Sarautar Mata

Chapter 33 of 94

wanan zancen haka dan Allah,
Hakan ba girman ku bane dakai da yaya ko ina duniya ko bana nan Aisha yar kuce don gaba dayan ku bazamu manta da halarcin da kukai mata ba na zaman ta gurin ku,
Ta juya gurin mama saude tace Yaya don Allah ki bar maganar nan aishi maso habaici dama maso fada ne,
Atika daga kofan kitchen tace nidai na fadi gaskiya don dama daci ne gare shi,
Da kyat Ummi ta rarashi mamata shiga dakin ya a cikin bacin rai don zancen atika da mijin su ya bata mata rai sosai,
****** ********** ******
Gidan yai muna tsauri saboda ga,damana tai nisa duk kudin Hamza ya watsa su a gona yana duban abinda zai girba idan lokaci yayi,
Don kwanciyar Umma ya jawo masu rashi kudi a hannun su,
Mun wayi gari dan kamun da zamu dama kunu a gidan yadan buwaye mu,
Gashi babu abincin da zan dafa muna da rana muci,
Hamza ya shiga dakin gurin Umma yana tambayar ta ko akwai dan kudi a hannun ta sai ta ara, mashi, har ya,samu ya mayar mata,
Amma sai Umma ta kyankyashe kasa tace batada ko kobo a hannun ta ya tafi gurin matar shi ai tana sana,a ta ara mashi,
Cikin dan marairaice murya yace Umma bata dashi ne dana karba a gurin ta ai,
Wani kallo Umma ta watso mai mai nuna owo kana goyon bayan matar ka ko,?
Cikin daga harshe Umma tace duk sana,an da take a gidan nan za,a ce wai bata da kudi a gurin ta,
Hamza ya kara cewa bata dashi ne Umma ni na san da hakan,
Daidai nan mama tafitowa daga dakinta taji wanan hayaniyan takaraso zuwa gurin,
Hamza yace Umma wallahi duk kudin danai ta amfani dasu a,sibitii gurin Humaira na karbe su,
Sai duk suka watso mai idanuwan su yace, wallahi mama a,gurin ta nai ta karba don su sauran yan uwana, sun ce min bazan samu ko sisi a gurin su, ba
Duk wanda ma na tambaya bana jin mai dadi a,gurin shi,
Shiru Umma din tayi don jin dan nata ya rantse cewa a,gurina ya karbi kudaden da ya kashe asibiti,
Juyawa tayi sai mama tace duk kudaden da akasamu a asibiti fa yaya ?
Bazaki bayar a rufa asiri dashi ba may ye amfanin samu a gida,
Daki, tashiga ta dauko dari biyar ta miko mashi a wullakance,
Yakarba yana godiya, yace zai je ya samo dan abinda za,a karya dashi,
Bai fita ba daki ya shigo ya zauna da dari biyar din a hannun shi yana dan juyawa a hankali,
Nafahinci cewa bazasu ishe shiba shiyasa ya rasa yadda zaiyi da daribiyar din, na hannun shi,
Dubu dayan da ya rage min a dakin dama kayan zobo zan saya dasu nadauko na mika mai nace ga wanan sai ka kara ko,
Yadago idanuwan shi da,su kai ja ya sauke su a kaina yana cewa cikin wani sanyin murya,
Wanan kuma fa nace cinikin da nasamu ne jiya da wanda ke a,gurina dama kayan zobo naso saye dasu,
Idan kin bani ke damay zaki hada zobon naki dashi ?
Tunda ba,wasu kudi a hannun ki,
Nace Alkah zai rufa min asiri insha Allahu na samu nayi ko da kadan ne,
Ya karbi kudin daga hannuna badon ya so ba ya mike yana ce min bari nadan fita nagani Humaira,
Zuwa wani lokaci yadawo da leda ya auno yar shimkafa a ciki da cefane yakawo min yana cewa nayi na rana kafin anjima yagani ko za,a samu na yamma
Acikin dabaran mu na mata nai tuwon shikafa na hada da saurwn gari na daure sai yakai muna har da na yamma,
Haka rayuwan wanan damanan tazo muna sai na,dan kulla cinikin dan zobon da kakaran nonon da nakeyi mu sai wasu abubuwa don har shagon namu ya kare,
Kubura tazo gida yini taba da kudi a,sayo mata idomie ta dafa don wai bazata iya cin abincin da aka,dafa a gida ba,shinkafa da wake,
Anya kuwa za,a samu abu a shagwan Hamza din nan don duk kwanakin nan duk abinda aka aika sai suce babu shi ina ga sun lashe,
Tawani juywa tana kallon mama din tace wallahi mun ta aikawa hatta maggi cewa suke wai babu shi,
Tsiya takai tsiya ke nan tunda har shagon ya kare ai nasan karya ta kare ke nan,
Ita yar agwai din fa to mama ?
Wanan mai gadon zurfin cikin aibazata taba fadin komai ba ita,
Sai dai taita wahala a ciki takare haka na a wahalce,
Wai shine da Baba yaso turani cikin wanan wahalan boni yaci har na lalace,
Ai har yanzi shi bai san da haka ba don kwanaki yadan bada Omo akawo muna shine munafukar nan kecewa wai suna kina,aure gidan mai kudine amma yar Agwai tafiki sa,an daki da kwanciyan hankali,
Halan maman Aina ko ?
Ta tambaya cikin canza fuskanta tare kufulowa,
Ita mana dawa zaiyi wanan zance in ba itaba mai kwarmaton banza,
Wallahi mama sai nayi maganin wanan munufukar matan agidan nan don bazan kara bata fuska ba dani take zancen,
Tamike tare da yafa dan yalalon gyalen da ta yafo a kanta tana cewa ina zuwa,
Zaune nake ina raba abinci shimkafa da wake da mai da yaji nadafa sai kamshi man dana,soya yake tashi naji sallaman Kubura,
A zatona ta shigo gaida Umma ce taji labarin bata da lafiya nai mata iso a cikin washe bakin naga yar uwata,
Nace tazo su gaisa da Umma tana kwance daga kofan dakin ta,
Cikin wani yatsuna duk da ta ramay ta fada yangan nan da kaudi irin nata yana nan kamar baya,
Mun koma dakina da ita,na gabatar mata da abinci na aje mata zobo da ruwan sanyi,
Nai mamaki kwarai danaga ta sake jiki ta kwashi abincin dana saka mata din,
Tana shan zobo Hamza ya shigo cikin daga labule yana ganin ta ya dan daure yace a kubura kece a gidan namu tace eh,
Nashigo ne naga yar Agwai tunda ka hanata zuwa gurina,
Ban hanata ba idan tace zata ai zan barta ko na kaita,
So kada kiga laifina bani na hana taba,
Ta kurbe zobon ta mike tana cewa zata koma tana gida sai da yamma zaya tafi don yini ta,shigo nai mataalkawarin insha Allahi zan shigo gurin ta,
Tana shiga gida mama ke cewa ke ina kuma kika,shige tun dazun,
Tai gyatsa tace gidan su yar Agwai na shiga naci abinci,
Kai amma Kubura baki san kunya ba a rayuwan ki wallahi da hat zaki shiga kici abinci a gidan wanan kaskantatun mutanen,,,




ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
👑 SARAUTAR MATA 👑
2⃣8⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA



JUMMA,AT MUBARAK YA JAMA,ATU MUSULUMINA ,,,
FATAN ALHERI GAREKU YAN UWA MUSULMAI,,,
FATAN DACEWA DA RAHAMAR UBANGIJIN MU DUNIYA DA LAHIRA,,,


Ina zaune inda na idar da,sallah sai addu,oi nake jorowa na neman tsari Ubagina daga sherin mutun, kwaro, dabba ,ko aljan, dama duk wani abin cutarwa gare ni,
Ina idar da wanan adduan najini wata wasai kamar har adduan nawa ya karbo ko,
Saboda sannu a hankali naji duk wani kunci da na yini acikin sa ya shige min ya tafi,
Sannu a hankali na fara jin hayaniyan mutanen gidan yana tashi, alamar sun fara,dawo daga guraren da,suka fita tsabgogin, tunda rana,
Allah yai min wani baiwa na yaran Umma duk da bata sha,awan su kyautata min a rayuwan ta,
Amma,su Allah ya saka masu damuwa da,al,amarina tare da nuna kulawar su a gareni koda kuwa sun min rashin mutunci ne yanzu yan mintina kadan zakaga sun huce sun biyo ni suna min magana,
Hakan yasa nima,duk abinda zasu bukata a gareni muddin ina dashi bazan hana masu ba,
Asmau ce tafara tambayan ina Aisha akace mata ina cikin daki na,
Can na tsikayo muryan
Hamza da Ibrahim sun shigo gida a tare, lokaci guda,
Su din ma a,saman tabarman da su mama suka,shimfida a tsakar gida suka yadda zangon, su,,,
Bayan sun gaisa da iyayyen nasu ne sai naji hira ta kaure a tsakanin su da mama hafsi wanda hirar ta,su akan yadda yake da gurin yin noma ne a,damanan bana, insha Allahu,
Yake cewa mama,din ya kara samu ilimi akan noman zamani sosai yanzu don abin zai zo mai da sauki indan har ya sayar da abinda ke gare shi ya hada
Yace kuma ya bada sakon a sayo mashi irin masu kyau da saurin fitowa,
Har wani kasar ya tura a,sayo mai irin masara da wake na zamani da,zasu yi kyaun nomawa,
Ibrahim ne yake cewa wai ina Uwargidan gidan na ta,shiga ne bangan ta,ba tun da na shigo,
Tana dakin ta tana hadiyan rai,,tun shigowar matan nan na dazun,
Umma ce take wanan maganar wace tun farko jefi, jefi, take saka masu baki a hirar su,,
Wasu mata sun shigo ne gidan nan yau, Ibrahim ya tambaya a cikin mamaki,
Mama ta bashi amsa da cewa wasu fitsararun mata yan zamani wai sun zo neman auren dan uwaka
Sunzo ne kamun kafa a gurin uwar ku, akan dan uwan ka ya so su da aure,
Wai da gaske kike ne mama Ibrahim din yake tambayan ta zancen cikin son jin gaskiya,a gurin ta,
Sun zo mana inji Umma ta bashi amsa a takaice cikin gadara abin da yasa shi yarda ke nan,
Ibrahim yace ikon Allah bako a,gidan nan ba don da ina gida,sai nai masu tsiya,da cin mutunci wallahi,
Don basu da mutunci ku biyo mutun har gida cikin iyalin sa, don rashin ta ido, ga matar mutum
agida,
Ai dama shi mijin mace hudu ne don haka haka kulba dade kulba jima, sai kishiya ta shigo gidan na watarana
Namiji fa mijin mace hudu ne don may zakuyi mamaki don ance ana son sa,
Mama ta juya inda Umma take tana cewa da yake ke an maki guda hudun da zaki ce wai mata hudu zasu shigo
Ai koda ma sun shigo din sai dai su,bi baya, in ma har sun shigo din, ke nan,
Fitowa nayi a lokacin da naji sun kaca may da hira Hamza tankar bai gurin saboda yadda yake jin bacin rai, tare dashi,
Fitowa na Idanuwan su a kaina sai a lokaci Asmau tace min a cikin zolaya Uwargida uwargida,
Ashe yau amarya tazo ziyara ne gidan nan bama nan,
Nai mata yar guntuwar tsuki ina cewa gashi ko bata samay ku ba sai ni aka sama a gidan nai maku kara ai,
Tace da kyau uwar gida nan san kinfi da nan ai don haka nake kara sonki sosai
Sannun ku da,zuwa nace yayin da na juya inda su yaya suke a zaune, tare da uwayen su
Nace cikin kallon fuskan shi yaya, akawo ma abincin ka a nan ne,?
Ibrahim yace dakin kyauta sai ma muci a tare ke nan tunda na shigo na juya don na dauko abincin,
Asmau takata cewa ashe kwanan nan zamu sha kallo ke nan, gidan nan,
Nace gawa kuma ga amaryan taki ko ? Ita da take bakuwar ku
Don ni kin saba kallona ai ba yau ba kin sanni tun ina yar karama,
Mama tace Ibrahim wasu irin tika tikan matane fa wai su yan mata ba kunya basuji suka,shigo muna, kamar uwayen mata,
Amma mama sunyi arziki ban gidan nan wallahi dana ci masu mutunci yau,Ibrahim din ya ce hakana,
Sai lokacin Umma tai magana tana cewa kaci masu mutunci a kan may don sunce kawai suna son dan uwan ka, ?
May ye a cikin aure in har ya,shirya yin auren, shi,,
Wa ?
Umma ni !
Hamza ya juyo a gagauce Yana tambayan Umma din,,
Aure yanzu haba Umma haba, sai kace wanda bai san ciwon kan shi ba don Allah Umma kibar zancen nan ,
Wallahi abin yana matukar bata min sosai idan na tuna wai,ni halima zata bude baki tace Tana Sona da aure sosai,
Ai, dole kafadi hakan tunda matarka rayuwan ta ya baci, kai ko baka,son bacin ran yar gwal din ka, a gidan nan
Ni abin yana bani mamaki don ban san lokacin da yarinyar ga,tai wani wayyon kishi ba haka, har da nuna bacin ran ta tashige daki Tana hadiyan Rai, it's daya,
Gurin randar ruwan mu na nufa ina zuba ruwa a butocin mu don safe,Amma Ina jin zancen sure Umma yadda take magana zafi zafi,
Kai haba Umma kishi ai dole ne ga mace tayi koda kuwa bata,son mijin ta,
Balle auren so irin na yaya da Aisha,
Asma,u tai farat tance, wani so kuma, auren hadi har yaushe ne so ya shiga tsakanin su,
Ke dai fada min inji Umma tacewa Asmau din da tai magana haka,
Ibrahim kasan halin yayana indai taga ci a guri bata da wasa da,wurin, mama hafsi ta fadi hakan was Ibrahim,
Duk ina jin su amma,sai harkokina nake cikin kwanciyan hankali batare da nuna,wani damuwa ba,.
Sai dai na ciki na ciki don wani irin tukuki nake ji a raina amma,sai na,daure na shanye a fill,
Mata haka tirka tirka,don raini hankali kuzowa mutane wai ku aure kuke so a kama,maku,
Inji mama hafsi ta Mike Tana fada Tana tafiya ita kadai,,,,,,,
****** ********** ******
Kwance take kanta a sama, Tana kallon silindin dakin da suke a cikin sa,
Yanzu kina ganin cewa wanan matar zata yarda ki aure ma,ta,da Bicky kewa Lima wanna tambayan,
Nice fa Lima, ta,dan bugi gaban ta kadan da hannayen ta,
. Tace na,fada maki sai na,aure yaron nan tunda ina,son shi,
Dayar tace ni wallahi kin san matar shi ta ban sha,awa yar yarinya karama kamar da ita kamar yar Fulani,
Gaskiya,sun dace da junan su don daidai auren su ke nan ,
Shi gashi matashi itama yar matashi dagwas da ita abinta, ga tsabta ji dakinta tas dashi har ma tsakar gidan duk a gyare,
Bicky idan kina,maganan yarinyar nan kina bata min rai sosai wallahi raina yana matukar baci don ban son na,ma,tuna cewa wai Hamze yana da mata a gida,,
Ta wani koma ragwab a saman kujera ta zube ta wani lumshe idanuwan ta a hankali tana sauke numfashin ta,,
Can zuwa dan wani lokaci ta,ware idanuwan ta, ta wani sauke ajiyan zuciya
Tace wallahi Bicky Hamze irin mazan da nake so ne a,rayuwa na,
Don komai nashi yayi min wallahi guy din ya hadu ya hadu, bazaki gane bane,
Ko ya hadu yaya zakiyi dashi tunda ba sa,ar yin ki bane shi
Ki tunafa irin yadda maza masu kudi ke nuna kwadayin su a kan ki,
Amma zaki zo ki wani mutu son yaro karamin wanda ko sa,an kannen ki bai kai ba,a,shekaru ai sai ki saka aimu na dariya wallahi,
Bicky ba zaki gane bane bazaki gane ba tunda ba choice din ki bane ke,
Bari kiji ko nawane zan iya kashewa akan wanan guy din don kawai na samu na mallake shi ya zama nawa, kuma no kadai,
Yaya zakiyi da matar tashi zan barta ta zauna man as pending, su zauna a gidan gado ita da yan uwa,suyi ta,fama ni kuma zan jaye shi mu koma wani guri can daban,
Na mantar da Shi kowa nashi da komai nashi Kinga baby masu saka muna ido ke nan
Ki dai yi a hankali don kada kwabar ki tai ruwa inji Bicky
Don tun farko kin dai ji abinda aka fada muna a kan shi,
Ki manta,da,wanan zancen nasan yadda zan bullowa zancen ai,
Hmmm ni nasan guy din yana da kyau kuma zai iya wadatar dake don nasan yana daga cikin abinda yasa kike son shi don ganin shi karfafa da kikayi ko ?
Tai wani kara lumshe idanuwan ta tana murmushi can ta,ware su tai ajiyan zuciya tace
Ashe kin fara fahinta ta ke nan Bicky kin dai san bai da,wani abinda zai bani ,idan ba,wanan harka ba
Don haka idan ba zaki tayani faiting ba to ki daina damuna akan zancen kawai,
Lima tasake cewa idan ma har baki son zancen to ki yi shiru ki daina,accusing din zance haka da yawa please,
Don ni ina,so kuma zanyi don nai niya, hakan,
Allah dai ya taimaka inji ita Bicky din ta juya taba Lima din baya wace ta mayar da sunan ta halima tun tana primary, sunan kuma yabita sosai yanzu, Tana mishon bat da musulmi da sunan,

****** ********* ******
Da,farko yasha jinin jikin shi sosai akan abinda yake zato ko tsanmanin zan yi,
Amma,ga,mamakin shi duk abinda,na,saba yi mai ban fasa,ba don haka yadan rage damuwar shi,
Ya shigo gida a lokacin ni har na kwanta inda ya,samay ni har na kwanta don nagaji sosai a lokacin,
Sai dai ina a cikin shirina na kwanciya kamar yadda na saba a kullun,
Naji ya,dawo daga,wankan da,ya,tafi duk a lokacin nan,ina lafe ban yarda na motsa ba,
Don kada ya gane cewa ai idanuwana biyu banyi barci ba,
Bayan ya gama komai na,shirin kwanciya naji ya hawo saman gadon a hankali,
Matsowa yayi zuwa jikina naji ya,matsoni gam a jikin shi ya fara sauke dan ajiyan zuciya,
Har a lokacin ban bude idanuwa na,ba,da,suke a rintse gam,ba
Wani ajiyan zuciyar ya sauke kamar ta mamaki batare da ya,sakeni ba daga jikin shi,
Cikin muryan shi mai sanyi naji ya ce min nasan yau ranki a,bace yake a gidan nan Humaira, ?
Nasan an maki cin fuska wanda zai sa ki zaci ko ki dauke ni a matsayin wanda ke can wani gari yana barikancin sa, da cin amnan ki,
Tare da matan banza kadangarun bariki ina yadda raina ke so, da su tun da har sun Kai ga biyoni gida you,
Sai a lokacin na bude idanuwana da sukai min nauyi tare da dan sauke ajiyan zuciya a hankali,
A cikin natsuwa na, kalle shi tare da sauke wani lalausar murmushi mai ma,ana, don kawai na gusar mai da zargin shi a kaina,,
Na soma magana da cewa nasan da cewa shi aure nufin Allah ne musali, mu diyan hausawa zan iya cewa mun gaji zama da kishiyoyi don duk macen da tai aure tasan cewa mace hudu Allah ya kindanyawa mazan mu musulmai su aura
Don haka banga wani abin

Download complete TXT · Novel page