Showing 150001 words to 153000 words out of 299981 words
Ni kashe auren zan yi kowa ya huta don bazan iya ba ace aure ba,wani karuwa sai dan banzan fitina, don iskanci har ya,fara zagin iyayye,
Umma tace ai sha anin yaran ne yanzu sai hakkuri Sa,a don abinda kai kake hango masu su basu ganewa sam,
Tamike tana cewa ga gidan naku shiru mana kodaya ke dama ku haka gidan yake ba,wani karuwan yara sai dai aci akaiwa masai kawai amma anki aje muna dan kama hannu mu rika mu samu dan rakiya zuwa uguwa,
Take Umma ta tabe baki tace bari kedai Sa,a ni wanan abin ya kai min inda yakai wallahi ace gida shiru kamar gidan bariki,
Can kuma tace umm bari dai nai shiru duk da yake dai baka ganin naka a cikin cutarwa ka kyale shi dole ne kafada mai gaskiya,
Wani irin dimm naji a raina sai da cikina yadan bada kara kulululu don nasan sabon fitina mama sa,a ta jawo min kuma,
A cikin karfin hali nai masu adawo lafiya ban tsanmani Umma ta amsa min ba suka fice,
Furan da nake dokin sha sai naji duk yafita min a rai annurin fuskana duk ta gushe a lokaci guda,
Sai nake tuhumar kaina da kodai ina da matsalanr dasu suke ganin laifin nawa ne ni kadai bada Hamza din ba,
Sai nice kawai abin zargi a kullun laifina kawai suke ganin naki daukan wanan cikin,
Na mike tare da,daukan furan nakai cikin fridge na je batare da nasha ba,
Ina zaune ina hadiyan bakinciki mama hafsi tashigo gidan tun daga karban sallaman da nai mata ta,fahinci ina cikin damuwa,
Tun daga tsaye take tambayana may akayi halan Aisha ?
Nace cikin kakaro murmushi ba komai mama , inadan dariyan yake,
Halan Sa,a ta shigo gidan nan yau ko,?
Nabata amsa da eh mama yanzu suka fita zuwa uguwa,
Wanan bakar makiran mace yaya taki gane halinta har yanzu duk irin abinda tai mata a gidan nan kan zance yaron nan amma wai shine yanzu suka kara dinkewa kuma,,
Haka mama taita mita bata daki bata waje har yamma da,su Umma suka,dawo,
Don tasan cewa zataji ko maye a gurin Umma tunda ni naki fada mata komai,
Ai ko suna zaune ana hira kowa na gida bayan
isha,i yan gidan mu suka shigo suna cewa, Kubura ta haihu da yamman nan su Ummi suna can sun tafi dauko ta wai,
Nifa hakkurina akan rashin haihuwan yaran nan yasoma kai karshe ace aure kusan shekara uku har wanda sukayi aure a,bayan su sun haihu suko shiru kakeji haka,
To tunda kina da ja da al,amarin ubangiji ai sai kiyi yadda zakiyi su haihu din ko,
Mamace ta bata amsa da haka daga inda take zaune tana cin abinci,
Tace ni wai har yaushe ne za,a ce yaran nan sun wani jima basu haihu ba har ana batun tayar da jijiya akai
Nifa nasan Allah ne mai bayarwa idan lokaci yayi bawai sai mutum yaso ba,
Dole na na fadi hafsatu don wanan abin ya fara damuwa na,arai ace gida haka shiru babu hayaniyar yara da mutum zaiji yaji dadi a ran shi,
Kin san kowa da irin bayan shi wasu guntun baya garesu wasu dogon baya ne dasu sai andauki lokaci mai tsawo,
Don haka kibar wanan zancen haka yaya duk fa yadda akeyi yarinyar nan tana yin shi a gidan nan,
Tau ai bance batayi ba,shi maganan haihuwa wani magana ce ta daban don kowa nason yaga nashi a cikin karuwa dashi da ita ai ina son ganin kowa ya samu karuwa,
To sai kici gaba dayi tunda ki fi bukatar ganin su a cikin tashin hankali, ko yaushe don zancen ki tayar masu da hankali kawai yake a gidan nan,
****** ********** ******
Da kwana biyu Hamza ya dawo don yanzu bai dadewa bai shigo ba tunda mansur yana da mota kuma ba,wani nisane tsakanin sokoto da mu ba,
Wajajen shidda na yamma suka shigo don yin weekend, kamar yadda suka,saba, yi muna,
Na tare shi da murna ina fada mashi zancen haihuwan Kubura azatona shima murna zaiyi sosai jin kubura ta haihu don ko banza ai an zama daya yanzu,
Sai naji yana cewa aiyya ashe ciki gare ta,
Yadda ya amsa min sai banji dadi ba sai dai nabi bayan shi da kallo kawai cikin mamakin irin yadda ya amsa min,
Can yadan leko daga waje yana ce min kikai min ruwa na,watsa na cire wanan kayan na jikina,
Ban tsaya ba namike zuwa ksi mai ruwan kamar yadda ya umurta nakai masa,
Zandawo nake jin Umma na cewa da zuwan ka an tare ka da zancen haihuwan wata can kai ba,a baka labarin maidadi na gidan ka ba,
Nikan gaskiya dole asan abinyi don wanan shirun yai yawa haka a gidan nan gida kamar gidan GRA ba wani hayani a cikin sa,
Sai lokacin jin yadda Umma ta ke sake zancen ta yasa shi yin yake kadan yace Umma itama idan lokaci yayi ai zata samu din lokacine kawai bai yi ba,
Daga haka yai shegewan shi bandaki ya barta tana ci gaba da mita ita sai dai mutum yai taci yana kaiwa masa kullun ba wani karuwa a kai,
Ina jin Umma don haka nai shigewa ta dakina ina dan kata kimtsa guri don samun hilin daki,
Da dare nace zan shiga gidan mu na gaidasu kafin da safe naje gidan Kubura don ance mijin yaki yarda ta,dawo gida,
Kamar ba zai amsa min ba can dai yace min sai kin dawo kawai,
Banyi fushi ba jiki ba karfi nai sallama dasu Umma na tafi gidan mu don nai masu barka,
Na dan dade gurin mama,saude nafito zuwa gurin Ummina bayan na gaida maman Aina,
A dakin mun gaisa da Ummina shine nake fada mata irin sakani gaba da Umma tayi ita da kawar ta,
Dariya Ummi tayi tana cewa kai Rabi ho ita yanzu har yaushe kike da zata wani matsa haka wai baki haihu ba har yanzu,
Ta manta cewa koda akai auren ki bawai wani shekaru ne masu yawa akanki ba,
Nace cikin nunadamuwa nikan Ummi har abin ya fara damuna a rai don yanzu nafara saka abin a raina wallahi,
Ji nan Aisha ke dai ba jahila bace don gwargwado kin san addini yanzu,
Mutum baiyiwa kanshi abinda Allah bai tashii mashi ba,
Ki dinga dogaro da Allah domin shine mai bayarwa kuma,shine mai hanawa,
Idan kin biyewa jahilcin Rabi kika cutarwa kanki ke kika,sani don ni ba ruwa na,
Ban iya hauka irin na sarakuwar ki ba mutum yana girma yana kara cin kasa saboda jahilci,
Shiru nayi ina kallon zanen tabarman da nake zaune akai ina sauraren Ummi din,
Tai min nasiha mai kashe jiki nai sallama dasu nafito zuwa gida tare da masu sallama,
Washegari da zai fita na roki zuwa gidan Kubura don na dibata da jaririyar ta,,
Bai hanani ba sai adawo lafiyan da,yai min inda na,shirya cikin wasu atamfa zani da riga na,sa hijjab dina wanda ya sauka min har kusan kasa,
Mashin na hau don gidan yana da nisa da uguwar mu don haka ban dade ba na isa gidan nasu, wanda zuwana nabiyu ke nan,
Tundaga wajenake jin hayaniyan mata agidan wanda nakarasa ciki naga gidan dam da mata sai dai zan iya cewa bakin fuskane a gare mu don ba yan uwan mu bane,
Na gaishesu na karasa dakin Kubura din tana zaune bakin gado rugumay da yarta wace tai kashi ta rasa yadda zatayi don tace min bata jin dadin jikin ta,
Mun gaisa sama sama da ita take ce min cikin dakiya, na samu ruwa na,wankewa yarinyar jiki duk ta bata da kashi,
Nafita na samo ruwan na karbi yar na wa ke mata tare da dan dauraye ta tsab nan naga kayan su da,suka bata anjibgesu a gurin famfon gidan,
Bayan na mayar da yarinyar nakoma na,wanke kayan tsab inajin matan falon suna gulmana suna cewa wai kila ni yar uwar ta ce,
Amma in bashiba ita watake taimakawa da za,a taimake ta idan taje gidan mutane tana masu kalkon raini wayo kamar diyar wani attajiri,
Na gyara mata har dakinta nafita na,sayo turaren wuta na,sa a,dakin take dakin yafara kamshi jego kamar na kowa,
Ni ce nai ta bata abin sha tana,sha har take ce min tai matukar jin dadin jikin ta ranan,
Ina gida har bayan sallah la,asar sannan nai mata sallama na tafi gida, tana tayi min godiya,
Ban shiga gida ba sai dana tafi gidan mu nai masu magana akan a samu wanda zai kula da kubura don tana bukatar tai mako,
Tun a gurin maman Aina take ce min gaskiya ita bazata ba don da tai ciwo kwanaki ta tafi mijin bai kawo masu shayi sai dai wanda aka hada gaba daya na gida,
Ummina ce take cewa idan malam ya dawo zata roke shi ta tafi dama tana gudun taje ne maman Aina tace tai mata cin layi,
Nai masu sallama na tafi gida duk da yamma yayi na samu komai ba,ai min ba don mama Hafsi bata nan ta tafi tallan kayan gwanjo da take sarowa kasuwa don samu rufin asirin ta,
Tun a,waje na aje hijjab dina na soma tara kayan wanke wanke nakuma yi shara tare da dora girkin dare,
Allah ya taimake ni nagama komai da wuri kafin duhu yayi don tuwon masara nayi da miyar kuka,
Nabawa kowa nashi na,debi ruwan wanka na watsa don naji sanyi a raina sai dai ziciyata fam take da tunanen halin da na riski Kubura acikin sa,
Ina tunanen cewa watau dai haka rayuwan auren yake ko ina ko wani gida da kalar tasu matsalar rayuwa ke nan,
Allah dai ya karawa ma,aurata daraja da rufin asiiri juna duniya da lahira,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABUIDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA YAR UWA DON HAKKIN WASU NE, BA,A YAFE BA ,,,
Haka Ummina ta dage taita kokari da Kubura da jaririyar ta wanda a,dan wanan zaman Ummi ta fahinci halin mijin su Kubura din,,
Haka yasa ta dinga kwantar mata da hankali tana mata nasiha gwargwadon yadda duk uwa ya dace taiwa yar ta nasiha, akan zaman aure,
Dafarkon zuwan Ummi sai ta lura cewa Kubura din tana wa yar ta wulakanci saboda laifin ubanta da ya shafe ta,
Ummi ta shigo gidan sun dan gaisa da Kubura din yan min tina kadan sai yar jaririyar ta,soma kuka,
Amma,sai Kubura tai biris da ita kamar bata jin may take yi,
A,a gyara mana ki bata nono tasha Ummi take cewa Kubura din,
Barta, tai tayi kawai Ummi idan ta gaji zatayi shiru ai,
Ummi tace auzu billahi may yai zafi kuma haka kubura da zaki horar da yar malaukar Allah da bata san momai ba a,rayuwa,,
Juyawa Ummi da yar jaririyar baya tayi yayin da jaririyar ke ta faman tsala ihu,,
Jamila ce kishiyar Kubura taji ihun yai yawa ta leko dakin don duba,yarinyar, turus taja ta tsaya, don ganin Ummi a dakin,
Gani yarinyar a hannun Ummi yasa ta cewa ai ina ce ba kowa adakin ne ta juya tana kallon Kubura wace ta kwanta ta,bada baya,
Ta gaida Ummi wace ke kokarin ba wa yarinya ruwa ta,sha,
Jamila take cewa kin gane ta mama bata son bawa yarinyar nan nono ko may zatayi dashi oho,
Ummi ta juya gurin da Kubura take kwance ta basu baya take cewa a fusace,
Tashi ki bata nono nace kamar ba,zata juyo ba sai can komay ta tuna sai ta dan dago daga kwancen a hankali,
Idanuwan ta da,Ummi ta dan kalla taga sunyi wani irin hulu hulu da su alaman tayi kuka,,
Mika mata yar Ummi tayi inda ta dan mike ta gyara mata rikon yar sai kawai ta kama zukar nono kamar mayunwaciya,
Ganin yarinyar tana shan nono yasa kishiyar tata,juyawa tafita tabar dakin,
Tana fita Kubura ta zare nonon daga bakin yarinyar ta kokari azata saman gado,
Idanuwa a,waje alamar tsoro Ummi tace lafiyar ki kuwa,Kubura,
Ta,dan dago kai ta kalli Ummi kadan ta danyi tsuki tare da juyawa, udanuwan ta sun kada sunyi jawur tace,
Ummi ko wanda yai sanadin zuwan ta duniya bai damu da ita ba balle ni,
Saboda tsabar kiyayya tun ranan dana haihu ina jinsa a falo yana tambayan may na haifa akace mai mace ce ya juya ya fita yana cewa wai mace a gidan nan kuma,
Nan ta dan fara bawa Ummi labarin irin kuncin rayuwan da take a cikin gida Nura,
Ummita ce cikin murya mai taushi bayan ta gama sauraren Kubura din,
Kubura ke kin san may kika haifa ne da kike taya shi jahilci,
Nasan ana zaluntar ki da,yawa Kubura amma kiyiwa Allah kada ki yarda ki fada a tarkon shedan ku aikata babban zunubi dake dashi,
Ki rungumi yar ki da Allah ya,baki, ki gode mai da wanan kyautar da Alkah yai maki,
Don darajan Annabi kada ki biyewa wanan zance har ki zalunci kanki da yar ki,
Kiyi hakkuri kinji ki nuna mashi ke kina da tauhidi kin san Allah a,rayuwan ki don haka kikama yar ki kisota kamar yadda kema iyayyen ki suka so ki,
Amma idan kema kina haka tankar kin ba da wani kafane natozarci wa yar ki,
A take kubura ta barke da wani irin kuka mai ban tausayi tana cewa,
Ummi tunda bai kaunar ta ni may zai sa naso ta ai gara ta mutu kowa ma ya huta,
Ummi ta girgiza kan ta tace wa zai huta don ko ta mutu shi baiyi hasara kece kikai hasara, don shi yana da wasu diyan da yake gani,
Ke kin taba ganin idan laifin wani ya,shafi wani har aiwa yarinya jaririya irin haka horo da yunwa,
Haka zalika wallahi daga ke har shi alhakin wanan yarinyar ya isa Allah yaki saka maki tunda kin dau fan sa da kanki,
Don haka ki tashi ki shayar da yarki ki barshi da Allah,
Tsayen lokacin da yarinyar ke a jikin mahaifiyar ta tana zukar nono Ummi kuma tana ci gaba da yi mata nasiha,
Tana kuma kallon yadda yarinyar ke zukan nono tare da sauke ajiyan zuciya irin ta wanda ya sha kuka,,
Da uwar da diyar sai duk suka bata tausayi don haka Ummi ta sha alwashin sai ta gano may ke faruwa ne tsakanin ta da mijin,
****** ********** ******
Muna daki ni da Hamza yayin da,duk sauran yan gidan muna,jin haya niyar su a waje,
Mukaji wani yaro yashigo yana sallama, ba,wanda ya karba mai sai mama dake can ta karshen gida,
Yaron yagaishe su yake cewa ance idan yaro mai shago yana gida ana sallama dashi,
Karasa can kofan ko zai ji yafito don ban sn may yake har wannan lokacin rana ya huduba a cikin daki,
Idan kayi sallama basu fito ba sai kayi tafiyan ka ka fadawa wanda ke sallama yana barci,
Mama hafsi ce ke cewa haba haba yaya ina fada maki wanan abin ba darajan ki bace wallahi,
Lokacin kafin Umma tai magana ya mike daga inda yake kwance dama ni zobo nake kullawa ina zaune,
Amma a zaton Umma a kwance muke muna wani abin na mata da miji ne,
Fuskan shi alamar barci da gajiya yake tsirga miyau yana cewa yaron wake sallama dani ne,
Yaron ya bashi amsa da cewa wani mutum ne a kofan gida,
Bayan ya fita dan ajima kadan sai ga shi ya shigo gidan ya samay ni a waje na fito da kayan da nai amfani wanda sai lokacin Umma ta fahinci aikin da nakeyi a cikin dakin namu,
Mama ya fuskan ta yake fafin mama yarki ce aka zo kira gidan malam sanusi wai zata duba masu wata mai ciki ce,
Murna mamata fara yi tana cewa ikon Allah ashe har lokaci yayi da zamu fara cin amfanin ilimin mu,
Maza shirya kije ki gani kin ji idan yafi karfin ki sai su tafi asibiti,,
Daga idan Umm take take cewa amma kuwa da an fadi, yanzu tana yarinyar mace za,a shigo sallama mata wai yazo duba mai ciki
To may amfani wayar da kan da aketa ma iyayye subar yara mata suyi ilimi, yanzu ba ga amfanin nata ilimin mun fara gani ba,
Mata nawa ke wanan uguwar may yasa ba aneme su ba sai ita yar karama da ita,
Kinga amfanin ilimin ke nan sai yaro komai kan kantarsa ya,zama babbba cikin manya,,
Hand glove na dauka tare da,sauran abinda zan bukata wanda zai taimaka min,
Sai faman yatsunan fuska Umma takeyi har ta kasa rufe baki tana cewa,
Daukan magana yaron da bai ko san yadda ake daukan ciki ba wai shine zai duba mai haihu kai zamani ina zaka da mu,,
Nafito ina saye da hijjab dina har kasa hannu na yana dauke da yar jaka nai masu sai na dawo,
Badai girin girin ba tai mai don idan har an dauko da zafi zai kare kan mutum,
Murmushi kawai nayi tare