Showing 102001 words to 105000 words out of 299981 words

Chapter 35 - Sarautar Mata By Makawa

04 Dec 2025

17634

mata health, good, good, yana da kyau hakan
Muna so mata suyi karatu sosai don taimakawa sauran matan mu nagida da basu son fitowa asibiti,
Kamar wanan maman taki sai da jiki ya kashe ta agida akazo muna da ita nan
Ai wallahi ta kuru don da sai dai wani ba ita ba a yadda akazo muna da ita ,
Mama Hafsi daga inda take zaune tace malama ai ita wanan yarinyar taba da shawaran mu wuto da ita asibiti
Don duba mai ke damun ta, saboda yadda jikin nata yai tsanani sosai,
Tace shine amfani karatun at list a dan samu wanda ya dan san wani abu zai iya taimakawa, ko, yaya ne, yafi a zauna dip gaba daya, a gida,
A daidai wanan lokacin da take bayani su Yaya Hamza suka iso gurin sukai tsatsaye cirko cirko suna sauraren bayanin da matar ke yi,
Tai setting din wani ruwa bayan taima Umma din allurai sai ta saka mata,
Ta juya inda nake tana cewa idan kinga yana rushing zaki iya rage mata don kada ya sakar mata da reaction,
Ta juya ta wuce sai mama hafsi tai magana bayan wucewan nurse din take cewa
Aikuwa munga alamar hakan don dai yarinyar nan ta taimake mu sosai kan wanan rashin lafiyan na yaya,
Ibrahim yake tambaya may yafarune wai,
Sai mama take mai bayanin yadda akayi da nurse har cire ruwan da nayi,
Ya juya gurin Umma yana cewa wallahi Umma Aisha babbace don dazu na hadu da abokina dake karatu a makarantar su yake cewa tana cikin dal8ban da ake ji dasu a school din nasu don first class ce ita,
Umma tai wani mayde baki tana cewa ai sai ka bari har takare karatun sai ka yabeta ko,
Hamza daga inda yake sai murmushi yake don yasan Umma bazata taba yabo na ba idai da bakn ta ne,
Muna gurin na hangi wasu mata tafe sunyi kwalliya sunyi kyau dasu hannun dayar, matar, dauke da basket din abinci,
Dayar kuma tana dauke dayaro karami a kafadar ta sai wani saurayi a bayan su dauke da flask din ruwan zafi da ledojin kayan tea a ciki sai na fruit,
Tsayawa sukayi inda gadon farko yake a dakin suna tambaya mutanen dake saman gadon,
Sai sukai masu nune da hannu a gurin da muke, direct gurin mu suka nufo,
Sai da suka zo gab damune na gane cewa su Hindatu ne ashe, tare da kannen ta suka shigo duba jikin Umma,
Nan aka shiga gaisawa da su ana tambayan ya jikin Umma din tare da mata fatan Allah ya bata lafiya,
Daga karshe suka gabatar muna da abincin da suka shigo dashi, a matsayin na dubiya,
Godiya muke masu tare da fatan Allah bar zumunci, tare,
Su waye Zarah take tambaya kasa kasa don son jin kosu waye su Hindatu din, don ganin su yan gayu da tayi,
Mama Hafsi ce ta cabe zancen da cewa mutanen arzikin Aisha ne suka zo ai kinga ita suka,sani,
Zancen yaiwa Umma zafi tana son cewa mutanen data ne, shi suka sani, bani ba ga kuma alluran da akai mata yana hawa mata kai,
Sai kuma ga yar yauri tashigo su ma har su uku suke cewa sunzo gidan mu ake fada mata shine tace bari su wuto direct asibitin,
Zarah take cewa yanzu ashe ita Aisha tasan mutanen arzikine haka take hurda dasu,
Hira,muke a tsakanin mu na,sake freely zakace bani bace ke yar hira har da dariya na a,cikin friends dina,
Bayan tafiyan yan gidan su,Zarah ta bude abincin da Anty Hindatu takawo muna,sai kamshi ke tashi cikin dakin duk ya,bure ko ina, a dakin
Mama hafsi ce ganin za ,a cinye abincin ni ina can tare da baki tai min tayi nazo naci abincin
Nace Mama sai da naci abinci na,fito daga gida a koshe na ke,
Ba wani kunya nan suka bude baki a gaban su hindu suka cinye abincin tas, akarshe ma suka bude wanda nazo dashi suna mai wani kallon wullakanci,
Sai mama ce ta shiga rigar arzikin su, take cewa su rufe mana anjima basai ankawo wani ba ai zai masu rana,
Ranan mama ta hana ni yin wani girkin dare tace aiki yai min yawa na huta hakanan,
Da dare dana dawo gida yaya ibrahim ya sayo kayan shayi yace na hada muna shi mu kasha muka kwanta, ni dasu,
Da dare bayan mun kwantane Yaya Hamza yake ce min,
Humaira zan so ace idan kin gama wanan karatun kici gaba da yin wani sai dai ina gudun fitanar Umma akan hakan,
Don ko wanan din da yaya aka samu ta yarda dashi balle a dauko wani,
Allah dai ya hore min nabar gidan nan kin ga alokacin duk abinda muka ga dama sai muyi abin mu a can babu sa idon kowa a kan mu,
Nace cikin gyara kwanciya na kadan Yaya aiko wanan din ma na gode don yai min rana,
Badon Allah ya hadani da gwarzon namiji irinka ba wanda yasan yakamata a rayuwa aida bankai ga haka ba, ma,
Da, har yanzu ina nan zaune ba wani karuwa a rayuwa na irin haka ni gaskiya ko a,wanan din ma nagode gaskiya,,
Ya rugumoni zuwa jikin shi yafara dan shafana hakan yasani gane cewa yau da dan karfin shi stress ya rage mai,
****** ********** ******
Kwanan Umma uku a asibiti aka samu sallama suka dawo gida take gida ya rude da yan shigowa gayar da Umma daga makwanta,
Yan uwan su baban su hamza maza biyu suka zo suna fadan ba,a fada masu ba,
Umma bayan sun wuce tace muna fukai afada maku kuzo kuga yadda nake ku karasa ni,
Cikin masu shigowa har da matan gidan mu, watau su Ummina,
Umma tana wani cika tana batsarwa wai ita tana da su a,rai tana jin haushin su a zuciyar ta,
Suma basu dade ba suka fito zasu tafi Atika tace su shiga mana su gayar da ni a dakina,
Duk da sun san cewa gulmace amma sun bi shawarata din sun shigo dakin nawa,
Wanda zance wanan ne karo na farko da su mamana suka shigo dakina
Don ko sun shigo iyakar su zauna awaje don haka shine karon su nabiyu da suka shigo gidan ina a cikin sa,
Sunyi, matukar mamaki kwarai dan ganin dakina a yadda basu zata ba don sun samu dakin acan acan duk da ba, wasu kayan zamani bane a cikin sa
Amma yadda yake a gyare yasa yana daukan ido, gwanin sha,awa
Don ga gadon yasha gyara ga kujera na tsab ga akwatina daga gefe na aza mai wani dan kyale fari sai fridge dina daga kofan shigowa dakin,
Ledan kasan dakin yana kyali sosai a lokaci don yasha guga kuma gashi babu yaran da zasu bata shi da dadti,
Mun gaisa dasu sukai min ya maijiki kamshin dakin yai masu dadi sosai,
Nace bari na basu sabon zobon danayi da rana yai sanyi sosai mama saude tace nabari idan sun tafi zasu aiko Aina ta karba masu,
Mama dai bata ce komai ba tun shigar su don kamar ma a takure take a dakin dole ce ma tasata shigowa dakin,
Hamza da yashigo ya tsaya rusunne daga kofa suka gaisa da su cikin girmamawa da mutunci,
Abinda yasa Atika cewa a lokacin da suka fito kai jama,a watau dai ana zaton wuta a makera sai a samay shi a masaka,
Gidan masu kudi babu tsabta ba tarbiya amma ga gidan tallakawa duk an samu abinda ake zaton samu gidan masu arziki,,
Wai ashe sunje gaida Kubura shine suka samu gidan da dakinta kaca kaca kuma mijin da yazo ya samay su shine ya wuce kamar bai gansu ba ita Atikar ce tai mashi magana cewa, baigane su bane yana tafiya yace nagane ku ma,na,
Suka fito ran su a bace kan irin yadda yai masu ita mama saude ce ma ta fara magana sai da Ummi tai mata magana cewa ba girman ki bane yaya,
Kowa da halinsa ake zama dashi tunda baiwa yar mu wullakanci ba kuma tana zaune lafiya da abinta banga abin bacin rai ga mutumin daba kai ka haife shi kai mai tarbiya ba,
Shine sukai shiru ba wanda ya kara tayar da zancen har suka dawo gida,
To shine fa ashe maganan na a cikin rayuwan Atika sai yau take sakewa mama saude habaici, akan shi,
Mama saude zatai magana Ummi take ce mata ai idan daji bai gama cin wuta ba yaya ba,aiwa kututure barka ko,?
Atika tagane inda zancen Ummi ya nufa kuma ita Ummi din tagane cewa badon Allah Atika ta yabi gidana ba don sheri ne kawai da kissa irin na kishiya,
Ai itama yaranta zasuyi aure aga inda suka dosa sai sukai shiru gaba daya,
Lokacin da Aina ta shigo karban zobon su Hamza na gurin don haka sai yafita waje shagon su ya shiga yadauko omo clean ya saka masu aleda da sabulun wanki,
Ranan kan habaici saida a kai fada da Mama Saude da Atika a gidan don ta kaita makura,
Da Baba yazo ya samu ana wanan jidalin yake tambayan ba,asi shine Atika tai tsagal tana cewa zance nake ina cewa ashe kwanciyan hankali da samun wadatan zuci yana ga auren tallakan da akai gudu shine yaya tace wai ita nake sakewa habaici,
Shi kuma Baba sai yace dama ai hakan gaskiyane ba karya bane,
Yau kin fara ganin gaskiyan maganata ke nan Saude,
Naso hada zuria da wanan yaron Hamza a rayuwata don gani da sanin halin yaron
Amma sai kikai min tutu arai keda yar ki kukayi kokarin watsa min kasa a idon jama,an da na gaiyato a gidan nan,
Allah ne ya rufa min asiri wanan yarinyar yar albarka ta share min hawaye na,
Yanzu don gaskiya tafara halinta shine zakice wai kada a fadi don may,
Ai dama kowa yasai rariya yasan dole zatayi yoyo indon wanan zaben tumun daren da kukayi ke da yar ki babu komai a cikin sa sai tarin bakin ciki da takaici don ko alhakina ya ishe ku,
Cikin kuka mama Saude tace lalai duniya malam yau kuma yar Agwaice abin yabo a bakin ka,
Ba hakana bane Saude dama ni yar Agwai ban dauketa komai ba sai "ya kamar kowa a gidan nan dama ai can sherin kune kuka,dauki tsana kusawa yar mutane,
Ummi dake dakin ta taji abin yaki karewa ta fito tana cewa haba malam haba kubar wanan zancen haka dan Allah,
Hakan ba girman ku bane dakai da yaya ko ina duniya ko bana nan Aisha yar kuce don gaba dayan ku bazamu manta da halarcin da kukai mata ba na zaman ta gurin ku,
Ta juya gurin mama saude tace Yaya don Allah ki bar maganar nan aishi maso habaici dama maso fada ne,
Atika daga kofan kitchen tace nidai na fadi gaskiya don dama daci ne gare shi,
Da kyat Ummi ta rarashi mamata shiga dakin ya a cikin bacin rai don zancen atika da mijin su ya bata mata rai sosai,
****** ********** ******
Gidan yai muna tsauri saboda ga,damana tai nisa duk kudin Hamza ya watsa su a gona yana duban abinda zai girba idan lokaci yayi,
Don kwanciyar Umma ya jawo masu rashi kudi a hannun su,
Mun wayi gari dan kamun da zamu dama kunu a gidan yadan buwaye mu,
Gashi babu abincin da zan dafa muna da rana muci,
Hamza ya shiga dakin gurin Umma yana tambayar ta ko akwai dan kudi a hannun ta sai ta ara, mashi, har ya,samu ya mayar mata,
Amma sai Umma ta kyankyashe kasa tace batada ko kobo a hannun ta ya tafi gurin matar shi ai tana sana,a ta ara mashi,
Cikin dan marairaice murya yace Umma bata dashi ne dana karba a gurin ta ai,
Wani kallo Umma ta watso mai mai nuna owo kana goyon bayan matar ka ko,?
Cikin daga harshe Umma tace duk sana,an da take a gidan nan za,a ce wai bata da kudi a gurin ta,
Hamza ya kara cewa bata dashi ne Umma ni na san da hakan,
Daidai nan mama tafitowa daga dakinta taji wanan hayaniyan takaraso zuwa gurin,
Hamza yace Umma wallahi duk kudin danai ta amfani dasu a,sibitii gurin Humaira na karbe su,
Sai duk suka watso mai idanuwan su yace, wallahi mama a,gurin ta nai ta karba don su sauran yan uwana, sun ce min bazan samu ko sisi a gurin su, ba
Duk wanda ma na tambaya bana jin mai dadi a,gurin shi,
Shiru Umma din tayi don jin dan nata ya rantse cewa a,gurina ya karbi kudaden da ya kashe asibiti,
Juyawa tayi sai mama tace duk kudaden da akasamu a asibiti fa yaya ?
Bazaki bayar a rufa asiri dashi ba may ye amfanin samu a gida,
Daki, tashiga ta dauko dari biyar ta miko mashi a wullakance,
Yakarba yana godiya, yace zai je ya samo dan abinda za,a karya dashi,
Bai fita ba daki ya shigo ya zauna da dari biyar din a hannun shi yana dan juyawa a hankali,
Nafahinci cewa bazasu ishe shiba shiyasa ya rasa yadda zaiyi da daribiyar din, na hannun shi,
Dubu dayan da ya rage min a dakin dama kayan zobo zan saya dasu nadauko na mika mai nace ga wanan sai ka kara ko,
Yadago idanuwan shi da,su kai ja ya sauke su a kaina yana cewa cikin wani sanyin murya,
Wanan kuma fa nace cinikin da nasamu ne jiya da wanda ke a,gurina dama kayan zobo naso saye dasu,
Idan kin bani ke damay zaki hada zobon naki dashi ?
Tunda ba,wasu kudi a hannun ki,
Nace Alkah zai rufa min asiri insha Allahu na samu nayi ko da kadan ne,
Ya karbi kudin daga hannuna badon ya so ba ya mike yana ce min bari nadan fita nagani Humaira,
Zuwa wani lokaci yadawo da leda ya auno yar shimkafa a ciki da cefane yakawo min yana cewa nayi na rana kafin anjima yagani ko za,a samu na yamma
Acikin dabaran mu na mata nai tuwon shikafa na hada da saurwn gari na daure sai yakai muna har da na yamma,
Haka rayuwan wanan damanan tazo muna sai na,dan kulla cinikin dan zobon da kakaran nonon da nakeyi mu sai wasu abubuwa don har shagon namu ya kare,
Kubura tazo gida yini taba da kudi a,sayo mata idomie ta dafa don wai bazata iya cin abincin da aka,dafa a gida ba,shinkafa da wake,
Anya kuwa za,a samu abu a shagwan Hamza din nan don duk kwanakin nan duk abinda aka aika sai suce babu shi ina ga sun lashe,
Tawani juywa tana kallon mama din tace wallahi mun ta aikawa hatta maggi cewa suke wai babu shi,
Tsiya takai tsiya ke nan tunda har shagon ya kare ai nasan karya ta kare ke nan,
Ita yar agwai din fa to mama ?
Wanan mai gadon zurfin cikin aibazata taba fadin komai ba ita,
Sai dai taita wahala a ciki takare haka na a wahalce,
Wai shine da Baba yaso turani cikin wanan wahalan boni yaci har na lalace,
Ai har yanzi shi bai san da haka ba don kwanaki yadan bada Omo akawo muna shine munafukar nan kecewa wai suna kina,aure gidan mai kudine amma yar Agwai tafiki sa,an daki da kwanciyan hankali,
Halan maman Aina ko ?
Ta tambaya cikin canza fuskanta tare kufulowa,
Ita mana dawa zaiyi wanan zance in ba itaba mai kwarmaton banza,
Wallahi mama sai nayi maganin wanan munufukar matan agidan nan don bazan kara bata fuska ba dani take zancen,
Tamike tare da yafa dan yalalon gyalen da ta yafo a kanta tana cewa ina zuwa,
Zaune nake ina raba abinci shimkafa da wake da mai da yaji nadafa sai kamshi man dana,soya yake tashi naji sallaman Kubura,
A zatona ta shigo gaida Umma ce taji labarin bata da lafiya nai mata iso a cikin washe bakin naga yar uwata,
Nace tazo su gaisa da Umma tana kwance daga kofan dakin ta,
Cikin wani yatsuna duk da ta ramay ta fada yangan nan da kaudi irin nata yana nan kamar baya,
Mun koma dakina da ita,na gabatar mata da abinci na aje mata zobo da ruwan sanyi,
Nai mamaki kwarai danaga ta sake jiki ta kwashi abincin dana saka mata din,
Tana shan zobo Hamza ya shigo cikin daga labule yana ganin ta ya dan daure yace a kubura kece a gidan namu tace eh,
Nashigo ne naga yar Agwai tunda ka hanata zuwa gurina,
Ban hanata ba idan tace zata ai zan barta ko na kaita,
So kada kiga laifina bani na hana taba,
Ta kurbe zobon ta mike tana cewa zata koma tana gida sai da yamma zaya tafi don yini ta,shigo nai mataalkawarin insha Allahi zan shigo gurin ta,
Tana shiga gida mama ke cewa ke ina kuma kika,shige tun dazun,
Tai gyatsa tace gidan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login