade ina,saka takalmana ita kuma ta idar zata fito,
Gaishe ta nayi irin na,addini a,cikin dan,sakin fuska itama ta karba min, da nata fara,an take ce min amma baki dade da zuwa school din nan ba ko ?
Nake ce mata aa mune yan fresh da aka dauka newly,
Wani department kike nece mata environmental nake sai take cewa tau ashe kusan department guda muke, ke nan,
Mun jero da wanan matar muna hira a hankali take ce min ke a garin nan kike ne ko kinzo ne nai dariya wanda ya dan baiyanar da fararen hakora na a fili,
Nakecewa a nan nake nan kuma nake aure, sai naga ta dan juyo tana kara kallona,
Ta ce k8na nufin ke matar aure ce na ce mata eh sai take ce min ita daga yauri tazo karatu ne matar aure ce tana da yara biyu,
Amma ta barsu a gida tana zaune ne a gidan haya da mijin ta ya kama mata, sunan ta Hadiza ,
Munkai inda zamu rabu kowa ya,shige department din sa,
Sai biyar da rabi nabar makaranta zuwa gida don na samu na karasa aiyukan dake gare ni,
****** ********* ******
Tsaye take rike da filo a hannun ta tana kokarin gyara gadon ta don hakan al,adan tane ta gyara daki tun da safe,
Kafin wani lokaci dakin ya,dauki kamshi tare da komawa neat gwanin ban sha,awa,
Tashiga,bathroom dinta dake mane da dakin ta, tai wanka, tafito inda ta zauna ta gyara jikin ta tsab a cikn wasu material dake cikin kayan lefen ta,
Tun bayan irin lafazin da Ummi tai mata ta daina sa damuwa, a,ranta, kamar farko,
Kwata kwata itama ta,daina shiga harkan shi sai harkokinta take a cikin taka tsantsan,
Shigowan mutum ta gani dakin ta bai,damu da yai sallama ba tunda gidan sa,ne,
Sau guda ta,dan daga idanuwan ta ta kalle shi sai ta,sunkuyar da kan ta kasa taci gaba da mayar da powder ta inda ta,dauko shi saman dressing mirror,
Tsayuwar shi ya gyara yana mai kallon yadda ta,ramay tawani koma yar fayau da ita,
Ke baki iya gaida mutum ba ke nan har da tarbiyan rashin gaisuwa baki da,,
Kubura ta dago kanta da,sauri ta dan kalle shi sai taga yai mata wani kwarjini a fuskan ta,
Za,a yi buki a gidan yan uwan mu ina,son kuyi attending din duk event din da zasuyi,
Kara kallon shi tayi a cikin mamaki ya fahinci tai mamaki yake cewa Jamila zata karbo maku kayan anko wanda zakuyi amfani da su a,can, don haka ban son naji wani fitina daga iyalina har a,watse daga wanan bukukuwan,
A hankali cikin sanyin murya ta amsa da fadar insha Allahu,
Sai yaji ta bashi tausayi sosai yaji abinda yake mata bai kyautawa, ko kadan ,
Hannu ya,saka a,cikin aljihun shi ya ciro kudi da zata iya cewa shima baisan yawan su ba ya mika mata yana cewa wanan ki rike a gurin ki
Nagode ta furtaxmai wanda shi kan shi yau yai mamaki da irin lafazin ta a cikin taushi don kuburan da ya sani ba ita bace yanzu, kwata,kwata,
Nan ya aje mata k7din yafita,dakin da,saurin shi kamar mai jin tsoron a ganshi dakin nata,
Bin shi tayi da kallo cikin wani irin yanayi wanda taji tausayin kanta ya kama ta,a lokaci guda,
Tai mamaki kwarai yadda akayi yau shi da kanshi ya,shigo mata daki da maganan lumana, a tausashe,
Shawaran Ummi ya fara mata amfani ke nan don ta fahinci yanzu matar gidan kamar hankalinta a tashe yake bata da natsuwa kuma,
Kudin daya,bata tafara adanawa sanan tafito don zuwa ta dauko breakfast din ta taci,
Sai ji tayi muryan Jamila tana cewa na fada maka matarka yar rashin kunya ce don haka bazan kai muna dinki tare ba tai min rashin mutunci
A marairaice taji muryan maigidan yana cewa haba Jamila yanzu duk abinda nake ma yarinyar nan a kan ki bakya gani,
Bata ji may Jamilar tace ba tafito daga dakin rai a bace ya fita,
Sai ga Jamilar ta fito dingis dingis tabiyo bayan shi, itama,
Ganin Kubur din zaune da kayan karin kumallon a,gaban ta yasa su gaba daya dan jin shock don sun san cewa taji zancen su,
Daga inda Kubura take zaune ta watsa masu yar karamar harara tace a,zuciyan tace lalai zancen Ummi hakkun gaskiya ne,
Tayar da hankali ko wani cin mutunci bazai barni na fahinci inda matsalar take ba,
Ta tabe bakin ta ta mike tana fadin kanku dai ake ji don na bar ku ga Allah ni,
Dole ne ta shiga gida,gurin Ummi don ta fada masu halin da tafara tsintar kanta a ciki yanzu,
****** ********** ******
Yau da,guri na,dawo daga school inda nai sallah azahar na dan dauko takarduna ina dan dubawa a hankali,
A gurin barci mai dan nauyi ya kwashe ni ba tare da na,sani saboda tarin gajiyan dake tare dani,,
Ko hijjab din da nai sallah ban cire ba yana,saye a jikina har akai kiran sallah la,asar
Ganin ban fito ba,ga yamma yanayi yasa Umma ta, nufi dakin nawa ,
A cikin barci nake jin kamar muryan ta hakan yasani bude idanuwa na da,sukai nauyi,saboda barci take cewa,
Aisha wanan barci fa haka yau ya kamata ki tashi hakana yamma yayi sosai,
Nan na mike zubur ina mamaki don ban zaci cewa lokaci ya kai haka ba,
Bandaki na nufa inda na yo tsarki nazo saman wani dutse da muke zama a tsar gida don yin alwala a gidan,
Umma tafito da mayafinta a kai tana cewa ina son na dan fita na zaga ko zan samu dan kudin da nake bi bashi na sayo muna dan abin minya daga can,
Alwalana nakeyi hankalina a kwance ta dan fara tafiya,sai kuma ta,tsaya tana cewa kudin hannuna baida yawa amma ina son mu dan ci dan abin kwarai yau,
Nakai ruwa a,bakina tare da karanto adduoin rufe alwala,
Namike ina cewa Umma da akwai dan canji a guri na bari na,dauko maki sai ki saya dashi,
Kafin nagama fadi Umma tace a,a ayi haka yar nan idan zakiyi wani lalura dashine fa,
Na dai shiga daki na zaro dari biyar daga cikin kudin da Anty hindu ta bani nakai mata,
Ta karba tana dan juya kudin tana mamaki kamar zatai magana sai kuma ta dake tafita tana cewa sai ta dawo,
Taufa ashe na daukowa kaina magana don Umma ta fita tana tuna ne, daga karshe shedan ya ruda tace Hamza ne ke bani kudi nake yadda raina yaso dasu idan zai tafi ,
Ita ko sai ya bata kalilan yace tayi hakkuri bai da kudi maneji yakeyi shima,
Nan ta hau tai fan saigata ta,dawo da nama danye a cikin leda a hannun ta,
Wace muka rabu lafiya amma,sai gashi fuskan ta ya canza sai tana,wani matsewa da daurewa,
Na fahinci haka don haka naci gaba da,aikina na gida kamar yadda na saba yi,
Bayan sallah isha,i ina zaune a dakina still ina,dan karatuna,naji muryan Umma tana cewa Ibrahim din ta,
Dan uwanka nake jira yazo garin nan don na,fahinci ya,canza sosai a,rayuwa,
Auren nan yasashi kwata kwata yanzu baya jin magana ta a gidan nan,
Ibrahim yake cewa may kuma yai maki umma tace ai barni dashi don ba shi da abin cewa sai dai yazo din ai zakaji mu,
To koma may yai maki kiyi masa hakkuri don ni kin san halin dan ki fiye da kowa Umma,
Yana gudun zuciyar ki fiye da duk wani da naki a gidan nan Umma,
Bata tsaya sauraren Ibrahim din ba ta mike ta nufi bayi,
Murmushi nayi ina cewa ikon Allah may Umma take nufi danine haka wai ?.
Duk al,amari ci gaba yanzu na fara fahintar bata son ganin shi a gare ni tafi da son taganni a,wullakance ke nan,
Allah ya kawo dan na ta taji da kunnuwan ta abinda take zargi,
Washe gari ma,da,zan tafi school har kofan ta naje sallaman ta amma,sai umma taki amsa min irin yadda ta,saba,ba,
Nafito na nufi inda zan hau mashi, don zuwa makaranta,
A kullun zanfita zsn saka sock a kafana nasa dogon hijjab har kasa sai na daura nikaf a fuskana tun lokacin da na,fahinci an saka min ido ga fitana,
Ina shiga na hagi wata mace tana mun hannu, sai dai ban gane ko wacece ba,sai da na karaso naga,ashe Hadiza ce,
Mun gaisa fuskan mu dauke da murmushi don mun sheda junan mu ko,
Take ce min tun ranan bamu sake haduwa ba kuma gashi kina a raina,
Dan gajeren murmushi nayi tare da cewa Allah ne bai nufi mu hadu ba,
Amma ai gashi yau mun sake haduwa dake ,sai take cewa ranan mun rabu bamu karbi nomban juna ba,
Na dan girgiza kaina a hankali ina cewa banda waya ni
Allah sarki tace min,
Yanzu dai idan kin fito ina gurin da muka,hadu ranan zan jiraki muci abinci,
Na dan girgiza kaina nake cewa wallahi a koshe nake naci abinci tun a gida ko
Hadiza din tace ni naso muyi hurda amma,sai naga kaman ki ja,da baya dani,
Murmushi nadan karayi mata inda nake cewa ba hakana bane kin san bamu da time din tsaya irin haka , anan,
Kuyi hakkuri dani da,wanan wallahi yau ba yawa da fatan zaku fahince ni,
ZAINAB IDRIS MAKAWA👑 SARAUTAR MATA 👑
2⃣0⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
YA ALLAH KA KAREMU DAGA DUK WANI SHERI DAKE CIKIN WANAN ZAFIN,
YA ALLAH KASADA MU DA ALHERIN DAKE A CIKIN WANAN LOKACIN,
YA ALLAH MUNA ROKON KA DAKA SANYA ALBAKA AGARE MU DA YAN UWAN MU DIYAN MU IYAYYEN DA KAKAN NIN MU,
ALLAH KA SADA MU DA RAHAMOMIN KA MASU DARAJA DA DAUKA A DUNIYA DA LAHIRA
YA ALLAH KA KARE MU DAGA DUK WANI SHERI NA MUTUM KO ALJAN KO DABBA KO KWARO DAMA,WANDA BA MUGANI DA IDANUWAN MU,,,,,,,
Ina duke ina wankin uniform dina,da yan sauran kayana da,sukai dauda ,
Naji sallama daga bayana, amma Umma ce dake tsaye take karba ma mai sallaman,
Sun gaisa naji matar da ta shigo tana cewa don Allah gidan Aisha Mudi muke tambaya,
Aisha,Mudi Umma ta maimaita sunan cikin mamaki jin muryan naso na,sheda ga kuma,sunana da,aka fada,
Na,mike don inga ko wacece ke min sallama Hadiza yauri ce da wata sai dai ban san sunan dayar ba,
Cikin murna da farin ciki na tare su na,dauraye hannaye na na nufo ina masu iso da,su karaso mu shiga daga ciki,
Na dauko dan tabarmana na,shimfida masu nafita debo masu ruwan sha,
Wanan damar ce yasa su kare ma,dakina kallo da kyau inda,suka fahinci ni din dai tallakace ta gaskiya don ba,wani abin azo a gani a gidan namu da dakina,
Nadawo dakin da cup na aje masu ruwan ina masu sannu da zuwa,
Hadiza ta,dauki cup din ruwan ta kurba kadan ta mikawa dayar amna,sai ta girgiza kai tace nagode, acikin murya kalar ta yan matan zamani yan gaye
Nace Allah sarki kiyi hakkuri ba yaron da zan tura ya,sayo maku ruwan leda ne,
Tace cikin daga hannu kada ki damu Iam OK ne aida zan sha wanan din, nace gaskiya nagode da,wanan ziyarar da kukai min ,
Hadiza tai murmushi ta dan gyara zama tana cewa ai dama zuwan bazata nake son nai maki shiya sa jiya naki fada maki cewa zan zo,
Nace to waya gwada maki gidan hankalina a,kwance banji wani kunya ko nauyin yadda suka samay ni ba ba yar kowa ba kuma ba matar kowa ba,
Tace wanan mai mashin da ya dauke ki ranan shine na gani da zan tafi BK sai yai min kwatance, da uguwar da gidan ku,
Nace ikon Allah to don Allah kuzo muje ku gaisa da sarkuwa ta ,
Dayar yarinyar da,ban san sunan ta ba take cewa wai da gaske ke matar aure ce,
Murmushi nai mata kawai na mike ina