Sarautar Mata

Chapter 34 of 94

da zai sani tayar da hankalina ba yadda kuke zato,
Kamar yanda Asmau tace auren hadi ne nida kai, ba bu so ko kauna a cikin sa,,
Sai dai zaman rufawa juna asiri ina ga ai zaifi kuyi auren ku da wacce ke sonka, don ni kaga auren hadine, aikai mun dakai,
Na sani babu abi da zai farantawa Umma rai a gidan nan kamar taga ka yo wata mace mai haihuwa da kuma wayewa yar masu hannu da shuni, ba, irina diyar talkawa ba,,
Shiiii naji ya yi min tankar yadda ake tsayar da yaro daga barna ko wani abu,
Bana son jin zance auren hadin nan dakike ta nanatawa a tsakanin mu,
Idan ma da farko muna zaton aure ne na hadi akai muna ai yanzu ni dake mun san mu wuce zancen wai hada mu akayi,
Don ni kinfiye min ko mai yanzu a duniya ina alfahari da kasancewar ki a matsayin mata,ta aduk inda naje duk inda na samu kaina,
Humaira ke mace ce da duk wani namiji ke fata da burin mallaka irinki a rayuwan shi,
Don may zan tsaya nayi sakaci da baiwa da kyautar da Allah yai min,
Hakkuri, tsabta, tattali, ni,ima uwa uba sanin ya kamata duk Allah ya,wadataki dasu,
A,rayuwa ke uwace da ko wani namiji zaiyi fatan malakarwa diyan shi irin ta,
Zance su Lima, kuma da suka zo wanan ki barni dasu don wallahi idan kin yarda dani rantsuwa musulmi daya ce,
Babu wani zance maka mancin abinda tazo muna dashi gidan nan a tsakanin mu,
To amma fa nasan cewa ba lalai ne ki yarda da zance na ba don sun riga sun saka muna zargi a tsakanin mu ko,
Wani irin sanyi naji a raina don ko ba komai Hamza ya gwada min ya damu da damuwata a fili,
Ban san lokacin da na daga hannaye na na makale shi a jikina na ba kamar yadda shima yake rungumay dani,
Nace ni matar ka ce yaya ka daina rantse min don ina kasa da kai akoda yaushe,
Jikin Hamza naji ya dauki rawa tankar wanda yasha wani irin tsumi ganin haka nai amfani da,damar na kara narke mai a jikin shi,
Nafara dan sarafa shi a hankali a nutse kamar yadda nasan yafi bukata,daga gare ni,,
Hakan ne ya ban damar mallake abinda dama can mallakata ce, sai yafara sake sambatu yana fadar maganganu akan Lima da Umma,
Hannuna na,sa na toshe mai baki daga haka muka nausa wata uwar duniyan baka jin komai a dakin sai gurnanin mu, da ya rude dakin,
Yana makale dani a jikin shi bayan komai ya lafa a tsakanin mu, ya samu natsuwa irin wanda nake son gani a gare shi,
Gyaran murya naji ya soma yi abinda yasani kara lafewa a saman cheast din shi ke nan,
Humaira, zan so ace mun bar gidan nan idan da, da hali mun canza wani guri badon komai ba sai don mu samu kwanciyan hankali daga fitinar Umma,
Haba yaya, ni fitinar Umma a gare ni tankara wani karin haske ne a,rayuwata,
Don kayi ba daidai ba an maka fada ai ya zama gyara kayan kane,
Ka ga ba zai zama lafi ba,
Wani irin sanyi Hamza ya kara ji a ranshi, tare da sauke numfashin ajiyar zuciya a hankali,
Yace hakane Humaira a hankali to amma kuma gyaran har ta kai ana son yiwa kwanciyan hankali na illi mai yawa, irin haka
Ya kamata duk abinda za,ayi ayi adalci a cikin don bawa kowa hakkinsa,
Naso ace Umma ta rike ki tankar yar ta data haifa komai za,ayi a gidan nan ai muna adalci akanshi,
Don fahintar da tayi cewa ina sonki Humaira kuma ina kaunarki shi yakara saka Umma nuna maki wanan halaiyar, ta tsana da kiyayya,
Umma sam, taki la,akarin cewa zamanki tare dani shine kwanciyan hankalina da su ma,Kan su,
Don haka na roke ki ina kuma kara jaddada maki cewa ina son ki Humaira kuma ina kaunarki fiye da duk wani abinda na mallaka a duniya,
Yanzu ni fatana da buri na shine na samu wani dama wanda zan nuna maki irin halarcin da kike gwada min na tabbatar maki da cewa ni cikakken da namijine ,
A hankali na kai hannuwana a,saman kirjin shi ina dan shafawa a hankali nace ni ko hakan ma na,gode
Don ka gwada min cewa kai dane na halak, don ka fahinci cewa wani irin zama nake a gidan nan wanda a kullun kokari kake koda a,sace ne ka,ga farin cikina, duk da matsin da Umma take muna akai,
Sai yai murmushi alamar yaji dadin zance na har a cikin ran shi ,,,

****** ********** ******
Mama hafsi a kullun cikin kwantar min da hankali take a gidan mu, sai rarashina take tana nuna min yadda zan zauna dama ko wacece a duniya,
Wanda hakan ba,wani bakon al,amari bane a guri na
Don, da shi na bude idanuwana, a gidan baba Mudi, shi, naga mahaifiyata, tana yi watau hakkuri ke nan,
Don haka idan ban gaji hakkuri ba ai naiwa Allah buttulci ke nan,
Duk wata diya ta gari da irin tarbiyan uwar ta take zuwa gidan mijinta dashi
Dashi kuma zata zauna da mutanen da Allah ya hada ta zama dasu,
Don haka tankar ban san Umma tana sake habaicin ta ba sai harkokina nake a cikin sakin raina,
Nakuma ji dadin shawaran mama hafsi a gare night at Don takara min haske masu yawa a rayuwata,
Umma ta matsawa Hamza akan sai ya, saka mata fankan da Lima ta bada kudi a samata a dakin ta,
Dole badon yaso ba ya sayo fankan mai hadawa yazo ya saka mata a dakin ta,,
Ranan zokiji zance a wurin Umma kamar tsokana,
Yi da mai arziki ka,dangwali arziki yafi zama da matsiyaci kullun tsiya,
Aini wanan tuntube ne da arziki har a gida,a kofan dakina,
Ina zaune a cikin harkan tsiya Allah ya turo min arziki har tsakiyar dakina,
Zama da yan arziki irin wanan har za ai min bakin ciki a hanani cin arziki ina kallo,
Mama Hafsi ne tagaji da habsicin Umma din, tabata ansa da cewa
Shi mutum in yana a,raye ba a debe ran arziki agare shi ,sai randa ya mutu,
Hakan yasa Umma yin shiru don tasan idan ta matsa abin ba,zai masu dadi ba,
Mama tace kuda dama ai,guri kwadayi yake mutuwa ,
Wanan dalili yasa Mama Hafsi cewa zata koma garin su yafi mata zaman da Umma
Don halin yar uwarta yana matukar bata tsoro yanzu,
Kwata kwata Umma ta canza a yadda ta San halin ya da farko, ta rasa gane may be damun rayuwan ta haka,
Hankali yaran Umma ya tashi don sun san cewa mama,hafsi tana da,matukar amfani a,gare su,
Ranan ba karamin tashin hankali akayi ba a gidan daga karshe yaran maza su suka yanke shawaran cewa zasu gyarawa mama dakin dake a,cikin gidan daga can gefen daki,na ta zauna a ciki
Tunda tace Bata shiga inuwar kafira ta sha iskan fan Kan da kafira ta saka masu a daki,
Amma said Umma tace ai kyauta tabata ba rokon ta tayi ba itace ta Bata, ganin ta bijere sosai yasa
Umma tai nadaman batawa yar uwarta rai da tayi duk da ba da ita, ta ke sake zancen ta ba dani take yi amma sai ta juya zancen cewa ita Umma kewa gori,
Ba bata lokaci aka gyarawa mama dakin taba da kudi aka sayo mata katifa dan madaidai ci tasaka tare da wasu yan tarkace,
Bayan hankali ya kwanta mama hafsi ta zaunan da yaran yar uwar nata ta maza, ta basu shawara da su fara sana,a don tallafawa rayuwan su,
Ta ware masu kudade daga cikin kudin ta taba su tace kuma tabasu ne kyauta Allah yasa wa kowa albarka a nashi,
Mata kuma hardani a ciki taba mu kyatan dubu goma goma tace tana son kowa tayi amfani da shi gurin tallafawa rayuwan ta,
Wanan abin da Mama hafsi tayi yasa Umma tai sanyi sosai don bata taba tsamani halarci yar uwar na ta ya kai haka ba,
Don Bata bakin ciki ga kyautatawa diyan Umma din Tana daukan su tankar itace ta haifi abinta,
Ga, Sabbin fankan daki guda biyu na sama, aka sayo mamata saka guda a dakin ta guda a namu dakin,
Wanan abin ya kawo muna kwanciyar hankali a gidan don mama ta kashe bakin Umma murus sai gida ya koma kamar farko,
Na kaiwa Ummi na dubu uku daga cikin kudina,
Nace ta dan juya itama ta dan fara sayar da dan wani abu, a gida Don income yadan din ga shigo mata,
Naba su mama Saude dari biyar biyar Atika yar iyawa nan ta fara cewa ikon Allah a she kwanciyan hankali da,sanin ya kamata yana a gidan tallakawa bamu sani ba,
Muna can muna na bakar wahalan banza said anmuna wulakanci a bamu,
Mama Saude ta fito tana cewa tau kaza aci a goge baki yau kuma dari biyar ya tsone maki ido har kika manta da komai,
Fadin gaskiya nayi koda kuwa zaki ji haushina ne dole ce a fadi gaskiya,
Ummi na tana dakin ta bata fito ba take sauraren su cewa take a,ran ta kan ku dai ake ji, ku karata can gasu gada,
An sayo wa Ummina,su kayan yaji da sugar ta dan kulla ana saye a cikin gida,
Wanan ne ya ke yankewa mata zaman banza yin sana,a a gida komai kan kan tar sana,a, zai kawo maki dauki ta hanyoyi da dama,în har kina Dan juya naira,

****** ********** ******
Sosai Hamza ya mayar da hankalin shi akan aikin gonar shi, Wanda zan iya cewa noman zamani, ne yakeyi, Mai amfani da taki irin na zamani da fasaha,
Idan ya fits tun safe baya dawowa gidan said da yamma list zai dawo a gajiye ,
Inda kafin ya dawo ya Sami na Dora Mai ruwan zafi don ya watsa ya watsake,
Zai Sami abinci Mai zafi yana jiran shi tare da kunun aya ko zobo Mai sanyi ya Kora,
You ma ya dawo kamar kullun a gajiye ya iso gidan duk da gajiyan da yadawo dashi gurin su
Umma yake fara zuwa ya gaida su tare da masu Yaya gida jin yan matsalolin su,
A kwance ya samu Umma wace take Dan dukule,
Yananayi yanuna yau Umma din batajin dadin jikinta,
Idanuwan shi kar akan mahaifiyata tashi inda yake tambayan ta cikin nuna damuwar Shi gare ta,
Umma lafiya like kwance a cikin wanna yanayin haka,ga yamma tayi,
Cikin dan marairaicewa take cewa you Ina dan jin kamar masasara yana son kamani ne,
Nai yai mata sannu tare da cewa bari ya dan watsa ruwa yafita ya Sami mata magani chemist,
Ruwan Sha na fara gabatar mashi said Kuma ruwan wanka, bayan yafito ya shirts take me min Humaira idan da Dan kudi a gurin ki kibani na Dan sawo was Umma magani tasha wai bata jin dadin jikinta ta you,
Da sauri nace subbahanallahi ai ban sani ba don naga Bata Dade da shigowa gidan ba,
Inda nake dan tara cinikin fridge Dina na bude na kirgo kudi dubu days na bashi ya fita,
Sai da nai sallah Don lokaci yayi na fita zuwa gurin,Umma don na duba jikin nata,
Da kyat Umma take karba min amma Sai na sa a raina zafin ciwone yasa ta bata iya ansawa sosai,,
Na dan dauki lokaci zaune a dakin daga gefe guda Ina mai mata sannu da jiki, Sai taga dama take karba min sannun da nake mata din,
Hamza da Ibrahim suka shigo dakin dauke da ledar magani a hannun su,
Ibrahim yana cewa Umma jikin ne Kuma yau yadan tabu Ashe,?
Nan sukai mata sannu tare da fatan Allah ya bata lafiya, ta amsa da Amin sai da tasha magani ta Dan Sami sauki masasaran ya dan sauka,
Duk muna dakin Mama Hafsi Tana dan mata magana da ta Dan tashi ta zauna ko hankalin yaranta zai kwanta,
Da kyat ta dan cewa mama Tana son Dan mikewa ne tane tayi sallah,
Nan nafita da sauri na fara aje mata takalman ta daga kofa, na zuba ruwa a but na aje mata daga kofa ,
Ganin ta kewaya zuwa bayi zatayi alwala idan tafito yasani komawa dakina,
Har tafito tashiga daki zata fara sallah ne yaran suka fito shi Hamza sai ya,yo dakin mu,
Abinci ya zauna yaci sai Kuma ya buge da waya da abokan karatun shi, ya dauki lokaci Yana kwance rigingine Yana wayan shi hankali a kwance,
Ina zaune Nima a kasan daga gurin kanshi idan baka luraba zaka iya, cewa a cinya Kan shi yake
Saboda zaman gab gab da mukayi da junan mu a lokacin,
Sai ga Sa,a datu, autar Umma ta shigo dakin take cewa yayan mu Umman mu tace na Kira ka,,
Yace Sa,a datu har yanzu baki San cewa kin girma bane baki iya sallama ba idan Zaki shigo guri,
Tajuya cikin zunburo bakin wai, an mata fada don may zai mata fada haka,
Tana shiga daki uwar taga yanayin ta take cewa,
May ya faru halqn may akayine wai?
Cikin turo baki gaba na shagwaba take cewa wait dan nashiga dakin Yana kwance a jiki Aisha shine ya Koro ni,
Bai wani Bata lokaci ba najin Umma tana Kiran shi yamike zuwa gurin karba Kiran nata,
Ai yana shiga Umma ta hau a lokacin, jiran shigowa shi kawai take yi,
Yashigo da sallama Yana cewa Umma sannu ya jikin naki, ya daina ko ?
Kai Mara kunya kamar want wanda ya dami da jin jikin nawa, kakoma can gurin wanna yarinyar da tai gadon iya hilla har tagaji,
Itace kawai damuwar ka a yanzu a gidan nan Sam baka san damuwata ba ballet ciwona ya damay ki,
Kana can gindin mace Tana Maka kisisina da kutungwila irin wanda ta gada ga uwar ta,
Shine har zaka want Koro min yarinyar don ta katse ma jin dadin da kakeyi ko, ?
Da sauri ya juya ya dan kalli Sa,adatun cikin mamaki, yace ita sa,a,din want abu tagane Ina yi,
Ina ways ta samu munayi da Kabir tashigo dakin ba sallama nai mata fadan takoyi shiga guri da sallama,
Ai sai ka koma gurin wace tafini daraja da kima idan ta sallamo ka sai kazo ka gwada min yadda zan kara Shan maganin,
Innalillahi wa,inna alaihim raji,unm ya furta yace Umma abinci naci sai ga wani abokina ya bugo min waya,,
Nan dai Umma take Mai fada a cikin kakausar murya abinda ya sa duk jikin shi yai sanyi,
Daga inda nake tsaye Ina jin may Umma ke fadawa don haka Nasha kwana na juya baya zuwa dakina,
Zaune nake a dakin nawa nai tagumi da hannu bibiyu don tuna laifin da naima Umma a rayuwana ko zan gane don abin yai tsauri da yawa tsakani na d ita,
Najin an dago labulen dakin nawa abinda ya haddasa min
Saurin dago kaina kenan da jajayen idanuwa na da suka rine sukai ja jajirdon bacin Rai,,




ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
SEENABU
👑 SARAUTAR MATA 👑
2⃣9⃣

RABBANA, LA TUZIGH QULUBANA, BA,DA, IDDZZI, HADAITANA , WA HAB LANA MIN LADUNKA RAHMATAN INNAKA ANT AL WAHHAB,,,,,,,


ZAINAB IDRIS MAKAWA


DON ALLAH YAN UWA INA BARAN ADDU,A AGARE KU KU TAIMAKENI KU TAYANI ROKON ALLAH AKAN ABINDA NAKE BUKATA A GURIN UBANGIJIN MU ALLAH SUBBAHANAHU WATA,ALLAH,,,,



Wasa wasa yanzu anfi sati Umma tana kwance masasaran yaki tsayawa har ya kaita a kwance, sosai,
Yar uwar ta mama hafsi ke faman dawainiya da rashin lafiyan Umma din, sai ni dake faman dafe dafe a gidan
Naka shiga dakin fiye da a kirga don na gaida Umma na Kuma duba lafiyan yata, nakuma wanke kayan da tai amfani dasu,
Ranan da ta cika sati Daya a ranan na shiga daki na Sami duk yaran Umma suna a kanta, tana cewa sanyi take ji su rufa mata bargo, sai rawan dari take daga kwance,
In tsaye daga gurin da nake ina nazarin abinda ke damuwar ta gashi sai faman dirka mata magani akeyi
Ina mai kura mata ido, sai naji suna cewa wai, za a Kira Mai chemist yai mata allura,
Ni ko na fahinci wani abu a jikin nata sai dai Ina tsoron magana suce ban San komai ba, na jawa uwar su mugun ciwo nake mata fata,
Daga inda nake tsaye daga bayan su nace amma yaya da kiran wanan mutumin ai da kawai akai Umma asibiti gurin doctor ya dubata zai fi wanan, kaura da kai din da ake tayi a gida da ita,
Duk kan su suka juyo inda nake suna masu sako min idanuwan su, gaba dayan su
Kaji malamar asibiti fa aida sai ki dubata idan har kin gane wani abune, jibrin ne yai wanan magana,
Mama da Yaya hamza suke cewa tun da kukaji Aisha tai wanan maganan akwai abinda take hasashe ke nan,
Ibrahim yake cewa, cikin, tambayana Aisha don Allah kokin fahici wani abin ne suna masu sako idanuwan su a kaina,
Cikin harshe turanci wanda zance duk gidan nan ko shi Hamza din bai taba sani na iya turan ci ba haka nake masu bayani, komai,
Don ina gudun yi da hausa Umma taji tace ina mata mugun fata ne,
Jikin su gaba daya yai la,asar suke cewa gaskiya ya kamata subi shawara na don bai kamata ace sun aje ta a gida ana magani daban ciwo daban,
Fita Hamza din yayi zuwa wani dan lokaci sai gashi ya shigo gidan a cikin, saurin shi tun a kofa yake kiran mama,
Duk muka yo waje don son jin may zai fada tunda kowa a tashe hankalin mu yake,
Ance mai baki bai iya ciwo ba don Umma ta wani koma ragwab da ita duk tafita hayacin ta, sai nishi take daya daya
Mama ga mota a,waje mu tafi ko?
Ina shiga dakin naga yadda idanuwan ta suka juye sukai, weak a lokaci guda,
Da sauri har ina ture Ibrahim na karasa bakin gadon a gaban Umma na kamo hannun ta ina dan massage din hannun nata a hankali har wani dan lokaci,
Sai naji

Download complete TXT · Novel page