Showing 147001 words to 150000 words out of 299981 words

Chapter 50 - Sarautar Mata By Makawa

04 Dec 2025

17649

canza idanuwan shi sai suka fara bani tsoro, saboda na hango wata irin muguwar sha,awa a tare dashi a lokacin,
Zancen Hindune ya fado min da taje cewa sai na dage sosai don yanzu zanga matukar canji a,tare dashi don haka naji wani rangwanta ya mamaye zuciyata,
Ganin yadda na nuna yadan sashi dan dawowa a cikin dan natsuwa ,
Yajawoni a hankali zuwa jikin shi tare muke sauke ajiyan zuciya idan kin gan mu a lokacin zaki tausaya muna don zaki fahinci kowa na daukin dan uwa,
Sai bayan komai ya kammala,a,tsakanin mu ne yake cewa cikin sauke ajiyan zuciyan shi,
Godiya ta tabbata ga sarki Allah wanda ya mallaka min Humaira a matsayin matar aure a gare ni,
Humaira har kullun ina mai alfahari da,samun ki a matsayin mata a,gareni wace ta san darajana dana iyayyena,
Ina,godewa Allah akan irin wanan baiwar da yai min a,rayuwata,
Yana fadar haka ya mike ya,suri buta zuwa ban daki a zatona kewayawa zaiyi yadawo ashe wanka ya tafi yayi a lokaci don jin maganan da yayi nasu liman na cewa kwana da janab a jiki yana saka,sgedanu samun galaba akan dan adam,
Yadawo har idona yadan fara nauyi ina son nayi barci ya tadani naje nai wanka haka na,fita nayo wankan nima,
Koda nadawo na tadda shi yana sallah nafila a lokacin ,
Nagaji don haka ban tsayaba na haye gado na kwanta abina kawai ina mai jin wani iri a rayuwa na,
Sai tunanen yadda muka kasance da shi yan min tina da,suka shige din duk yadda nai tsan mani abin ya,wuce nan ga Hamza don ya canza min gaba daya,

****** ********* ******
Ance mai hali baya barin halin sa don tunda safe nake jin motsin Umma a tsakar gida wanda ba komai bane don taga may ya,faru a tsakanin mu ni dashi,
Sai sabanin zatin ta tagani don alwala yayi yafita zuwa masallaci nima dai shi taga nafito nayi na shige dakina,
Don haka ta,shige dakin ta don ta fahinci ba komai a,tsakanin mu ke nan,
Tunane da mamakin halin rayuwa irin na umma nake may yasa da yake tare da wata bata samu irin damuwa haka ba,sai da ya dawo gare mu ta fara aikin ta na saka idanuwan ta gare mu,
Na gyara kwanciya na tare da lumshe idanuwa na a hankali, sai ji nayi ya dawo yana dan shafa min jiki a hankali wanda ban tsira ba haka ya kara afka min sai da ya samu natsuwa ya barni,
Jin mu a,daki shiru yasaka Umma kwada min kira wai na fito na kwashe ruwan saman da ya taru a robobi na juye a randunar ruwan mu na,sha,
Dukkanmu mun fahinci manufar umma don haka na yunkura zan mike naji muryan mamatana cewa haba yaya kibar yaran nan mana su futa,
Ni zan juye ruwan tunda ba komai nakeyi ba don haka ki barta kawai,
Yan kwanakin da Hamza yai muna,a gida kafin ya koma school haka mukai ta fama da Umma aace ta hanamu shakat a gidan gaba daya da,sa idanuwan ta,
Sai dai hakan bai hanamu kasancewa tare ba don sai ma,abinda ya karu gurin nuna min so da kaunar da yake min,
A haka mansur yazo suka koma school tare yabar mu da kewa a gida,

****** ********* ******
Satin shi daya,da komawa school yana ta kokarin covering din inda aka wuce shi,
Bai ko kawo zance wai wata Lima ba aranshi don shi kwata kwata yama fita zancen ta,
Tana zaune a class ya nufo hanyan da suke daga inda suke zaune Bicky ce ta fara hango shi a tafe yana rungumay da littatafan shi a hannun shi,
Ta zuguri Lima tace ke ashe da gaske guy dinki ya,dawo gayanan tafe da,sauri Lima ta juya don ganin shi,
Kallo daya tai mashi taji wani iri gaba,daya taji tsoro ne ko farga ya mamaye mata zuciya a lokaci guda,
Har yazo ya,shige daga inda suke zaune ba wanda ya iya daga kai ya kalle shi ko yai mai magana,
Sai daya shige take cewa cikin dan dafe kirjinta Vicky kin ji abinda naji danaga wanan guy din kuwa,
Har tsawon wani lokaci take jin gabanta yana,faduwa bab bab bab take taji gaba,daya gurin ma ya gundure,
Bashiri tabar cikin makarantar zuwa gida hankali a tashe sai dai tana zuwa gida sai a lokacin ta,samu natsuwa a tare da ita,
Sai zaraya take a cikin falon su hankali a tashe take ta rasa may ke mata dadi a,rai,
Don ganin da tai ma Hamza din yau yasaka zuciyan ta a cikin rudani don taga ya kara zama mata yaro karami yai wani kyau dashi ya,samu natsuwa,
Amma kuma tana jin wani tsoro da fargaba yana shiganta akan shi anya kuwa yanzu zata iya kara shawo kan wanan yaron yadda taga yai mata kwarji da kuma jarunta, a idon ta,
Lumshe idanuwan ta tayi don abinda takwji yana son fin karfin zuciyar ta ,,,,


Ayi hakkuri da wanan baida yawa amna ce gare ku don zalunci ne turawa wani ya karata batare da hakkin mu ba,

********************** ⬇ **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > aihausabooks@gmail.com

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels

WhatsApp Number: 09017242889


Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.

********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABUIDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,


Ba karamin farin ciki abokan karatunshi masu kishin addini sukayi ba ganin yanzu ba ruwan shi da,zance wan Lima din da tai mashi yaudara,
Duk wani abinda ya wuce a baya an sahilcewa juna andawo daidai kamar farko,
Yanzu dashi da Mansur koda yaushe kamar tip da taya,suke don suna gudun shu,umancin Lima,
Duk dai itama yanzu bata batun shi don ji take wani irin koda sunan shi aka kira tana,gurin hankalinta duk sai ya,daga,
Kwata kwata tafita zancen gaba daya bata batun shi kuma don ya fice mata a rai,
Sai dai acan kasan zuciyan ta tana yawan begen kasan cewa da shi,
Ga Bicky kuma tana yawan fada,mata cewa ita yanzu ta tsani al,amarin hurda da matasa yara kanana,
Don ba karamin zubar masu da mutunci zaman Lima da Hamza yayi ba a idanuwan jama,a,
Dalilai da masu dama suka sa zancen yafita a kawunan Jama,a kamar yadda malam Liman yai alkawari zai faru komai ya koma normal,
Yau sun dawo daga lectures kasancewa ana mugun zafi ya saka shi dan cire shirt din shi na sama ya zauna daga shi sai singlet a jikin shi,
Hannun shi rike da handout din da yake karantawa yana dan fitara,
Mansur ya shigo dakin a gajiye ya fada saman kujeran dake a dakin
Hamza yake mai sannu da shigowa kamar yadda sukeyiwa ju an su,
Yadan juya yana cewa Hamza ance damanan bana ana samun ruwan sama sosai a gida da alamar cewa damana zatai kyau ke nan,
Wani irin abu Hamza yaji a zuciyar shi don yasan cewa wanan damanan sai ahankali ke nan do bazai samu noma ba,
Saboda bai aje ba bai bawa wani ajiya ba, gashi a baya Allah ya taimake shi ya samu amfani masu yawa da albarka,
Sai dai kaddara ya riga fata ga kayan don wanan iftila,in da ya afka mai duk ya ruguzar mashi da plan din shi gaba daya,
Duk hiran da mansur yake ta zuba mai hankalin shi ya gurin tunanen abinda zai samu ya taimaki rayuwan shi dashi yadan noma koda kadan ne daga abinda ya samu,
Amma kuma baida wani madogara bayan Allah don babu mai baka,aro ko taimako dan katashi kaci gaba a wannan zamanin,
Kunci da tashin hankali duk sun mamaye mai zuciyan shi don baida wani madogara sai dai kawai abinda Allah yai mai,

****** ********** ******
Alhamdullahi yanzu komai ya wuce hankali ya kwanta, don kowa hankalin shi a kwance yake,
Dama haka rayuwan dan adam ya kunsa a lokacin da ake a cikin fitina zakaga hankalin kowa a tashe amma da zaran an roki Allah ya kawo saukin al,amari sai kaga an dan sha,afa da komai,
Duk da hankalina yana a kwance ban daina adduan da na keyi ba na neman samun rinjaye akan kowa ta irin masifa da zata iya kunnu min kai a gaba,
Musan man ma ta kishiya don Ummina, takan ce min sai nayi a hankali don mijina mai sha,awan mata ne,
Duk da maganan yakan bata min rai don a lokacin sai na dauka baki Ummina take min,
Amma kuma da mukai hira da anty hindatu take ce ita fa a tsaye take kyam gurin kokarin ganin ta kare kanta daga matan da ke kawo wa mijin ta hari ko, nuna kauna a fili,
Take ce min matan yanzu suke kokarin kamun kafa daga gurin yan uwa miji ko abokan shi har a tursasawa namiji ra,ayin aure, koda baida niyar karawa
To balle ni da miji tun farko nasan cewa mutum ne mai sha,awan mace tare da shi kuma macen yar gayu,,
Don haka na mike na zama mai yawan rokon Allah akan duk macen da mijina zai aura Allah yai min rinjaye a kan ta ta ko wani hanya Allah ya fifitani,
Wanan adduan wasa wasa ya zauna min a bakina don duk abinda nakeyi hankalina yana akan wanan adduan, dauke a bakina,
Ance mai hali baya barin halinsa yanzu Umma ta kara dinkewa sosai da, aminiyan ta mama Sa,a,
Abu dayane shine ta rage yawan zuwa can ta zauna amma dai suna tare da juna,
Don ko unguwa a tare sukan tafi indan haka ya kama masu fitan,
Don haka a sannu bakin halin Umma ya fara dawowa tafara sakani gaba da hattara da tsangwama a gidan,
Sai dai yanzu abin da dan sauki saboda na rage yawan aiyukan danakeyi a baya,sosai don mama hafsi ta kashe wasu aiyunkan a kaina,
Don dole su Asmau da Sa,a sukan fito su kama yi su ma,
Idan baki mata ba acikin labarinda nake baki a baya kin san na saye wake buhu biyu da dan kudin dake a hannuna lokacin da Hamza yazo ido rufe zai sayar da kayan amfanin gonan shi,
Yanzu gashi lokacin sayar da waban waken yayi don haka na bayar Ibrahim ya sayar min ida na samu riba sosai akan su,
Ranan da aka sayar min ranan Hamza ya zo weekend garin yazo da zuman neman kudin da zai dan yi noma dashi koda kadan ne don ya saba da sha anin noma sosai,
Ganin ya fada nan ya fada can amma babu inda ya samu ko dubu daya a,ro, kowa sai yakawo uzuri ya kindaya mashi,
Ya dawo gida jiki da sanyi baida wani kuzari duk hankalin shi a tashe,ya rasa mafita yadda zaiyi,
Mama hafsi tace ya sayar da wanan kangon gidan daya saya mata a,baya ya samu kudi yai abinda zaiyi dasu,
Sam bai sha,awan taba hakkin marayu da sunan zai juya su don yasan yakan karye a kan mutum lokaci guda duk su ruguje baki daya,
Haka ne ya dan nuna wa mama cewa tabari har a samu mai saye,
Sam bai san cewa ina da kudi a hannu na ba sai dai duk maganan da suke ina jin su daga inda nake a zaune,
Bayan ya shigo daki yana zaune abin duniya yakai mashi ko ina don ko magana na lura da baya,son yi sosai,
Ance tsakanin miji da mata sai Allah tsab na mike na sauke akwatina na inda na boye kudin da aka,sayar min da wake na kirga kudin na miko mashi gurin da yake zaune,
Cikin mamaki yake kallo na yana kallon kudin, cikin nuna mamaki yake tambaya na kudin maye wanan Humaira,
Nakai zaune a hankali daga inda nake tsaye nace kudi nane wanan yaya,
Kudin ki ?
Ya tambaya cikin tsureni da idanuwan shi yana son jin amsar tambayan da yai min,
Nake ce mai eh na wane kudin da na,sayar da,wanke dana saya a gurin kane,
Sai naga ya dukar da kanshi cikin dan jin nauyi da kunya sai kuma ya dan dago kai yana mai kallona a cikin jin nauyi,
Nace a hankali idan zasu ishe ka sai ka fara dasu mu gani,
Cikin wani murya mai ban tausayi yace Humaira kina ganin ba matsala idan nai haka ban tauye ki ba,ashe,?
Nagirgiza kaina nace ba matsalan komai dama fridge naso na canza dashi don wanan da nake amfani dashi ya fara tsufa yana son canzawa,
Amma zan ta maneji dashi har zuwa lokacin da Allah zai hore min na,sai, wani kuma,
Ajiyan zuciya naji yayi mai karfi tare da fadi a fili Allah nagode maka,
Yadda kika taimaka min kema Allah ya taimake ki Humaira nagode,
Haba yaya ai abina abinka ne basai kai min godiya ba a kan shi don nima da taimakon ka na samu haka ai,
Wasu kudin zasu kai goma sha biyar na kara mika mashi again,
Da sauri ya kara tambaya na sukuma wa yan nan na maye kuma nace nakane ,
Nawa ?
Ya tambaya a cikin mamaki yana kallon kudin batare da ya karba ba,
Nace eh ka manta kudin da kasamu a gurin gasar amfani gona kace nabar wa yan nan a guri na har ka tambaya,
Ido ya zaro yana mamaki tare da nuna kudin yana cewa kina nufin duk tsawonokacin nan kudin nan su a jeye a hannun ki, har yanzu,
Nace eh mana ba cewa kayi na aje ma,su ba har ka tambaya,
Shiru yayi yana tunane a ranshi cewa wanan yarinyar wata iri ne ita, kudi kusan shekara biyu da rabi zuwa uku tana ta faman boyon su haka ba tare da ta kashe su ba,
O ni Hamza Allah nagode maka da,wanan baiwar da, rufin asiri da kai min a cikin dakina,
Ya kara juyowa inda nake yana cewa Humaira na gode nagode da wanan rufin asirin da kikai min bazan taba mancewa da irin wanan halarcin da kikai min ba a duniyar nan,
Mikewa tsam yayi da kudin zuwa waje gurin iyayyen shi ina jin shi yana masu bayani dalla dalla ,
Zan iya cewa yaune rana na farko a,rayuwan zamana a gidan su Hamza danaji Umma ta bude baki tana sa min albarka kamar yadda ko wace uwa takewa dan ta,
Naji dadin wanan adduan da suke min don har da fatan Allah ya bamu zuria masu albarka tai muna,
Sai naji a raina a gaskiya nima yanzu ina bukatan haihuwa a rayuwana
Don Hindatu tace min idan har na haihu kila kiyayyana da Umma zai dan rage don albarkacin abinda na haifa,
A hankali nakai hannu na a cikina karo na farko ina mai adduan nima Allah ya bani haihuwa hakana,
Don ko Kubura da na riga aure duk da tafini cika yanzu tana da tsohon ciki a jikin ta haihuwa ko yau ko gobe,

****** ********** ******
Noma haikan Hamza ya fara da dan kudin daya samu a hannu na,sai dai da yake noman yanzu kudi yake bukata sai gashi tun ba a kai ko ina ba kudin duk sun shige ga a aikin noman,
Fada nan fada can haka har Allah ya taimaka gonan ya samu tsayuwa,sosai, komai yai kyau yadda yake bukatan gani sai da muce Allah ya albarkaci gonan ta mu kawai yanzu,
Ranan na dawo da gajiya,daga makaranta don yanzu muna rubuta final exam din mu ne a school din, mu,
Ban samu abinci ba don yanzu dama ba ko yaushe muke girki ba a gidan kamar baya, can,
Ina zaune daga kofana ina dama yar furar da na shigo da ita a cikin jakata don yanzu wani kwazaban shan fura ne yazo min sosai,
Ga yunwar da nake ji don haka nake sauri na dama ko zai rage min yuwan da nakeji don ji nake kamar banda hanji a cikina don yunwa,
Muryan mama sa,a ce ta,shigo tana sallama daga kofa ,
Daga inda nake zaune na karba mata tare da gaishe ta a cikin ladabi a matsayinta na,sarakuwana itama,
Take tambayana bayan ta karba gaisuwa na da cewa Umma fa tana cikine ,
Nace eh amma tadan kewaya yanzu zata fito namike nakawo mata kujera don ta zauna,
A lokacin itama Umma din tafito daga bandaki hannun ta dauke da butan data kewaya dashi,
Daga inda mama Sa,a take a zaune sai bingidan da kallo da dan yatsunan da takeyi,
Tun daga nesa Umma ke mata sannu da,shigowa tana cewa ashe har kin karaso yanzu nake cewa kindan taushe hannu kada rana yai muna don da kafa kikace zamu tafi,
Tace eh nadan tsaya ne balaraba ce ta shigo shine yasa na dan taushe hannu kin san halin dakaren mijin nata mai hali baya barin halin sa,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login