Sarautar Mata
Chapter 28 of 94
fa ban fahinci wanan irin zaman ba ace mace da mijin ta bata ganin shi sai dare daren ma sai ya raba fiye da tsakiya zakiga mutum yazo maki daya biya bukatun shi ya barka sai kuma,wani lokaci,
Gaskiya nina fara gajiya da wanan irin rayuwan haka ba wani kulawa,
A fusace yace wata irin kulawa kike bukatar na baki bayan wanan,
May na ragaku dashi a gidan nan daga dangin abinci dasha da sutura,
Kubura tace cikin turo baki shi kuma,rashin kulawa fa,?
Mace ta zauna ba wani soyayya a tsakanin ta da na miji sai na irin haka ,
Namiji baya shigowa gida gurin iyalin shi sai tsakiyar dare,
Yayi tsaki yace ohh tuhuma ta kike kenan ko may,?
Ba kudi kike son samu ba dake da iyayyen ki to kin samu aiko,
Wanan madin da kike gani idan bakya so ba,dole bane sai na kwanta dake don ni banda yunwan hakan ?
Jikin ta babu kwari tadago kai ta kalle shi, tayi dan dumm sai kuma tace niko nasan da hakan don naga alama,sosai,
Kalli fa yadda duk na koma na canza nai wani baki da rama kamar wata mara galihu a duniya,,
Amma aikin san ni ba mai zama bane tun farko na fada maki kuma kika amince da hakan ko,
Asalima kin san ni banzo maki da zancen aure ba kece kika matsamin ke da iyayyen ki don ni matata ta isheni rufin asiri basai na daukowa kaina wata fitina ba kuma,
Kubura wace takaici ya rufe, a lokacin ta rasa may zatace don haushi,
Sai kawai tajuya tabashi baya tare da sauke ajiyan zuciya gami da lumshe idanuwan ta, zuciyan ta na mata kuna,
Yacd bari kiji daga yau kika kara cewa zaki min fada akan abinda kikasamu a gidan ina yi sunaki sorry,
Kubura ta harzuku tana cewa muddin ina gidan nan naga abinda ba daidai ba agidan nan dole ne na yi magana akai,
Ganin yadda Kubura ta butse mashi ta bude mai wuta yau din yasa shi shima bude mata sukayi ta musayan zance a tsakanin su,
Yake cewa wai an fada maki cewa,saboda wani abu na kawo ki gidan nan ne tausayin mahaifinki yasa na har na amince da zancen auren ki,
Amma shigowanki duk kina son ki tada min hankalin gidana, indan ma wa i neya ture ki akan na fada maki inda nake zuwa bazan fada ba, ki kuma kama kan ki,
Kubura wace hawaye ya gama wanke ma fuska ta kalle shi ido jajir tace tunda da wani manufa ka ajeni a gidan ka sai ka salamay ni na futa kaima ka huta,
Yaja tsuki tare da watsa mata harara yana cewa zaki san ko ni waye, ya fita fuuu,
Itama ta rakashi da harara har ya shige wa ganin ta, ta juya ta kwanta gadon tana jan tsuki, duk ranta a bace,
Dakin shi ya koma barci ya gagare shi sai tsuki yake yana juya gashi baida enough time din da zai wadace shi haka ya dan taba barci sama sama kafin safe,
****** ********** ******
Tun ranan da mama Sa,a tai man wanan maganan zamana da Umma Rabi ya canza,sallo a gidan,
Don yanzu takai har su Asmau ko kadan babu wanda nake jin dadinsa sai hausa suke sake min a gidan da cewa sun matsu wallahi ace an haihu a gidan nan muma ai buki a gidan mu,
Jibrin kuma ya kance min idan baki haihu ba Aisha sai na saka yayan mu yai aure ya kawo muna mai haihuwa, ta haihu na dauki dan ina yawo dashi a gari,
Murmushi nakan yi nace aiko nima sai na goya shi naita yawo a gida dagari,
Ji wayiya maimakon kiyi kishi ko kiyi zuciya ke ma ki haihu, shine zakice wai ki goya dan,
Nai murmushi nace to ba dan yaya hamza bane may zai sa nayi kishi a kan dan,
Kai amma ko kinban sha,awa Aisha daki ka fadi haka don kin san kan ki ashe,
Mama hafsi ce ta fadi haka daga gurin da take zaune, ta gyara min shikafan da ta karba a hannu na,
Bayan na wuce zuwa dakina jibrin ya zauna yana cin abinci yana cicika, yana batsewa,
Shigowar Umma gidan ke nan daga gidan mama Sa,a ta sha zuga har ta gaji,
Tana shigowa idanuwanta a kan dan ta wanda yake a batse cikin fushi,
Tace a,a kai kuma may ye haka kana cin abinci kana batsewa,?
Yace cikin dan guna guni wallahi Umma mama zata sa Aisha ta raina mutane, a gidan nan dakai magana yanzu mama zata gwale mutum a gaban ta,
Daga inda mama hafsi take a zaune tace mara kunya ka fada mata ne ta bugeni ko kuwa,
Ita Aisha a,sama ta fado ke nan ko da zaku zauna kuna mata cin fuska yadda ran ku ke so ,
Umma wace son yar uwar ta dakuma irin halin ta bai bari taga laifin ta yasa tai ajiyan zuciya
Tace, kun dai san halin uwar ku don haka indai akan wanan yarinyar ne kama bakin ka kawai ,
Mama hafsi tace shi dai yafi kan don ni baza a zauna ana wa yar mutane wullakanci don kawai dan uwan ku ya auro ta,
Kuba ga na ku yar uwar can tana aure ba ta haihu ne ?
Wa ya saka maku ita a gaba?
Sai kune da baku san Allah ba zaku saka yar mutane a gaba da zancen banza,
Jibrin ya mike ya fice a gidan tare da barin kwanon da yaci abinci mama hafsi tace maza dawo dauke shi waye bawanka da zai dauke ma,
Ina daga dakina naji su nai murmushi duk da bacin ran da nake a cikin sa,
Umma tayi tsaye daga kofan ta duk da ranta ya baci tana cewa, Jibrin dauke kwanon nan maza ,
Mama hafsi bata ce komai ba don tai niyar a ranta cewa sai tayi maganin marasa kunyar yaran nan,
Yan min tina kadan mama hafsi tace wai niko yaya ina su malam Mudu ne ko zancen su ban jiba dana zo,
An,tabowa Umma inda ke mata kyakayi tace hafsi tun yaushe,
Aini tunda yaran nan suka kawo girma na fita zancen su na tatara,su gaba daya na,watsar tunda ba, ban saura neman wani a gurin su ba,
Dandama dama,shi babana hamza shine ma mai dan sauran zumutun dasu,
Mama hafsi tace humm,ummm, amma ko yaya bakiwa yaran nan adalci ba a rayuwa,
Ai ance kowa da dangisa yake takama a duniya koda ko a bola suke a zaune,
Yanzu yaya ko dan yan matan nan har biyu da suke a gabanki ai zaki bisu,
Idan auren su ya tashi yaya wane uban daurin auren nasu, dole fa sune,
Ai kamata yayi ace yanzu tunda Allah ya raya maki diyan ki har sun kawo karfi da saiki, nuna masu cewa ke kinfi karfin su ta ko ina, ki dinga zumunta dasu
Don kinga hakan da kikayi bakiyiwa marigayi adalci ba,
Karki manta yadda yai ta rayuwan shi dasu suna kuntata mashi amma bausa ya daina alaka dasu ba,
Shi baba abinda yasa kike ganin kamar yaki jin zancen ki yana hurda su saboda,shi namiji ne,
Kai sai ma ince wallahi bai rage halin mahaifin shi ba ta ko ina,,
Umma tace ashe kin fahinci haka hafsi tace kwarai kuwa yaya aiduk halin marigayi shiga baba don har ma ince yafi uban saukin kai,
Watau hafsi idan na tunairin wullakancin da mutanen nan sukai muna sai naji kwata kwata sun kara fita,raina,
Ta yaya yazakiyi tunda zuria ta hadaki dasu sai hakkuri don kan su sukaiwa,
Yau bagashi Allah ya,raya maki yaran ba,da,dadi da,wuya dama ance maikarami shike da babba watarana,
Allah dai ya,sa masu albarka a,rayuwan su ki more ma abinko tun anan duniya,
Ameen hafsi Amin ya Allah,
Alokacin nafito dakina hannu dauke da plate din da naci abinci zan kai gurin wanke wanke,
Umma tabini da wani irin kallo wanda mutum ba zai iya fassara shi ba,
Azuciyar Umma tace wanan yarinyar sai ci kawai agidan nan ba wani karuwa a gurin ta da Hamza wani mai hali sai kawai tace ya kara mata tagani,
Muryan mama hafsine ke cewa Aisha ki aje kayan nan idan yaran nan sun dawo sa wanke su,
Mama bari na,wanke kada kuda,su hausu da yawa,ai kayan basu da yawa,
Tsabtan yarinyar na bata sha,awa sai take cewa a hankali wallahi yaya yarinyar nan babu ruwanta kiyi hakkuri da abarki,
Ki godewa Alkah da yar zamani aka kawo maki a gidan nan da yanzu kun fara kai ruwa rana da ita saboda wanan tsangwaman dakike mata har yaran nan sun dauka,
Umma taja tsaki tace ba itace ta tsangwami kanta ba yarinyar karama da shigen iyayi
Kibari mijinta yazi gatin nan kiga yadda take wani shige mashi tana manne mashi kamar gare ta farau aure,
Haba yaya kar ki manta fa zamanki da marigayi shine fa yaja maki tsana ga yan uwan shi har yanzu,
Wai hafsi to ni may nake matane bakin halinta ne irin na uwar ta ,
Ta hana kanta kwanciyan hankali a gidan nan sai wani rama take mutane su gani suce nice umul,abaisin haka,
Haba yaya yar nan ko ai duk yadda ake a gidan nan tanayi gwargwadon hali, don Allah ki sarara mata a rayuwa,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
👑 SARAUTAR MATA 👑
2⃣6⃣
SI,RATTAL, LAZINA, AL,ANNTA ALAIHIM,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
Washegari ban fito da wuri ba don ina jin mama tana,aiyukan gida don kuma nasan ba yau ta,fara taimaka min da hakan ba,
Don nasan cewa koda na fito zatace na barshi kawai na huta, amma dai sai na dan fito din cewa mama tayi koma ki huta abinki kinji Aisha,
Yau dana yana gari yana bukatan ki kusa dashi ki barshi zanyi komai don saura ma kadan na kammala,
Barci muka sake koma don dama kowan mu yana da gajiya a jikin sa,
Umma da batasan cewa munyi haka da mama sai zaraya take tana duban kofan dakin mu,
Don ganin har da Hamza wanda yake fita da wuri yau bai fito ba,
A,a su wa yan nan yau lafiya basu fito ba har yanzu?
Sai ta nufi kofan mu tana bugawa bugu daya biyu ga na ukku mama dake fitowa daga bayi take cewa,
A,a yaya mau zasu yi maki kuma,
Kallon yar uwar nata tayi cikin mamaki basu fito ba haka har rana ya hudo suna kwance,
Ikon Allah inji mama haba yaya wanan abin naki fa k8na,shiga hakin yaron nan da yawa,
Yaro ya dawo gari da gajiya ace bazai huta da matar shi ba ?
Yanzu idan sun fito may zasuyi maki ina aiki ne duk na kammala komai da zata fito tayi,
Yanzu don bata da kunya shine zata shige daki da miji tabarki kina aikin ke ?
Nice nace ta koma daki don mijin ta na bukatar ta a kusa dashi,
Watan su nawa basu tare yaya sai yanzu da yazo suna shaukin juna kuma za,a takura masu,
Tafe Umma ta fara yi da hannun ta tana cewa lalai hafsi zaki bata yaran nan,
May kuma za suyi da ranan nan tsakiya , komay mama ta fada mata sai kawai tai dariya ta juya tana cewa ke kan hafsi sai abarki don zaki sagarta dan nan naki idan anbiye maki,
Muna daga daki duk abinda suke fadi a kunnuwar mu, na yunkura don natashi amma sai Hamza din ya mayar dani sai da ya gama abinda yakeyi sannan ya dan sarara min,,
Mintina kadan muka fito daga dakin shi ya,fara fitowa don ya kewa ya,wanka,
Su Umma suna a waje suna shan tea wanda mama hafsi ta hada da kayan yaji dan citta kadan sai kanumfari da ya tayar da kamshi sa,
Fitowan shine Umma tabishi da idanuwa wani abu taji a zuciyar ta wanda ya,sata dan jin wani takaici a ran ta, can kasar zuciyar ta,,
Kamar ina tsaye a kofa fitowan shi sai gani na futo a cikin hijjab dina hannu na,dauke da buta,
Da kyat nake taka kafana don nauyi da kunyan da nake jin don dai sun san may nayi har zan kewaya,
Nagyara jikina nafuto da,daya daga cikin kayan da ya dinka min nai bukin su Hindatu dashi,
Nasaka kayan ya kara amsan jikina tsab ni kaina sai da naga sha,awan kaina,
Tsab dani nafito sai kamshi nakeyi a lokacin Hamza ya gurin iyayyen sun gaisa yana hira da mama hafsi,
Nafito ina tafiya a nutse a hankali nazo inda suke gurin da Umma take a zaune fuskan ta har zuwa wanan lokacin daure tamau,
Nace Umma ina kwana cikin sanyin muryan nan nawa mai kama,da ta yanga, ko rowa,
Na,samu Umma ta amsa min ciki ciki da kyat da fadan lafiya kalau,
Na juya inda su mama,take da dan ta nace mama ina kwana,
Aisha kin tashi lafiya ya gajiyan aiki a cikin fara,ar ta da sakin fuska,
Inda yake a zaune yana kallon mu yai yar murmushi jin dadin yadda mamatake haba haba dani,
A kunyace na amsa da lafiya mama,
Zan mike tace maza dauki abin karin kumallon ku ga yacan a flask din can kikai maku daki ku karya ai ina na da,akwai breadi a gurin ku ko na amsa da eh mama,
Inda flask din yake na nufa don na dauka sai Umma ke cewa rike min flask da kyau kar ki mayar dani baya tun flask din haihuwan autana nane nake maneji da abina,
Sai na mayar da flask din nace bari na dauko cup na juye muna,
Mama hafsi tace tafi dashi mana ki rike mata shi da kyau ,
Hamza yace bari ta juye mama zaifi ta dauki flask din ai,
Ni dai ba zan yarda a fasa min abuba don maneji nakeyi dashi gaba dayan wurin shiru mukayi,
Don haka sai nabi umurnin hamza na juya na koma na dauko cup na juye ruwan zafi aciki,
Banji haushin Umma ba don nasan cewa a gidan mu banzo da wasu kayan amfani ba, ai irin na aiyukan mata,
Kwaliya na taiwa Hamza kyau sosai sai bina yake da kallon sha,awa,
Suna zaune shi da su Umma inda suke hira da mama hafsi Umma na daga gefe take cewa,
Dama ina jiran zuwan kane, don naji shawaran da zaka bayar,
Kaga an raba gadon mu gidan da aka bar muna an sayar abawa kowa kudin shi da yan sauran kaddarorin da aka bar muna, baki daya ,
Shine na hado kudin nazo dasu nan don mu san abinda za,ayi dasu,
Banda kowa a duniya yanzu sai ku da yar nan guda da Allah ya bani ita kuma kaga shi Alhaji ba mahaifita bane ga mijinta dan kwaya ne ita kuma ba lafiyayya bace don haka ba dama na,sakar mai kudi su lalace a banza,
Shiru sukayi baki dayan su mamata ce yanzu tun da Alkah ya,dawo da kai kaga sai ka ba da,shawaran yadda za,ayi da kudin nan,
Zama Hamza ya dan gyara tare da,dan numfasawa yace,
Mama kin san shi kudin gado wani abune mai nauyi da karfi,
Don haka yanzu abinda za,a yi shine asamu gida ko fili a,saya maku dashi a je a matsayin kaddara wanda ake gani,
Don ajiyan su a haka ba zaiyi ba don aje kudi masu yawa kasa dane babba,
Mama Hafsi tace a,a Hamza ba zaa sayi gida ko fili ba dasu ni a nawa shawaran may zai hana ka,karbi kudin ka,fara dan juya su kana kasuwanci da su, har zuwa lokacin da zaka samu naka sai ka biya na dai idan kudin suna gurin ka ko ibrahim wallahi hankali na a kwance suke Hamza,
Murmushi Hamza din ya,dan sake yace a,gaskiya mama nagode da karamcin da kika nuna min amma gaskiya na Allah bazan karbi ko kwandala daga kudin ki na juyawa ba,
Don kin san yadda kudi na amana kuma na gado suke da saurin samu kaddara, don haka shawaran da na bayar shine kawai abin dubuwa da mafita,
Amma gaskiya ban so ka musaya min shawarata ba Hamza na sanka tun kana karamin ka na san halin ku zaku iya rike wanan amana, kai da dan uwan ka,
Hamza yace mama yanzu abinda za,a yi sai nayi shawara zan san abinda za,a yi da kudin don ci gaban su,
Nan suka dauko zancen tsohon mijin nata wanda ya rasu tai mashi wanka da irin taimakon da yai masu a lokacin da suke da bukatan hakan,
Har zuwa wani lokaci ya mike zuwa waje don ya gana da mutanen shi ,
A kofan gida ya hangi Baba Mudi ya karasa su ka gaisa yake tambayan shi cikin murnan yaushe garin yake bashi amsa da cewa jiya da yamma ya shigo,
Ya tambaye shi karatun shi da kuma yadda ya samu mutanen gida,
****** ********** ******
Ina dakina zaune bayan na dora muna abincin rana sai nake jin sallaman daga kofa, muryan mamana Rahana nake ji,
Nafito daga dakina a cikin murna da yar tsalena na tare ta nai mata sannu da zuwa na karbi abinda ta shigo dashi a cikin wani dan buhu,
Sai take ce min ki rike da kyau don akwai abin fashewa a cikin sa,
Gurin Umma taje suka gaisa dasu tare da maso godiya da rike mata 'ya da,suke yi,
Suna tare na,wani lokaci ta mike tana cewa bari su gaisa da ni a dakina,
Mun gaisa da Mamana na,rasa ina zan sakata dan murnan ganin ta yau gida na,
Mama ta aika ka,sayo mata ruwan masu sanyi takawo mata har dakina,
Nan nake nuna mama ga mama Rahana nace kaunar Umma ce ta dawo zama damu,
Ta jajan ta mata akan rasuwan mijin ta da kuma yi mata godiya,
Bayan fitan Mamane Mama Rahana take tambayana cewa tana fatan ba wani matsala dai ko, a zaman mu,
Nai yar dariya nace babu komai mamana lafiya muke da kowa a gidan,
Sai naga tana sance habar zanin ta kudi tafito dasu take cewa na tafi gida Aisha har gurin yan uwan mahaifin ki na tafi, ganin su tinda kin san yan uwan mune,
Tsit nayi ina sauraren ta