Showing 75001 words to 78000 words out of 299981 words

Chapter 26 - Sarautar Mata By Makawa

04 Dec 2025

17666

bani zatayi ai na fada mata,ba kishiya a gidan nan,
Kai kai kun isheni da shirmay irin naku inzakuci abinci kuci idan kuma surutu zakuyi min ku cika min kunnuwa da,shirmay ku bani guri don Allah na karya,
Mikewa Hamza yayi daniyar barin dakin Asmau ke cewa yaya tsaya mana na,zuba maka masan kaci,
Yace No ki barshi Ma,u na gode zan fita na,samu abinda zamu ci,
Fushi kayi ne yayan mu inji Ibrahim yake tambayan dan uwan nashi,
Yace idan naci wanan ita Aisha fa may zataci daga ciki bari na fita sai na,samo abinda za,a kara dashi,
Wanan din ba zai isheku ba ku biyu idan zataci ?
A lokaci har ya kai kofa yace abarshi kawai yasa kai yafita yabar su nan,
Ina duke a,murhu yake cewa ki sa,ruwan zafi bari na,samo bread asha tea,
Na amsa a,sanyaye ya fita daga gidan inda naci gaba da,aiyukana sai dai rayuwana ya,bani cewa,Hamza din ya,fara dan zare wa mahaifiyar tasu,
Na hada tea din gaba,daya,wa kowa inda na zuba namu a jug dina nakai daki na dauki bread guda da guntu nakai dakin Umma,
Bayan a je zan juyo Umna ke 'cewa kece kika raba da ka ki ke nan Aisha,
Cikin dan jin nauyi nai tsaye ina dan dukar da kai murya kasa kasa nake cewa,a yi hakkuri Umma shine yace na hada adebo akawo nan dakin,
To aikin san mijinki ne ya,sayo muna shiyasa zaki min gaba gadi,
Umma dan Allah kiyi hakkuri nayi kuskure bazan sake ba insha Allahu,
Umma a gabana fa ta hada komai kuma,dan kadan ta zuba masu su biyu, Sa,ade ce kaunar shi ke wanan magana,
Rufe min bakinki yar nema mai bakin surutun tsiya basu bari mutum yai magana,
Haka na,samu dama na koma dakina,sukuku jiki ba kwari na,samu guri na zauna nai shiru a cikin damuwa,
Yace may akayi may yafaru kuma ?
Ba komai na furta yayin da wani abu ya tokare min zuciya cikin bacin rai nai magana,
Shi da kan shi ya zuba min a cup ya miko min agaba tare da turo min ledan bread din a gabana,
Dauki ki sha ya furta min tare da kafeni da lausasaun idanuwan shi masu firgita mutum,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
👑 SARAUTAR MATA 👑
2⃣1⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA



BISSIMILAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,



Zaune nake a gaban dan mirron dakina ina kwaliya da kuma kara gyara jikina,
Sai dai zuciya ta tana fam da tune da zullumi wanda bai wuce duk sanda Hamza yake gari ina cik8n matsi da tsangwama a gurin Umma,
Wanda na rasa gane ko maynene ke jawo min wanan matsalar ba haka a tsakanin mu,
Ni dai a iya sanina ina kokarin ganin cewa ina kyautata mata yadda ya kamata,
Amma kuma hakan bai sa na samu maslaha daga gare ta ba ,
Hamza din ne ya,shigo daki da,sallama a,bakin shi, na amsa mai da,wa,a,laikussalam,
Sannu da zuwa nai matare da son mikewa tsaye amma,sai ya,mayar dani na zauna ta hanya saka hannayen shi ya,rugumoni ta bayan shi,
A hankali ya dan rada min a kune matar Hamza kin yi kyawo Allah ya ba hamzan ki kudi na,di ga saya maki kayan kwaliya masu kyau k8na min kwalliya saboda ina son ganin mace tai kwalliya a,rayuwa na,
Ta cikin mirror da nake zaune gaban shi muka hada ido yadan daga mi gira a hankali, sai na sune fuskana cikin kunya ina fadin ameen ya Allah,
Mikewa yayi daga dan rankwafo min da yayi yana cewa bari nima na watsa ruwa na zo mu tafi ko,
Don har gidan mama Rahana nake son yau mu shiga insha Allahu don ina son matar nan don tana da hali mai kyau wallahi,
Duk lokacin da na zo garin nan sai ta aiko danta ya gaidani da sakon gaisuwa,
Murmushi nayi mama Rahana ai ba ruwan ta da,sauki ta dauki rayuwa ita,
To bari na je na,watsa ruwan nai wanka na,danzo na shirya mutafi,
Bari to naje na zuba ma,ruwan wa ka ko kafin ka fito na gama,shirina,
Ya ce a,a zauna abinki zan diba a kaina ai watsawa kawai zanyi don naji sanyi,
Na koma naci gaba da shirina yafita ina jin shi yana zuba,ruwa a randa, dake daga kofan mu,
Lokacin Umma ta fito daga dakin ta ina zaton daga,barci ta tashi,
A,a Hamza kai da kan ka ke diban ruwan ne ina matar taka,ne kake diban ruwa da kan ka,
Ummz ni nace ta,bari na diba da kaina don ina sauri ne zan fita,
To, to, Allah ya kyauta don kana sauri ita kuma shine ta zauna kai mata aiki ko ?
Daukan ruwan yayi zuwa banda daki yabarta a wajen tana jinini ita daya,

Tsab nafito cikin shirina na,fita zuwa uguwa gaida iyayyena kwaliyar tai min kyau sosai don ni kainaxnasan yanzu na,fara faso gari,
Kofan Umna muka nufa gaba dayan mu don muyi mata sallama akan zamu fita,
Shi ya fara shiga ina,daga tsaye waje ina,rufe kofan dakina wanda duk masifan Umma banyarda in zan fita na barshi a bude ba,
Muryan ta nake ji don dama nasan za,a rina don bata kaunar taga zamu fita a,tare dashi,
Hamza duk zuwa kayi wai sai kun fita da Aisha a gidan nan ne don may wai baka da ta ido ne kai,
Kana biyewa mace tana sakaka a hanyar shedana don ita tariga ta bushe nata fitilar kunyan bata jin nauyin fita da miji da rana tsaka haka ga,
Umma bafa wani guri zamu tafi ba gidan iyayyen tane zata shiga gaidasu kawai, kuma dai kin san ya,kamata taje gaida su,
Sallaman Zarah ne ya katse mata fitinar ta tana cewa umma sauri mu keyi nazo ne na,duba lafiyan ki,
Ganin yayan ta taja tai turus tana cewa yaushe kashigo gatin nan banda labari ni,
In badon na,dan biyo gudu gudu na da har ka koma,ban samun ganin ka, ko,
Ya juyo yana kallon ta a,cikin murmushin jin dadin gani yar uwan shi, yake cewa Zarah may kike ci kika koma haka, ne wai,
Tace kwanciyan hankali yayana banda matsalar komai a gidan daga mijin har matan shi muna zaman mu na lafiya,
To may zai damay ni tunda banda wanda ya sakani a gaba,
Sai a lokacin ta hangoni a tsaye ta kofan dakina ina a tsaye ina mai, kallon su a cikin sha,awa,
A,a yanzu kina ciki shine kika kyaleni bayan kinji shigowa na ,
Nace wace ni na kyale ki anty nadai ga kuna magana da yaya ne,
Fita zakuyi ne halan ta tambaya acikin kallon kwayan idanuwa na,.
Shi ya bata amsa da cewa zata shiga gidan su ne yau ta gaidasu,
Zarah tace Allah sarki kasan ita Aisha halinta irin na mutane da ne,
Idan da nice ke kusa hakan nan, ai wallahi da kullun sai na,shigo gidan nan,
To bake bace inji Umma daga inda take a tsaye take fadawa zarah din haka a cikin fada,
Sai lokacin ya,dan dago kai yana duban gurin da nake a tsaye yake cewa to ya muje ko ?
Na tako a han zuwa gurin da Umma take a tsaye nace cikin sanyin murya
Umma zamu tafi sai mun dawo,
Ke nan yau baza a girka muna abinci ba ke nan don ban san dawowar ki gidan nan ba,
Zarah tace Umma ita da zata gida dubiya gasu Ma,u nan bazasu girka ba, su, ?
Allah kai lafiya don wanan bazata bari na kai ga zance na ba take cabewa,
Yana gaba ina bin sa a baya cikin dan takona a nutse,
Inda Umma ta raka mu da harara har muka kure ma ganin ta,
Take cewa wanan badon ina tsaye ba da yanzu ta dade da mayar da yaron nan susu, a gidan nan,
Zarah take cewa Umma ita Aishan har tasan mayar da,wani miji susu yarinyar da wayau ma bai gama isarta ba,
Kike gani ko wanan wanan mai suffan muna,fukai din barta nan kawai inda kike ganin ta, don ina maganin ta ne a gidan nan aida kin ga yadda zata mayar da dan uwan ki,
To ni bazan yarda ba ace ina kallo wata ta zo ta mayar min da da solobiyo, agidan na ,
Amma gaskiya Umma kinawa Aisha kallon na,rashin fahinta don dai gaskiya yarinyar nan tana iya kokarin ta ga hakkuri ,
Ki duba fa Umma ko suturan kwarai fa bata dashi amma bata damu ba sai harkokin ta takeyi kawai,
Haba Umma koma irin yadda akai auren nan ai ya kamata ace ta samu karbuwa a gurin ki da gurin mu muma,
Amma sai gashi tayi don fitar da mu da kuma uban rikon ta daga kunya kuma,shine za,a mata irin wanan taron a gidan nan,
Ikon Allah wai yaran nan may kuke nufi dani ne a gidan nan,
Kuna nufin ban san abinda nakeyi ba ne ko ku zaku gwada min yadda zan zauna da ita nifa na haifi mijin ta,
Yi hakkuri Umma kawai dai na ga cewa yarinyar babu ruwanta ne inda watace da yanzu anji ku a gidan nan wallahi,

****** ********** ******
Muna fita kofan gida na ga mashin a bakin shagon shi yake ce min najirashi yadan zo,
Shagon ya shiga gurin ibrahim wanda na hango yana cin wani abu,
Tun da na,shigo gidan su da,sunan aure ban taba shiga shagon nan yin wani abu ba,
Hakan ma yau din ina tsaye dafa kofan gidan yazo dauke da leda a hannin shi,
Yace oya mu tafi, ko?
Ina zaune a bays muka bar uguwar mu, zuwa inda ya tsara zamu fara zuwa,
A kofan gidan mamana Rahana muka tsaya da mashin din inda na sauka ya mika min ledan da ya dauko a,shagwan shi,
Nice na fara shiga daga ciki inda ya,dan tsaya daga kofa yana,jiran abashi iso ya,shiga daga ciki,
Na,samu Mama Rahana a kitchen tana kokari dora girki abincin rana,
Daga inda take bayan ta karba sallama,na take cewa a,a a wa nake gani yau a gidan nan kamar Aisha,
Murmushi nayi nake cewa cikin dan sone kai nice mama,
Kodai yau kin bace hanyane Aisha ?
Ni har na,debe tsan manin cewa i a,da,wata ya wai Aisha a,garin nan,
Hamza ta hango daga kofan shigowan su tsaye tace kai amma yar nan baki cewa tare kike tafe da maigidan naki,
Nai yar murmushi nace mama a tare muke ai, munzo mu gaida ke ne,
Aiko na gode take fadi yayin da take dauraye hannun ta,da,ruwa mai tsabta,
Kaishi daki mana kin barshi a,tsaye waje,
Na fara shiga dakin da yake tana da kujera a,dakin ta ba kamar na Ummina da babu kujera sai siminti dakin hondakwai,
Amma sai Hamza din yace bazai zauna a saman kujera ba yana kokarin zama a saman tsohon rough carpet din dake malale a dakin,
Mama Rahana akwai tsabta don zan iya cewa da ita da Ummi kamar gadon tsabtan sukayi, don komai nasu tsab zaka ganshi
Mama Rahana tana shigowa dakin ta samay shi a kasa tace Subbahanallahi haba tashi ka,hau saman kujerar mana Hamza ka zauna a kasa kuma,
Yace cikin yar dukar da kai yana ayar kunya mama nan din ma yayi tace ke dauko mai tabarma ki shimfida mai kada ya bata kayan shi,
Na dauko tabarman na,shimfida mai yadan daga kadan yahausama rabin jikin shi a kasa yake,
Suka fara gaisawa da mama Rahana acikin girmamawa tana mai mai godiya tare da kara mai bashi hakkuri da azauna lafiya,
Yakuma yi hakkuri dani ya rike ni amma kamar yadda yakeyi take cewa yarinyar nan abin tausayi ne hamza idan kai la,akari da yadda rayuwan ta ya taso,
Ni abinda yasa kaga hankalina yake a kwance tunfarko wallahi don nasan cewa kai mutumin arzikini yato ne da halin dattako,
Yace cikin kwantar da kai mama insha Allahu ba matsalar komai, ku daiyi muna,addu,a shi muke bukata,
Addua ai muna maku Hamza sai dai mukara kawai,
Yace mungode mama, nace bari wanan shigowan da nayi mu zo mu gaida ku kafin mu koma tace Allah sarki na,gode kwarai wallahi Allah ya,sa maku albarka,
Bari na kira,abokiyar zamana ku gaisa ko kafin ku tafi yace zan dan barta na,shiga can cikin kasuwa kafin nadawo kin gaisa da ita,madallah na gode kaji,
Sai ta dan mike tafita,da,sauri tana kiran mariya mariya kizo ku gaisa da,surukina,
Hamza ya dubeni ya na cewa ki bata wanan ledan tayi hakkuri damu nace angode bai tanka min ba
Mariyan ta shigo ashe cikine da,ita tsoho suka,gaisa itama sai godiya take zab ga mai da nasihan a zauna lafiya,
Bayan tafiyan ta ya mike yana cewa zai je sai yadawo mukai mai adawo lafiya,
Yana fita Umma ta dube ni tana cewa bari na zuba shimkafa nazo nace bari na zuba mama tace zauna abinki Aisha na hutar dake,
Tafita taje kitchen din su bayan ta,dawo dakin ne nake mika mata tsaraban inda tafara fitarwa tana cewa kai amma ko angode clean ne da,sabulu da,man shafawa, guda biyu biyu a cikin ledan,
Aisha wanda ke karatu kikasa yai muna wanan tsaraba haka mai yawa,
Mama wallahi ni ban ma,san da,su basai da muka zo nan,
Hira muke da mama acikin sakin jiki tana tambayana ina bata amsa cewa ba matsalar komai lafiya muke a gidan,
Tace ita uwar mijin naki tabar mugun halin naya ne ko tana kai don kwanaki Fatima tana fada min abinda ke faruwa tsakanin ku,
Tunda Ummi ta fada mata kuma mama Rahana itace yar uwa ta,shakiki da muke da ita a garin yasani fada mata gaskiya,
Nace sai abinda ya karu ai amma ni ban damu da abinda takeyi ba tunda ba zaman ta nakeyi ba,
Tace aini wanan matar tabani mamaki wallahi da farko kamar ta Allah ashe yar sheri ce bamu sani ba,
Nace matsalarta guda shine kada tagan ni tare da,dan ta muna,raha, ko wani jin dadi yanzu zata canza min fuska,
Ikon Allah ashe dai da,gaske shan fitsari da yana,saka kishi irin haka tsakanin ka da matar dan ,ka,
Nace mama ita,fa Umma idan bai gari kusan lafiya kalau muke sai idan yazo ne matsala ke tasowa a tsakanin mu,
Barta Allah ya,fita ke dai kiyi hakkuri kinji ki maida komai ba komai ba,sai a zauna lafiya,
Nace a,sanyaye tau mama insha Allahu zan tsare,
Nafi, awa biyu a gurin mama Rahana muna hira a tsakanin mu irin na da da mahaifi,
Hamza ya dawo ya dauke ni mama Rahana tabashi yaji mai yawa tace yai tsaraban dashi idan zai koma school
Har kasa,yakai gwiwa bibiyu yana mata,godiya inda ita ma take mai godiya a kan tsaraban da ya,kawo mata da kuma ziyara,
A zatona,gidan mu zamu tafi sai naga munsha gwanan zuwa wani uguwa,
Shagon wani
tela mai dinki muka tsaya inda muka shiga telan yake cewa ba,sai ya aunani ba yaga size dina,
Muka,juyo muna tafe yana,min hiran wani abokin shi da,muka fani a,shagon maidinki,
Dadin wanan yanayin na,dinga ji sai nake ji kamar kada mu tsaya mu yi ta tafiya a cikin wanan yanayi
Mun iso kofan gidan mu gabanin shabiyu da,rabi na rana yai min umurnin na, tsaya yazo ledoji guda biyu a cike suke ya,dauko muka shiga dasu ciki,
Ni na fara sallama tare da danshigewa gaba mun samu baba yana gida a lokacin sai dai kamar yana,shirin fitane daganin yanayin shi
Sosai baba ya,nuna jin dadin ganin mu tun kan mu karaso gurin shi yake muna sannun ku da zuwa,
Muka,gaishe shi a ciki ladabi da girmawa tare da tambayan shi yaya,kazuwa don a lokacin babu aikin gona,,
Baba yake cewa matar noma kune tafe da,ranan nan cikin dan murmushi nake cewa mune Baba,
Banga mama Saude ba nake cewa,da,yar fara,ata ina mama take, maman Audi,?
Tace ta kewaya ne nake gaishe su yayin da mama,din tafito daga,bayi tana ,cewa,Aisha kune tafe yanzu na amsa da eh mama ,
Muka gaisa da mama,din tana,min yaya,gida yaya makaranta Ummi tana daki tana shara, muka,shiga gurin ta na bar Hamza da baba suna magana a tsakar gida,
Ummi tace kune tafe a she nace na aje lededojin da muka,shigo dasu daga gefe wanda Atika idanuwan ta,suke akai tana kwankwaton taga abinda ke a cikin su,
Tabarma na,dauko na,shimfida mu na tare da cire hijjab dina na,dora,saman gadon Ummi, wanda ya,sha gyara da,wani farin zanin gado, tsoho ya,kode amna,da,aka shimfida yasha gyara sai yai kyau,
Na zauna ina cewa wasshh duk nagaji kamar nai wani aiki Ummi ina,su yan biyu ?
Tace yanzu su kabi Bintu zuwa,sayen icce, nan bayan mu,
Lokacin ne Hamza ya,shigo dakin da Sallama a bakin shi Ummi ce ta karba mai,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login