Sarautar Mata

Chapter 5 of 94

yanzu wai naje asibiti gobe a dubani don wahalan yai min yawa,
Inda Aisha take tana mayar da kayan ta ga jakar ta,
Ina ta samay su haka ita kuma ?
Fatima tacee nima ai tambayan da nai mata ke nan yanzu haka,
Sai uwar take fada mai bayanin da Aisha din tai mata akan kudin,
Kudin yaron ya kara dubawa yake cewa ai wanan basu isheki ba bari na,dauko wanda nake tarawa nasayi keke dashi,
A,a Babangida kabar shi kawai naje da,wanan din ai zai isheni sayan kati, dashi,
Shima gurin kayan shi ya nufa ya ciro nashi kudin ya kirga ya mika mata ta raba kudin biyu
Ta mayar mai da,saura tana mai sawa yaran albarka ,
Tace wa Aisha ta miko mata plate tasawa kishiyoyin ta dan naman da,yaron ya sayo mata taci,
Haba mama dan wanan abin shine zaki raba ke may zakici a ciki abinda baida yawa,
Bari dai na basu ai suma suna bamu idan sun samu,
Haka al,adan gidan nasu yake duk wanda yadan samu abu komai zaman shi kasan sai yabawa sauran abokan zama sun sa albarka su ma,
Hakane yaje dan kara kawo masu zaman lafiya a gidan don suna kokari ganin sun danne kishin su,
Daga waje aka daga labulen dakin maigidan ne a tsaye yana,saye da wando sai babban riga da ya aza a sama kawai babu yar ciki,
Lokaci daya ya kare masu kallon yana mamakin irin yadda ko yaushe take zama da diyan ta kamar abokan ta ,
Ya kika kara jin jikin naki ?
Ya tambaye ta a cikin yanayin son kulawa gare ta ,
Ta amsa a cikin dan matse fuska iri yadda mace maiciki idan tana da kishiya take amsawa,
Daga gurin da Aisha take, zaune gefen uwar take cewa Baba sannu da,dawowa,
A,dakile ya ansa mata batare da,wani sakin fuska ba ,
Daga gefe Yusuf ke ce mai Baba sannu da,dawowa,
A,a Babangida andawo yaya shagon naku ba matsalan komai ko ?
Yaron yadan gyara,yana cewa ba komai Baba kuma,muna,samun aiki sosai a gurin,
Tau ka,dai mayar da hankali ga,aikin ka,don ka,samu ka iya,abinda ya kai ka,
Yana kokarin sake labulen dakin ne Fatima ke cewa malam,
Gobe idan Allah ya kaimu ina son zuwa asibiti awo ,
Awo Fati gaskiya ban da kudin zuwa asibiti don kinga yanzu ba,wani Kasuwa sosai karfin hali kawai nake ina maneji,
Kabar kudin ka izzinin ka kawai nake nema ni,
Yace Allah ya kaimu gobe lafiya yajuya yafita daga dakin ,
Summa suka bishi da kallo kowa da irin abinda yake kiyastawa a ran shi daga,cikin su,,,

****** ********* ******
A cikin wata irin kasalaliyar murya mai nuna yanayin shi ya canza yake magana a lookacin,
Haba baby ki bari mu dan kara time mana tun yanzu zaki ce zaki wuce gida ni da na zaci cewa zamuyi till down ne a gurin party,
Cikin bude baki a cikin sauri take cewa Haba sweetie na baka son na kara fitowa ne yau din ma fa,dabara nayi a gida don ba,ranan zuwa islamiya bane,
Badon yaso ba yaja motan zuwa wani shago inda yai mata sayayyan abubuwan tabaa alashe ,
A hankali yake jan motan kamar wanda nai son yin tuki,
Hannun shi guda ya mika zuwa jikin ta inda ya dan fara shafan ta
Da sauri ta dago kai tana cewa haba sweetie kabari mana don Allah kaga kana tuki ne fa,
Au to na tsayar da tukin ke nan ko ya ce a cikin wata irin murya irin na mayaudaran maza,
Ganin yana son yai galaba a kanta yasa Kubura sauri dan ture shi daga jikin ta tana cewa haba dear ban son haka gaskiya kaga wani yana iya ganin mu a hakan a fadawa mahaifana,
Fushi yayi yanu baiji dadin hakan ba da tai mashi,
Har suka kawo gurin da ya,dauke ta ya tsayar da motar a gurin,
Sai a lokacin ya furzar da iskan takaici daga bakin shi yace a kasalance sai yaushe kuma ke nan baby na, ?
Tace a lokacin da take kokarin bude motar ta,sako kafan ta daya daga waje,
Tace sai wani lokacin tamikaa,hannun ta tajawo hijjab din ta daga bayann motan shi ta zumbula abinta kamar wata ustaziya,
Tajuyo inda yake zaune yana akallon ta acikin wani yanayi tace zan tafi sai mun kara haduwa kuma,
Nan ta bude motar tafita zuciyar ta fes dashi don ta hada abubuwa da dama,
Ta samu saurayi kamar mansur gashi kuma sunje gun fati ,sun cashe kamar yadda take so, gakuma kayan kwadai da,ak,siya mata,

A daidai shiga daga cikin gida suka hade da mahaifinta wanda yabita da kallo yana cewa Gwagona sai yanzu akadawo ne ko,
Murmushi tayi daga can ta,cikin gida muryan mahaifiyarta ce ke cewa ai na tura Aishi ta,kirata tadawo tana cewa ai tasamu tana that's
Uwar Hamza aiki shiyasa bata,dawo ba tun dazun,
Sosai yaji dadi hakan inda yake saka mata albarka ta,shige ciki simi simi da ita,
Bayan tashiga mahaifiyar ta take tambayan ta mutanen gidaan take cewa duk suna lafiya,
Tafaki idon uwar nata ta kwabe kayan jikinta don gudun kada tafahinci irin kaya da ta, fita dasu
Shi,
Hamza wanda yake zaune daga shagon shi ya hango dawowan Kubura a lokacin,
Cikin mamakin inda tafito a wanan lokacin da daren nan haka,
Bayan yan mintina ya aika kiranta sai ta aiko mashi da cewa a gajiye take bazata fito ba,
Sam ya rasa may yasa Kuburan ta canza mai yanzu don kwata kwata, bata da lokacin shi,
Abu gudane idan ya aika mata da abin makulasa zata karba ta lashe ko kuma idan tana son wani abin kwadayi zata iya aiko mashi, da bukatun ta,
Abin ya fara damun shi a,rayuwa saboda ya fara dan tuhumar ta,don ganin iri sauyin rayuwan dake tare da ita,
Saboda ta waye irin wayen da baza,a ce diyar gidan malam mudi bace ita,
Shidai yasan ada can baya bata da wani suturu irin haka amma yanzu ta zama wata yar gayu gaba daya,
Gashi ta nuna a fili cewa ita yanzu tafi karffn shi don bata da lokacin shi samm,
Ya tunkari Umma Rabi da zancen abinda ke damun shi a rai indz take cewa ita ma ta gane wanan sauyi ga KUBURA din,
Uwar shi tafi kowa bukatan akan aiyi wanan hadin tsakanin yan gidan mala.
Don haka ta,samu mahaifan Hamza ta turasu zuwa zancen don a,tsayar masu da,matsaya,
Kamar yadda malam Mudi yayi alkawari hakan akayi don anyi baiko a tsakkanim su kowa ya sheda cewa Kubura ta a matsayin kamay Hamza ne a garri,,
Wanan baikon shi ya tayarwa Kubura da hankali sosai inda har ta kasa boye bacin ranta ta ,soma nunawa a fili wai bata son Hamza yanzu,
A gareta abin kunyane a ce kamarr ta wai zata auri Hamza dan gidan tallakawa talas,
Marasa galihu agari da gurin dagi tallakawa masu neman abinda zasu ci wa ran su a rana,
Ganin tanuna bata so ita kuma mama Saude yanzu irin abin duniya da yar nata ke shigo dasu gida yafara bude mata idanuwan ta,
Don haka tafara goyawa yar ta baya akan bata son wanan hadin itama don yanzu Kubura ba matar Hamza bace,
Kubar ba matar tallaka bace kalman da mama saude take yawan fada ke nan a tsakar gida a gaban su Fatima da Atika kishiyoyin ta,
Shiko malam Mudi ya dage akan cewa sai anyi wanan auren ko basu so
Don shi haka kawai Allah ya,dora mai son wanan yaron Hamza a ranshi don irin kwazon shi,,,



Don Allah muyi hakkuri da,wanan ba yawa sai mun hadu a na gaba da fatan za,a rike min amanata kamar kullu na gode da taimakon ku a gareni,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU👑SARAUTAR MATA👑
0⃣5⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

RABBIG GAFIRLI WAL WALIDAYYA WAHARHAMHU KAMA RABBA YANIY SAGEERAH 👏👏


Tun daqon Ummin ta daga asibiti hankalin Aisha yake a tashe don jin irin bayanin da Fatima take wa maigidan ta,
Akan cewa da likita yayi wai sai tayi scanning a cikin don tantance lafitan baby saboda suna ganin kamar a gilmay cikin yake mata,
Don inhar tunanen su gaskiya ne to bazata iya haihuwa da kanta ba kenan sai sun mata aiki,
Gaba daya yarinyar duk da karancin shekarunta ta,fahinci may hakan yake nufi ga zancen,
Sulale jiki tayi daga gidan zuwa gidan mama Rahana yar maahaifiyar nata, tafiya take a cikin tashin hankali bata ko ganin gaban ta,
Ta isa gidan acikin tashin hankali don Mama Rahana tana ganin ta take cewa lafiya dai nagan ki a haka kuka ?
Dakin ta tafada tazube a kasa gefen kujera ta fara rusa kuka a hankali,
Abinda yai matukar tayarwa mama Rahana da hankali ke nan,
Acikin dan daga murya take cewa ki daina wanan kukan ki fada min may ke faruwa ne wai ?
Ki natsu kifada min kukan may kike haka wai,
Aisha bata boye mata komai ba take fada mata irin abin da taji Ummin ta tana fadawa maigidan ta akan zancen cikin dake a jikin ta,,
Shiru Mama Rahana tayi, inda ta dago kai tana kallon Aishan acikin tausayawa,,
Tace cikin sanyi murya tauki daina wanan kukan haka don idan har kin tayar da hankalin ki Ummin ki zata kara shiga tashin hankali ne sosai,
Don kinga kowa da irin tashi kaddaran rayuwa, wanan ba,wani zancen tayar da hankali bane don su likitocin ai sun san irin dabara da zasuyi mata,
Kuma ta haife shi lafiya da yardan Allah don haka maza ki share hawayen ki ki shiga yi mata addua, Allah ya sauke ta lafiya,
A hankali taji sanyin maganan da mama Rahana tai mata don haka tafara dan share hawayen dake a fuskan ta da habar hijab din ta,
Nan mama Rahana tashiga kwantarwa da Aisha hankali da kawo mata yan musalai daidai fahintar ta,
Batai wani dadewa ba tai sallama da mama Rahana inda mama Rahanan take ce mata zata shigo gidan taji yadda za,ayi zancen zuwa asibitin,

****** ********** ******
Daida shiga gidajen su ta hango Hamza dake dawowa daga gona yana dauke da buhu da wasu, yan kayayyaki,
Da sauri ta nufi gurinshi ta karbi dan kullin buhun dake a hannun shi,
Duk da kokarin hana yarinyar da yayi amma,sai daa ta karba
Tana shiga gidan ta samu Umma Rabi tana wanke wanken kwanonin abincin su ,
Sallaman ta yasa Umma Rabi din saurin dago kanta tana kallon Aisha din,
A,a kece ?
Karaso mana
Kofan dakin Umma Rabi tanufa ta aje buhun dake a hannun nata,
Taso ta karbi aikin amma,sai taga cewa har ta karasa din saura kadan shi kuma take daurayewa,
Ta gaida Umma din ta juya ta fita a kofan shigowa suka hade da HAMZA yana kokarin aje yar keken shi a gefen ginan daki,
Yace tau Ai na gode kin ji da ki tsaya na baki akwai sauran rake yana nan a,daki,
Cikin murmushi wanda yadan sa dimple din ta dan lotsawa kadan tace haba kabar shi kawai na gode bata tsaya ba tafita ta nufi gidan su,

Shigowan ta gida yai daidai da Uwar nata ta,dan fito waje, tun a kofa ta kafe yarinyar da idanuwa don son fahintar wani abu daga idanuwan ta,,
Hawaye ne suka kara ciko mata a idanuwan ta Fatima ta kawar da kanta tankar bata gan ta ba,
Ina kika shige ne haka wai Aisha ?
Idanun yarinyar taga sunyi dan hulu hulu alamar kuka da tayi sun baiyyana a fuskan ta kadan,
ina kika shiga nace hakan,
A hankali tace gidan mama Rahana na tafi amma ban dade ba acan,
Ki shiga ki dauko abincin ki a daki kici kada yai sanyi da yawa ,
Har zata shiga dakin take cewa Mama tace tana tafe dan anjima,

****** ********* ******
Yana fitowa daga daki dauke da yar ledar gyada soyayya a hannun shi don ya bata sai yaga bata gurin ta tafi ko,
Umma tace ai ta tafi bazata karba ba indai Ai ce narasa gane irin rayuwar yarinyar nan don bata da sabo,
Hamza dake kokarin zamma a kasa cikin turbanya yace rayuwan ta daban ne dana,sauran yaran gidan duk da kuwa a cikin su ta tashi amma sam bata irin halaiyan yaran,
Dan jingina jikin shi yayi da,bango yayin da,Umma tazo ta shige ta gaban shi zuwa cikin dakin ta,
Tafito dauke da kwanon abinci wanda ta dafa masu shimkafa da wake da mai da yaji, acikin sa,
Tace a lokacin da take zama, daga kofan ta, ai ni ina,son hali irin na,yaro wandda yasan darajan kashi tun yana katami ammaa kaga ita,ta gurin nan naka sai munyi daga da ita sosai a gidan nan,
Murmushi yayi don jin dadin furucin ta a akan cewa KUBURA ta gurin shi ce,
Umma ai duk yanzu kurciya ne bari zatayi nan gaba ai,
Uhummm Allah dai ya kyauta dan nan amma gaskiya babana yarinyar nan al,amarin ta ya fara bani tsoro,
Hamza yadan lumshe idanuwan shi a hankali tare tare da dan tunanen wasu abubuwa a,ranshi,
Mama Rahana kamar yadda tai alkawari ta shigon gurin yar uwar nata don ji daga,bakin ta,
Cikin daga hankali Fatima take bawa yar uwar ta bayanin da likita yai mata a kan cikin ta da take dauke dashi wanda,ake zargin ya,samu matsala,
Mama Rahana tace Allah ya sauwa ka yanzu ki kwantar da hankalinki sai muje wani asibitin muji may zasu ce a akkai,,
Don haka ki kwantar da hankali kin ga hankalin Aisha duk a tashe yake tana zaton wani abu,
Ta amsa a hanakali da cewa tau, yaya insha Allah zan bar komai a gurin Allah tace dadai yafi maki,

****** ********* ******
Zaune KUBURA take a saman gadon mahaifiyar ta tana karatun wanni littafin hausa mai sunna wayasan gobe wallafan wata shahararra marubuciyar littafin hausa SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA,
Yar gurin Atika ce ta shigo dakin tana cewa Kubura Hamza yana waje wai na kiraki,
Tadago kai fuska a,yatsune take cewa yana ina ?
Yarinyar ta amsa mata da cewa yana daga kofan gidan nan,
Jeki ce mai ban samun fitowa tace, cikin jan yar guntuwar tsoki,,
Yarinyar ta juya ta,fita jim kadan sai gata ta,dawo tace wai yace nace kizo don Allah sako ne zai baki kawai,
Ai sai tai wani hargago yarinyar da wani irin daga murya inda tai wuf ta,fice daga dakin,
A zaure suka hadu da malam Mudi yake cewa kin fada mata yaron yana waje, ko,
Yarinyar ta take mayar mai da cewa, ai takoreni da ihu wai na bata guri na bace mata da gani,
A harzuke ya shiga cikin gidan tare da kwadawa Kubura kira cikin tashin hankkali,
Ita ma din dai a gigice ta fito daga dakin tana cewa na,am Baba,
Ba,a fada maki cewa yaron nan Hamza yana kofa yana jiran ki ba,,
Ciciki ta amsa da an fada min Malam Mudi ya ce to sai kika shanya shiko,
Shiru tayi yace zaki wuce ki fata, tun ranki bai baci ba yanzu,
Daki ta koma inda ta saka kuka wai ita bazata fita ba gurin Hamza din,
Mama Saude wace shigowan ta ke nan daga bandaki, ta soma cewa ke may yafarune wai may akai maki,
Tace ba Baba bane yake son takura min cewa wai sai na tafi gurin Hamza a waje,
Ni wallahi mama banyin wanan hadin da Baba ke son yi min nidai na fadi wallahi bazan yi ba
Bari na fita na gayawa Hamza din daga yau kadda ya kara zuwa gurina da sunan wai yana sona,
Haka ta saka hijjab din ta zuwa gurin da Hamza din yake zaune saman dan dakalin da ke kofan gidan,
Hamza yana zaune yana dan bubuga kafan shi a kasa a hankali saboda irin yadda yake dan ji a ranshi,
Tafito fuuu da ita tana cewa kai wake ne ma Hamza ne ko wa,
Da maki yadago kai yana kallon ta don jin abinda tace mai,
Yadan murmusa tare da dan dago kan shi ya dan kalleta yace tau fa yau kuma sunana ma baki sani ba Kubura,
Hamza din dai nake ba wani ba
Ranki shi dade barka da fitowa
Tana tsaye kerere a gaban sa tace ai ba fitowan arziki nayi ba tace a zuci,
Idan da sabo yaci a ce hamza din ya saba i yanzu don haka din yanzu shine halaiyar ta gare shi,
Sam bata kallon shi da dara bata nuna mai wani almar kauna ko kadan,
Sam duk wanan abin da takeyi sai ya dan saka Hamza dan murmushi,
Don yasan cewa dama can a rashin ji ta tashi daga kurciyar ta,
Don haka yasan cewa wanan irin halaiyar nata idan sunyi aure duk daina su zata yi,
Don haka hankalin shi a kwance yake don ya riga da ya nasa a ranshi cewa zai mata, tarbiya irin wanda shima mahaifiyar shi tai masu,
Fuska a daure tace malam nazone naji lafiyan kirana da kakeyi wai,
Yace ba ko gaisuwa Khadija, tace gaisuwa a nawa za,a yita ,?
Hmmm Khadija da ki gaishe ni da kada ki gaisheni duk daya a gareni ,
Don watarana muna tare dake a daki daya don haka kinga bazan damu da gaisuwan a yanzu ba,
Ta dago idanuwanta ta re da kara tabe fuskanta ta dube shi tace cikin wata murya ,
Au dama kazo ne ka karanta min wanan,
Idan har wanan ya kawo ka zan koma daga ciki don ina da abinyi aciki,
Mikewa yayi daga gurin da yake a zaune da farko yace dama zuwa nayi naga lafiyar amarya ta kawai kuma na gani tunda kina lafiya Alhamdullahi zaki iya shigewa, ai,
Ta dan gyara tsayuwar ta tace kana so yin wasa dani Hamza,
To tsaya kaji idan ma har mafarki kake to ka farka don ni,
Nafi karfin dan talkawa irin ka,wallahi kaje can ka,nemi daidai da kai zaifi maka alheri,
Don idan har kai rigimar kai kan ka idan ba kaiba ka zata kwabewa,
Don ni KUBURA nafi karfi dan tallaka iri ka don tsayawa dakai a,gareni barnan suna ne sosai,
So dan Allah malam daga yau ka da ka kara zuwa kofan gidan nan da sunan

Download complete TXT · Novel page