Showing 78001 words to 81000 words out of 299981 words

Chapter 27 - Sarautar Mata By Makawa

04 Dec 2025

17678

Suka fara gaisawa tana mashi yaya gida ya jama,a ya karatu da sauran su ,
Ummi take cewa yanzu kuka fito ashe na amsa da cewa daga gidan mama Rahana muke tace ikon Allah,
Yau har can kuke tafi kai amma ko naji dafin jin haka wallahi kun kyauta kwarai da gaske,
Baba ya dan daga labulr yana cewa matar noma ya ita Umman taku take tana lafiya ko,
Na ce lafiya take baba tana,gaida ku ,
Baba yake cewa tau ni zan fita indan kun koma ku gayar min da yayan taku,
Hamza yace a nan ai zata wuni sai yamma zata koma idan Allah yakai mu,
Hannu Hamza ya,saka ga aljihu ya,ciro kudi wanda,ni ban san ko nawa bane yana mikowa baba yana cewa ayi hakkuri da wanan ba su da yawa sosai,
Abinda ya,dan sa Baba shigowa daga cikin dakin ke nan yana cewa, a,a kai ai ba zancen hakkuri a nan
Wanan dawai niya haka Hamza nagode nagode irin kyautan da,aje kiran kyautan yan aljannna ke nan,
Lokacin da baka da shi gaba baka dashi baya,sai Allah yai maka budi ta hanyar alheri,
Wallahi yau kwana,biyu mudina nake a gidan nan
Yanzu sai gashi Allah ya kawo min alheri ta dalilin ka nagode nagode,
Aisha kiyi min godiya,a,gurin mijikin kin ji na gode,
Murmushi nayi ban iya amsawa ba naiwa baba a,dawo lafiya yafita muna jin shi waje yana nunawa su mama alherin da,akai mai,
Godiya Ummi take yi mai yace kai haba Ummi a dai muna addu,a shi muke bukata kawai,
Yace min kasakasa da murya wanan ledan kibawa Ummi dayan kuma idan sun dauka su raba a tsakanin su,
Ummi na mikewa,ledan nai mata bayani kamar yadda yai min bayani,
Ummi tace Hamza kai da ke karatu kai muna,wanan tsarab haka mun gode kwarau da,gaske Allah yasa albarka a rayuwan ku muka,amsa da Ameen ,
Kadai yi ta,hakkuri da kaunar taka hamzs kasan wayon sai a hankali don Allah kakara hakkuri ,
Yai muna,sallama ya fita muna ji yana wasu mama Saudde sai anjimsa,
Sai lokacin muka, jawo leden muna budewa kayane irin n
👑 SARAUTAR MATA 👑
2⃣2⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ARRAHAMANIN RAHIM,,,

Dinkuna masu kyau a ka dinko min irin na zamani wanda mata ke yayi alokacin daga buje da riga sai wrafer,
Kala biyar ne atamfa sai shedda cikon na shidda, takalma gyale da mayafin su da hijjab guda biyu,
Maimakon nayi godiya sai hawaye suka dinga silalowa daga idanuwa a hankali,
Hamza wanda yake tsaye yana kallona sai faman murmushi yake a fuskan shi, ganin yadda yarinta da kurciya ke aiki a kaina,
Ji nayi ya dan rugumoni daga bayana yana cewa haba matar Hamza godiyan ne haka ?
Ko kayanne basu yi maki yadda kike so ba ya sakaki kuka,?
Da sauri na daga fuskana da,sukr taf da hawaye ina cewa cikin girgiza kai ,
Ba haka bane ina kuka ne ksn bansan irin kalamin da zanyi maka godiya da su ba,
Yaya Hamza wanan kayan masu yawa da kyau da tsada duk ni Aisha ce da su ?
Aisha yar agwai ?
Rugumani yayi cikin jikin shi yana dan bubuga min baya a hankali alamar ana lalashi yaro,
Yace nai maki su ne ki samu na shagalin buki ki samu suturan shiga cikin sa,an ki,
Aisha ba yau ba ina da gurin maki sutura idan kinyi la,akari da cewa ban maki laife ba a,baya,
Amma kuma sai ban samu goyon baya ba,a,gurin Umma,
Wanan din ma Mansur ne yabani shawara na,saya tun a,sokoto batare da kowa ya sani ba,
Don haka ki share hawayen ki hakkin ki ne bana,wata ba banga abin kuka aciki ba,
Kara shigewa jikin shi nayi ina dan sheshekan kuka a hankali da kyat na iya furta Yaya Hamza na gode Allah ya kara rufa asiri,
Jin muryan Umma ta shigo gidan yasani sauri watsakewa na dan goge fuskana don kada ta gane cewa nai kuka,
Idanuwan Umma,a kofan dakin mu yadire inda tai ido biyu da takalman danta a kofan dak8n wanda haka ya sanar mata da dan nata yana gida a lokacin,
A,a kuna daga cikine Hamza ne ya amsa mata da cewa eh Umma sannu da zuwa,
Abinda yasashi mikewa ke nan yayowaje adaidai lokacin da Umma take kokarin zama saman dan kujeran da ke a kofan ta wanda ta aje don zama,
Aisha na,amsa da na,am Umma nagyara gurin da na,boye kayana don kada kowa ya gani, sai ranan da zan sa a jikina,
Na fito daga dakin ina cewa sannu da zuwa Umma ta karba min da yauwa, yar nan,
Zo ga dan zogala na sayo ki gyara min ina fatan kin gama abinci na amsa da eh Umma,
Umma ya cire dan kwanli dake kanta tana dan fitaran jikin ta dashi tana fadin yau ana rana a garin nan,
Hamza ya amsa da cewa wallahi Umma lokacine ya fara na damana,
Gashi bana ina son na kara fadin gonana sosai fiye dana bara,saboda nadan kara samo ilimin akan aikin gona,
Umma tace aini nafison kafara yin noma a,gonar ku ta hanyar Kalgo,
Umma wanan gonan yai min girma kuma a halin yanzu yai min nisa sosai don haka kinga sai nan zuwa mu dan kara girma idan da rayuwa, takai mu,
Nifa hankalina bai kwanta ba ga azzaluman yan uwan mahaifinku,
Haba Umma inji Hanza wanda har ga ranshi baijin dadi idan Umma din tana zagin dangin mahaifin su,
Cikin dan bacin rai Umma ke fadin nifa inba don ku ba da tuni na koma gida don wanan zaman danake nabar mahaifana da yan uwana ina zaune nan cikin bare,
Hamza yace haba Umma yaya zamu kwashi jiki har mu Bakwai mu kai masu lalura su ma,suna fama da kan su,
Mai karatu na fada maku cewa Umma yar bauchi ne amma ba bauchi state ba,
Wani gari ne da akecewa bauchi har sarautar garin sunan shi sarkin bauchi,
Garin yana acikin jahar Niger state, gab da garin Zuru na kebbi state,
Garine wanda ya tara alumma kaman Dakkarawa, Dukkawa, Hwakkawa, kabarawa,
Aiki nake amma hankalina ya na,akan hiran da sukeyi a lokacin,
Na kawo mata ganyen da,na,gyara mata a,gaban ta tace kin saka komai aciki ko nace eh Umma,
Najuya na,dauko mata abincin ranan ta wanda tuwone mukayi, shima na girke mata tare da debo mata ruwa,
Sai da Umma ta gutsuri towo tare da ganyen ta takai ga bakin ta take cewa,
Wai kuwa kana da labarin Baba n ka Madu yana fama da ciwon kafa sosai,
Subbahanallahi inji Hamza yace tun yaushe hakan yafaru Umma,
Takara kai abincin ga baki tace an kwana biyu fa amma ai ina ganin yaji sauki yanzu tunda ban kara jin komai ba akai,
Hamza baiji dadi ba sam a rayuwan shi saboda ya fahinci mama din bata je duba dan uwan mahaifin nasu ba ke nan,
Aiki nake amma ban yarda cewa na nuna ina sauren su ba

****** ********** ******
Da yanma Hamza yafita ya,shiga gari ya sayo guro kursa kursa cike a leda, don yasan cewa Baba Madu maciyi goro ne sosai,
Ya,samayni ina kwasan abincin dare yake ce min idan kin yi sallah zamu gidan su Baba mu duba jikin nashi,
Yadda yace hakan akayi don ina gamawa na shiga wanka tare da daura alwala nai sallah,
Najira,akai sallah i,shai, alokacin nashirya a cikin suwa,wax dina mai ruwan yello da green din flowers,
Sai ko gashi ya shigo dakin yake ce min idan kin shirya sai mu tafi kada,dare yai muna,
Mun futo muna sallaman Umma aiko sai ta fara sababi inda take shiga ba nan take fita ba tana fadin,
Na fahinci kacanza rayuwanka kana,son ka,gwada min cewa yanzu ka fi karfina hakan yasa kake kokarin koya wa matar ka tai min rashin tarbiya itama,
Amma in bashi ba yaya za,ace tunda kazo garin nan baku da aiki sai fita,kaikenan goya mace a mashin kuna yawo a cikin gari,
Ya fahinci manufan Umma so take ta hanashi zuwa sada zumuncin da yai niyya gurin yan uwan mahaifan shi,
Don haka cikin girmamawa yake cewa Umma Baba Madu, zamu je dubawa ba dadewa zamuyi ba,
Kuma ai kinga itama ya kamata ace na nuna mata yan uwana don tasan su,
Wasu yan uwa yan uwan da suka watsar daku lokacin da kuke bukatan kulawan su gare ku,
Umma duk abinda,sukai muna sune dai yan uwan mu duk wani da nagari da yan uwan shi yake kadagi,
Sai mun dawo,
Bata amsa mai ba yasa kai yafara tafiya yana ce min mu tafi ko,
Nabi bayan shi simi simi cikin karfin hali nace mata sai mun dawo Umma,

A kofan gidan su na gado muka,samu Baba Madu kwance a saman wani tabar roba tsoho da gani a,kwai talauci a tare dashi,
Farin gashi ya, rufe mai gemun shi ga,wani tsohon filo a bayan shi,inda yake dan jingina bayan shi,
Kafar shi dake ciwo yana a mike tadan hau sosai alamar tana mai ciwo,
Inda ya,dan motsa kafar a cikin dan cije bakin shi yana cewa Hamza kune tafe yace eh Baba mune a tafe,
Mun dan zauna daga gefen tabarshi kadan muka,fara gaishe shi da jiki yana karbawa da kyat,
Baba tun yaushe kafan ke ma ciwo hakane ?
Hamza yakewa dan uwan mahaifin nashi wanan tambayan acikin nuna yar damuwa,
Dattijon yadan kara cizon baki yace ya kwana,biyu ai sannu sannu ya fara min wanan ciwon har yakai haka,
To Baba bakaje asibiti bane a,dubaka?
Yai murmushin karfin hali yake cewa, ai sau daya na tafi suka ruboto min magani nasha dana shafawa,
Har na,fara,sha shi na,shafawan ne ya gagareni saye har yanzu,
Hamza ya dan matsa gap da kafar yana dan dudubawa yana cewa sannu Baba,
Nima daga bayan shi inda nake a zaune nake cewa cikin yar muryana sannu Baba,
Baba ya juyo yana cewa mai dakin nakane nan ko ?
Cikin dan jin kunya yace ita ce Baba ,
Ikon Allah ai ina ganin baku taba zuwa da ita gidanan ba ,
Uwar ku ta hana kuyi zumunci da mu Ibrahim ne ma da yakan danzo yanzu ma,sam ya dauke kafan shi,
Cikin jin nauyi Hamza yace ba hakana bane Baba don ko yanzu itace ma ta fada min cewa baka jin dadi nazi na,dubaka,
Sai naji Baban yace hmmm kawai batare da yai magana ba,
Yace ita Zarah ai sun zo da maigidan ta har sau biyu suna dubani,
Ledan goron ya,tura a,gaban Baba din yana cewa Baba ga,wanan a yi hakkuri ya dauka yana saka muna,albarka wanda naji dadin hakan,
Hamza yace ya bashi takardan magani ya gani yace Hamza maganin yana da tsada dan har gurin dubu ukku akace,
Ya,dafa filon shi ya dauko takardan maganin wanda don dadewa ya,tsufa har ya murmurde,
MOVE yaga an rubuta muryan babane kecewa ance kala,biyu ne akwai na india yafi kyau da amfani shine dubu uku din,
Ya saka takarda a cikin aljihun,shi ya cr zamu shiga mu gaisa da sauran mutanen gida,
Sai ga Baban guda tun daga nesa yake kallon mu yana,son ya gane ko su waye,
Sai da ya karaso gab damune ya gane Hamza din inda,shima yake gaidashi da cewa sannu Baba,
Kai dan gidan Rabi kaine yau an tuna damune aka shigo ko kuma,wani abin ne ya kawo ku,
Baba Madu dake zaune yace hmmm yaran nan maye laifinsu su,
Mun gaisa dashi ya amsa muna tsatsaye zai shige gida Hamza yace mai baba ga,wanan ba yawa ya dan mike a cikin ladabi yana mika mai takardan dari biyar,
Sai a lokacin ya dan tsaya yana cewa duk ni daya ke da wanan din yace eh baba kayi hakkuri,
Mun mike zuwa cikin gida lungu lungun gidan munshiga mun gaidasu yabasu dubu daya yace su raba,
Muka juyo zuwa gida sai da muka,dan yi nisa nace ashe gidan yana da yawa ne,
Ai mu yan yawane Aisha muna da yan uwa da yawa amma bamu zumunta dasu,
Nace yaya kakuwa,san irin azaban da aka tanadarwa wanda bai kula da hakkin zumunci ranan gobe kiyama,
Yace ai ba,sai gobe kiyama,ba Aisha tun a,nan duniya mutun zasan ya yi kuskure,
Don idan abinka ya tashi babu yan uwanka a kusa zaka san kai ba kowa bane,
Ban san haka ba,sai a lokacin auren mu don babu yan uwa na,da,suka halarci komai na,sha,anina,saboda suna jin haushin mu tun akan auren Zarah,
Shi baba,Madu ne ma na,samu yazo daurin auren namu,
Har gobe wanan abin yana ci min rai har gobe a,rayuwana,wallahi,
Wanan abin da Ummi taje gani ina yi batasan cewa ina kokarin yiwa yan uwana gata,bane,
Don mu samu su sauko kafin bukin auren su Asmau ya tashi su juya muna baya,
Allah ya huci zuciyar ku gaba daya na furta a fili tare da,ajiyan zuciya,
Ya amsa min da Amin ya Allah,
Maimakon mu koma gida sai gidan su Anty Hindatu muka nufa,
Munyi hira sosai take ce mi ranan saka lalai zata aiko azo a dauke ni zuwa gurin event din da za,ayi na,saka lalai,
Koda muka,dawo gida mun samu Umma ta,shige don haka muma muka,shiga namu dakin,. Duk da nai wanka da zamu fita amma sai da na,dan kara kwara ruwa don naji dadin kwanci da mijina,
Shima ruwan ya watsa nasan Umma batai barci ba tana jin mu kyale mu kawai tayi don ran ta ya baci,
Yana tsaye a kofa bayan ya,rufe muna kofan dakin ne sai naga yaja ya tsaya,daga kofan daki kamar mai tunane,
Mikewa nayi zuwa inda yake a tsaye na,saka hannayenata cikin kunkumin shi kadan,
A hankali na kai kaina,a,saman kirjin shi na kwantar da kaina a hankali, abinda yasa shi sauke ajiyan zuciya ke nan, hankali,
Nadan dago kaina na kalli fuskan shi sai naga tarin damuwa,a,tare dashi,
Cikin baci rai naji ya,dan furza iska yana cewa, Aisha yau ganin yan uwan mahaifina yasa na tuna da mahaifina ,
A lokacin da mahaifina yake da rai duk jumma,a idan an sauko a babban gidan mu muke zarcewa har sai bayan sallah la,asar zamu dawo gida,
Wai kin san may na tuna ne yau wanda ya tsaya min a rai,
Nadan girgiza kai nace a,a yace zakiga mutane yan uguwa suna kai da komo zuwa gaida baban mu mai taro mai sisi haka zai tabawa mutane shiya,abinda Allah ya horewa mutum,
Amma ki duba yau babu ko kaza a gaban gidan mu balle dan mutum,
Allah ka hore mu na Aisha,
Na amsa da cewa Ameen yayana,
Humaira muje mu kwanta a gajiye nake yau kin san na,shiga gona yau da,safe,
Na,dan kalle shi na,sakar mashi lalausar mumushi don in kara,samun damar shige mashi kamar yadda naga anayi a,gidan ma,aurata,
Saboda nayi niyar kwatar zuciyar mijina na rike a hannu na duk abinda Umma zatai min bazai girgiza mu ba,
Ni yanzu nasihan da Ummi da mama Rahana sukai min ya kara ratsa min zuciyata,
Na fahinci Umma dantane bata son taga yana nuna min hakkin na da ya rataya a wuyan shi, ko kadan,
Din ita burin ta,shine tagan mu a cikin rashin so da kauna shine zaman lafiyan mu don na fahinci kamar yadda take so shine ko kwana dani zaiyi sai ya nemi izini daga gare ta,
Gashi yau Anty hindatu takara min dan hasken rayuwa a fakaice,
Nace yayana kada ka damu wata rana sai labari insha Allahu,
Ya jani muka,fada saman gado a cikin wani irin yanayi,
A take jikin mu ya,dauki wani irin bari inda na,samu damar aiwatar mai da,sabon plan din da na,shirya mai a,daren yau din,
Mun dauki lokaci mai tsawo acikin wani yanayi da ni kaina bazan iya cewa ga irin shi ba,
Lokaci mai tsawo muka dauka,a,tare bamu san inda muke ba,

****** ********* ******
Washegari na tashi duk jikina yai min tsami amma sai Hamza yake ce min na kwata nai barci na zai sayo muna abin karyawa,
Haka yasa wani barci ya,daukeni ban sani ba bani na tashi farkawa ba,sai musalin karfe goma da,wani abu abinda ban ta kawar hakan ina barci ba a gidan,
Hayaniyar su Umma yasani saurin bude idanuwa na ita,da yaranta ne suke aikin gida inda nai saurin saukowa daga saman dan gadon katakona mai cin mutum biyu,
Na,saka hijjab dina don na kewaya sai naji Asamau na cewa kin tashi Aisha yaya jikin naki,?
Da,sauki na bata amsa,
Nai saurin fahintar cewa shi yafada masu cewa ban jin dadin jikina ,
Ina,fitowa daga bayi Umma,na,waje ta tsure autar ta, sai tai wanke wanke,
Ita ko sai shagwaba take tana cewa wallahi Umma,sunyi min yawa ni daya,duk zan wanke wanan,
Ina fitowa Umma tace a,a,Aisha kan ya lafa ko ashe jiya kin kwana a,wahalce ne kai na ciwo, da mara,
Nace a,sanyaye eh Umma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login