Showing 153001 words to 156000 words out of 299981 words

Chapter 52 - Sarautar Mata By Makawa

04 Dec 2025

17699

da hade zuciya saboda wanan mugun fatan da Umma take min ya kuma sa jikina yai sanyi ban jin courage akan akin da zan tafi yi,
Innalillahi wa,inna,alaihim raj,un,
Shine abindayazo min a,rai daidai lokacin da zan kada kafana a zauren gidan malam Sanusi tare da furta Allah kataimakeni ka rufa min asiri,,
Nashiga gidan da,sallamana yayin da na hango mata a tsatsaye daga kofan wani daki wanda hakane ya tabbatar min da nan ne dakin mai cikin,
Ku jaye nan ku bata guri ga malamar asibiti nan ta iso,
Na,gaida matan da na samu a gurin cikin mutunci suna karba min ina shiga nake jin ana cewa,
Wanan Yarinyan ce mai karban haihuwan wai ikon Allah shi malam karaman yarinya zai kira duba mai tsohon haihuwa,
Kiyi nishi da karfi mana ki samu ki rabo dashi lafiya,
Cikin murya na mai sanyi nace a,a mama ki barta na duba nagani kada ta yawaita nishin nan da yawa,
Saurin juyuwa inda, nake tsaye mata biyun dake dakin sukayi, suna kallo na,
Cikin mamaki amma kuma ba wace tai magana kowa a zuciyar ta take magana a rai,
Na karasa gaban matan dake zaune duk tai zuba ina mata sannu ya jikin ta ce da sauki na juya gurin matan nace ku dan bamu guri dan Allah,
Basu mussa ba, sukai waje kowa tana wani tabe bakin ta, sune ce wa matan waje zamuga ikon Allah,
Sannu ya jikin ta amsa min da kyat na kara gab da ita nace kwanta mu gani ba mussu matar zata iya haihuwa na na duba naga haihuwa da saura sosai,
Ga kuma zazzabin dayai mata yawa a jikin ta sosai shine suka gani suke cewa wai nakuda ne ya ta so,mata,
Nadan leko tare da daga labule ina cewa, don Allah ko maigidan yana kusa ashe bai fita ba yace a razane gani,
Nace mai, ya shigo ya,shigo dakin muka tsaya inda take zaune nace mashi ba haihuwa bane zazzabine ke damun ta idan ba an samu ya lafa ba nakudan bazai iya tasowa ba,
Amma insha Allahu idan ya kwanta nan da kwana uku mai zuwa ma zata iya haihuwa da yardan Allah,
Yace tau bakaji ba ai dama ni naga wanan wahalan yai yawa wallahi,
Nan na rubuta mai alluran da zai sayo muna nai mata tare da kwayoyin da zata sha,
Naiwa matar allura tare da bata kwayoyi nai mata sannu na fito sai bina da kallo matan gidan ke yi,
Na juya gurin ta ina cewa, don Allah kada ki kara irin wanan nishin haka don zai iya jawo maki matsala a rayuwan ki,
Nai masu sai anjima suna cewa ikon Allah ga haihuwa muna gani amma karamar yarinya tace muna wai wani zazzabine can,
Ta samu barci sosai wanda ya nuna alluran ya karbe ta sosai ga abinci da nace a bata taci sai ta koshi,
Tare muka fito da maigidan, yana min godiya tare da kokarin bani wani abu amma sai naki karba nace Allah dai ya bata lafiya,
Nakara zuwa duban su Kubura da yar ta na samu tana barci wanda hakan ya nuna min ta samu, lafiya,
Sai da,ba magani ko kwalba daya a gurin yarinyar, ba a saya mata komai ba na sa yaro lafiya,
Nafita don ina da dan kudin dana hada zan ba uwar buki shina fita wani chemist na kwaso mata kwalabe har guda biyar,
Ko da na dawo na samu ta tashi tana zaune tana shayar da yar ta nanuna mata yadda za,a bawa yayinyar magani,
Godiya ta fara yi min sai kuma ta kasa saboda idanuwanta da suka ciko da hawaye,
Ummi ta dauko abinci ta aje mata agaban ta tace takawo yarinyar ta sauko taci abinci,,
Tana cin abincin muna hira da ita ni ranan har ta ban mamaki don ba daukan kai kamar yadda ta saba yi min a baya tana daukan kanta wani abu, can,,
Ban jima a gidan ba nai masu sallama na tafi don ina gudun kada ranan suna a hanani fita don karamin aikin Ummane wanan,
Aikin gonan shi ya hana Hamza yabi, Mansur su koma don za ai mai aikin karshe a gonan,
Don haka yana garin za ai sunan Kubura wanda ban gane mashi ba sam bai kaunan yanzu nai zancen ta sai naga yana wani daure fuskan shi,
Yana nuna min bai ra,ayin zancen ta wanda hakan yake matukar bani mamaki sosai, don haka yau ma da nake son tambayan shi cewa gobe suna ina son shiga gidan mu gurin aiki kafin a tafi gurin maihai huwa,,
Ai kuwa ina tambayan shi kaman wanda yake jirace dani yai cikina da masifa sai da nai mamakin shi don ban taba zaton haka ba,
Har yana cewa may kike a gare su ne wai da kike cewa sai kin shiga harkokin sune wai,
Rana na farko dana fara bashi amsan maganan shi don zan iya cewa tun dawowan shi yanzu ya canza min halaiyar shi ba kamar yadda muke ada can baya ba dashi,
Aganin ka ne ban komai a gare su amma ni nasan komai nake a gurin su tunda duk abinda ya faru dani gidan nan tare suke zuwa da Ummi,
Ni ki ke bawa amsa haka yau Humaira to nace bazaki ba shi ke nan ko?
Yama fice yabar min dakin ina zaune cikin bakin rai da mamaki don na,rasa ma, may zanyi,,
Ranan haka muka kwana baram baram ba wanda ya kula dan uwan shi saboda kowa ya hau,
Da safe na tashi nai aiyukana kamar yadda na saba nai wanka na koma dakina nai kwanciyana,
Ina jin yan uwan shi suna tambayana ko har na,wuce ne gurin sunan gidan mu don sunga mutane suna shiga,,
Wani irin bakin ciki ne naji ya kumay ni amma sai na dake kawai don ban da yadda zanyi tun da banice keda ikon kaina ba,
Zuwa sha daya ya shigo gidan fuskan shi ba wani walwala a tare dashi,,
Nasan yai hakane don kada naga daman shi nayi mai maganan fita zuwa gurin sunna,
Kawai nima na fulanin ya taso min sai nai zuciya na share shi ban ko kawo zancen ba a raina balle a fili,
Sallama mukaji daga kofa na wani mutum abinda yasashi fita don duba mai sallaman ke nan,
Zuwa can sai gashi ya,daga labule yana cewa malam Sanusi yake son kije ki duba mar matan sa,
Kamar ba zan tashi ba don yana fadi haka ya sake labulen dakin ya koma inda yake zaune yana karyawa,
Dan jim nayi zaune wata zuciya na ci na don ji nake kamar nace sukai ta asibiti don rai na duk a bace yake, a lokacin,
Sai kuma na tuna cewa ai ceton rai zan tafiyi don ba itace tai min laifi ba da zan ki dubata,,
Nashirya tsab nafito zuwa gidan tare da mashi sai nadawo na yiwa su Asmau dake gida sallama su ma,
Na samu matan gidan a tsaye cirko cirko don maigidan ya hana kowa shiga gurin matar tashi,
Badon komai ba sai don bayanin da nai masu ranan na cewa,
Idan mace tayi dan haihuwa da yawa ko ta fara manyan ta idan tazo haihuwa ba ,a,son ta yawaita nishi dayawa saboda yana haifar mata da illoli da yawa arayuwan ta,
Zai iya jawo mata yoyon fitsari zai iya jawo mata wani sanadi wanda zai haifar mata da hyniar, da dai sauran abubuwa da dama,
Wanan bayani yasa zuciyan malam sanusi a cikin tsoro da fargaba don haka ya hana kowa shiga gurin matar shi,
Ina shiga dakin na hango matar can kuryan dakin ta tayi daidai da kafanta tana sauke nishi a hankali ga gumi ta hada sharkaf a fuskan ta saboda zafi ta kunkumay labule babu ko ventolation a dakin,
Cikin gagawa na isa gurinta ina mata sannu da ya jikin,,
Kanta kawai ta iya gyada min tare da cizon leben ta duk ta hada gumi,
Da sauri na nufi gurin window din dakin na dan daga kadan don iska ya samu ya dan shigo muna,
Na dan zo gurinta nace mata ko zata yarda na duba stage din da take don mu san abinyi,
Na samu ta gyada mun kai da kyata nadan dubata inda naga ai gap take da haihuwa insha Allah don kiris ya saura mata,
Nadan fara bata taimakon gagawa gurin tracing din kan yaron daidai,,
Sai naga haihuwan yazo daidai lokaci inji Allah, nace mata a hankali ki tayani rokon Allah ya bamu sa,a ki haihu lafiya tace tau Aisha,
Da ikon Allah nabata taimako daya dace nasamu Allah ya bamu sa,a ina addu,a tanayi take jikinta ya dauki wani irin bari, nace takara dan nisawa da karfi ,
Gabaki daya naji taimin wani irin nauyi nace tadai daure takara dan nisawa sai ko ga jariri ta sunbulo shi gabadaya har da uwar tafiyan sun fito tare ,
Jinayi nima jikina ya dauki bari don shine karo na farko dana karbi haihuwa ni kadai batare da manyan mu a gabana ba ,
Sai naji yaron ya dauki kuka dole na tsaya nadaure don na taimaka mata,
Naji tawani nisa tana fadin alhamdullahi Aisha nagode nagode nace ki godewa Allah, Anty,
Sannu sannu kinji Allah ya,raya muna Allah baki lafiya ke da danki tana nishi take cewa Ameen,
Idanuwanta a lumshe ta koma daga bakin gado ta dan jingina,
Na tambayeta inda reza yake don na taimakawa dan dake kwance saman leda yana ta tsala ihun neman agaji,
Tace nakira Suwaiba a waje tazo tabani rezan nan nakwasa da sauri zuwa wajen dakin ina cewa ina suwaiba
Nan nasamu matan gidan da suke tsaye cirko cirko sai murna sukeyi, hannuna yana saye da hand glove da dan jinin haihuwa sukabi hannun da kallo,
Nace wace suwaiba don Allah ki zo kibani reza,
A tare muka dawo dakin da mai sunan Suwaiba ta dauko min duk kayan da suka aje na haihuwan,,
Na yanke cibin yaron nai mata komai yadda ya dace namikowa matar mai suna suwaiba, dan bayan na nade yaron a zanin da tabani,
Saida naiwa itama uwar yadda ya dace nai mata sannan na tatara komai nafito dashi daga waje ina maigodiya ga Allah ubangiji subbahanahu wata,ala,,
Nan nakama tsinkayo muryoyin matan dake waje suna cewa ikon Allah yanzu ashe yarinya karama haka har ta iya karba haihuwa kai amma gaskiya bature mugun mutum ,,
Nabasu izinin su shigo su ganta inda na koma daga baya gurin da Suwaiba take rugumay da jariri nadan bude zanin ina kallon dan yaron dake lafe ajikin zani yana ajiyan zuciya idanuwan shi a rufe amma yana dan tsotson baki,,
Wani dan abu naji a raina dama ace wanan yaron nawane da yau na,wuce gorin Umma,
Nace a raina karo na farko nima Allah yabani haihuwa naga zuria ta,
Nace a cikin murmushi tau sai anjiman ku zan tafi Allah ya raya muna,
Sai dai a,samu zam, zam da dabino adan bashi, suka ce insha Allahu,
Har kofan gida tsohuwar gidan da takaini tana min godiya da fatan gamawa da duniya lafiya,
Shiko malam sanusi sai faman washe baki yake saboda farincin don gani suke nice nai dabaran da matarshi ta haihu ba,wani wahala,

****** ********** ******
Wanka nashiga na tsabtace jikina nafito nai alwala don lokacin sallah ya gabato, ko,
Mama Hafsi ce da taga takalmana a kofa ta leko tana ce min a,a dama kina gidan nan Aisha nace eh mama sai dai yanzu na shigo don na dan shiga nan gidan malam sanusi karban haihuwa ne,
Tau tau madallah ince dai an sauka lafiya ko ? Murmushi nayi nace eh mama ta haihu tunda zu lafiya cikin ikon Allah,
Da sauri mama tace kaji ikon Allah ko yanzu kece kikai karban haihuwan da kan ki,
Murmushi kawai naiwa mama ba tare da na bata amsa ba umma wace ke fitowa daga bandaki take cewa ikon Allah ashe an sauka din ,
Cikin zolaya mama tace ance maki sarakuwae tawa ta wasa ce hmmm ai sai ki bari a yabe kuko ?
Sai duk aka tuntsire da dariya a tare mama tana ta faman yaba kokarina,
Hamza ne yashigo gida hannun shi dauke da leda mai zanen yellow da baki yake cewa su Umma barka da gida,
Yana kokarin miko min leda ita ko Umma idanuwan ta kyam a ledan da yake miko min tare da kara miko min wasu kudi zasu kai dubu biyu,
Nakarba da mamaki sai yake cewa malam sanusi ne yace nabaki kuma ya hada ni da Allah kada mu mayar mai wai ya baki ne saboda Allah,
Wanan kuma wai kayan sayine ki jika makoshin ki dashi kiji sanyi,
Wani kunya naji sai nace a hankali nagode juyawa umma tayi zuwa yin alwala tabar gurin,
Har ya juya,zai tafi sai kuma ya juyo yana ce min idan baki gajiba kina iya shiga gidan sunan yanzu,
Haushi takaici duk ya rufe ni suna a gidan mu ne zan shiga da karfe biyun rana bayan gani nan baki da hanci,
Nanu su Umma da ledan ina cewa mama ga kayan nan sai a bawa kowa ya sha ko,?
Mama takarba tana cewa Allah dai ya baki naki kema robon mu dauka har mu aika,
Na kirga kudin dubu uku nr cif na bude baki don ganin suyi yawa tare da juyawa gurin mama ina cewa mama har fa dubu uku ne kudin,
Kodai zan rage na mayar mai da kudin ne don suyi yawa wallahi,
An ma kinji abinda mijinki yace yace ya rantse ko kin mayar bazai karba ,
Nace cikin jin kunya na gode na cire dubu daya nabawa su Umma su raba ita da mama din,
Kamar nai fushi naki zuwa gurin sunan sai dai, na daure kawai na tafi don gudun zargin rashin shiga na,
Aiko na,samu an kwasa za,a tafi gidan su Kubura a gagauce na shiga gurin Ummina ta hauni da fadan rashin zuwa da,wuri da banyi ba,
Naimata bayani yadda duk mukayi tave to al,amarin mazane sai hakkuri don haka idan dai kin san bai barki ba ki koma gida kawai ban son fitina,
Nace a maraice da idanuwa da suka kawo kwalla shi ya barni da kan shi ai yanzu din,
Jin ana kirana,waje nazo mu dauki kayan da za,a tafi gidan Kubura dasu yasa nabar dakin da sauri na,samu yan uwana muka kwasa sai gidan maijego tare da kayan arziki niki niki, irin su masa, guguru, dibbila, su man gyada shimkafa, maggi kifi albasa, da sauran su,,
Mun samu gidan sunan da yan uwan miji Kubura makil sai ita da kawayen ta duk da basu da yawa a dakin ta,
Nan ta fara muna korafin rashin zuwan wasun mu mu zauna da ita take cewa tundai ke yar Agwai na zaci ko banga kowa ba ke zanganki kinzo zama dani,
Murmushi nayi kawai ina bata hakkuri din banda abincewa saboda nima gaskiya haka na so nai mata nazo na zauna da ita tun safe sai hakan bai samu ba,
Nan aka,shiga sha,anin suna yarinya,ansa mata,suna Fatima wai sunan yar maigidan ke nan,
Ashe anty Hindatu tana gidan ban sani ba,sai da ta leko dakkin tana nemana nan muka fita muna hiran yaushe rabo da ita,
Can take ce min wai yaya alkar mu da Kubura yake sai nake fada mata yadda muke,
Tace mijin ta dan iska ne baida mutunci saida iyayyen su sukai mai tas yau da safe wai baiyi murnan da haihuwan ya mace da tayi mashi ba,
Kin san ance wanzan bai so a jikin sa yana gudun a rama abinda yakewa diyan mutane a yar shi,
Aiko ita yar uwar taki ance cafkeshi tayi don yaso ya yaudare ta ya gudu da farko da yake ita yar duniya ce itama sai ta kamashi,
A raina nace ko ina kuma suka samu wanan labarin haka kai mutane a kwai tsegumi,
Take ce min ai kila bata,san halin dan iska bane har ta yarda ya aure, ta,
Dan cacane fa kuma ga kalwanci da yakewa manyan gari yana daukar masu mata ana,bashi kudi da manyan motoci,
Da sauri nace Subbahanallahi shi Alhaji Nura din tace shi mana ai bata rasa sanin halin shi ita,
Ko ita uwargidan nashi yar uwar namu ai don tana da dan nakasa aka hada su dashi hakkuri take da dan iska sam baida hali baida mutunci, ko kadan,
Itace ma takai karan shi yau da safe wai yaki yiwa maijegon da yarta sayayyan komai na suna,
Takr naji tausayin Kubura ya kamani har cikin raina na tausaya mata matuka,
Nace mata cikin muryan tausyi kin ko san da itace zata auri yaya Hamza ana gobe a saka ta a lalai taki yarda tasa baba kuka ganin baba yana kuka nace ni a daura dani,
Ta tambaya a gagauce da cewa ke ki bari dan Allah dai Aisha ?
Nan na dan bata labarin yadda abin ya kaya tace kinga ikon Allah ko,
Gashi tayi zaben tumun dare tafada gurin dan caca kuma kalwani,,,


Ina muna fatan fara azumi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login