Sarautar Mata

Chapter 42 of 94

a,sukwane suka kawo da mai mashin din hankalin ta a tashe tana cewa, wai da gaske ne yayan mu yadawo,
Ta na ganin shi tafada mashi tana kuka tana cewa yayan mu munzaci mun rasaka ke nan,
Allah mun gode maka da kadawo muna da dan uwan mu gida lafiya,,
Sai kuka,suka kara sakewa haka mutane yan uwa da abokan arziki sukai ta kai kawo gurin shigowa har wanda bamu sani ba sunzo, taya mu murnan dawowan shi,
Wasu suna cewa wai akaini asibiti amma sai mutumin da suka tare yace a,barni a gida damuwar da na,shiga ne yake sauka,
Sai bayan kowa ya rage agidan an watse sai mu yan gida,da,baki koshi sai da aka,rufe kofan gidan,
Sai su Baba Madu baba Mudi, da Baba Liman sai mutumin ya fara bayani kamar haka da cewa,
Ku godewa Allah daya nufe shi da,dawo cikin ku bai halaka ba ko canza akida,
Da,safiya na,samay shi a hanya shine ina ganin yanayin shi nasan ba daidai yake ba sai aka,saka,salati a,dakin baki daya,.
Nan dai yai masu bayani akan yadda suka shirya zai fadi shida su Mansur,,
Don gudun kada, agane cewa daga gurin su ya,fito shima hamza din yana cikin class akakira shi ana sheda mai baiyyanar Hamza din cikin jin dadi da,sowan su suka,ruda guri da ihu eh anganshi anaganshi,,
Abin waya kafin wani lokaci labari yakai wa su Lima cewa anga Hamza dama a under beli take don haka sai tai wani irin ihu da murnan jin dadi sosai,
Nan take tafara planning din yadda zata dawo dashi gareta kafin iyayyen shi su dauke mai hankali gare ta,
Take ta shiga kullawa da,warwarewan yadda abin zai tafi mata daidai,

****** ********** ******
An natsu kowa yana sauren bayanin mutumin da,sadudan yadda mace shu,uma zataiwa dan adam irin wanan kuli haka,
Hamza ya rarafa daga,inda yake zaune zuwa gaban Umma cikin kuka yake cewa,
Don Allah Umma da mama ku gafarce ni kuyi hakkuri ku yafe min laifin da nai maku
Umma fushin ku a gareni zai iya janyo min fadawa acikin masifan da yafi wanan nan,
Umma ta ce cikin kuka yanzu babana abinda kai muna a rayuwar ka ka kyauta ke nan kasayar da abincin mu da duk abinda ka malaka a gidan ka,sayar kabi mace macen ma kafira guzuma ba,sa,ar yin ka,ba,
Mama ta cabe zancen da cewa Hamza mu bamu rike ka,da komai ba godiyan mu ga,Allah shine yakwato muna kai daga hannun wanan macuciyar matar kafira mai mugun aniya,
Sam baka da laifi garemu tun da mun san cewa bayin kanka bane mun san ka mun san halinka Hamza don may zamu dora maka laifin dabakai kayi shi ba,
Kowa gurin ya dauka da cewa wanan gaskiya gaskiya ne kika fada ,
Suka juya gurin Umma suna cewa boyar Allah don Allah dai kiyi hakkuri kiyafewa wanan yaron kamar yadda yar uwar ki tafadi ,
Umma ta,share hawaye tace nasan da haka bacin rai ne yai min yawa har na,fadi haka amma nayafe maka Hamza duk abinda kai mun,
Sun kai wani lokaci a gurin sai dai duk abinda akeyi hamza hankalin shi ya gur8n yar matarshi don yaganta ko zai ji sanyi a ranshi, irin yadda yake son ganin ta a rayuwan shi,
Bayan Anfito daga sallah isha,i aka taru a tsakar gidan mu Liman Baba Madu bakon da yazo da Hamza sai Baba Mudi makwabci su,
Liman ya bude taro da,addu,a tare da karayiwa Allah godiya da,sauran mutanen da suka taimaka a kan wanan al,amari,,
Yakara yi mai nasiha akan riko mai karfi ga ibada ta yadda zai tsamo kan shi daga fitinar zamani,
Nan dai ya nuna mai matukar kuskuren shi dayayi wurin yin sakaci da,addu,oi, saboda neman kariya ga,hadduran zamani,
Malam Liman yaci gaba da bayani cewa, yanzu bukatar da muke son ku dashi shine,
Har nan da sati uku kada ku bari yayi arba da,wanan matar don kun san bazata barshi ba haka banza don dole ta canza sallon yaudaran ta,
Don haka za mu roki Allah duk abinda tazo dashi ya koma mata zamu tafi dashi can guri na mu zauna har wa,adin da aka kidanya na,sati uku cur ya cika kinga alokacin duk wani hari da zata kawo mai, ba zai yi tasiri a kansa ba,
Mama ta cabe zancen da cewa insha Allahu, zanyi kokarin ganin haka
Anyi sallama da juna inda aka kai bakon masauki ya sauka sai tururuwa mutane keyi shigowa muna barka da arziki har cikin dare,
Duk da musan cewa wasu don gulma ke kawo su a lokacin bawai don Allah sukeyi ba,
A hankali, ya mike daga cikin taron ya nufi, hanyar shiga dakina ,
A,lokacin, ina zaune a kasa gefen kujeran dakina, saman salaya na na dan kifa kaina a saman kujera hannu na daya yana rike da tasbaha ina ja a hankali,
Sam ban yi tsanmanin shigowan shi dakin ba a lokaci sai ganin shi nayi ya fada min bakin shi dauke da sallama,,
A hankali na,dago kai na da dube shi saudaya sai kuma,na,sada kaina tare da amsa sallama shi,
Ya samu guri ya zauna, saman kujerar danake zaune ta gefen, guda,
Humaira ke ma kina fushi da nine kuma, kamar Umma,
Nadan kada kaina a,hankali tare da cewa ,a,a ba hakana bane don dai na ganka da mutane, ne,
Huci yayi mai fitar da iskan zafi daga bakin shi, tare da furzo iska yana furta Subbahanallah cikin wani yanayi, na bacin rai,
Shiru dakin yayi ba mai magana daga cikin mu sai karan fankan sama dake tashi,
Mikewa nayi tsab daga gurin da,nake zaune na dauko mai ruwa nazo gaban shi na durkusa na,aje mai plate din ruwan gaban shi ya,duka,ya,dauka naje na,dago sai muka,shaki, numfashin junan mu a lokaci guda
Take, kowan mu ya shiga reacting, don shock din da mujaji a zukatan mu lokaci guda,
Da sauri ya dago kai dai dai lokacin dani ma na dago nawa sai muka kara,arba,dashi nasada kaina kasa,a hankali tare da dan kokarin dagawa daga gurin da nake tsugun ne a gaban shi,
Rugumoni yayi da hannayen shi bibiyu gaba daya zuwa jikin shi inda ya,dan mike don yaji dadi rugumoni da kayau,
Noke kaina nayi ina kuka don wani irin bakin ciki da takaicin dake sukar ziciyana,
Kamar mai rada naji muryan shi daidai kunnuwa na yana,magana cewa, Aisha kiyi hakkuri dani ba wai yin kaina,bane don da ban maki haka,ba arayuwan na,
Wanan matar ta cuce ni Aisha ta,raunana min rayuwana,sosai a duniyan nan,
Tabar min babban tabo wanda bacewar sa sai gyaran Allah,
Hawayen, shi naji suna digo min a fuska na a hankali tare da jin yadda sautin kukan shi ke tashi yana kara sakani cikin tashin hankali mara misaltuwa,
Nan mukai kukan mu mai isar mu ba wanda ke iya bawa wani hakkuri a cikin mi kowa da abinda ke ci mai ziciya a cikin mu,
A hankali muka zauna daga bakin gadon inda yadan dago min haba na yana cewa
Nasan duk abinda zan fadi ba zai yi tasiri a gunki ba dan zargi mai girma ya,shiga tsakanin mu dake a yanzu don haka,
Dai ina mai kara baki hakuri akan kiyi hakuri ki yafe min don Allah akan yadda wanan matar ta yaudari rayuwana ta,cuta mim ta ida ban taba zato,,
Muryan su Baba Liman ce ta,ratsa kunnuwar mu yana cewa,Hamza kazo mu tafi, kada wani ya,san zancen kum,
Dole ba don ya so ba ya dan kura min idanuwan zuwa dan lokaci kadan ya mike yana mai sharan hawaye yabar dakin cikin sauri zuciyar shi tana mai tafasa,
Ina kwance a kan gadona tun bayan fitan Hamza a,dakin wanda ya fita ya barni a cikin kunar rai, wanda bai missaltuwa,
Ina kwance nai kuka nai tunane har baya kirguwa a lokacin,
Ina gurin tun ina jin hayani har na daina jiyo motsi wanda hakan na nufin bakin sun fita harda Hamza a cikin su,,
Kara lafewa nayi saman dan gadon katakona ina hadiyan rai don abubuwan da sukai min yawa a lokacin,
Mama hafsi ce naji muryan ta a kaina tana cewa ki tashi ki kulle kofan ki Aisha don dare yayi sosai kowa zai shige,
A zatona ta juya ta tafi ina mikewa don bin umurnin ta naji tana cewa kiyi hakkuri gaduk irin jarabawan da kika gani a rayuwan ki, komai mukkadari ne ga bawa,
Inda anyi hakkuri sai a cinye jerabawan abin ya wuce don wanan yana daga cikin kaddarorin ku gaba daya,
Adduan, mu yake mubukata don samun kubuta daga sherin shedan,,
Kinyi kokari sosai sai dai ki kara don Allah da kikeyi a kansa ya sanar maki,
Haka kuma jama,an dake gani Aisha kowa yasan kinyi hakkuri a kan wannan al,amarin,
Don har yau baki nuna gazawan ki ba akan zancen, don haka ki kara dagewa,kin ji yar nan Allah ya,baki ikon cinye wanan jerabawan a hankali na amsa da,amin, ya Allah mama,
Kullun kalaman su mamana, yana min yawo a zuciya ta tare da kara kwantar min da hankali,

****** ********** ******
Kwana biyu da,dawo wan shi gida, komai yadan fara lafawa don mutane sun dan lafa da shigowa ganin shi, saboda an fada masu cewa ya koma makaranta ko,
Ina tsaye gurin igiyar shayin kayan mu ina kokarin shaya tufafina da na wanke naga mata kwatsan a tsakar gidan mu babu ko sallama har su uku,
Har sun shigo daidai tsakiyan gida babu ko sallama balle muji shigowar su,
Zarah wace tazo tun da safe yini tana tsaye daga kofa tana gyara shikafa a cikin dan wani faranti a a hannun ta,
Ganin katan mata tsakar gida kamar kabila ashe su, don sauran biyun ma ba gyale a tare da su, ga,gashin doki sun aza a kan su,,
Dayar ce ta dan daura dankawali ta yafa wani dan yalalon gyale iya kafadan ta kawai,
Zarah tace a,a kuka wani dabia ne wanan shigowa gida babu sallama hakan nan, don ita a zaton ta masu zuwa ganin Hamza ne,
O sorry bami yi maku sallama ba ko sai kowan mu ya kyale su,
Nidai na sheda su don na san su saboda zuwanda suka taba yi har sau biyu, take nafara jifan su da abinda yazo min a rai,
Addu,a nake daga cikin bakina ina fadar La,illah ha,ilallah mohammadan rasullillah,,
Nazo gaban su na gilma ina dauke da bokitina na silver danake wanki a hannu na suna tsaye a tsakar gida cirko cirko,
Ina mama suna, tambayan Zarah, wace take masu kallon mamaki,
Sam ban kula su ba sai aikina nakeyi hankali a kwance, batare da na kula dasu ba,
Sai dai a can kasan zuciyata kamar na sheka da gudu nake jin kaina,
Jin suna neman Umma yasa su Asma,u da mama hafsi wace ke dayan dakin fitowa, waje da sauri don ganin ko su waye
Sai muryan ta mukaji tana cewa tau munafuka may kuma ya kara kawo ku gidan mu, wani sabon sherin kikazo muna dashi ke nan, kuma,
Tau ta,Allah ba taku ba don Allah yafiku yafi sherin ku muguwa muna fukai kawai,
Look mama mu ba wanan ne ya kawo mu ba mun zone don naga mijina naga halin da yake ciki, ? Saboda munji labarin cewa angan shi
Tashin hankali wai fadawa sarki gaiyya, don kalman mijina da ta ambata bani da nake matar shi ba har Umma da mama, da zarah da yan uwan ta dake gidan a lokacin hankalin kowa ya tashi don kalman ta zama wata mumunar kalla mai lahani a gare mu, baki dayan mu,
Zarah ta nuna ta da yatsa tana cewa wallahi a,hir dinki da kiran dan uwana mijinki don Allah ya raba mu da hadawa da mace shu,uma irin ki a rayuwar mu,
Ke ki iya bakin ki don ban da time din irin ku saboda ba gurin ki muka zo ba,
Wanan zance shiya kara tunzura Umma wace dama take a kule da su, take cewa wallahi ahir dinku da zuria ta don ban haifi dana donku ba wai ku wasu irin mayun mata, ne haka wai da bakin nacin tsiya
Murmushi sukayi a tare tare da wani yin har da idanuwan su sai ita Lima ce tace mama kiyi hakkuri son dan ki nakeyi tsakani da Allah
Ke rufa muna baki kinji macuciya wazaki yaudara haka ake so ko bala,i inji mama hafsi, Umma tace,
Yadda Allah ya kwato min dana,daga,sherin ki da makircinki Allah bai kara baki sa,a a kan sa,insha Allahu,
Kiyi hakkuri mama ni mai son dankine ba,wai sheri ba, zakiji dadin zaman mu dashi nan gaba,
Abinda su umma basu lura dashi ba shine cewa, Lima daga gurin da take tsaye tana wani saddabaru ne,
Nice nafara hango yadda take saka hannu a hand bag take yarfa abu a tsakar gidan mu daidai saman hanya da,zai shiga da mutum gurin da dakunan mu, suke a jere,
Ashe mama ta gani daga inda take tsaye zata kara na uku mama hafsi ta nuna ta da hannu tana fadin dakata hakana don idan kika kara wallahi sai kin gane kurenki a gidan nan,
Tsintsiya da Parker na dauko batare da nai magana,ba baki ina karanta lai,la ha, illah anta subbahanika in,ni kuntu minal zalimin,
Nafara tatara daidai gurin da ta yarfa ruwan magani a gaban mu nai hanyar toilet dashi, suna kallo na,
Ibrahim suka,shigo shida abokan shi akai masu tas don kiris ya rage a bugesu a gidan,
Sai cewa suke wallahi tunda mijinta ne dole a bari su gan shi saboda itama ai tana da hakki a kan sa,
Fitina yai fita ancika sunga rashin mutunci a filin Allah haka ya,saka su barin gidan takalmi a hannu don sunga ruwan bala,i saboda matasan shiya sunce sai sun kashe su sai dai su ma a kashe su tunda sun zo har cikin gida yiwa mutane rainin wayyo,
Rikici yafi wani rikicin cikin tashin hankali suka bar uguwan don ganin dandazon jama,a yadda suke karuwa a kan su,
Suna barin uguwar Bicky tace wayyo Allah na yau mun ketare rijiya ta baya aida mun fada a jikin mu,,
Don wallahi wa yan nan katai indan sun dake mu sun daki banza wallahi,
Dayar Mary tace nikan ba zan sake zuwa irin wanan risky din life dina ba,saboda wanan village people, sun fimu hauka,
Ke da kikaga kina iyawa zaki iya zuwa for your own, risk ba dai dani ba again, gaskiya,,
Sai lokacin Lima tace, hmmm ni duk ba wanan ba wai kun kula da yadda wanan yar ficikan yariyar tawani canza gaba daya kamar bata a cikin wani case haka,,
Kina nufin matar Hamza din tace eh ita mana Mary tace wace daga ciki ?
Wanan da tazo ta kwashi abu a gaban mu da Parker mana abinda na zuba ne fa wai wanan yarinyar tagani take kwashewa a gabana,
Ki duba irin kudin dana kashe kafin na,samu a hada min wanan magani amma duk da haka nasan cewa, dole za,a samu wani da zaiyi amfani a gurin,
Muddin Hamza ya bi gurin dole maganin nan yayi aiki a kan shi,
Kawai ni bukatana shine yabi gurin kawai koda sau daya ne,
Amma ashe matar yarinyace haka karama gata kuma tana da kyau wallahi sosai,
Duk lokacin da naga wanan yarinyar nakan ji matukar bala,in kishin ta ya kama min zuciyana sosai,
Duk yadda zan raba shi da wanan yarinyar zanyi na shiga tsakanin su muje zuwa suna wasa dani wallahi,,
Shiru sauran sukayi don su abin yafara basu haushi sosai don dai sun san suna samun biyan bukatan su ga,alhazawa masu kudi balle wanan yaro karami
Da baida ko sisi inba jikin shi da take moraba basuga abinda take mora a gare shi ba,
Suna fita mama Hafsi tace a zuba fitsari da ruwan tsami yadda asiri zai kare, a duk gurin da,suka bi suka zuba maganin,,
Ina tsaye imani da tsoron duniya duk ya kamani yau naga mai abu ja mara abu ja a filin Allah yadda mace tazo ba kunya tana duban idon mutane tana cewa wanda ba,a,san yadda suka daura aure ba wai mijin ta mijin auren ta,
To ni ma,wai yanzu a wani matsayi nake da auren shi da ke a kaina, ne don banga alamar wanan matar zata bar min mijina ba don babu kunya babu tsoron Allah a tare da ita, ko kadan,
Ina gurin banyi aune ba sai ji nayi kamar numfashina zai tsaya min don irin bacin ran da nake ji, atare dani,
Da kyat na,samu na nemo natsuwana ina fadin innalillahi, wa,inna alaihim rajji,un,
Sannan na dan samu natsuwa a tare dani, duk kace nacen da mutane keyi ban iya cewa uffan ba don mamaki,
Gaba daya ji na nake kamar ta kwace min miji ko, don may zan gane wa mutumin da ke mu,amula da mace irin wanan matar,
Mace ga jiki ga haske ga sutura na alfarma, ga kayan karau ko yaushe da take dazawa,a jikin ta,
Nasan kowaye hamza gwarzon namiji a cikin mazaje yabiyo tarihin mai sunan gurin karfi da hazakan nema,
Nasan bako wace mace ce zata mallakeshi ta bari ya shige mata kai tsaye ba, batare, da wani jayyaya ba,,
Haka naja kafana da kyat zuwa dakina inda na,fada saman gadona na fara wani sabon kukan gwanin ban tausayi dani,
Ganin ba sarki sai Allah ni daya a cikin daki sai na,fara jero tasbihi inayi tare da neman sauki a gurin Allah ubangiji subbahanahu wata Allah,,
Don wanan masifa yai muni saboda yadda suka shigo muna a cikin fitsara babu burbushin kunya a idanuwan su ko kadan,
Wai mijina take kira mijinta a gaban bainan jama,a ina ji ina gani don rainin wayyon da take min, ta daukeni ni da banza duk daya,
Haka nake kwance ni kaidai a daki sai juyi danake a saman gado ga tunanen kala, kala da ya addabi zuciya ta,
Don sai nake kiyasta irin rayuwan sha, shanci da tambadewan da su kayi tare dashi a idanuwana,
Na kara rintse idanuwana raina yana ci gaba da baci don zafin kishin da nake ji ban taba sanin cewa na iya kishi ba sai a wanan ranan da naiwa

Download complete TXT · Novel page