Sarautar Mata

Chapter 4 of 94

da sauran su,
Tun mutane basu sani ba har suka fara saka mata idanuwa suna fahintar irin rayuwan ta, dama yanzu haka,duniya take,
Kafin jama,an gida,su ganne halin dan yau jama,an unguwa har su gane mai yaro ka ke ciki ko,,
Tana zaune kofan mahaifiyar ta tana gyaran kumbar kafanta a hankali daga inda take a zaune, tana iya hango duk wanda ke shige da fice a gidan,
A haka ne yaron makwabtan su ya shigo gidan da,sallama yana dauke da wata bakar leda a hannun shi gari yai zafi,
Inda Kubura take zaune ya,nufa yana mika maya ledan tare da cewa inji Hamza yaro yace na kawo,
A tsiwance ta karbi ledan tana dan wani yatsuni fuskan ta kamar wata babban mace,
Beridi ne da,Awara sai karas da lemo daganin tsaraban da alaman cewa ya yadawo daga cin kasuwan wani kauye ne,
Yaron ya dan tsaya ta,dago kai a fusace tana cewa to may kuma ka tsaya jira dan gulma ya juya simi simi yafita yana hade yawun abinda ya gani a ledan ana fitar wa,
Ke yar AGWAI miko min tasan can na,saka abu a ciki daga inda take tsaye tana yan aikace aikacen ta tajuya inda suke kife kwanonin abincin su ta dauko mata,tasan da take nufi,
Tamika mata tawani fisga kamar mai fada ita dai ta juya tana wani ya mutsaa fuska kamar maijin warin ta,
Ita dai ta juya zuwa inda take yan tsabgoginta taci gaba da aikin ta hankaali kwance,
Tsab taciye abubuwan ta batare da taiwa kowa tayi ba,sai uwarta data danyi wa tayi ta,tura mata dan kadan
Ke yar AGWAI zoki dauke kwanon nan daga nan ki mikomin ruwa nasha,
Daga daki muryan Fatima ce ke cewa a cikin kakausar murya tana cewa
Ke Aisha aje kwanon nan kibar gurin nan,
Iyyeh inji Kubura take cewa kuma dai,
Aisha ta,aje kwanon tsab tabar gurin kamar yadda mahaifiyar ta umurce ta dayi,
Daga daki Fatima taci gaba dacewa ai ba bauta tazo yi a gidan ba,
Lalai to ita waye bawan ta kuma dahar za,a nuna min hassada yanzu a fili,
Ke Kubura inji Hannatu mahaifiyar ta tace rashi kirkin naki har yakai ga iyayyen ki kuma,
Cikin da guna guni take céwa nikan aida uwata ce bazatai ,,,,
Pap taji an mangare ta daga bayan ta abinda ya hanata karasa zancen datake son fadi ke nan
Nan tafara dan yin zance cikin kuka kuka tana hi a ciki ciki,
Kai amma gaskiya Kubura baki kyauta ba don dai yarinyar nan ta na iya kokarin ta a gidan nan,
A cikin ku wake irin abinda Aisha take muna a gidan nan,
Atika ce dayar kishiyar uwar su Kubura ke wanan zancen daga inda take
Tun,daga kofa yake jin muryoyin su abinda ya sashi hanzarin shigowa gidan ke nan don jin ba,asi,
Wai mah ke faruwa ne haka inda Kubura tana ganin mahaifin nata takara dan kaimin kukwn nata,
Shiru sukayi gaba dayan su babu mai ce mai uffan daga cikin su,
Kara tambaya yayi a karo na biyu don son jin ba,asin zancen,
Fatima ce daga dakinta inda take zaune tana fama da laulayin sabon shigan cikin dake gare ta wanda yazo mata da futina kalakala
Nan ta mayar mai da abin da ya kawo zancen da ya samu anayi,
Juyawa yayi a cikin dakiya yake cewa Ohho hakane to mukuma ashe bayin ta,
Ashe ko idan kin ce hakan saidai wanan yarinyar tabar min gida don ban yarda akanta ko da yaushe ana, batawa yarana rayuwa haka,
Haba malam inji matar tashi wanan zancen bai kamace kaba gaskiya akan wanan magana zakace haka,
To ai sai ki koya min yadda zanyi a gidana yace mata a harzuke cikin masifa,
Take itama Fatiman tahau zuciya daga daki tana cewa ai sai ta koma din don nima wanan gorin ya,isheni haka kullun zance guda akan yarinya guda nima nagaji wallahi,
Amma ta tsaya kowa yadebo sgaran shi yana watsa mata bazan dauka ba yanzu,
Acikin kuka irin mai tsima rai take fidda zancen ta tare da tausayi yarinyar nata a ranta,
Ganin yadda Fatima yau ta dake ta harzuka akan yarta yashi yin shiru don yasan cewa zata iyayin komai yaudin,
Maman Kubura ke cewa Fatima don Allah abar zancen nan haka ya isa don Allah, ban son abin da baikai yakawo ba,adinga ta da jijiyoyin wuya akai,
Fita yayi don bai son zance yakara nisa kodon halin da Fatima din ke ciki na wahalar shigan cikin dake gare ta,
Gurin da Kubura take tsaye ido mirsisi tana sauraren badakalar da akeyi a gidan a kanta uwar ta juya,
Tace yanzu aikinji dadi tunda kin haddasa abinda kike so wallahi Kubura kiwa kanki fada hakana,
****** ********** ******
Ruwan sama yafado don haka duk maza sun koma gona don har da,rago yana dan zuwa gona,
Hakan yajawo yanzu Hamza bai zama cikin shagon shi saboda akoda yaushe yana zuwa gona aiki,
Kubura wace rashi shagon shi da bai bude kowani lokaci yajawo mata goslow din kwadayin ta,
Har yakai sun dan fara samun matsa saboda yawan aikowan da take cewa yabata kudi zata sayi abu kaza ,
Uwar shi Umma Rabi taimashi fur akancewa duk ta kara jin cewa ya bata kudi rqnan sai ta bata mashi rai,
Hakan yasa yazo koda zai aika kirantq sai tace ace mai bata gida ko tana wani abin,
Gashi mahaifinta yafi kowa jin dadin wanan hafin nasu don yasan Hamza bazakarin yaro ne zata dan more miji anan saboda yana da sanar yi,
Sannu a hankali tafara hira da,wasu samarin tun Hamza yana ji har takai ya fara gani da idanuwan shi,
Abinda yai matukar tayar mashi da hankali ke nan don haka ya matsawa mahaifiyan shi a kan ta tafi tayi zancen don ai masu matsaya da ita,
Umma Rabi batai kasa a gwiwa ba ta tafi tasamu malam mudi makwacin su wanda shine kuma mahaifin Kubura din akan zancen yaran nasu,
Malam mudi yace duk da ba itace ya dace tazo zancen auren yaron nata ba amma ta koma zance yana nan insha Allahu ba zai tayar ba don yayi alkawarin haka,
Shi tun farko yana da,sha,awan so hada zuria da Hamza din saboda hazakar shi,
Umma tai maganan cewa zata gurin yan ywan mahaifin Hamza din duk da su yarda su amma akan sha,anin aure aidole a tuntube su suji don sune manema auren diyan ta, dole
Abinda yasa Hamza yakara mayar da hankali ke nan sisai ga gonar shi don yaga cewa yayi kyau har ya samu abinda koda zancen auren shi ya taso yana da abinshu ga hannun shi,
Ita ko Fatima masifan cikin da tasamu yanzu yasa ta koma wata mara lakka don haka a yanzu Aisha ce take mata duk wani laluran gida kamar wata babban ma e don komai ta iya saboda training din data samu ga mahaifiyar ta din,
Ba mahaifiyarta ba kawai harma da sauran abokan zamanta Aisha tana kama masu aiyukan su ranan aikin ta da ita za,a gama komai,
Wanan yakara,sa ta,samun wani tsana da tsangwama daga mutanen gidan da ake mata,


Novel dina a zaman Amana yake a gare ku don haka wace tafitar min tunda kunce banja Allah ya isa ba dole tunda kun saya zaku fitar nabar mutum da Allah, kawai,
A hada mutum da darajan Annabin rahama baiyi ba ai sai kabarshi tsakanin shi da Allah duk wace ta,fitar ita da Allah,,


ZAINAB MAKAWA YELWA
SEENABU,,,👑SARAUTAR MATA👑
0⃣4⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA


WALLAHU GALIBUN WALLAMM,RIHI,,,




Zaune take tana faman shafe shafe a jikin ta saaiu kuma wakan da takeyi a hankali na wata zabaya,
Agogon bangon dake dakin mahaifiyar ta ta,daga kai ta dan duba abinda, yasata saurin mikewa ke nan,
Wani riga mai ruwan light chuckulet ta jawo yar hannun shi kamar ta shimi ,
Jikin rigar duk yabi lafiyan jikin ta ya,shafe mata,shi tsab, sai turaren da ta dan kara murzawa a,parts din jikin ta,
Wani katon hijjab di ta ta dauko ta,saka daga sama sai ka rantse shigar arzikine a jikin ta,
A kitchen ta hango mahaifiyar ta tana kwasan tuwon abincin dare da ta girka,
Aisha tana daga tsaye a gefen ta tana kwasa zuwa gurin da,suke aje abinci daga waje,
Muryan KUBURA ce ya daki kunnuwan su daga inda take zaune tana cewa mama zan dan fita sai nadawo,
Dakatar da kwasan tuwon datakeyi tayi tana mai juyowa inda yar nata take tsaye,
Ina zaki da yamman nan haka Kubura don dai yau ba ranan islamiya bace,
Cikin dan inda inda take cewa mama ina son nashiga nan gidan su Hamza na gaida Umma Rabi,
Dadi mama Saude taji jin cewa yar ta tayi hankalin shiga gaida sarakuwar ta,
A cikin washe baki take cewa ki gayar min da ita kice muna gaida yaran gidan,
Fat tafice da sauri gudun kada mama tace ga sako takaiwa Umma Rabi din abinda yasa ta cin karo da mahaifinta malam Mudi ke nan wanda ke kokarin shigowa gidan a lokacin,
Cikin washe baki yana binta da kallon mamaki don jin yadda ta ke kamshin turare yace Gwagon Baba yau sai ina hakan ga,?
A ,a Baba nan zan shiga gaida Umma Rabi na fito yanzu yadan jaye mata daga gefe kadan don ta,samu full hanyar da zata fita daga zauren gidan nashi,
Kubura tana fita wajen gidan su tasha wani kwana inda zai sada ta da wani titin mota haka,
Tun daga nesa ta hango motan da take tsan manin gani inda ta usa da sauri don gudun kada wani ya ganta ya sheda ta,
Tana,bude motan ta shiga taji na cikin motan ya sauke a jiyan zuciya yana cewa ai na zaci bazaki ffito bane don har na debe rai ga fitowan ki yau,
Tace cikin dan yin wani har da idanuwanta kaima ai kasan cewa dole ne na fito don alkawari ne,
Hijjab din jikin ta yadan duba yana cewa ya haka kuma, ?
Yadan nuna hijjab din yana cewa wanan abin nake nufi fa,
Sai a lokacin ta sa hannun ta tayene katon hijjab din dake a jikin nata,
Woow yace tare da dan fito yana cewa beautiful wanan irin haduwa haka baby,
Daga haka ya harba mota suka nausa wani uguwa can mai nisa dda nasu uguwar,,
Buki ake a gurin yan mata matasa da samari ne an saka kida sai tashi yake ,
Shigowan shi da Kubura yasa gurin ya dauki wani irin shewa da sowa a lokaci guda nan aka saka wani sabon kida wanda ya ruda samarin da yan matan dake gurin suka,shiga, wani rausayawa,

****** ********* ******
Gani har magriba ya soma yasa mama saude tura Aisha gidan Umma Rabi don ra kira Aisha,
Duk da dadin hakan takeji don yar ta tafara sabawa da matar da zata zama,sarakkuwar ta nan gaba kadan,
Aisha tajawo wani tsohon hijjab din ta tasaka a jikin ta zuwa gurin aiken da akai mata,
Sam in ba,dole ba bata kaunar fita waje a wanan lokacin don sanin cewa iwar haka kofan gidan nasu aa cike yake fam da matasan shiya,dake zama a kofan shagon Hamza yaro don hira
Tafe take a natse kamar kullun yayin da abinda ta sani cewa sai anyi shi ake kan yin shi
Don idanuwan matasan gurin duk caa a kanta kowa na kallon ta,
Kanta a duke a kasa take tafiya tana zuwa gab dasu duk da matasa ne amma sai da tace masu ina,wunin ku,
Wasu suka karba,wasu kuma suka kyale suna ci gaba da hiran su,
Tun batai nisa ba taji muryan salisu yana cewa wai ita wanan yarinyar bata da gatane a gidan nan ko,?
Naga ko da yaushe kuca kuca zaka ganta gwanin ban tausayi da ita,
Sani yace yarinyar dai babu ruwanta wallahi naga ita sam bata damu da kowa ba ashiyan nan,
Nafiu yace yar fulanin gidan malam mudi ko ma may suke ce mata farat Audi dake daga gefen su yace Yar AGWAI,
Yarinyar kamar a taba takare saboda rama haka aiko taci sunan ta wallahi,
Kai na,rabaka irin matan nan masu kama da a kara su sunfi kowa zama manyan mata idan sun girma,don kiba suke sosai,
A hakan inji Sani yake nuna inda Aisha tabi da signal don su gane,
Sai suka tuntsire da dariya ga baki dayan su sai Hamzane dake ta cikin shagon shi yana mikawa wani abinda yazo saya yake ce masu,
Kai haba hakan ba girman ku bane ai ina laifin yarinyar na har fa gaishe ku tayi amma duk bata tsira daga sherin ku ba, sai kun zubar da girman ku da take gani, haba hakan bai yi ba wallahi,
Cikin wasa dayan daya fara magana yake cewa ku bari fa kunsan cewa yar gidan su eehhe din shi ce don kada ace a shagon Hamza yaro ake zagin gidan sarakan shi,
Bai iya ce masu uffan ba sai dan daga kai da yayi yana kallon yar yalalon yarinyar da,sukewa zari rana shiga gidan su,
Nan ya gane cewa a gidan sune ma zata shiga abokan hiran shi suke matc a sheri haka,
Allah ya shirya ku yace yaci gaba da aikin shi don yasan ba,bari zasuyi ba,
Da,sallama ta shiga gidan Umma Rabi din tare da ganin tana shara duk da saura kadan amma,sai da Aisha ta karba ta kara mata ta kwashe ,
Ganin ba alamar Kubura a gidan yasa Aisha jan bakinta ta tsuke tai shiru abinta,
Tana gama zubar da shara daidai Umma tana fitowa daga daki take cewa Umma ni zan tafi,
A,a Aisha har zaki tafi ke nan ai ina ce zaki tsaya ne don yau ba karatu ai,
Tace aa Umma dama na shigone na gaida ke da wuni an aikeni ne sayar kalanzir nashigo nan,
Kai aiko na gode kwarai Allah yai maki albarka gashi harda shara na,samu anyi min ai nagode sam barka,
Shigar Aisha gida takecewa mama saude na fada mata tana tafe na samu tana taya Umma aikine,
Dadi sosai ya shiga ran mama saude ganin yar ta yanzu ta fara sanin ya kamata a rayuwa,
Sai dai gaban ta,sai faduwa yake don gudu kasa asirin karyan da tayi ya tonu,,

****** ********* ******
Dakin mahaifiyarta ta,shiga tanq kokarin cire hijjab a wuyan ta,sai dai idanuwanta suna a kan mahaifiyar nata,
Wace ayanzu tausayi take bata ganin irin yadda take wahala akan cikin dake a jikin ta a lokacin,
Sannu Ummi Aisha tacewa uwar tare da dan kashe da idanuwa a cikin tausayawa take cewa
Ko na shimfida maki tabarma a,waje zaifi iska acan din,
Ki barshi don nan din ma yayi ai inji Fatima dake cije bakinta don wahalan nauyin cikin dake a jikin ta,
Tace mama kije asibiti ma ko da sau daya ne don su dan baki magani su duba ki,
Aisha ke nan tace a cikin dan sake murmushi danawa zanje asibiti adubani,
Kedai bari Aallah da ya bani wanan cikin shi tasan yadda zaiyi dani insha Allah,
Gurin dan kantan da kayan ta,suke yarinyar ta nufa ita kam Fatima sai taci gaba da dan fitaran da ttake da mafefecin kaba daje a hannun ta,
Muryan uwar taji tana cewa halan baki samu Kubura a gidan Uwar Hamza ba,
Tadan juyo daga gurfanen datake tana tonon kayan ta tace a hankali bata gidan,
May kika fadawa uwar ta to tace nace tana tafe aiki take taya Umma din a gidan,
Yadaifi maki ga sherin Kubura don bake ba har ni uwar ki yau sai tai muna zari ina fama da kaina,
Kudine tafito dasu daga cikin kayan ta tazo gaban uwar tana kara gyara shirya su da kyau,
Da sauri take cewa ina kika fito da wanan kudi haka Aisha,?
Umma wallahi kudina ne danake tarawa dama nace idan kin haihu sai na baki ki yi hidimar suna dasu,
Kudin ki a ina kika samau su ka take tambayan diyar nata acikin tashin hankali,
Ummi kudin break fast dinane da Baba ke bamu bani kashewa ina tarawa sai kuma kudin da mama Rahana ta bani idan naje gashe ta,
Wanan kuma,wasu sabbin kudi masu dan yawa zasuka dari uku tace na barka da sallah nane na boye,
Murmushi uwar tasake tace haba Aisha may kike ci a makaranta idan kin tafi,
Mama idan munsha koko a gida sai sauran tuwon da ake gyara muna shi nake ci har na dawo gida,
Rai uwar ta bata taje cewa gaskiya ban yarda kina zama da yunwa ba haka,
Idan wani ciwo ya kamaki fa na yunwa ya kike son nayi gashi ban da kudi ni,
Wazai kaiki asibiti kindai san wanan Baban naku bazai damu da ciwon ki ba,
Murmushi Aisha tayi tanacewa insha Allahu mama zan dan dinga kashewa tana mikewa tsaye bayan ta hada kudin ta mikawa uwar nata take cewa,
Ai Ummi ban iya cin abinci a makaranta sai naga kamar kowa ni yake kallo idan ina ci,
Dariya ta sa uwar nata tace kai kedai Aisha bafillatan gaskiya ce wallahi,
Juyowa tayi tace wa uwar wai da gaske Ummi ni bafillata ce dama kamar yadda ake ce min din,
Take ran uwar ya baci ta tsuke fuska da sauri Aisha ta juya don ita ma zance subul da baka yazo mata,
Kiyi hakkuri don Allah Ummi idan na bata maki rai ne bazan sake ba,
Yusuf dan Fatima na farko shine ya,shigo dakin da,sallama jikin shi yana saye da kayan aikin kanikawan da yakeyi,
Idanuwan shi a kan kudin da suke aje a gaban mahaifiyar tasu yace Ummi wanan kudin fa haka ?
Kai ko gaisuwa baka iya ba har yanzu babangida kasancewa sunan mahaifin mijin su ke ga yaron,
Ummi ya jiki yace cikin dan zaunawa daga gefen ta yana kokarin ciro dan kunshin naman da ya sayo mata da kudin da,aka,sallamay shi a gurin aiki na yinin ranan,
Ta karba tare da,sawa dan nata albarka inda tai masu jam,in gaba dayan su da kuma sauran diyan musulmai baki daya kamar yadda sunna ya koyar akan kyakyawan adduan don ta karbu da sauri a gurin Allah,
Tana kokarin bude takardan naman ne take cewa yar uwar kace tabani su

Download complete TXT · Novel page