Showing 72001 words to 75000 words out of 299981 words

Chapter 25 - Sarautar Mata By Makawa

04 Dec 2025

17685

masu jagoran zuwa gaida Umma a dakin ta,
Abin mamaki a saitin tagan dakina muka samu Umma din cikin dan rashin gaskiya take cewa daga ina muka,samu baki, kuma,
Nace Umma abokan karatuna ne suka zo gani na daga makaranta,
Wani kallo naga Umma din tai masu wanda hakan ya,dan sani shan jinin jikina kada ta masu halin ta,
Sai take cewa wanan ma karatun sukeyi suma tirka sa,
Dariya hadiza tayi tana cewa eh mama da yara na kuwa a gida har biyu nabarsu nazo karatu,
Ikon Allah inji Umma Allah ya kyata take cewa muka mike zuwa dakina, hira muke dasu zakace mun dade da sanin juna inayi ina duba girki na dake a,wuta,
Nayi sa,a shimkafa da wake mukeyi da salad kamar yadda mu kan danyi in muna son cin dan dadi, a gidan,
Yaya Ibrahim ya,shigo ya,samay ni ina raba abinci na,da,shake murya kada Umms taji nake cewa don Allah Yaya kadan taimaka min da ruwan leda mai sanyi baki nayi daga makarantar mu suka zo min yini,
Yace madallah aiko sun kyauta bari na fita na,sayo maku,
Ban zauna ba ina yi ina dan leken kofan shigowa gida,
Allah ta taimakeni sai gashi da bakar leda maigiwa ya,sayo min lemon gora masu sanyi har guda biyar da kuma ruwan sanyi,
Zan maí godiya ya wuce ciki yana cewa kai haba ai rufin asirin mu ne baki dayan mu,
Ina,son na debawa su Umma ruwan sanyi ina jin tsoron fada kartace na,saka dan ta,a lalura na don haka na,ajewa wasu Hadiza gaba daya a,gaban su,
Nai mamakin yadda suke cin abincin hakali a kwance muna hira,
Ban yarda na ci abincin sosai ba don baida wani yawa sosai ina tsoron Umma tace min na kwashe abunci nabawa kawayena,
Naji dadin wanan zuwan da sukai min don ko ba komai sun sake jikin su dani munci mun sha dan abinda Allah ya hore min, batare da kyankyami ba,
Wuni sukutun sukai min don sai bayan karfe biyar suka,bar gidan mu sun sake jiki abinsu da kowa,
Bayan tafiyan su ne Umma take cewa su kuma haka akeyi kazo gidan mutum ka,wani shagala,har wani lokaci, haka,?
Banji dadi ba amma na godewa Allah da,bata fada a gaban su ba,sai bayan sun tafi take zancen ta kamar mai fada, da wani,

****** ********* ******
I yanzu hanakali na ya fara dan kwantawa a gidan don nasan halin kowa a cikin gidan,
Sai dai kullun ina cikin taka tsatsan ne da abinda zai ita jawo min fitina daga Umma da kannen mijina
Haka zalika ita ma Umma din yanzu ina da dan sasauci daga gurin ta tunda yanzu Hamza din ya dade baizo garin ba,
Umma da yayan ta take komai, lokuta da dama koda ina zaune tare dasu ne zata iya kebe ni tai al,amarin ta da yaranta,,
Wanda hakan na daga cikin halaiyar ta dake iya kawo matsala a cikin gida,
Wata rana bayan an sauko daga sallah jumma sai da na dan kai wani lokaci na mike tare da dan gyara fuskana na leka dakin Umma ina mata ina wuni tare da dan tambayan ta ko may zan dafa,muna a ranan,
Don a kullun sai abinda Umma tace min na girka nake girkawa a gidan ko ina ta tafi tane dole sai na jirata duk inda ta,tafi ta dawo zan tambaya na dafa muna,
Na,samu Umma da wata bakuwa a dakin suna magana su biyu,
Haka,kawai ganin matar ya sanya girjina bugawa don sai naji sam matar batai min ba a raina ,
Na gaida,su a cikin ladabi inda matar ta dan kalle ni cike da fara,a take cewa ashe kina ciki yar Agwai ai na zata kin futa ne,
A takaice nace ina ciki barci ne ya kwshe ni ,
Na juya har zan fita daga dakin sai na kalli Umma nake cewa Umma may zan dora muna ne, tace ai muna da sauran gari ki girka muna shi mu ci,
Na bada baya kadan nake jin bakuwar Umma wace aminiyar tace tana fadin,
A,a Rabi wanan yarinyar fa tayi min gwabi a idanuwana,
Kardai nace gashin kanta take ci tai wanan kyau haka tabarki a lahaula,
Don kin san yaran yanzu sai kin gama wahala da danki sozo suce sun fiki son shi da kaunar shi,
Su saka,namiji a gaba suna mai wayyo duk abinda ya samu a hannun su yake,
Ke Uwa kina zaune sai dan abin da a ka tsakuro maki zaki gani,
Umma tace cabdi ai ban yarda da,wanan sakacin ba shiyasa kikaga na kafa dokan komai a hannu na yake don bazan yarda da rainon inuwar giginya ba,
Diyana a tafin hannu na,suke bsn yada sun mami kowa ba gatin nan,
Lokacin da nai wahala da abina tana ina da zata zo tai min ikon banza a gida,
Wanan ma dabata da,wani galihu ko agidan malam Mudi din yaushe zan tsaya ina kallo taiwa dana yadda suke so,
Take naji wani irin zazabi ya,sauka min a jiki da kyat nake aikin danakeyi don irin yadda nake jin zuciyata tana,suya a,ranan,
Bayan na kamala aikin da nakeyi na shige dakina ban fito ba,
Ina kwance a kan gadona zube kamar wata mara lafiya, nake jin kaina,
Idanuwana suna lumshe sai zuciyana dake dan bugawa gap gap gap,
May ye laifina a,cikin auren Hamza da nayi da har Umma take min wanan kallon mara galihu,
Tambayan da nakewa kaina kenan ni kadai a cikin dakin,
Wanda hakan yasa hankalina gushewa daga jin duk wani hayaniya dake a tsakar gidan,
Alamar motsin mutum naji a kaina wanda hakan yadan sani bude idanuwa na don ganin waya shigo min daki a lokaci,
Hamza na gani tsaye a,saman kaina yana min wani irin kallo a cikin shaukin so da kauna irin na mata da miji,
Take na nemi damuwar dake damuna a,rai na,rasa inda na dan yi yunkuri mikewa daga kwanciyar da nake,
Cikin wani hanzari ya mayar dani kwancen inda yayo min runfa da kirjin shi ta yadda bazan iya dagowa,ba,
Magana kamar mai rada yake min yana tambayana may ke damun ki ne may samay yasa yau na samay ki a kwance,
Dan murmushi na kirkiro a fuskana tare da mashi sannu da zuwa a cikin sanyi murya,
Dan mikewa yayi yai zaune a,bakin gadon da nake a kwance ,
Sannu da zuwa na kara,mashi a karo na biyu ya amsa da,mun samay ku lafiya nace lafiya kalau
May kike tunane haka nake sallama baki jini ba har nakai ga,shigowa,
Murmushi nayi nace barci ne ya,soma dauka ta ba tunane nakeyi ba,
Takon shigowa dakin muka ji inda da sauri na karasa kaiwa zaune nima ,
Daidainan ne kanin shi Jibrin ya,shigo da jakar kayan shi sai naji Hamza yana ce mai ina wanan ledan guda biyu dana zo dasu,
Jibrin yadan duka yana aje jakar kayan yake cewa suna,gurin Umma tace na barsu a can gaba daya,
Kace nace ka kawo min sakon Aisha ne a cikin su da,sauran kaya na,
Jibrin din ya,fita ajima kadan yadawo dakin yana cewa daga kofa,
Yaya wai kazo da kanka inji Umma din abinda yasa shi saurin mikewa ke nan daga zaunen da yake,
Mikewa nayi don dama kamar a takure nake a inda nake kwance din da nake,
Ruwan sha na fita na debo mashi a randa tare da abinci,
Muryan shi naji kamar a rai bacd yana fadin mama idan ba aiko ni akayi da su ba kin taba ganin nazo ma Aisha da wani tsaraba wanda ba,gaba daya zan kawo maku shi ba a gidan nan,
Tankar banji su ba yafito daga dakin mama da ledan a hannun shi ran shi a bace, ya nufi dakin mu,
A tsakiya mukai kicibis dashi ranshi a,bace fuskan shi babu annuri a cikin sa ko kadan,
Ina waje ina kokarin hada mai Abinci naji Umma tana cewa wanan ai wani sabon sallon magana ka,dauko min ,
Gaka da kanne a,gida zakace wai matar ka kawai zakayowa tsaraba to su yan uwanka fa,
Na,shigo dakin namu da,sallama yana tsaye yana cire rigar dake jikin shi shirt mai dogon hannu,
Abinci na aje daga gefen tabarma inda na ke ce mai ko zaka watsa ruwa ne ko zakaji dan sanyi don ana zafi,
juyowa yayi inda nake tsaye yana kallo na jikin shi babu riga sai yar farar singilet,
Aisha kwana biyun da nayi banzo yana,da nasaba da irin yadda mama bata son ganini a gida koda yaushe,
A hankali ya tako zuwa inda nake tsaye nadan bi lafiyan bango ina sauraren shi,
Hannuwan shi ya bude yake ce min nazo a cikin signal ,
A hankali na taka zuwa inda yake na,shige cikin jikin shi,
Gaba dayan mu sauke numfashi muke a cikin ajiyar zuciya gwanin ban tausayi,
Kin canza Aisha kin ramay min a idanuwa na kin na cikin damuwar halin Umma ko ?
Na,dan dago kaina dake sune a jikin shi ina cewa banda wani damuwa halin Umma kuma ai ba bakona bane,
Karatune kawai a,gabana,shine damuwata yanzu,
Murmushi yayi yakara mannani a jikin shi yana cewa tare da dan bubuga min baya,
Ohoo sorry da ina kusa da baki da matsala yan mata sai dai kashh nesa baya maganin kusa,
Amma nasan aike ma baki da sauki gurin kawo wuta ga karatu,
Ki dai cire damuwa a,ranki kinga ki kuwa kin wani dan fada haka dake,
Bari na baka ruwa sai ka watsa kazo kaci abinci ka huta gajiya, ko
Nakai kofan daki yake cewa ga tsaraba nan hajiya, Nurat tace na kawo maki sai dai ina gani Umma ta,debawa yaran nan wai,
Kai Allah ya umfana nace acikin dan murmusawa wacece kuma hakana yaya ?
Wata course mate dina ce sai da ba yarinya bace shiyasa nake taimaka mata Allah sarki nace sai nafita, daga dakin,
Bayan yafito daga wanka ya,zauna yana cin abinci kafin ya fito na canza kayan jikina nai yar kwaliya yadda ya dace nayi,
Ina,daga,gefen shi zaune autarsu Sa,ade ta,shigo dakin tana cewa yayan mu, Umma tace wai kazo kaci abinci,
Ya dago kai yace a,a autar Umma,ba ko gaisuwa, kin shigo daki kina kumbura haka,
Tace a dan shagwabe ba Asamau bane ta kwshd kayan da kazo muna dashi ni ban samu powder ba,
Dan jin mu kaji gaba dayan mu amma,sai nake cewa, zo ki bude ledan ki duba idan akwai abinda zaki dauka,saiki hada da,wanda ta bar maki,
Ba mussu yarinyar ta nufi inda ledan yake wanda ban ko bude ba tafara dudubawa, a hankali ,
Naji yana cewa ina turaren dake a cikin ledan suke tace Asmau ta dauka,
Jekice wa Umma abincin nake ci Asmau kuma ta baki turaren ki dawo min dashi ,
Ina dan tsiyaya mai ruwa a,wani dan karmin cup dake a gaban shi naji Umma tana fadin ke Aisha
Wani abinci kika bashi bayan ga abinci nan an hada mashi a daki,
Da sauri Hamza ya katse uwar da cewa Umma can naga ta debo min mana,
O lalai mai mata ko har tasan zafin ka ashe ban sani ba,?
To turaren dakace a karbo gurin ma,u na ce tabarshi don matarka batafita ba ai,
Mama nawa ne fa bana Aisha bane wanda nake amfani dashi ne a makatanta,
Tace nace baza,a bayar ba ko zaka kwatar matane ?
Da idanuwa nai mashi nuni da ya kyale don Allah don banson suna jan zance kar yai girma,
Haka ya gama cin abincin a dan hasale ran shi a bace amma don na kawar da zance sai nake cewa,
Da engineer kukazo neina nufin mansur mijin anty hindatu,
Yake cewa, tare muka zo kin san akwai buki a gidan su matar shi a karshen sati mai zuwa,
Da sauri na,dago kai nace kenan yaya kana nan har wani sati mai zuwa,
Yace insha Allahu haka nake tsamani idai ba wani abin bane ya taso aka kira mu,
Allah yasa kada a kiraku baki na ya furta cikin subbucewa ban sani ba,
Cikin murmushi kamar mai rada yace baki son na koma ne yanzu,
Kunya naji nace cikin dan dafe fuskana ba haka nake nufi ba ,
Na mike zuwa gefen akwatin kayana da mamana Rahana ta bani lokacin da zantare a gidan,
Sunana ya kira inda na tsaya cak na,ansa ciki,ciki gami da juyowa, zoki zauna ba mussu nadawo inda na zauna dafarko na zauna,
Yace kiyi min lissafin abinda keke bukata na,saya maki wanda zakiyi fitan bukin su matar Mansur dashi don ina son kije gurin sha,anin bukin ayi shi dake,
A sanyaye nace duk abinda ka saya min ina son su yaya basai na fada ma abinda nake so ba,
Anty Hindatu din ma tazo gidan nan takawo min anko dina tare da kudin din ki, shine zan dauko maka ka gani,
Hindatun ta kawo maki nace eh har da kudi dubu biyar wai nakai dinki,
Shiru yayi na mintina sai ya sauke ajiyar zuciya yana cewa Allah sarki ,
Wa yannan mutanen Allah ya,saka masu da,alheri,
Mijin ta haka yake min dawainiya a makaranta wallahi tun ina jin kunya yanzu har na daina jin kunyan shi,
Banda abinda zan bashi don shi mai haline tunda yana,aikin gwaunati haka yasa nazama mai kamar yaron shi, shima bai son haka amna dole ya gaji ya kyale ni,
Kayan da Hindatu takawo min na,dauko mashi tare da kudin nai mai bayanin naba Umma dari biyar daga ciki,
Da,sauri yace dama Umma din tasan cewa ankawo maki kayan ne?
Nace a,a don Anty hindatun ta hana na nuna ma kowa wai sai in na,saka a,gani a jikina,
Murmushi yayi don yasan ko wacece Hindatun tunda yana da labarin ta,a gurin mijin ta,
Nasan da Umma tasan da kudin nan bazata barsu a hannunki ba don haka sai kiyi laluran dakike bukatan yi dasu,
Nace cikin kara tausa muryana Ummina nake son nabawa wani abu daga ciki don tun da nai aure ban taba bata alheri ba,
Yace kin kyauta kwarai wallahi sai ki bari idan na huta kwana biyu sai mu shirya,mu shiga mu gaidasu,
Shigowan Ibrahim ne ya katse muna hiran mu inda na samu daman tashi na dan kimtsa kaina don taron bakona na wanan ranan,
Daga cikin tsaraban hindatu da zarah nai amfani na kamala komai ina jin hiran su a tsakar gida har na kai ga kwantawa,

****** ********** ******
Washe gari natashi agajiye saukina guda,shine ranan ban zuwa school,
Don na gaji sosai saboda Hamza bai raga min ba,a wanan daren don komawa yai min kamar ya,zautun,
Zakace a,wanan ranan ne ya fara kwanciya dani saboda irin yadda ha zarce min,
Ni kaina,sai da abin yadan ban tsoro amma haka na,daure na biya mai bukatun shi don Hindatu tace min kada na,yarda na nunawa namiji gazawa koda kuwa bana jin dadi ne na,daure na gamsar dashi ta fannoni da dama,
Duk yadda naso na,fito da,safe don yin normal aiyukana hamza din ya hanani yana makale a jikina kamar ba gobe,
Sai da ya gaji don kan shi ya,bari muka,fito lokacin gari yai haske sosai inda muka,samu Umma ta cika fam damu,
Amma haka na dake nafito nai wankana na koma,daki nai sallah na na gyara jikina inda na,saka,wani dogon riga na material ne don tun a,gida nake dashi,
Nafito zuwa gurin da muke girki yau Umma bata dora,wutan girkin ba don haka nice na dora da kaina,
Aiki nakeyi amma zullumi nakeyi don zuciyata tana fargaban abin da, Umma zatai muna, ranan,
Hamza ya fito daga dakin mu tsab ya shirya acikin wani simple yadi assh, na maza a mai dinki mai dane jiki,
Dakin Umma ya nufa inda ya shiga da sallama ya samay ta a,zaune, tare da yaranta sun sayo masa suna ci mai zafi,
Nanya,shiga gaisawa da yan uwan shi a cikin jin dadin yan uwan shi,
Umma tana daga gefe ko daga,kai ta kalle shi batayi ba sai cin masan ta takeyi hankali kwance,
Cikin dan sanyin murya yace wa,Uwar ina kwana Umma,?
Lafiya ta amsa mashi dashi a,takaice,
Ibrahim ke cewa azubo ma masan ne kaci ko don naga yanzu ka,a
shigo,
Matar shi ai tana da,abin bashi ya karya a can don haka kudai kuci kuda, kuka,dogara a,kaina,,
Wani irin kumci yaji irin yadda Umma tai mai shi haka gaban yan uwar shi, batare da ta bari sai suna su biyu ba,
Jibrin wanda bai san dawan gari ba yace ai Aisha akwai kokarin hada abinci wallahi shi yasa nake son ta,don ko yaushe kazo zaka,samu ta gama abinci kaci,
Dariya sauran suka saka mai har da Hamza din wanda ran shi yake a bace,
Ibrahim yace kaiko don cin abinci kawai kake son ta a gidan nan,
Yace a,a komai fa nake so idan tana dashi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login