Showing 141001 words to 144000 words out of 299981 words
Nace a hankali da tau Anty insha Allahu zan bari da yardan Allah,
Mun kai wani lokaci tare da ita taimuna sai anjima ta tafi taba ni alheri mai yawa wai na sai Omo da sabulu,
Bayan fitan ta ta ba su Umma tai masu fatan alheri zan rakasu tace na zauna kawai ta hutar dani,
Haka mukai ta zama sai magan ganu muke ji suna zaga gari iri iri wanda ba dadin saurare,
Ga abinci yai muna tsaye a gidan wani bi daga gidan mu ake taimaka min da dan abinda zanci a bakina,
Wanan maganan yaso ya dan taba karatuna amma da taimakon Mansur na,samu aka gyara komai ya koma normal,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABUIDAN BAKI BIYABA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE CIN AMANA NE KARANTAWA BA BIYA PLEASE,,,,
Akwana a tashi ba,wuya a wurin Allah don gashi yau har sati ukun da,su baba liman suka kindanya ya cika,
Don haka duk wani abinda suka shata cewa ya dace suyi don neman ma Hamza tsari gurin Allah daga sheri shu,um Lima sun yi shi,
Nikan ina ganin mutanen gida suna zuwa a,sace gaida Hamza amma,ba wanda ya taba taya min hakan,
Ina zaune yau a saman kujera yar tsugunno a tsakar gida,
Ina tunane ace mace da mijin ta amma a hanata ganin shi sai dai taga mutane su na zuwa gun shi ita ba,a damu da nata damuwan ba, balle a taya mata zuwa duban shi,
Tau sanyin kaina,ne ya kamani don dai zan iya cewa ni dai arayuwa na godewa Allah zance,
Wani irin zazzabi naji ya na batun rufe ni saboda bayanin da naji Ibrahim yanawa su Umma din,
Wai ni Aisha da mijina amma ace bazan gan shi ba sai lokacin da aka ga daman bari nagan shi ko ya ganni,
Na nisa ina fadin Allah na godema kai kadai kasan dalilin jefa rayuwan mu a cikin wanan halin,
Ina zaune gurin nai zurfi ga tunanen da nakeyi mama tafito daga dakin don ta karasa aikin da takeyi sai gani na tayi a cikin wani yanayi,
Taja tai turus tana kallona a cikin mamaki da tausayawa ta karaso gare,ni tana ,duk ban farga ba sai ji nayi tace,
Aisha may kuma kike tunane haka kikayi zurfi a acikin tunane,
Jin ta,a kaina batare da na,sani ba yadan sani kaduwa da,dan firgice ,
Na dago idanuwana cike da firgici mai nuna razana na kalle ta, tana cewa may kike tunane ne haka har baki jin magana,
Nace cikin sanyin murya mama babu komai ina,dai zaune ne, kawai,
Tace to ki daina ir8n wanan dogon tunanen kada ki jefa kan ki a fitina bayan komai ya kusa kai karshe,
Takara matsowa gare ni tare da,dan dafa kafada na tana cewa Aisha kin yi kokari fiye da tsan mani don da watace cewa zatayi fita zatayi bazata daure da,wanan fititinun haka ba,
Umma daje fitowa ashe taji mu take cewa wanan ai hakkuri ya zama dole ne don ko an tafi ina,gurin zuwa,
Haba mama bata da gurin zuwa kamar wace bata da gida adaji aka tsinto ta, inji Ibrahim wanda ke daga bayan ta,
Gaskiya Umma Aisha ta wuce haka garemu don tai muna halarci wanda ba ko wace yarinya mai karamin shekaru irin nata zata iya muna shi ba,
Har yau ba mai cewa ga abinda yarinyar ga tace a garin nan tana gida tana kokarin ta duk abinda ta,sabayi da yake nan bata daina ba, don bayanan gashi yadawo acikin wani hali amma duk da haka bata kyamace shi ba ,
Haba dai Umma wanan abin fa yai ishe mu isharan rayuwa,
Jikin Umma yai sanyi ga maganan dan ta don haka,ta juya ta,shige zuciyan ta ba dadi don a gaskiya itama tasan cewa inba Aisha bace da yanzu an kai ruwa rana ga tonon asiri ko kan abincin da basu dashi a gidan,
Amma sai gashi wani lokaci da dan sana,an yarinyar suke samun rufin asiri a gidan don komai ya kare masu,
Mama tace min ki kara hakkuri kinji Ya ta mahakurci mawadaci a,rayuwa,
Na amsa cikin dan sake murmushin yake da cewa tau mama insha Allahu tare da mikewa nabar gurin naci gaba da tsabgogin gabana,
****** ********* ******
Allah maji rokon bawan shi Alhamdullahi an roki Allah kuma ya amsa muna,
Don gashi yau su malam Linan sun dawo da Hamza a cikin iyalin shi lafiya ranan bawan Allah nan kuma yai sallama da mutane ya kama hanyan garisu,
Anyi gwaji ansamu Hamza lafiyan shi kalau sai dai yar damuwa da take damun shi a zuciya wanda likita ta bashi shawara akan ya daina tunane don gudun kamuwa da wata cuta da ka iya cutar dashi,
Ance akwai masana masu hikima da da sani daga cikin alkur,ani maigirma,
Wanan zancen haka yake don kuwa sun nuna hikimar da amfani da ayyoyin Allah,
Don babu shirka ko wani kaucewa a cikin sa da haka,suka ci galaba akan shu,uma Lima akan Hamza,
Kwata kwata yanzu ko kadan baijin komai a gamay da Lima sai jin da yake a shirye yake yai mata cin mutinci idan ta tun kare shi,
Damuwar shi yanzu guda da hankalin shi ya dawo shine rashin abin hannu da basu dashi a gida don komai ya kare mashi,
Bai aje komai ba ta dalilin yaudaran da Lima sukai mai ta hanya asiri ya,sayar da komai nashi,
Suka wullakanta kudin da sunan wai zai ga yan uwanta da aminata dashi,
Mama Hafsi itace ta dage gurin bashi shawaran kan ya fitar da komai a ran shi yabarwa Allah Al,amarin yai mashi mafita a kai,
Da yamma yai wanka yafita waje don har yanzu majalissan su tana nan a bakin shagon shi duk da shagon a rufe yake,
Amma haka bai hana matasa taruwa gurin saboda sabo sukan zauna hira da yamma idan kowa ya dawo daga gurin neman rufin asirin shi sai su zauna hira,
Yana fita nan suka shiga nuna farin cikin su suna jajanta mai da fatan Allah ya tsare gaba,
Baba mudi ya hango a kofa zaune ya nufi gurin shi suka gaisa yakara dan tsawata mai akan yadda duniya ta koma yanzu ba kowane zakai saurin yadda da shi ba,
Sai kuma na yakara dagewa ga ibada don samun kariya daga al,amuran duniya baki daya,
Sosai yaji dadin nasihan Baba mudi, dattijon da yake daukan shi a,uguwa tankar mahaifin shi don mutuncin dattijon,
Yaran shi dai ne masu rashin jin magana amma bawai maijawo mai futina ba,sai dai rashin kunya da jan magana,ashiya kawai,
Nan ya zauna a cikin abokai yana sauraren hiran su abinda ya tuna mai da,baya ke nan lokacin yana Hamza yaron shi da yar tiredan shi yana,samun rufin asirin Allah daga ciki,
Amma kuma duk abinda ya samu ya tafi ga banza alokaci daya,
Sai imani da tawakkali kawai ya,saura mashi don tuna wani abu fitina ne da tashin hankali,
Yana zaune yarinya takawo tallan kayan miya da yake ya saba saye a gurin ta take mai talla,
Murmushi kawai yayi cikin zuciyan shi yana jin kunan rai tare da radadi don baida ko kwandala a aljihun shi,
Har magariba yana zaune a gurin kamar yadda suka,saba ana ta hiran kamar kullun,
****** ********** ******
Nagama komai na gyara dakina duk da kullun a gyare dakin yake min na dauko sabon kulan abincin da na,saye saboda shi alokacin da zance auren shi yake yawo,
Nadan yi saye saye na na,wasu abubuwan bukatun mata don gudun kada a,burgeni ni banda komai,
Ba,wanda yasan na,saye su sai yau dana fitar don na sa mai abinci a cikin sa,
Na shimfida mai sabon zanin gado wanda nabawa Hindu tasayo min American cotton mai kyau jada fari, kala,
Nafshe dakin sai kanshi ke tashi har waje, da turaren da Hindu tabani don wanan ranan wanda tace turaren yana da,siri a cikin sa,
Sabon ledan kasana yana sheki da haske a dakin gwanin ban sha,awa,
Duk wanan shawaran uwar dakina hinduce ta sakani yin shi da tazo gidan mu last da dan ta datakara haihuwa wanda lokacin muna cikin tashin hankali,
Tafada min cewa kada na nuna mai komai koda a fuskane na nuna tankar babu abinda yai min zafi a kan zancen,
Kuma tunda Umma tana adawana a zaman gidan haka zai kona mata rai sosai sai dai indan anyi sa,a Allah ya,taro ta ta saduda ,
Tana zaune kofan ta kamar an kafe ta tana kallon yadda nake harkokina a tsanake ba wani nuna bacin rai a tare dani,
Bayan fitowan maza daga gurin sallah ishai shima ya shigo gida kamar yadda suka sabayi a baya can,
Nafito masu da babban tabarma na,shimfida kafin su gama gaisawa da,su Umma,sai hadari ya tashi kura ya kora kowa dakin sa saboda iska daya murtuke guri,
Badon Umma taso ba ta barshi ya,shigo daki lokacin ina tsaye gurin mirro ina gyara, kayan mirron nawa,
Sallama yashigo dashi na karba mai tare da mashi sannu da zuwa ya karba min a cikin shakku ba kamar yadda ya saba ba ,
Nake cewa na dauko mai abinci ne ko sai an gama iska, zaici yadan furza iska tare da shafan fuskan shi alamar abu yana damuwar shi a ran shi,
Yace bari kawai naci yanzu don akwai alamar ruwa tafe ga hadarin baigama rufe baki ba ruwa masu karfi suka,sauko gaba,daya lokaci guda,
Kayan abincin na dauko mai na aje mai a gaban shi, tare da girke mai sabon jug din ruwan da na,saye tare da kulolin,
Kanshi ya na,sagale a makarin kujeran idanuwan shi a lumshe suke yana dan buga hannayen shi a hannun kujeran,
A hankali har nagama shiri na tsab cikin wani dan rigan barcina dark blue mai igiya sirara, iya gwiwa,
Saidai na daura zani daga ciki rigar kawai na saka daga sama,
Nadawo bakin gadona na zauna duk da banci komai ba ban jin yunwa a lokacin,
Jin shirun da yayi na,daina motsi yasa shi dago kan shi ya,sauke idanuwan shi a kaina ina zaune a bakin gado da yar wayata eitel ina dan dakilawa,
Sai kuma ya dawo da kallon shi ga kulolin dake a gaban shi suna kyalin sabon taka,
Humaira duk da abinda nai maki bakiyi fushi ba dani har da karramani irin haka kikayi,
Daga inda nake a zaune nake cewa aini bakai min wani abuba sai dai kawai kanemi gafara ga ubangijin ka shine mafi alheri don Allah gafurun rahimun ne,
Sai kawai naji ya,sake wani irin kuka mai karfi wanda ban taba zaton zai iya yin sa ba a,rayuwan shi,
Badon karan ruwan saman da akeyi ba,da ba abinda zai hana gaba daya yan gidan mu kowa yazo dakin mu a lokacin,
Cikin tashin hankali na mike tsaye ina kallon shi yadda ya ke kuka tare da dafe kan shi,
Tsoro ne ya kamani a,zatona ko wani abin ne kuma, ya sake faruwa dashi again,
Da sauri zan fita zuwa kiran jama,a sai naji ya riko min hannu tare da kokarin zaunar dani daga gefen shi kadan yake cewa cikin muryan kuka,
Humaira ki bari nayi kukan nan ko zan samu relief a mind dina don na dade iba,son nayi shi ban samu halin yi ba,
Humaira yau ni Hamza ne nai taraiya da wace ba musulma ba a rayuwa na, wai kuma matsayin matata,
Ta yaya bazanyi kukan gamuwana da ubangijina ba ranan gobe kiyama,
Jikina yai matukar sanyi don jin kalaman shi yai matukar bani tausayi, sosai tare da jin haushin wanan kafirar matar da ta jefa rayuwan mu a haka,
Cikin sanyin murya na bude baki na,da kyat ina cewa, yaya kayi hakkuri komai a,rayuwan bawa mukaddari ne don hakan umurni ne na ubangiji Allah( S.W.A)
Yace Humaira kunyar ki nake ji a,rayuwa na,ban san da,wani ido zan kalle kiba yau,don nauyin ki da nake ji,,
Humaira kiyi hakkuri ki manta da komai bawai don ban so ki bane nai maki haka,
A a wanan kaddararen al,amari ne a kaina an rubuto min cewa sai nayi shi a rayuwa na,
Nace a cikin sanyi murya kamar ta mai kuka ni ban kullace ka ba yaya don ni musulma ce yar musulmai,
Nasan mata nawa aka kidan yawa namiji ya,aura,a,rayuwan shi duk da,dai kai naka karin auren yazo a,wani bakon al,amari ne,
Amma hakan bazai sa nai fushi dakai ta yadda har nima Allah zai iya yin fushi dani ba,
Tabbas yaji dan sanyin magana na don yadda naji ya,sauke ajiyan zuciya yai shiru tare da dan kada kan shi,
Nace kaci abinci ka cire damuwa a ranka kada ka jawa kan ka matsala fatana shine Allah ya kara nisanta wanan bakar mace nisa damu,
Ya,dago idanuwan shi da suka rine sukai ja sun canza kala kamar gauta, abinka ga mai manyan idanuwa, sunyi wani jawur sunfito,
Abincin da na dan yunkura na fara zuba mai a cikin plate yabi da kallo har na kara kadan yace min in barshi hakana amma a,tare zamuci don yaga nima banci komai ba, ai,
Zan musa yake cewa idan banci ba,shima ba zai iya ci ba dole na zauna muka dan tsankwara kowan mu ya tashi,
Sai dai gaskiya mun kasa sake jikin mu da juna kamar baya, can,
Nake cewa ga ruwa babu daman yin wanka kuma saboda ruwan saman dake zuba da karfin Allah,
Yake cewa ai bai dade da yai wanka ba don haka,ba matsala zai bari har wani lokaci,
Munyi shirin kwanciya don kowan mu da zancen dake cin zuciyar shi, kowa da,tashi kuncin
Sai neman agaji a,gurin Allah muke don samun saukin yadda,muke ji, a rayukan mu,
Addu,a nake abakina don wani irin zafi da bacin rai nake ji nashi sai dai na,dake ina daurewa kamar ba komai,
Yadda hindatu tace na zake nima na nuna mai tawa hikimar irin yadda ta koyar dani haka zai sa indan ma wani abu yakoyo daga gurin tsohuwar kilakiyar ya manta dashi,
Yana tsaye a bayana,sai kallona yake a cikin tausaya min yana anyanawa a ranshi,
Watau ita Humaira komai nata daban yake ke nan ko don komai a tsanake cikin kwanciyan hankali da nuna sanin addini takeyin sa,
Har kwanciyar ta daban ne dana,waccan makirar mai kwanciyan kafirai, gashi suranta kamar ita tai kanta, komai dan dagwas ya,daure ya,danne yadda yake ji a,ranshi,
Yakai zaune daidai bayana tare da dan tabani a hankali, yana cewa,
Humaira ina,sonki ina,son irin haliyar ki, ni kadai nasan irin wahalan da,rashin ki a kusa dani ya janyo min nasha wahala sosai idan na tuna daku sai dai banda halin zuwa gare ku dan irin yadda nake ji idan na kudurta zuwa gare ku,
Ina mai rokan Allah da kada ya kara nisantani fa iyalina da iyayyena,
Ina mai fatan muyi rayuwa da insha Allahu sai mutuwa zai raba mu,,
Jin ya tabani yasani juyowa a,dan tsorace nakalle shi sau guda naga duk yanayin shi ya canza idanuwan shi sai suka fara bani tsoro, saboda na hango wata irin muguwar sha,awa a tare dashi a lokacin,
Zancen Hindune ya fado min da taje cewa sai na dage sosai don yanzu zanga matukar canji a,tare dashi don haka naji wani rangwanta ya mamaye zuciyata,
Ganin yadda na nuna yadan sashi dan dawowa a cikin dan natsuwa ,
Yajawoni a hankali zuwa jikin shi tare muke sauke ajiyan zuciya idan kin gan mu a lokacin zaki tausaya muna don zaki fahinci kowa na daukin dan uwa,
Sai bayan komai ya kammala,a,tsakanin mu ne yake cewa cikin sauke ajiyan zuciyan shi,
Godiya ta tabbata ga sarki Allah wanda ya mallaka min Humaira a matsayin matar aure a gare ni,
Humaira har kullun ina mai alfahari da,samun ki a matsayin mata a,gareni wace ta san darajana dana iyayyena,
Ina,godewa Allah akan irin wanan baiwar da yai min a,rayuwata,
Yana fadar haka ya mike ya,suri buta zuwa ban daki a zatona kewayawa zaiyi yadawo ashe wanka ya tafi yayi a lokaci don jin maganan da yayi nasu liman na cewa kwana da janab a jiki yana saka,sgedanu samun galaba akan dan adam,
Yadawo har idona yadan fara nauyi ina son nayi barci ya tadani naje nai wanka haka na,fita nayo wankan nima,
Koda nadawo na tadda shi yana sallah nafila a lokacin ,
Nagaji don haka ban tsayaba na haye gado na kwanta abina kawai ina mai jin wani iri a rayuwa na,
Sai tunanen yadda muka kasance da shi yan min tina da,suka shige din duk yadda nai tsan mani abin ya,wuce nan ga Hamza don ya canza min gaba daya,
****** ********* ******
Ance mai hali baya barin halin sa don tunda safe nake jin motsin Umma a tsakar gida wanda ba komai bane don taga may ya,faru a tsakanin mu ni dashi,
Sai sabanin zatin ta tagani don alwala yayi yafita zuwa masallaci nima dai shi taga nafito nayi na shige dakina,
Don haka ta,shige dakin ta don ta fahinci ba komai a,tsakanin mu ke nan,
Tunane da mamakin halin rayuwa irin na umma nake may yasa da yake tare da wata bata samu irin damuwa haka ba,sai