Sarautar Mata

Chapter 31 of 94

Yana magana da bakon shi da ya kawo mai maganin feshi amma zuciyar shi na ga yadda nai mai ko in kula,( kishi)
Ledar da suka shigo da shine daya daga cikin su ta aje a gaban Umma tana cewa Umma baida yawa dama mun ce bari dai muzo mu gayar da ke, ne
A,a,a duk wanan ni kadai wanan ai yayi yawa ga,zuwan da kukayi ga kuma,dawainiya haka mai yawa,
Angode Allah sa albarka nagode nagode kunji sai dayar tace Umma wanan ce Halima itace dama suke tare da Hamza a can makaranta tana yawan taimaka mashi da abubuwa da dama shine tace ya kamata muzo mu gaida ke don ki san da ita, itama,
Tau taufa Umma ta dago kai da sauri ta dubi maimaganan tace wani irin magana ne wanan kuma yaran nan,?
Tace to may zamu boyewa Umma tunda da aure take son ka ita ?
Aure inji Umma ?
Gaskiya yarinya kin zo da sabon zance Hamza marayane bamu da kowa sai Allah kinga yar matan shi da muke maneji a gidan tare da ita,
Ina muka ga kudin auren irin ki a gidan nan ko ainda zamu aje irinki ai mu bamu dashi,
Dariya sukayi Umma wanan ai mai sauki ne a gare mu mu kawai yarda ki muke nema ki bamu baki ya aure ta,
Don shi mun rasa gane kan shi bai bata hadin kai yadda muke so,
Kuma wallahi a tsakani da Allah take son ta aure shi ita,
Kafin Umma tai magana mama Hafsi ta,shigo dakin tana cewa,
Ku da kata don Allah wani irin magana kukazo dashi, gidan nan,
Yanzu ku don baku da kunya shine zaku shigo muna da wanan zancen haka ba kuyan bajin wani nauyi, a idanuwan ku,,
Hafsi ki barsu su fadi abinda ya,kawo su aiji ba aiki bane, dashi dole don haka ki barsu muji shakuwan su ko,
Shiru sukayi don jin mai matan gidan suke fadi inda Mama Hafsi tace duk cikin ku wacece sa,ar auren hamza din ,
Don haka na roke ku da kubar min yaro na ya zauna lafiya da iyalin shi kada ku kawo muna,sabon fitina a,gida,
Boyar Alkah dakata ki ji mu bawai munzo ne akan zancen yanzu yanzu ba
Mun dai zo ne dan mu nuna kan mu asan da zancen a gida,
Hummm,ummm
Ikon Allah,
Allah ka kawo mu zamani kuma ,
Ba wai hakana bane mama kawai dai kada ace ana abu baku da labarin komai,
Sai zuwa wani dan lokaci a na zaune dasu zugun zugun tsakanin su da su Umma nikan sai sintirina nake ina aiyukana a tsakar gidan,
Ya shigo yana cewa sorry Halima na barku a zaune ko,
Kuzo ku gaisa da madam dina mana din ta san ku itama,
No kabarshi idan mun fita zamuyi sallama da ita ai,
Sai ta juya gurin Umma cikin dan kashe murya suna cewa,
Umma da,fatan zaki duba zancen mu da idon basira ki fahince manufan mu a gare ku,
Wani kallon mamaki yakewa bakin nashi don bai fahinci akan may suke magana ba,
Don bai taba tsan manin cewa zasu iya fadawa Umma zance maka man cin haka ba a,gaban ta,
Jin ana kiran sallah ko ina yasa su dagawa suna cewa,
Yanzu zamu koma sai wani lokaci ta juya inda Hamza yake a tsaye tana cewa dear na zamu, koma amma ga wanan ,
Tafara kokarin sa hannu a jakkanta tana ciro kudi tace a,sayawa Umma fanka a saka mata a,daki, ko,
Ke Halima baki gajiya da yin dawainiya ko yaushe sai kinyi hidima a mutum,
Umma itace fa ta aiko da kayan kwaliya kwanaki nakawo wasu Asma,u da sa,a,
Yafada cikin yar fara,ar shi batare da fahintar komai ba, a zuciyan shi,
Ina a zaune duk zancen da,ake ina jin abinda ake fada dama tun farkon fitowa na mama tai min signal da na kyale na kada kaina kawai ban ce komai ba,
Sun futo ana yan dararaku tsakanin su sunayiwa Umma sai watarana,da godiya ita dayar mai suna Bicky tana cewa Umma a diba muna zancen mu dan Allah,
Wai wani zance ne wanan kuke ta magana a kan shi Hamza din yake tambayan su don son jin maganan,
Babu ruwanka Bicky din ta fada maganar ce da maman mu,ai,
Sun mikawa Mama Hafsi kudi tace ku barshi in kunzo ne don ku saye mu ku cuci dan mu toni ba haka nake ba,
A,a mama wanan ba haka bane kawai munzo ne don mu gaida da ku kuma ku san mu,
Har zasu fita ya sake cewa baku gaida wife dina ba fa tana ciki dakin ta,
Dole suka,shigo dakin namu ina zaune na idar da sallah a lokacin na karba masu fuska ba yabo ba fallasa
Sun wani zauna suna kallon dakin dawaini irin karkada kafafuwan su,
Mikewa sukayi suna cewa zamu tafi sai wani lokaci mun kara haduwa,
Nace, sannun ku mun gode da kulawar ku gare mu,
Dariyan yake sukeyi suka ce ai ba komai, sai anjima ko,
Rakasu na yi zuwa kofa na yadda shari,a tace kaiwa bakon ka,rakiya ladane,
Daga nan nai masu Allah ya tsare hanya na koma ciki,
Zama nayi zuciya na tana wani harbawa don sai a lokacin nai masu kallon tsab don zan iya cewa sun haife ni dukkan su don ba yara bane gyarane kawai ya rufe shekarun su,
Suna ficewa gidan mama hausi tafara fada tana sababin inda take shiga ba nan take fita ba, ba wanda ya tanka mata
Abin duniya duk ya,sha min kai ko magana ban samu yi ba,
Don ita Umma sai farin ciki take tana cire kayan da,aka,kawo mata,sai faman yabawa take tana sa albarka,
Turumin zani ne sabulai, man shafa, turare da takalma silifas mai kyau,
Ya kai wani lokaci a,waje bai shigo gidan ba,sai zuwa yamma liss ya shigo ya samay ni a bakin murhu ina kwasan abinci,,
Sannu da,zuwan da nai mashi batare da na,dago kaina kona juyo in dubi shigowan shi ba,,
Buta,ya,sura zuwa,ban daki yafito ya zauna ya na son daura alwala,
Umma ce ta shigo gidan da ledan kayan da ta tafi nuwa,makwabciyar ta, aminiyar ta,
Ganin Hamza a gida yasa ta dan tsaya,gurin shi bata karasa isa gareshi ba,
Tace ashe ka,dawo sun tafi ko,?
Yace ai tun fitar mu suka tafi dama daga Birnin kebbi suka karaso nan, din,
Tace kaga,abinda ta zo min dashi ko ?
Gasu nan, na tafi nunawa Sa,ade tagani itama ta samasu albarka,
Kaya kuma ita Halima,din ta,za maki dasu mama,bafa musulmai bane kin san halin kiristan din nan da son shigewa,mutane,
Kirsta,kuma inji Umma ta fada a gagauce cikin mamaki,
Umma kina,mamaki ne, kin san su yan zuru ba, a gane musulman su sosai don kirstocin shigar musulmai suke harda hijjab da,gyale suna yafawa,
Cudan yan su gida guda da musulmai da kiristocin yasa kowa ya iya aladan wani,
Zaki shiga gida guda komai a,tare akeyin sa,amma,kowa da,addininsa uwa daya Uba daya
Daga daki mama hafsi take fitowa tace haba biri yai kama da mutum ai, yanzu yaran nan kafirai ne suka zo muna da,wani zancen banza a gida wai yaya ta bada baki ta bari ka auri dayar matar,
Mama su suka,fadi hakan da kan su mama tace aiga yaya nan gurin ta,wai, su kazo suna neman hadin kan ta ta,yarda ka,auri mai sonka din,
Wallahi mama sam, ni ban san da wanan zancen ba,don wani makamancin irin wanan zancen bai taba,shiga tsakani na dasu ba,
Sai dai harka kawai na karatu saboda likewar da tai min yan ajimu ke cewa,wai ni kanin Halima ce, haka yasa muke mutunci da ita amma ba zancen soyayya a,tsakanin mu,,
Sai a lokacin ne ya,daga kan shi yana kallon guri da,nake na mike zan kwashe kayan abincin da,na,raba,
Yake cewa a,ranshi amma halima,yau ta cutar danin ta,zubar min da mutinci na a,gurin yan uwana,
Ya kara dago kan shi kara na,biyu ya,bini sa kallo fuska kawai ya nuna mai canjin yanayi a tare dani,
Umma tana kokarin nuna mai kayan ya fara alwala yana cewa, Umma bari kawai zan ciwa wanan matar mutunci ne don kada ta kawo min iskanci har a gida,
Ina wanan zancen ya fito haka har take kulla min sheri, haka har a gidan mu zata zo tana irin wanan maganan kamar wace ta samu tabin hankali,
Wallahi mama ni a zatona ko zuwa sukayi don zumunci kawai,su san gidan mu,
Kayan da bai duba ba ke nan yai, alwala ya fita abinshi kawai ya bar Umma rugumay da kayan a hannuwan ta

****** ********** ******
Duk yadda mutum yai tsan manin rayuwan kubura yan zu abin ya,wuce nan,
Gashi mahaifinta ya saka mata dokan cewa duk tafara ta kashe auren ta ba dai gidan shi ba,
Don ya fahince ta ita da uwar ta,so suke ta kashe auren ta ta,dawo gida tana mashi iya,shege cikin iyalin shi,
Haka yasa dole ta koma dakin ta, tazauna tana hadiyan hakkurin ta ita,daya,
Wani iskanci da iya,shegen da tai dammaran yin shi a gidan Alhaji Nura yanzu duk ta sauke wanan mugun hali ta koma bi, da, rarashin kawai,
Wani jiji da kai da basarwan da take a gidan duk ta,sauke su don ba wani wanda ya damu da ita kowa ya fahinci halinta tun farko an kama kai da ita,
Dole badon taso ba ta sauke fadin rai din yau Jamila tana zaune a falon gidan nasu tana kallon wani Indian film, sai ga Kubura din tafito saye da wani don riga baki ta daura dankwalin shi a,kanta,
Jamila tana ganin futowan ta kamar kullun taja mata irin addu,oin da ta,sabayi akan Kubura din kamar haka,
La,illah haillah mohammadan rasullillah, sau uku,
A,uzu bi kalamatillahi tamatati min sherin min halaq,
Muryan Kubura ne ya ratsa kunnuwan ta tana cewa yau India aka i muna,
Ta dan dago kanta tankar a lokacin ta ga,fitowan ta daga dakin ta, tace eh wani film nake kallo a tashan,
Kubura ta kai zaune tana cewa ni ban faye son tashan irin haka,ba nafi son na kallli hausa ko yaya yake,
Don baki saba dasu bane aida bazaki barsu ba don suma,suna fadakarwa a ciki ai,
Nura ne ya,shigo gidan wanda dawowan shi ke nan a lokacin don bai kwana a,gida ba,
Yana rataye da couth din shi a kafada ya,dan sasauta nicktie din wuyan shi, kadan,
Kallon mamaki yake masu gaba dayan su don bai taba tsanmanin ganin su a haka,ba, ya kalli wancan ya juya ya,dubi waccan,
Cikin rashi sakin fuska Jamila tace sannu da dawo,
Kubura wace take zaune a gefe guda ko kallon shi bata yi ba tace mai ina kwana kawai,
Ya dan shiga da yan min tina Jamila wace ita ce da girki a ranan ta dan mike dingis dingis zuwa dakin shi ,
Idan ba kunnuwan ta ke mata karaya ba zata iya cewa fada tadan ji Jamila din tanawa maigidan nasu, don tafahinci akan dawowan shi lokacin take magana daashi,
Mikewa tayi zuwa dakinta don rashin ganin dacewan hakan, don zamata a,gurin tana sauraren sirin su tankar wani abinda bai dace ba take yi,
Kwance take tana nazarin abinda taji suna fada wa junan su,
Yanzu Nura ya dace ace mutum mai iyali kamar ka dai yanzu zai dawo gida cikin iyalin shi,
Yace cikin irin halin shi na,dakawa mace tsawa wani ya turo ki kimin fada ko kuwa,
Jamila tace amma kasan hakan baidace ba ace namiji mai iyali baya kwana cikin italin shi yana can yana bariki sai lokacin da yaga dama ya,dawo don kan shi,
Tun yaranka basu da,wayo har yanzu sun fara fahintar halinka cewa a can ka kwana ko,
Yau Amira dagewa,tayi wai bata zuwa school idan bakai zaka kai su kullun ko wani yaro baban shi ke kai su,
Yace look ki fita ki bani guri ina bukatan hutawa kin zo kin cikani da surutun tsiya haka,
Sai ka tafi ka,wullakanta kan ka a,duniya ka dawo gida kana wa mutane cika da batsewa,
Jin motsin ta yasa Kubura shawaran komawa daga cikin dakin ta
Tambayan ta anan shine ina Nura ke zuwa haka wanda duk dare sai ya tafi,
Kardai ace neman mata yake haka har yai muni kada fa ya jawo masu matsala ko wani mugun cuta ya saka masu,
A hankali ta furta cewa Allah gamu gare ka ka kare mu daga mugun ciwon zamani, a rayuwan mu,
Mirginawa tayi tanamai jin haushin kanta akan rashin kwantar da hankalinta tun shigowan ta gidan ta fahinci mai gidan ke ciki,
Ta dauki fadin rai ta saka a ranta tana ta wahala tsayin shekara da,watanni,
Gashi yau yau da,fara kwantar da kanta tafara fahintar wani abu a gidan,
Lalai sai tasan ko may mijin nasu yakeyi wata,sana,a ce yakeyi irin haka har yake hadasu fada da Jamila mata mai hakkuri, kamar ta,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
👑 SARAUTAR MATA 👑
2⃣9⃣

RABBANA, LA TUZIGH QULUBANA, BA,DA, IDDZZI, HADAITANA , WA HAB LANA MIN LADUNKA RAHMATAN INNAKA ANT AL WAHHAB,,,,,,,


ZAINAB IDRIS MAKAWA


DON ALLAH YAN UWA INA BARAN ADDU,A AGARE KU KU TAIMAKENI KU TAYANI ROKON ALLAH AKAN ABINDA NAKE BUKATA A GURIN UBANGIJIN MU ALLAH SUBBAHANAHU WATA,ALLAH,,,,



Wasa wasa yanzu anfi sati Umma tana kwance masasaran yaki tsayawa har ya kaita a kwance, sosai,
Yar uwar ta mama hafsi ke faman dawainiya da rashin lafiyan Umma din, sai ni dake faman dafe dafe a gidan
Naka shiga dakin fiye da a kirga don na gaida Umma na Kuma duba lafiyan yata, nakuma wanke kayan da tai amfani dasu,
Ranan da ta cika sati Daya a ranan na shiga daki na Sami duk yaran Umma suna a kanta, tana cewa sanyi take ji su rufa mata bargo, sai rawan dari take daga kwance,
In tsaye daga gurin da nake ina nazarin abinda ke damuwar ta gashi sai faman dirka mata magani akeyi
Ina mai kura mata ido, sai naji suna cewa wai, za a Kira Mai chemist yai mata allura,
Ni ko na fahinci wani abu a jikin nata sai dai Ina tsoron magana suce ban San komai ba, na jawa uwar su mugun ciwo nake mata fata,
Daga inda nake tsaye daga bayan su nace amma yaya da kiran wanan mutumin ai da kawai akai Umma asibiti gurin doctor ya dubata zai fi wanan, kaura da kai din da ake tayi a gida da ita,
Duk kan su suka juyo inda nake suna masu sako min idanuwan su, gaba dayan su
Kaji malamar asibiti fa aida sai ki dubata idan har kin gane wani abune, jibrin ne yai wanan magana,
Mama da Yaya hamza suke cewa tun da kukaji Aisha tai wanan maganan akwai abinda take hasashe ke nan,
Ibrahim yake cewa, cikin, tambayana Aisha don Allah kokin fahici wani abin ne suna masu sako idanuwan su a kaina,
Cikin harshe turanci wanda zance duk gidan nan ko shi Hamza din bai taba sani na iya turan ci ba haka nake masu bayani, komai,
Don ina gudun yi da hausa Umma taji tace ina mata mugun fata ne,
Jikin su gaba daya yai la,asar suke cewa gaskiya ya kamata subi shawara na don bai kamata ace sun aje ta a gida ana magani daban ciwo daban,
Fita Hamza din yayi zuwa wani dan lokaci sai gashi ya shigo gidan a cikin, saurin shi tun a kofa yake kiran mama,
Duk muka yo waje don son jin may zai fada tunda kowa a tashe hankalin mu yake,
Ance mai baki bai iya ciwo ba don Umma ta wani koma ragwab da ita duk tafita hayacin ta, sai nishi take daya daya
Mama ga mota a,waje mu tafi ko?
Ina shiga dakin naga yadda idanuwan ta suka juye sukai, weak a lokaci guda,
Da sauri har ina ture Ibrahim na karasa bakin gadon a gaban Umma na kamo hannun ta ina dan massage din hannun nata a hankali har wani dan lokaci,
Sai naji tai wani irin ajiyan zuciya a hankali sai da kowa yaji a,dakin,
Duk sai suka kara rudewa hankalin su ya tashi,
Nace Mama ku kamata a tafi sai dai aiwa driver magana ya tuka ta a hankali don Allah saboda tana bukayar resting sosai,, saboda jikin ta is already been weak,
Hankalin su gaba daya ya tashi sai wasu suka fara kuka suna cewa wayyo Umman mu Umma don Allah kada ki mutu ki barmu,
Cikin tsawa mama take masu fadan wani mugun fatane haka sukeyi ai ciwo ba mutuwa bane,
Ke Humaira dauko hijjab dinki mu tafi asibitin a tare zaifi,
Ba musu na shiga daki kamar yadda ya umurce ni na dauko hijjab dina a tare muka tafi,
Ni da mama muka zauna a baya tare da Umma ina dan mata masage yadda ya dace ce,
Mun shiga inda duk wani abinda ya dace ayi na ganin likita tare da Yaya Hamza mukayi kasancewa akwai yan makarantar mu da su kazo practical a gurin,
Sosai zuwana ya taimaka nan da nan muka shiga gurin likita don bada bayani, abinda ke damun ta,
Likita ya tambaye, ta ta kasa magana kamar maijin tsoron shi, dole ban san lokacin da na bude baki nafara yiwa likita bayanin yadda Umma din tafara ji har zuwa yanzu da abin ke son zama mata blood pressure,
Tambayana yayi wasu irin medication mukai mata a gida nan ma tirya tiryan nai mai bayani har zuwan mu asibiti ,
Yadan bugi taburin gaba shi yace she is, very luck dat you are around if not she will die or be in critical condition,,
Umma tana rike a hannuna sai nishi take guda,guda, tana kara kamay wa,cikin tashin hankali,
Are you a student ?
Tambayan da yajefo mi ke nan lokacin da nake kokari gyarawa Umma zanin ta daya rankafo,
Nabashi amsa cikin gyada kai da cewa yes,
Where are you schooling ?
Health and technology nabashi amsa a takaice tare da mikewa ina kokarin jan Umma gurin gadon da yace tahau,
Sai yace, interested,,,
Yakamata ace parents naki nursing suka kaiki ba health ba,
Don you are very intelligent gaskiya yakamata ace nursing kika tafi,
Maigida na nan yake son nayi

Download complete TXT · Novel page