Showing 93001 words to 96000 words out of 299981 words

Chapter 32 - Sarautar Mata By Makawa

04 Dec 2025

17640

Hamza ne daga bayan yaron shima hannuwan shi dauke da jakar kayan shi da wasu tarkace da yazo dasu,
Yaron ya nufi kofan dakina da kayan dake daga hannuwan shi sai daga cikin daki nake cewa ya kai kayan dakin Umma,
Shima kanshi Hamza din da kayan dake a hannuwan shi dakin Umma suka nufa,
Lalai marhabi inji mama hafsi take cewa cikin jin dadin ganin dan nata ya,shigo gari wanda ta,dade bata saka shi a idanuwan ta ba,
Shima Hamza din cikin jin dadin ganin kaunar mahaifiyar tashi a gurin su yayi murmushi yana cewa mama sannu da zuwa,
Ita ko mama hafsi duk ta rude cikin jin dadi sai farin ciki take nunawa
Umma dake daga gefen ta sai murmushi take na dadi yadda yar uwar ta ke matukar nuna kaunan ta ga 'ya'yan ta,
Mama hafsi tace wa yaro kai kai kayan dakin can mana, ka yo nan dasu,
Hamza cikin fara,a yace kayan tsaraba ne a ajewa Umma zata raba,
Sai fara,ar mama ya dan rage tace kamar ya zata raba ba dakin ka za,a kai kayan ka ba in yaso matar ka ta gama sauke ka sai ta kawo muna abinda muka samu,
Umma ma rage faraar fuskan ta tayi don tasan mama bazata yarda da wanan halin ba ke nan tunda tai magana,
Aisha fito ga mijin ki yazo ki karbi kayan shi mana,
Na,am mama nafito daga daki na yana tsaye daga kofan Umma ya zama dan birni wayayye dashi,
Nai mashi sannu da zuwa ida idanuwan shi a kaina
Ji yake kamar ya rugumay ni irin yadda yake ji a ran shi,
A hankali cikin natsuwa na karaso gare shi na karbi jakar daga hannun shi inda na doshi dakin Umma,
Yo ga yar nema kikai mai kaya daki zaki shigo nan dasu kuma nace cikin da sakin fuska, anan ake ajewa,
Haba tafi dasu dakin ku mana ban iya mussu da ita sai na juya zuws dakin namu da kayan har na ledan da yaron ya,aje a kofa na shiga dasu,
Kai yaka nan inji mama tace karbi nan sheka ka,sayo ruwan leda mai sanyi na,duka kawo muna,
Dakin ya fada Umma tana zaune cikin fara,a yake cewa Umma sannun ku da gida,
Baba a she kana hanya sannun ku da zuwa, yace yauwa Umma,
Ashe mama tazo ne tace ta tuna damu gata nan ai ta kwana biyu ya durkusa har kasa yana gaishe su,
Yaron yana kawo ruwan ya mika min na karba na juye a plate na kai mai a lokacin yana zaune saman kujeran dake ta kofan dakin daga ciki,
Na ajeruwan a cikin ladabi zan juya mama take cewa dauki saura kikai mashi daki kafin ya,shigo,
Har na duka sai Umma ke cewa miko min na dauka na jika raina nima don ita dan ta kawai ta,sani,
Nakaiwa Umma ruwan ta dauka har guda biyu nafita da sauran, sai mama ke ce min yanzu Aisha may za a bashi yaci, ne,?
Abinda ban taba jin Umma tayi ba ke nan idan ya,shigo gari haka zamu barshi sai ruwan randa kawai zamu bashi,
Nace mama abinci ya kare,
Tace to ko a,sayo mashi wani abin ne a,waje,?
Mama abarshi kawai ai saida mu kaci abinci muka fito ,
Yanzu haka zaka zauna da yun wa har yamma ?
Babu komai mama a koshe nake,
Kafin ya,shigo na kara gyara dakin da jikina don taron shi kada yaji ba kamshi,
Yai yan mintina yasuna hira ya mike yana cewa bari na dan rage kayan jikina na,watsa ruwa mama,
Ya,shigo dakin a lokacin ina tsaye zan dauke jakarshi na kai gurin da nake aje mai,
Ta baya naji shi ya,rugumoni yana matse ni da jikin shi cikin yar sauke ajiyan zuciya,
Sannu da,zuwa,yaaaa sai naji ya hada bakin shi da nawa abinda yasani dan shiga,yanayi ke nan,
Ya furta,min kamar mai rada da cewa miss you my wife,
Nai murmushi ina kokarin zullewa sai ya kara riko ni a jikin shi ya matse yana mai kai min kiss har ta wuyana,,
Na samu ya,dan sasauta min yake cewa mun samay ku lafiya, nace cikin dan gyara rigana lafiya ya karatu,
Ya amsa yana kokarin balle botton din rigar shi yana cewa karatu Alhamdullahi ya,school din naku ?
Alhamdullahi yaya mun kusa fara exams, nace na zuba ma ruwa ne ka,watsa,
Yace kamar kin san shi nazo yi duk zafi nake ji a jikina,
Na fito daki mukai arba da Umma wace fuskan ta yana a kofan mu tana gani na ta,wani kawar da kan ta,
Wanka yaya Hamza yayi ya canza tufafin jikin shi sai ya,fita don ya gaisa da mutanen uguwa yana,shiri ne yake tambayana yaya su Ummi da,sauran mutanen gida,
Nace a takaice duk suna lafiya, duk da ban shiga ba tun wancan zuwan da mukayi tare da kai,
Ya juyo da karfi yana veea har yau baki shiga kin dubo su ba ?
Nace ina jin tsoron tambayan Umma tace min na faye yawo,
Wa,yai maki kitso da kumshi to nadan daga hannayen nawa nace haulatu ce na aika tazo tai min, jiya,
Gaskiya ta iya kwalliya don yayi min kyau sosai wallahi,
Nace mama ce ta bata kudin da tai min ai,,
Ya ce ashe mama tana garin nan ne ?
Nace eh tazo yanzu ai yakai sati uku zuwa hudu Allah sarki tayi kokari wallahi,
Mama tana da kirki kwarai yaya don zuwan ta yai min dadi a gidan nan saboda tunda tazo ina jin dadin karatuna wallahi,
Don duk wasu aiyuka ita ke yi kuma ta,sa su asmau su tai maka min
Ai kadan ne daga,halin ta,don ita,daban take a,cikin su,
Ya,fita yana cewa bazai dade ba zai dawo yanzu suma ina jin yai masu sai ya dawo,
Futan shi na,dauko ledan da ya,sayo muna breadi da,su lemo kwakwa da Carrots, nakai dakin Umma,
Nace Umma ga kayan tsaraban da yaya yazo dasu,
Na barsu a dakin na fito waje abina na barsu suna maganan su,
Nai mamaki kwarai a irin kason bread din da muka samu a dakin mu,,
Ina aikin girkina yaya Hamza ya,shigo gidan da ledojin mayan bakake har guda uku dauke da kayan abinci a ciki,
Bayan na karba na gama fitar da komai a inda ya dace,
Nashiga aikin girka abincin na Allah ya taimakeni nai girki na tsab sai kamshi ke tashi a gidan,
Dama dana a cikkin kayan da ya,shigo dasu a kwai vegetables na gane miyar taushe zan yi ke nan a,daren nan,
Tuwon shimkafa nai muna ya tuku ya kwanta gwanin ban sha,awa
Na saka a cikin leda na,daure su gaba daya na zuba a cikin babban kulan da muke zuba abinci a ciki,
Na,dauka nakai kofan Umma kamar yadda na,saba ajewa idan na gama,
Na koma na kwaso kwanonin abincin nazo na girke su a guri guda nabar gurin,
Wanka na shiga tunda na gama kafin ayi sallah magriba,
Nafito nai alwala na juya zan shiga daki sai naji muryan mama tana cewa,
Aisha anan kuma kika girke abincin baki raba kin ba kowa nasa ba,
Nadan tsirgar da miyau din dake a bakina ,
Nace mama ai ba nice mai rabawa ba Umma ce take raba abinci idan nayi,
Mama tace ikon Allah ita yaya din ce mai raba abinci a gidan kuma,
Na juya zan shiga daki mama tace idan kin idar da sallah kizo ki raba kibawa kowa nashi,
Na shiga daki azuciya ta ina nasa cewa bazan raba abinci ba don bani ce na,saba rabawa ba,
Ina gama sallah na,zauna a gurin tare da dan kishingidewa,
Muryan mama daga waje tana cewa Aisha fito kibawa kowa abinsa mana ko so kike sai dan nawa ya shigo baki aje mai abincin sa ba,
Shirun da taji yasa mama daga labulen dakina tana cewa a,a kwanciya kikayi ne baki ji may nake fada bane,
Nace mama kaina ke ciwo bari kawai a raba ,
Murmushi tayi tace hmmm rabon abincin ne yasa ki ciwon kai yan nan,
Tajuya tana rayawa a ran ta inko har haka Umma take yi a gidan nan bata kyauta ba,
Allah ya hutar da ita ya bata yarinyar arziki a matsayin sarakuwa amma tana wasa da damar ta da,sa,an ta da Allah ya bata,
Dakin Umma ta shiga tana cewa sai ki raba abincin tunda kece kika saba robon
Umma tace ni dama nasan cewa yarinyar nan bazata raba ba cewa zatayi bata san yadda zata raba ba,
Naji Umma ta fito tana raba abinci sai surutu takewa mama hafsi tana amsa wa ciki ciki,
Can ta kwada min kira na fito ina saye da farin hijjab dina mai hannun roba, don na dauka,
Yaya ki kara masu miya tunda kinga su biyu ne aka sakawa, ta bude tadan kefato miyan ta zuba, muna,
Najuya na,shiga dakin mu da abincin Umma tana kallo ba daman tai magana tunda mama ta na a kusa,
Don ta hana na,shiga da abincin Hamza daki wai kada aiwa danta barbade magani, a cikin abincin,,

****** ********* *******
Haka nake shiri na irin wanda ya dace mace tayi idan mijin ta zai zo gare ta a cikin natsuwa na dan sha kwaliya na tare da dan kamshe jikina da dakina,
Hamza suka shigo gida shi da Ibrahim suna hira da alaman hiran shagwan su sukeyi, don shagon ya fada sosai naji Hamza din ya na fadin cewa zai samu lokaci ya kara dan kayan shagon don gudun kada kudin cefanen su ya kare,
Tabarma yace ya shimfida masu na,dauko babban tabar ma na,shimfida masu a tsakar gidan suka zauna
Daya bayan daya suke shigowa gidan suna taruwa a gurin inda na gabatar mai da abincin shi ,
Kowa ma,nashi abincin yana a gaban su suna ci a take yadda na gan su naji sha,awan su ya kamani a zuciyata,
Ban kawo komai a,raina ba nima na,samu gefe daya na zauna ina son cin abincin, nawa
Umma tace wanan zaman da kukayi abu daya ya rage min jin dadin shi shine rashi jika a cikin ku,
Gaskiya na matsu naga an haihu a gidan nan nima nazama kamar ko wace mace mai alfahari da jika da zurian ta,
Shiru gurin yayi gaba daya kowa da abinda yake rayawa a ran shi,
Asma,u tace wallahi nima Umma ina son naga an haihu ace wai har yanzu ko ciki babu a gidan nan,
Muryan mamace ke cewa ai basai a gidan nan ba koke kya iya aure ki haifa aiki kawo mata ko,
Mara kunyar yarinya kawai manya suna magana ki wani saka bakin ki a ciki,
Ina ita Zarah ma har yanzu Allah bai bata,ba idan da mutum kebawa kan shi da zarah yanzu ta haihu ai,
Sai a lokacin kowa ya fahinci zancen da Umma take nufi haka yasa gurin yai shiru na,dan lokaci,
Na kasa cin abincin nai shiru sai kallon shi nake a gabana,
Hamza ya hankalta dani sai yake jin ba dadi a cikin ran shi don bai dace ace Umma ta fadi haka ba da bakin ta har nawa Aishan take da za ace wai har yanzu,
Kuma ai maganar mama gaskiyane ai Zarah ta riga su aure idan ma
Yan mintina kadan tsam na mike ban ci abinci ba zan shiga daki,
Yabini da kallon tausayi yace Humaira bazaki ci abinci bane,?
Nace a hankali ciciki na koshi sai anjima nashige abina daki,
Umma tace aikin banza ba dai za,a fadani fadan abin dake damuna a,rai ba,
Gaskiya Umma haka bai dace haihuwa ina Allah ne ke badashi ba,wai mutum ba,
Ki ka sani ma ko matsalar daga yayan mu yake ba daga gare taba, baga zarah ba mijin ta ai yana da yara amma ita ai bata haihu ba ko,
Umma tace Ibrahim ka fita daga idona ina fada maka idan ina zance a gidan na kana cewa zaka tsayar dani zan saba maka fiye da tsan manin ka wallahi,
Hamza shiru yayi yana jin daci a cikin zuciyar shi don sam bai taba kawo zancen wani haihuwa ga Aishan ba ma yanzu,
Ban shiga daki ba na fara hada kayan dake a,wajen tsakar gida don kada su kwana a wajen,
Duk sintirin da nake hankalinshi ya na gareni Sa,a autar Umma tace Aisha kara min miya sai lokacin mama hafsi da take zaune duk ta kai makura tai magana,
Tace ungo naki an kafeki ne dabazaki tashi ki kara da kan ki ba, ko boyar gidan ku ce Aishan,
Miyan na debo na kara mata yadda ta bukata na juya na,shiga dakina,
Kamar jira hawaye suke nashiga,su fara zubo min ina cewa a,raina,wanan kuma wani sabon masifa ce Umma ta ke kokari sakani a cikin sa,
Hamza bai jima ba gurin su ya,shigo dakin ya samay ni na kifa kai a filo ban ma san shigowan shi dakin ba,
Jin mutum ya zauna daga gefena yasani dan motsawa, a hankali,
Muryan shi naji yana cewa kardai nace kuka kike Humaira,
Zance Umma zai saki kuka haka ban sanki da,saurin fushi ba Aisha, don haka,share hawayen ki ki saurareni kiji,
A,hankali na,dago jajayen idanuwa da,suka kada,sukai ja nace a,cikin da shakaken muryan da yaci kuka yaya yanzu,,,,,,
Sai kuka ya hanani karasawa dole na,dakatar da zancen da na,so furtawa na,sake kuka mai ban tausayi,
Shiru yayi ya kasa,magana na wani dan lokaci sai naji ya jawoni zuwa jikin shi yana cewa idan kikai min haka Humaira baki kyauta,min ba,
Yau ina hakkurin ki ya,shiga Humaira zancen Umma zai tayar maki da hankali har ki na kokari yiwa kanki illa,
Maganganu masu sa zuciya taushi, ya dinga min har na fara dan jin taushi a raina,
Sai naga ya mike tsaye ya fita, daga dakin gurin su Umma ya nufa inda suke zaune yace,
Mama ina abincin Humaira yake, ?
Mama hafsi ta mike ta dauko mashi inda t rufe min ya sa hannu ya dauki ledan ruwan mai sanyi guda ya nufi dakin mu dashi,
Umma tai wani irin tsuki na takaici batare da tai magana ba sai mama Hafsi ce tace Allah dai ya kyauta,
Amana dai guda ce duk wanda yai dakyau don kan shi saboda son kai mutum ya hana diyan shi zaman lafiya,
Yanzun dai don na fadi gaskiya kuke jin haushina ko waye bai son yaga karuwa a gidan shi, kuma dole ne nai magana
Mama tace, ai, sai ki yi tayi in har yin naki zai sa ta samu Allah bai tashi bayarwa ba,
Ganin shi da nayi da kwano tafe ya dan sani mikewa don na karba sai yace zauna abinki,
Har gabana yazo da kwanon abincin ya,zauna darsha a kasa yace oya bude bakin,ki na baki,
Abin da yasani dan murmusawa ke nan nakarbi kwano ina dan kai abincin a hankali a baki, na,
Na danci kadan yana zaune ya kura min ido ya na kallon yadda nake cin abincin
Na tura mashi plate din ina batun tashi yake cewa
may wai ?
Badai wai kin koshi ba ke nan ?
Cikin wani murya kamar ta mai shagwaba nace na koshi yaya kamar zanyi kuka,
Ki dan kara mana shi, ma ya fadi kamae zaiyi kuka cikin marairaicewa da make murya irin yadda nayi,
Nace Allah yaya na koshi amai nakejin kamar zanyi,
Yai sauri kawar da kwanon daga gaba yana cewa tashi ki wanke hannuwan ki ko na,debo maki ruwa ne ?
Nai saurin girgiza kaina ina cewa zan fita na wanke a waje,
Nafito wajen nan na,samu mama da Umma a zaune suna hira na wanke hannuna na,shiga daki
Yaya Hamza yafita daga dakin zuwa kofan gidan nikan na,shige daki a abina na fara shirin kwanciya ,
Tun ina jin hiran su har na fara jin kadan kadan nima barci ya soma dauka na,
Motsin shigowan shi naji yana ce min kinyi barci ne Humaira,
Tashi ki ci wani abin kada ki kwana da yunwa, a cikin ki ciwo ya kamaki,
Kokarin bude kumshin naman da ya shigo dashi tare da gorunan juice drinks,
Sosai naci naman tare da kora ruwan lemon sai a lokacin naji duk bakin cikina ya dan gushe min,

Yaya Hamza ya samu damar sauke nayin da kishin da ya dawo garin da shi, ,
Shima,sai zuwa lokacin ya samu, dan sauki a rayuwan shi,
Bayan mun dan samu natsuwa,a tsakaninbmu ne naji ya kira sunana a cikin wata irin kasalaliyar murya inda nima na amsa ciki ciki,
Yace magana nake son muyi ni dake ta,fahinta jin haka ya sa ni dan gyara,kwanciyana a cikin natsuwa, a hankali,
Humaira, don Allah daga yau ina son na baki shawara akan Umma a gidan nan,
Duk wani abinda zata fadi ko zata aiwatar maki matukar ba daga gareni kikaji wanan zancen ba, ban son ki kara nuna,bacin ran

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login