Showing 132001 words to 135000 words out of 299981 words

Chapter 45 - Sarautar Mata By Makawa

04 Dec 2025

17625

musulmai,
Dattijon yace yanzu abinda nake jira isowar yan uwan ka da suka taimaka maka kafita cikin wanan ukubur wanan bakar kafiran da ta tashi nakasar maka da rayuwa kana dan karamin ka haka, saboda ha,inci da cutarwa wai da sunan so,
Idanuwan Hamza ne ya ciko da hawaye yace baban ban san da wani irin ido zan kali iyalina ba dashi,
Mahaifiyata yan uwana duk nauyi da kunyan kallon su nake ji kan abinda na aikata don wasu sam bazasu taba yarda cewa wai ba a hayacin kaina na aikata wanan abubuwan ba, a rayuwa na,
Kada ka damu tare dani zamu tafi har gida nakaika nakuma yi masu bayani gamsashe yadda zasu fahince ni,
Hawaye ne masu zafi da radadi suka malalo mai daga idanuwan shi zuwa idanuwan shi,
Acikin zuciyar shi wani zafi yake ji kamar zuciyar shi zai fasa kirjin shi yafito waje,
Lima Lima tsakanin shi da,wanan matar Allah ya isa kawai,
Ya rintse idanuwan shi daya tuno cewa, ta mayar dashi kamar wani mashi ba dare ba,rana gurin amfani da ita, duk sanda yai mata,dadi haye ta kawai zaiyi yai ta mata abinda take so take bukata shi baida na cewa,
Gashi dan kaddaran shi a lokaci guda ta umurce shi da ya,sayar dasu gaba daya yanzu baida komai wanda zai iya nunawa a matsayin nashi koda kuwa kaza ce,
Wanan tunane yasa shi fashewa da wani irin kuka mai ban tausayi yana rausauya wa kan shi yana kuma tausayawa mahaifiyar shi da matar shi,
Aisha yarinyar kirki mai hakkuri da sanin ya kamata ko tana cikin wani hali yanzu oho,
Allah dai yasa iyayyen ta,da ita basuyi fushi sun dauke yar su ba,daga gidan shi,
Don tun auren su bazai iya cewa ga wani abin arzikin daya kara ta dashi ba a rayuwa banda karatun da ya mayar da ita,
Yanzu kuma bai san makomar karatun ta,ba tunda ya kaurace masu na tsawon wani lokaci wanene zai tallafa mata a karatun ,
Ya lumshe idanuwan shi yayin da hawaye suke ci gaba da kwaran yowa daga idon nashi yana dan matse su,
Baya kaunar ko a cikin mafarki yaga wanan kafirar mata kuma balle a fili,

****** ********** ******
Kwana biyu sun cika mama ta kasa hakkuri ta koma gurin malam Liman tace malam gashi yau har kwanakin daka,ba,mu sun cika anya kuwa malam yaron nan yana,a,raye kuwa,
Malam yai murmushi yace kizama mai tawakkali a,rayuwan ki domin gagawa ba alheri bane, wani lokaci,
Tunda nace maki zai zo zai zo din insha Allahu don haka kwantar da hankalin ki kawai,
Badon taso ba ta dawo gida jiki babu kwari don sai take gani kawai dubarun liman sun kare ne yasa yace mata haka kawai, don ya kwantar mata da hankali ne yake ta fada masu hakan,
Daki mama ta,shige sai kukan ta kawai mukaji abinda yasa gida ya kara rudewa ke nan da wani sabon kuka tashin hankali zalla,
Da kyat su Baba Mudi da suka,shigo suna tambayan mu lafiya ko anji labarin shi cewa ya mutu ne da muke wanan kukan haka,
Nan mutane suka,taru sukai ta,bamu magana har muka hakkura ranan baba har dakina ya shiga yazauna a saman kujera na yai min nasiha akan hakkuri don ance mai hakkuri baya tabewa duniya da lahira,
Haka yasa muka dan kara dada hakkuri a zukatan mu har muka koma dan normal
Ganin har karfe uku yau Ibrahim bai kawo abinda zamu ci ba yasani mikewa na hura wuta tare da,tsabatace gurin sanwan nawa dama cikin gidan,
Umma tafito daga dakin ta don ji na hura wuta ta tambayeni mai zanyi sai nake ce mata zan gyara muna kanzo dana tara ne aci,
Tace tau sauran kayan miya fa nace ma Umma, na aika adan sayo mun tankwa da manja na hamsi da gishiri zan zuba muna,
Nagama dama kowa yunwa yake ji agidan na,raraba mu a kuma yai dadi sosai don yana kamshin dadi,
Muna zaune a tsakar gida har su Ibrahim mukaji dirin din mota ya tsaya kamar a kofan gida,
Ba,wanda ya kawo wani abu a,ranshi sai cin abin mu mukeyi hankali a kwance,
Kamar daga waje muke jin hayaniya,amma,sai ba,wanda ya kai hankalinshi don yunwa kowa keji ko karyan wan safe bamuyi ba,

****** ********** ******
Sallaman yara muke ji suna shigowa da ihu ga Hanza yaro ga Hamza yaro abinda ya ja hankalin mu gaba daya ga yaran ke nan,
Mikewa Ibrahim yayi zuwa waje don duba gaskiyan maganan yaran,
Mutane ne cinjim.a kofan gidan sai rugumay hamza din sukeyi,
Daga inda nake tsaye naji abin da yaran ke fadi zancen yazo min kamar a mafarki sai ji nayi,
Dif dif dif ban san inda nake ba kuma daga haka sai farkawa nayi naganni tare da,su Ummi su mama saude suna dan mani hitara, da sannu,
A hankali na bude bakina da kyat nai magana cewa mama da gaske ne Hamza din yadawo,
Mama saude tace da gaske ne Aisha gaya can suna gaisawa da mutane,
Na mayar da idanuwana a hankali na lumshe su tare da wasu haye masu dumi da suka biyo fuska na,
Gida da uguwa ya cika da masu zuwa muna barka da arziki,
Yan uwa duk sun rike shi sai kuka,sukeyi tare godiya ga,Allah da ya,baiyanar dashi,
Zarah mijin ta yabugo mata waya cewa tazo gida ance Yayan ta yadawo gari,
Ta hawo mashi a,sukwane suka kawo da mai mashin din hankalin ta a tashe tana cewa, wai da gaske ne yayan mu yadawo,
Ta na ganin shi tafada mashi tana kuka tana cewa yayan mu munzaci mun rasaka ke nan,
Allah mun gode maka da kadawo muna da dan uwan mu gida lafiya,,
Sai kuka,suka kara sakewa haka mutane yan uwa da abokan arziki sukai ta kai kawo gurin shigowa har wanda bamu sani ba sunzo, taya mu murnan dawowan shi,
Wasu suna cewa wai akaini asibiti amma sai mutumin da suka tare yace a,barni a gida damuwar da na,shiga ne yake sauka,
Sai bayan kowa ya rage agidan an watse sai mu yan gida,da,baki koshi sai da aka,rufe kofan gidan,
Sai su Baba Madu baba Mudi, da Baba Liman sai mutumin ya fara bayani kamar haka da cewa,
Ku godewa Allah daya nufe shi da,dawo cikin ku bai halaka ba ko canza akida,
Da,safiya na,samay shi a hanya shine ina ganin yanayin shi nasan ba daidai yake ba sai aka,saka,salati a,dakin baki daya,.
Nan dai yai masu bayani akan yadda suka shirya zai fadi shida su Mansur,,
Don gudun kada, agane cewa daga gurin su ya,fito shima hamza din yana cikin class akakira shi ana sheda mai baiyyanar Hamza din cikin jin dadi da,sowan su suka,ruda guri da ihu eh anganshi anaganshi,,
Abin waya kafin wani lokaci labari yakai wa su Lima cewa anga Hamza dama a under beli take don haka sai tai wani irin ihu da murnan jin dadi sosai,
Nan take tafara planning din yadda zata dawo dashi gareta kafin iyayyen shi su dauke mai hankali gare ta,
Take ta shiga kullawa da,warwarewan yadda abin zai tafi mata daidai,

****** ********** ******
An natsu kowa yana sauren bayanin mutumin da,sadudan yadda mace shu,uma zataiwa dan adam irin wanan kuli haka,
Hamza ya rarafa daga,inda yake zaune zuwa gaban Umma cikin kuka yake cewa,
Don Allah Umma da mama ku gafarce ni kuyi hakkuri ku yafe min laifin da nai maku
Umma fushin ku a gareni zai iya janyo min fadawa acikin masifan da yafi wanan nan,
Umma ta ce cikin kuka yanzu babana abinda kai muna a rayuwar ka ka kyauta ke nan kasayar da abincin mu da duk abinda ka malaka a gidan ka,sayar kabi mace macen ma kafira guzuma ba,sa,ar yin ka,ba,
Mama ta cabe zancen da cewa Hamza mu bamu rike ka,da komai ba godiyan mu ga,Allah shine yakwato muna kai daga hannun wanan macuciyar matar kafira mai mugun aniya,
Sam baka da laifi garemu tun da mun san cewa bayin kanka bane mun san ka mun san halinka Hamza don may zamu dora maka laifin dabakai kayi shi ba,
Kowa gurin ya dauka da cewa wanan gaskiya gaskiya ne kika fada ,
Suka juya gurin Umma suna cewa boyar Allah don Allah dai kiyi hakkuri kiyafewa wanan yaron kamar yadda yar uwar ki tafadi ,
Umma ta,share hawaye tace nasan da haka bacin rai ne yai min yawa har na,fadi haka amma nayafe maka Hamza duk abinda kai mun,
Sun kai wani lokaci a gurin sai dai duk abinda akeyi hamza hankalin shi ya gur8n yar matarshi don yaganta ko zai ji sanyi a ranshi, irin yadda yake son ganin ta a rayuwan shi,
Bayan Anfito daga sallah isha,i aka taru a tsakar gidan mu Liman Baba Madu bakon da yazo da Hamza sai Baba Mudi makwabci su,
Liman ya bude taro da,addu,a tare da karayiwa Allah godiya da,sauran mutanen da suka taimaka a kan wanan al,amari,,
Yakara yi mai nasiha akan riko mai karfi ga ibada ta yadda zai tsamo kan shi daga fitinar zamani,
Nan dai ya nuna mai matukar kuskuren shi dayayi wurin yin sakaci da,addu,oi, saboda neman kariya ga,hadduran zamani,
Malam Liman yaci gaba da bayani cewa, yanzu bukatar da muke son ku dashi shine,
Har nan da sati uku kada ku bari yayi arba da,wanan matar don kun san bazata barshi ba haka banza don dole ta canza sallon yaudaran ta,
Don haka za mu roki Allah duk abinda tazo dashi ya koma mata zamu tafi dashi can guri na mu zauna har wa,adin da aka kidanya na,sati uku cur ya cika kinga alokacin duk wani hari da zata kawo mai, ba zai yi tasiri a kansa ba,
Mama ta cabe zancen da cewa insha Allahu, zanyi kokarin ganin haka
Anyi sallama da juna inda aka kai bakon masauki ya sauka sai tururuwa mutane keyi shigowa muna barka da arziki har cikin dare,
Duk da musan cewa wasu don gulma ke kawo su a lokacin bawai don Allah sukeyi ba,
A hankali, ya mike daga cikin taron ya nufi, hanyar shiga dakina ,
A,lokacin, ina zaune a kasa gefen kujeran dakina, saman salaya na na dan kifa kaina a saman kujera hannu na daya yana rike da tasbaha ina ja a hankali,
Sam ban yi tsanmanin shigowan shi dakin ba a lokaci sai ganin shi nayi ya fada min bakin shi dauke da sallama,,
A hankali na,dago kai na da dube shi saudaya sai kuma,na,sada kaina tare da amsa sallama shi,
Ya samu guri ya zauna, saman kujerar danake zaune ta gefen, guda,
Humaira ke ma kina fushi da nine kuma, kamar Umma,
Nadan kada kaina a,hankali tare da cewa ,a,a ba hakana bane don dai na ganka da mutane, ne,
Huci yayi mai fitar da iskan zafi daga bakin shi, tare da furzo iska yana furta Subbahanallah cikin wani yanayi, na bacin rai,
Shiru dakin yayi ba mai magana daga cikin mu sai karan fankan sama dake tashi,
Mikewa nayi tsab daga gurin da,nake zaune na dauko mai ruwa nazo gaban shi na durkusa na,aje mai plate din ruwan gaban shi ya,duka,ya,dauka naje na,dago sai muka,shaki, numfashin junan mu a lokaci guda
Take, kowan mu ya shiga reacting, don shock din da mujaji a zukatan mu lokaci guda,
Da sauri ya dago kai dai dai lokacin dani ma na dago nawa sai muka kara,arba,dashi nasada kaina kasa,a hankali tare da dan kokarin dagawa daga gurin da nake tsugun ne a gaban shi,
Rugumoni yayi da hannayen shi bibiyu gaba daya zuwa jikin shi inda ya,dan mike don yaji dadi rugumoni da kayau,
Noke kaina nayi ina kuka don wani irin bakin ciki da takaicin dake sukar ziciyana,
Kamar mai rada naji muryan shi daidai kunnuwa na yana,magana cewa, Aisha kiyi hakkuri dani ba wai yin kaina,bane don da ban maki haka,ba arayuwan na,
Wanan matar ta cuce ni Aisha ta,raunana min rayuwana,sosai a duniyan nan,
Tabar min babban tabo wanda bacewar sa sai gyaran Allah,
Hawayen, shi naji suna digo min a fuska na a hankali tare da jin yadda sautin kukan shi ke tashi yana kara sakani cikin tashin hankali mara misaltuwa,
Nan mukai kukan mu mai isar mu ba wanda ke iya bawa wani hakkuri a cikin mi kowa da abinda ke ci mai ziciya a cikin mu,
A hankali muka zauna daga bakin gadon inda yadan dago min haba na yana cewa
Nasan duk abinda zan fadi ba zai yi tasiri a gunki ba dan zargi mai girma ya,shiga tsakanin mu dake a yanzu don haka,
Dai ina mai kara baki hakuri akan kiyi hakuri ki yafe min don Allah akan yadda wanan matar ta yaudari rayuwana ta,cuta mim ta ida ban taba zato,,
Muryan su Baba Liman ce ta,ratsa kunnuwar mu yana cewa,Hamza kazo mu tafi, kada wani ya,san zancen kum,
Dole ba don ya so ba ya dan kura min idanuwan zuwa dan lokaci kadan ya mike yana mai sharan hawaye yabar dakin cikin sauri zuciyar shi tana mai tafasa,
Ina kwance a kan gadona tun bayan fitan Hamza a,dakin wanda ya fita ya barni a cikin kunar rai, wanda bai missaltuwa,
Ina kwance nai kuka nai tunane har baya kirguwa a lokacin,
Ina gurin tun ina jin hayani har na daina jiyo motsi wanda hakan na nufin bakin sun fita harda Hamza a cikin su,,
Kara lafewa nayi saman dan gadon katakona ina hadiyan rai don abubuwan da sukai min yawa a lokacin,
Mama hafsi ce naji muryan ta a kaina tana cewa ki tashi ki kulle kofan ki Aisha don dare yayi sosai kowa zai shige,
A zatona ta juya ta tafi ina mikewa don bin umurnin ta naji tana cewa kiyi hakkuri gaduk irin jarabawan da kika gani a rayuwan ki, komai mukkadari ne ga bawa,
Inda anyi hakkuri sai a cinye jerabawan abin ya wuce don wanan yana daga cikin kaddarorin ku gaba daya,
Adduan, mu yake mubukata don samun kubuta daga sherin shedan,,
Kinyi kokari sosai sai dai ki kara don Allah da kikeyi a kansa ya sanar maki,
Haka kuma jama,an dake gani Aisha kowa yasan kinyi hakkuri a kan wannan al,amarin,
Don har yau baki nuna gazawan ki ba akan zancen, don haka ki kara dagewa,kin ji yar nan Allah ya,baki ikon cinye wanan jerabawan a hankali na amsa da,amin, ya Allah mama,
Kullun kalaman su mamana, yana min yawo a zuciya ta tare da kara kwantar min da hankali,

****** ********** ******
Kwana biyu da,dawo wan shi gida, komai yadan fara lafawa don mutane sun dan lafa da shigowa ganin shi, saboda an fada masu cewa ya koma makaranta ko,
Ina tsaye gurin igiyar shayin kayan mu ina kokarin shaya tufafina da na wanke naga mata kwatsan a tsakar gidan mu babu ko sallama har su uku,
Har sun shigo daidai tsakiyan gida babu ko sallama balle muji shigowar su,
Zarah wace tazo tun da safe yini tana tsaye daga kofa tana gyara shikafa a cikin dan wani faranti a a hannun ta,
Ganin katan mata tsakar gida kamar kabila ashe su, don sauran biyun ma ba gyale a tare da su, ga,gashin doki sun aza a kan su,,
Dayar ce ta dan daura dankawali ta yafa wani dan yalalon gyale iya kafadan ta kawai,
Zarah tace a,a kuka wani dabia ne wanan shigowa gida babu sallama hakan nan, don ita a zaton ta masu zuwa ganin Hamza ne,
O sorry bami yi maku sallama ba ko sai kowan mu ya kyale su,
Nidai na sheda su don na san su saboda zuwanda suka taba yi har sau biyu, take nafara jifan su da abinda yazo min a rai,
Addu,a nake daga cikin bakina ina fadar La,illah ha,ilallah mohammadan rasullillah,,
Nazo gaban su na gilma ina dauke da bokitina na silver danake wanki a hannu na suna tsaye a tsakar gida cirko cirko,
Ina mama suna, tambayan Zarah, wace take masu kallon mamaki,
Sam ban kula su ba sai aikina nakeyi hankali a kwance, batare da na kula dasu ba,
Sai dai a can kasan zuciyata kamar na sheka da gudu nake jin kaina,
Jin suna neman Umma yasa su Asma,u da mama hafsi wace ke dayan dakin fitowa, waje da sauri don ganin ko su waye
Sai muryan ta mukaji tana cewa tau munafuka may kuma ya kara kawo ku gidan mu, wani sabon sherin kikazo muna dashi ke nan, kuma,
Tau ta,Allah ba taku ba don Allah yafiku yafi sherin ku muguwa muna fukai kawai,
Look mama mu ba wanan ne ya kawo mu ba mun zone don naga mijina naga halin da yake ciki, ? Saboda munji labarin cewa angan shi
Tashin hankali wai fadawa sarki gaiyya, don kalman mijina da ta ambata bani da nake matar shi ba har Umma da mama, da zarah da yan uwan ta dake gidan a lokacin hankalin kowa ya tashi don kalman ta zama wata mumunar kalla mai lahani a gare mu, baki dayan mu,
Zarah ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login