Sarautar Mata

Chapter 29 of 94

don jin ta ambaci yan uwan mahaifina, da tayi don ni sai nake gani basu kaunana na ko da yake basu da laifi wanda ma ya haifeni bai damu dani ba balle yan uwan shi,
Muryan Mama ke cewa sune suka hada wanan kudin suka ce na kawo maki kya,samu ki dan sayi wani abin sana,a kina dan juyawa,
Kudin da ta ciro a zanin ta ta miko min a,gaskiya kudin suna da dan yawa don za su kai dubu talati da yan kai,
Sunce kudin gadon mahaifinki ne da,aka,sayar da gonan su na gado nashi kason suka dan baki daga ciki,
A hankali na,dago idanuwa na,da,sukai ja nace har yanzu Mama ba asan inda Baba yake ba ke nan,?
Tace haka,suke fada min amma,wai wani mutum yace ya ga,wani a kasar Niger ko shi ne bai sani ba,
Nace cikin murya mai rauni Allah ya baiyanar dashi duk inda yake in har yana raye,
Mama tace min Amin nakaiwa mahaifiyar ki kudin shine tace na zo maki dasu nan ki gani, ko akwai abinda zakiyi dasu,
Mama ni kan ai banda ta cewa duk yadda kukayi min dasu daidai ne ba matsala shawaran ku itace tawa nima,
Mama Rahana tace ni da,shawaran da nayi shine a dan saya maki dan ijimin nika ko dan fridge, kina dan sana,a kudi na shigo maki basai kin dogara ga miji ya baki ba kullun,
Tajawo dan buhun da ta shigo dashi tace daga ciki mukai maki wanan sayayyan tun a sokoto,
Tafara jawo kayan zanin gadone flask ban san lokacin da nace wayyo Allah na ba mama na gode wallahi,
Kinga yau din nan Umma tai min gorin flask a gidan nan sai idanuwa na,suka ciciko da hawaye,
Sai kuka nafara yi ina hawaye mama tace ki bar kuka ki fada min may ke faruwa ne ni uwar ki ce baki da wanda zaki fadawa damuwar ki sai ni,
Mama abinda Umma take min a gidan nan yai min yawa mama saukina zuwan mama hafsi,
Nan nake fada mata zancen haihuwan da ta fara bijiro min dashi da kuma yawan gorin ban da komai a dakina sai tsiya,
Hmmm duniya yanzu ita Rabi har ta manta da irin halarcin da,akai masu kika fitar da dan ta daga dariyan shiya,
Idan ba aure nufin Allah ba har may zai zaunar da ke a gidan ta ko don basu san asalinki ba ,
Duk da yan uwan mu a kauye suke zaune ai muna cikin rufin asirin mu gwargwadon hali,
Idan ta matsa maki ni zan fito na fada mata,gaskiya wallahi don ba,rasa mai so kikayi ba ko don mun kyale kawai don malam Mudi,
Ganin da takewa uwar ki a gidan mijin ta haka ai rayuwan aure ne yakawo hakan,
Taci gaba da fitar da kayan ledan kasa sabo spoon, plate sai saitin kula na abinci mijina mai kyau,
Mama taso ta lissafa min kudin kayan amma sai nace cikin shagwaba haba mama haba mi zaki lissafa min ni wallahi na gode ,
Tace akwai bahohi da uan sauran tarkace za,a kawo maki daga gurin Fatima idan an sayo maki nace na gode mama,
Muryan Hamza ne ya shigo gidan cikin sallama daga kofan su Umma mukaji muryan shi,
Mama hafsi ce ke fada mashi shigowan Mamana Rahana,a zaton shi mamana Fatima,
Sai da ya,shigo yaga mama Rahana ce tazo muna, yace,
A,a mama sannu da zuwa idanuwan shi a kan kayan dake baje a tsakiyan dakin gaban mu,
Nan mama tai mashi bayani, akan komai da tazo dashi sai a lokacin yake cewa mama mahaifin Aisha baya gari ne cikin mamaki yake tambayan,
Tace baka sani bane Hamzs nan take dan mashi bayani tare da kara bashi bayani har da wanda ma ni ban sani ba,
Yace Allah ubangiji ya baiyanar muna dashi lafiya idan yana raye,
Mama hafsi ya fita yana fada mata tare da nuna mata kudin sai gata tashigo dakin tana cewa,
Ashe alheri akazo muna dashi haka ?
Mun gode Allah ya sa ta amfana da abinta muka ce amin ni da mamana,
Umma shiru tayi kamar ruwa ya cita don taga isharan Allah taga rashin amfanin yiwa mutum gori a lokaci guda,
Tun mamana tana tsaye mama Hafsi ke cewa sai a sai fridge zaifi samun karbuwa,
Don ko samarin nan masu zama kofan shago ai za,a samu ciniki a gurin su,
Mamana tai muna sallama inda fitan ta bada dadewa ba sakon sauran kayan suka samay ni nai murna kwarai,

****** ********** ******
Na gyara dakina da sabon ledan kasan da aka sayo mun, tare da yan sauran abubuwan amfanin da mama ta saya min,
An samu fridge dan madaidaici da kayan hadin shi sauran kudin da ya rage min yaya, Hamza yace zai cika ya sayo min dan maidaidai cin kujeran zama maicin mutum, biyu,
Hakan yasa dakin namu yakara wani kyau, gwanin ban sha,awa na idar da,sallah ina zaune na karewa dakin kallo naji wani dadi ya kumay ni a,raina,
Ina kallon dakin yadda ya sake min kamar ba dakina ba ga dan fridge dina,yana aiki sosai don nayi sa,a samun lafiyeyen fridge yana aiki sosai,
Ruwan farko da nafara sakawa,har gidan mu na aikawa wasu Ummina da abokan zaman ta dashi su sa min albarka,
Hamza da ya dawo yasamu yadda na gyara muna daki ranan bakin shi har kunne yake don dadi,
Wata sabowa inji yan caca don Umma ta saka dan ta daki akan cewa bata yarda cewa bashi ya bada kudin da akai min wanan sayayyan ba dasu,
Ai ba,a tashi sayo min ba sai da yazo gari kuma sai da tai min maganan flask ai,
Wanan sabon maganan da tazo dashi ne daga gidan aminiyan ta, da taje ta fada mata cewa iyayyena,sun kawo min alheri,
Sai take mayar mata,da yadda akayi da zancen flask din ranan,
Tace amma Rabi gaki kamar mai wayo ashe baki dashi ,
Yanzu yara kanana ne zasu yi maki wayo mai yasa ba,a tashi saye ba,sai yanzu da yazo gari,
Aikuwa take hankalin Umma ya tashi inda tahau zancen mama Sa,a ta zauna a kai,
Kamar an ce nazo gurin taga Umma daukan kwano sai naji Umma din nacewa ko sau nawa zaka rantse min cewa,bakai kaba da kudin wannan sayayan ba zan yarda ba,
Cikin ladabi naji yana,cewa Umma baki mamakin ina zan samu kudi haka masu yawa nai mata wanan sayayyan,
Ai duk inda zaka samo ka,sani tunda kayi niyar gyarawa matar ka,rai don nai mata gori,
Innalillahi wallahi Umma ko kur,ani za,a kawo na dafa wallahi na yarda Umma bani na,saya mata ba,
Tace tashi ka bari guri tunda ka zama dan bi bawan mata sai yadda karamar yarinya tayi da kai waikai gaka dan soyayya ko ?
Da,sauri nabar gurin gudun kada wani ya shigo ya samay ni azaci ko labe nake masu duk da na, yi dan laben, ai
Innalillahi nake uya furtawa a zuciya ya ina fadin na shiga uku da Umma a gidan nan,
Take zuciyana ya raya,min cewa fitan da tayi zuwa gidan mama, Sa,a ta dawo da wanan sabon zancen, a gidan,
Hakalin na yai matukar tashi a gurguje na,samu na karasa aikina ina waje naga fitowan Hamza din dakin mahaifiyan nashi rai a bace kamar zaiyi kuka,
Kofan gida ya nufa cikin bacin rai nan ya hadu da mama Sa,a wace dawowanta ke nan ta,shiga cikin gari,
Ganin yanayin shi ta matsa mai da tambaya sai da ya fada mata abinda ya faru tsakanin shi da mahaifiyar shi,
O Allah jama,a wai ina yaya ta,samo wanan halin daga sama haka ?
Don dai a da can baya,ban san ta,da,wanan halin ba sai yanzu,
Duk zama da wanan bakar aminiyar nata wace bata kaunar ta da,alheri amma ita,bata gane ba har yanzu,
Wannan matar, da tana da hali, ko, ku, diyanta, da tarabaku da ita don kalaman ta babu na alheri daga cikin sa,
Nan dai mama tace gabar zance kada ya,sa a ran shi ya,wahala, don Umma yanzu addu a ya kamata muyi mata don Allah ya yaye mata,wanan matsalar,
Maganan Mama yasa shi dan jin sasauci ga zuciyan shi har ya dan dawo normal,
Ina karasawa na koma dakina ina kwance saman sabon kujera ina,shan iska daga kofan dakina,
Yaro ya shigo yana cewa wai a bashi, ruwan sanyi ya saya, amma sai Umma take cewa ba,a sayar da ruwa ya fita ya damay ta,
Yaron sukayi kicibis da mama take tambayan shi ko may ke faruwa may yake so ne,?
Yaron yace na zo sayan ruwa ne ance wai ba a sayarwa a gidan nan ,
Zo kawai tace mai suka shigo tare inajin duk abinda ke wakana,
Labulen dakina ta daga take cewa tashi kibawa yaro ruwa ya,saya,namike nafara sayar da ruwana sana an da tazo min a cikin sa,a,
Umma tana jin mu amma takumay tankar bata jin mau kewa kana a gidan, har ruwan hamsin yaron ya saya ya fita,
Mutane suna shigowa saye abamu ruwa a ba mu ruwan sanyi,
Ibrahim yace min na dan yi zobo ko za,a saye ya aje min a shagwan shi,
Shi da,kan shi ya,sayo min abin hadin zobon da gorunonin da zan zuba a ciki idan nayi,
Take na,dan fara tara taro sisi na kaina daga kudin fridge dina da aka,saya min da kudin mahaifina,
Kishi karara da kyashi da hassada Umma ta nuna duk da tana wai kokarin taushe zuciyar ta,
Hamza ya fara zanceb noman shi duk ya manta da zancen fitinan Umma,
Don idan ya fita da safe sai da yamma,zai dawo gidan ,
Haka yasa fitina yanzu shi da Umma ba lokacin hin hakan saboda bai zauna ba balle suyi,
Ina zuwa school ina,sana,ata ga kuma hidimar mutanen gida da ta Hamza,
Ina zaune a baki kofana ina kokarin hada zobo ga girki kuma da,nake a dayan bangare,
Umma wace shigowan ta ke nan gidan ta,soma cewa aaa wanan wutan fa na may yenewa haka kamar za a dafa
Nai saurin daga kai ina kallon gurin da akaice wai ancika wuta a murhun,
Tsam namike nabar abinda nakeyi zuwa guri girkina na jaye iccen kamar yadda, tace nabar gurin zan koma,



ZAlINAB IDRISMAKAWA

SeEENABU
👑 SARAUTAR MATA 👑
2⃣5⃣


I,HHIDINAS SIRRATAL MUS,TTAQIN,,,,,


ZAINAB IDRIS MAKAWA



Matakin da mama ta daukar min a gidan ya kawo muna sauyi a cikin gidan don, sosai
Don a nawa bangare bana yarda abu ya hadani wanda zai kawo cin fuska a tsakanina da kannen mijina duk da sun girmayni sa,adatuce kawai zan iya cewa na girma acikin su,
Don haka suma suke taka tsantsan da ni don gudun fadan mama hafsi dake zaune da mu a gidan yanzu,
Ba,wai ba a magana ta bace kawai dai an daina min irin yadda ake min a baya can,
Don haka samun sasaucin da nayi yasa ni kara kyautatawa uwayen mijina, don kawar da komai,
Haka kawai na tashi ina son na gyara dakina don ba,zan shiga school sai Monday,
Ganin ina,wanan aiki mama hafsi da,suke zaune da Umma a kofan su suna shan iska sun gama cin dumamay da na kawo masu,,
Mama Hafsi tace a,a sarakuwana ko dan nawa zai shigo gari ne naga yau kin tashi da gyaran daki,
Daga gurin da,nake tsaye nsi murmushi, kawai,
Muryan Umma ce take fadin aikin san dan naki tunda kikaga tana gyara, zai iya fada, maya yana tafe,
Haba yaya ko ya,fada mata ai ba laifi bane yanzu bagashi tana gyara ba,
Tsab na dan kara,sanfarin dakin nawa washegari kuma nai kitso da kumshi, a gidan inda,na,kira wata,budurwa,mai sana,an kitso da kumshi tazo tai min,
Washegari ,ban da aikin komai, kasancewa duk na gama aiyukana da wuri ranan,
Don haka na dauko littafaina ina dan dubuwa don kara fahinta,
Wani yaron makwabtan mu Aliyu ya shigo gidan da,wasu leda guda biyu a hannun shi bakin shi dauke da,sallama, ya shigo gidan
Hamza ne daga bayan yaron shima hannuwan shi dauke da jakar kayan shi da wasu tarkace da yazo dasu,
Yaron ya nufi kofan dakina da kayan dake daga hannuwan shi sai daga cikin daki nake cewa ya kai kayan dakin Umma,
Shima kanshi Hamza din da kayan dake a hannuwan shi dakin Umma suka nufa,
Lalai marhabi inji mama hafsi take cewa cikin jin dadin ganin dan nata ya,shigo gari wanda ta,dade bata saka shi a idanuwan ta ba,
Shima Hamza din cikin jin dadin ganin kaunar mahaifiyar tashi a gurin su yayi murmushi yana cewa mama sannu da zuwa,
Ita ko mama hafsi duk ta rude cikin jin dadi sai farin ciki take nunawa
Umma dake daga gefen ta sai murmushi take na dadi yadda yar uwar ta ke matukar nuna kaunan ta ga 'ya'yan ta,
Mama hafsi tace wa yaro kai kai kayan dakin can mana, ka yo nan dasu,
Hamza cikin fara,a yace kayan tsaraba ne a ajewa Umma zata raba,
Sai fara,ar mama ya dan rage tace kamar ya zata raba ba dakin ka za,a kai kayan ka ba in yaso matar ka ta gama sauke ka sai ta kawo muna abinda muka samu,
Umma ma rage faraar fuskan ta tayi don tasan mama bazata yarda da wanan halin ba ke nan tunda tai magana,
Aisha fito ga mijin ki yazo ki karbi kayan shi mana,
Na,am mama nafito daga daki na yana tsaye daga kofan Umma ya zama dan birni wayayye dashi,
Nai mashi sannu da zuwa ida idanuwan shi a kaina
Ji yake kamar ya rugumay ni irin yadda yake ji a ran shi,
A hankali cikin natsuwa na karaso gare shi na karbi jakar daga hannun shi inda na doshi dakin Umma,
Yo ga yar nema kikai mai kaya daki zaki shigo nan dasu kuma nace cikin da sakin fuska, anan ake ajewa,
Haba tafi dasu dakin ku mana ban iya mussu da ita sai na juya zuws dakin namu da kayan har na ledan da yaron ya,aje a kofa na shiga dasu,
Kai yaka nan inji mama tace karbi nan sheka ka,sayo ruwan leda mai sanyi na,duka kawo muna,
Dakin ya fada Umma tana zaune cikin fara,a yake cewa Umma sannun ku da gida,
Baba a she kana hanya sannun ku da zuwa, yace yauwa Umma,
Ashe mama tazo ne tace ta tuna damu gata nan ai ta kwana biyu ya durkusa har kasa yana gaishe su,
Yaron yana kawo ruwan ya mika min na karba na juye a plate na kai mai a lokacin yana zaune saman kujeran dake ta kofan dakin daga ciki,
Na ajeruwan a cikin ladabi zan juya mama take cewa dauki saura kikai mashi daki kafin ya,shigo,
Har na duka sai Umma ke cewa miko min na dauka na jika raina nima don ita dan ta kawai ta,sani,
Nakaiwa Umma ruwan ta dauka har guda biyu nafita da sauran, sai mama ke ce min yanzu Aisha may za a bashi yaci, ne,?
Abinda ban taba jin Umma tayi ba ke nan idan ya,shigo gari haka zamu barshi sai ruwan randa kawai zamu bashi,
Nace mama abinci ya kare,
Tace to ko a,sayo mashi wani abin ne a,waje,?
Mama abarshi kawai ai saida mu kaci abinci muka fito ,
Yanzu haka zaka zauna da yun wa har yamma ?
Babu komai mama a koshe nake,
Kafin ya,shigo na kara gyara dakin da jikina don taron shi kada yaji ba kamshi,
Yai yan mintina yasuna hira ya mike yana cewa bari na dan rage kayan jikina na,watsa ruwa mama,
Ya,shigo dakin a lokacin ina tsaye zan dauke jakarshi na kai gurin da nake aje mai,
Ta baya naji shi ya,rugumoni yana matse ni da jikin shi cikin yar sauke ajiyan zuciya,
Sannu da,zuwa,yaaaa sai naji ya hada bakin shi da nawa abinda yasani dan shiga,yanayi ke nan,
Ya furta,min kamar mai rada da cewa miss you my wife,
Nai murmushi ina kokarin zullewa sai ya kara riko ni a jikin shi ya matse yana mai kai min kiss har ta wuyana,,
Na samu ya,dan sasauta min yake cewa mun samay ku lafiya, nace cikin dan gyara rigana lafiya ya karatu,
Ya amsa yana kokarin balle botton din rigar shi yana cewa karatu Alhamdullahi ya,school din naku ?
Alhamdullahi yaya mun kusa fara exams, nace na zuba ma ruwa ne ka,watsa,
Yace kamar kin san shi nazo yi duk zafi nake ji a jikina,
Na fito daki mukai arba da Umma wace fuskan ta yana a kofan mu tana gani na ta,wani kawar da kan ta,
Wanka yaya Hamza yayi ya canza tufafin jikin shi sai ya,fita don ya gaisa da mutanen uguwa yana,shiri ne yake tambayana yaya su Ummi da,sauran mutanen gida,
Nace a takaice duk suna lafiya, duk da ban shiga ba tun wancan zuwan da mukayi tare da kai,
Ya juyo da karfi yana veea har yau baki shiga kin dubo su ba ?
Nace ina jin tsoron tambayan Umma tace min na faye yawo,
Wa,yai maki kitso da kumshi to nadan daga hannayen nawa nace haulatu ce na aika tazo tai min, jiya,
Gaskiya ta iya kwalliya don yayi min kyau sosai wallahi,
Nace mama ce ta bata kudin da tai min ai,,
Ya ce ashe mama tana garin nan ne ?
Nace eh tazo yanzu ai yakai sati uku zuwa hudu Allah sarki tayi kokari wallahi,
Mama tana da kirki kwarai yaya don zuwan ta yai min dadi a gidan nan saboda tunda tazo ina jin dadin karatuna wallahi,
Don duk wasu aiyuka ita ke yi kuma ta,sa su asmau su tai maka min
Ai kadan ne daga,halin ta,don ita,daban take a,cikin su,
Ya,fita yana cewa bazai dade ba zai dawo yanzu suma ina jin yai masu sai ya dawo,
Futan shi na,dauko ledan da ya,sayo muna breadi da,su lemo kwakwa da Carrots, nakai dakin Umma,
Nace Umma ga kayan tsaraban da yaya yazo dasu,
Na barsu a dakin na fito waje abina na barsu suna maganan su,
Nai mamaki kwarai a irin kason bread din da muka samu a dakin mu,,
Ina aikin girkina yaya Hamza ya,shigo gidan da ledojin mayan bakake har guda uku dauke da kayan abinci a ciki,
Bayan na karba na gama fitar

Download complete TXT · Novel page