Showing 156001 words to 159000 words out of 299981 words

Chapter 53 - Sarautar Mata By Makawa

04 Dec 2025

17642

lafiya Allah ya hada mu da rahamomin sa dake cikin wanan wata mai albarka,
Sai dai muyi hakkuri da juna don idan azumi ya kama ba kullun ne zaku dinga jina ba sai a hankali, zandinga post idan na samu time insha Allahu,
Masu fitar min da novel waje zuwa wani group na bar su da Allah ya isar min da isar sa,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA,,
SEENABUIDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE

Wanan karban haihuwa danayi a cikin shiyan mu shi ya taimaka min sunana ya samu daukuwa ga mutanen uguwar mu har suka fahinci na yi karatin health nasan wani abu,
Yanzu mutane suna dan shigowa guri na don neman taimako,
Yaran su dama su kan su matan sai suke ganin sun samu hanyan sauki ba sai sunje asibiti ba,
Idan naga abin yafi karfina,saina turasu su tafi asibiti don ban yarda nai kasadan dubu ciwon da,bazan iya treating din sa ba na jawa kaina matsala,
Don duk bakin ciki da hassadan su Umma ya kai min ko ina yanzu sosai ban jin dadin irin yadda Umma take yawan, nuna min hassada akan wanan ci gaban da na,samu,
Don duk wace tai sallama da zaran Umma ta fahinci cewa mace tazo ne don gani na yanzu zata bata ran ta ta,shiga yadda magana ke nan a tsakar gida kamar yarinya karama,
Sannu sanu har ankai ga cire amfanin gona yanzu mutane sai aikin gona ake ko ina ana faman cire amfanin da,aka saka,a gona, duk da dai daman ta bana ta dan zo wa mutane da yar gardama,don duk wanda bai yi shuka,da wuri ba ya samu dan matsalan fari na ruwa da,akayi a karshen damana,
Shi ya kawo lalacewan gonakin mutane sai ba a,samu anfanin gona wadattace ba, sosai,
Duk da wanan korafin na jama a mu dai zamu iya cewa Alhamdullahi don gaskiya mun samu ci gaba sosai don shi kan Hamza ya samu amfanin gona mazu yawa, a gonan shi har ma yadda bai taba tsan mani ba,
Ranan da yazo yana zancen yadda ya samu albarkan gona kowa na murna da farin ciki, a gidan sai mama Hafsi kawai ta kada baki tace,
Gaskiya hannun Aisha yana da kyau don a gaskiya da badon taba da bazamu san yadda zamuyi ba har ma da ace a wajen wani aka karbi kudin nan ba lalai bane a samu amfani mai yalwa irin haka don wani hannun ribas gare shi,
Koda anyi amfani da abin shi sai kaga komai na mutum ya tafi ya lalace kamar yadda gara take cinye duk abinda yai karo dashi,
Azatona Umma zata ji dadin abinda mama ta fadi a kai na ,
Amma abin mamaki sai naga daga ita har dan ta kamar ba wanda yaji dadin zancen don ita umma cewa tayi
Wanan ai ba yin wani bane hannun wanda ya dafa abin ne kawai da albarka,
Shi ko Hamza ji nayi yace hmmm mama ke nan ai wanan abin ba haka yake ba,
Zataci gaba da magana amma sai Umma ta saka wa mama waigi da cewa don Allah hafsi kibar wanan zance
Ina wanan taimako ne tsakanin mata da miji bawai abin wani zance bane,
Mikewa Hamza yayi don yasan cewa yanzu uwayen nashi suna iya kaurewa,akan wanan zance,,
Duk da banji dadi ba yadda Umma ta zage tana wa yar uwar ta akan dan maganan da baikai ya kawo ba, don kawai ta yaba zance na, ta rufe ido tai mata tas tadai shige daki ta bar ta nan,

****** ********** ******
Alhamdullahi don komai ya kammala ancire albarkan gona gashi kuma Hamza ya kammala karatun shi lafiya yanzu yana zaune a gida suna jiran sakamako,
Wanan dalili yasa ya fara sana,a haikan wanda cikin yarda Allah sai abin nasa ya fara bunkasa, mai,
Sannu sannu ya fara shiga kauyuka ya na,sayo hatsi yana kawowa birni ya na,sayar wa,
Inda ni kuma ina dan buga bugana a gida ina samun dan abin rufin asiri ga yar sana,ata,
Dan maganin ciwon kai maleria, ulcer, pain relief da,sauran yan magani duk ana shigowa gurina sayen su, don haka na,rage wasu yan bukatuna,
Ganin yana samu akai akai, yasa mutane ganin ai Hamza ya dan samu ci gaba a irin kudin mutanen kauye,
Nidai tunda aka cire amfanin, gona bai min zancen kudin da ya karba a guri na ba balle nayi zance canza sabon fridge da nake son yi ba,
Haka yasani dan kokarin kukutawa gurin tara dan kudina don na,sai wani sbon fridge din don ina da niyan yin hakan,
Da kyat da taimakon Allah da mutanen arzikina na sayo sabon fridge dina LG mai saurin yin sayi da kuma kankara,
Aikuwa sayen wanan fridge din ya kara jawo min bakin jina sai umma take gani dan tane ya bani wanan kudin na,sayo fridge din,
Ranan da,nake kwana biyar da,sayen fridge din sana,an tawa naji Umma ta tutse dan ta yana ta mata rantsuwar kan cewa wallahi ba shine ya saya min ba asailima bai san da cewa zan sayi fridge shi,
Amma ina sam Umma bata yarda ba,sai cewa take gasu da lalurar auren Asmau a gaban su, amma shine zai kwashi kudi don tsoron bacin raina ya sayo min fridge dashi,
Idan bashi ya saya min ba wa nake dashi da zai sayo min wanan dalele fridge haka,
Ya marairai ce murya yana cewa wallahi Umma bani na saya mata ba ki yarda yadda kika gan shi nima haka nagan shi a gidan nan,
Amma sam Umma bata yarda da rantsuwar shi ba sai fada take zazaga mashi tace sai fa ya mayar ko ya,sayowa Asma,u abubuwan da ta bukata ya sayo wa yar ta mai shirin aure,
Don haka ita yanzu tunda ta fahinci cewa duk neman kudin shi a kaina yake karewa zata dauki mataki a kai,
Daga inda mama take tsaye tai min nuni da na kyale kada na tanka, don haka ma nai shigewa na daki kawai,
Can naji yafito yana cewa zata iya bincikawa taji in har shi yasaya min ta dauki matakin da tace din,
Nan ya shigo daki rai a bace ban kula shi naji har zai fita ya juyo yana ce min,
Humaira kina son ki hadani fada da mahaifiyata a gidan don ta kasa fahintar cewa bani ne nake saya maki wa yan nan abubuwan ba,
Duk da nasan cewa kokarin ki kike kina sayan abubuwan ki amma ya kamata ki san yadda kike abubuwan ki don gudun jefa zargi a zuciyar umma,
Mamakin zancen shine ya kamani a zuciyana kwarai da gaske, don ban san may ma zan ce mai ba sai binshi da kallon mamaki danayi a lokacin da yake fita daga dakin ,
Zuwa rana Zarah ta,shigo gidan inda tazo kamar yadda take zuwa kwana bibiyu don duba mahaifiyar ta da yan uwan ta,
Nan suka gaisa ina jin su harda mama wace tafito daga dakin ta don ranan bata fita ba tana gida,
Don yanzu har da,su turamayn zanuwa take dan daukowa ta sayar wa mata bashi ,
Nafito muka gaisa da zarah wace ke zaune saman kujera dan tsuguno tana shan raken da ta saya a hanya da zata zo,
Na juya zan tafi naji tana cewa Aisha ashe kin samu dauko fridge din dazun Karimay ta shigo take ce muna kin karasa biyan ta kudin har kin dauka,
Amma gaskiya kinyi kokari dan nai maki murna kinga shawaran dana baki yayi don ita karimay bata da matsala indai kana bata kudi ko kadan kadan ne sai ta tara ma har lokacinda ka gama,
Balle ke ta yaba kwarai da yadda kikai mata biyan kudin tace duk kika dan samu kike kai mata ko baida yawa,
Murmushi kawai nayi na wuce zuwa aikina, don nasan zata fadawa mahaifiyarta yadda na samu na sai fridge din da takewa wa bakin ciki duk kwanakin nan,
Aiko banko yi nisa ba naji Umma na cewa ta,saye ko aka sai mata ai duk na gane wayon yaran nan don sun mayar dani yar kauye wai nice zasuyiwa wayau ko,
Zarah tace haba Umma kamar yaya yanzu fa ta kai wata hudu tana kokarin sayen fridge din nan nice ma nasa yaya taiwa kaunar ta Karimay magana a gurin ta ta,saya,
Yanzu ke Umma hakan ba dadin ki bane yau ace sarakuwar ki matar dan ki tasai abin karuwa a gidan ku,
Wallahi baki ga yadda ake yabon ku ba kan wanan abin ,
Baki Umma ta tabe tana cewa, ke dallah matsa min can ke may kika sani ke ,
Ina zata samu kudin sayen wanan fridge in ba shi yabata ba ta,saye don sun raina wa mutane da hankali,
Yanzu in ba itaba ba mai cin abin yaron nan sai dai kagan ta tana yadda take so,
Ina duke na fara wanke tukunya,wani yaro ya shigo yana cewa ance a bani maganin ciwon kai dana ulcer,
Tace ummu jifa mai sanan chemist za ace wai ina ya samu kudi, haka ga karban haihuwa da take dan yi, don Alkah Umna kibar wanan zargin wallahi ita ce ta,sai abinta da kanta,
Umma dai bawai ta yarda da bayanin zarah bane sai ma fita zancen da tayi,
Da yamma sai ga mama Sa,a wai tashigo ganin fridge da taji ana na saye yana kankara ,
Tana gani suka koma daki da Umma sai abinda suka rage a gurin zagina da kuma dan ta
Wai inba aure ya kara ba Umma bazata taba gane kan dan taba don nariga na asirce mata shine, sai abinda nace,

****** ********* ******
Wani abokin shi yabashi shawaran yafara sana,an kai hatsin shi kurmi ya gani don akwai ci sosai,
Sana,an mahaifin shi ke nan shiga kasan kurmi dama don haka ya shawarci Umma
Da farko taso takiya mashi amma daga baya sai ta yarda ta barshi inda ya dan kara kulla jarin shi ya,saro kaya masu yawa ya fara zuwa lagos kai wa,
Sannu sannu tafiya tafa kyau dan idan zai dawo sai yadan sayo yan abubuwan da za,a samu karuwa dashi a nan arewa, ga kuma tsaraba da yakan dan sayo muna mu ma,
Ai kuwa take abin nashi ya fara bunkasa don ya kara bude idon shi sosai a harkan business din yanzu,
Shine Kano shine har kasar Niger yake zuwa dauko kaya yanzu,
Ya sai mashin irin na matasa idan yana gari ita yake hawa zuwa yawo ga suturu wanda ke nuna mutum yai lafiya,
Nidai saukina dashi shine yabarni ina yan sana,ata bai matsa min akan harkokina kamar yadda Umma takan so yai min,

Diyar mama sa,a data fito daga gidan mijinta takan yawan shigowa gidan mu idan Hamza yana gari da,safe ko da yamma,
Zatai wanka tashigo takan dan yi wasan kaunar miji dani wai ita kaunar Hamza ce itama,
Amna yanzu sai naga idan ta shigo zatai wani fuske min ko ina mata wasa irin yadda muka saba sai naji ta mayar min da mai zafi,
Mama Hafsi ce ta jiyo a gurin tallan ta cewa wai Hamza ne yake neman ta yanzu,
Ranan da mama take fada min na so na tayar da hankalina amma sau ta kwantar min da hankali da cewa,
Akan may zaki daga hankalinki haka Aisha bar su ai yanzu za,aji kan su akan wanan hadin da suke son yi,
Don Allah ba azzalumin kowa bane ba sunce wai sakin wawa bane basu san cewa sakin mai wayyo bane,
A gaskiya bayanin mama bai kwantar min da hankali ba don sai naga ai cin amana ne wanan,
Rasa wace za a aura mashi sai Sadiya wace tasan komai na gidan mu tasan ciki da baidin komai namu,
Gidan mamana Rahana naje da rana ina kuka ina fada mata abinda mama ta fada min,
Saida na gama fada mata sai naji tanisa tace amma kuwa Rabi ba mutumiyar arziki bace ashe,?
Yanzu ita sakaiyan da zata bimu dashi ke nan duk irin wanan halarcin da mukai mata,
Nace cikin kuka mama ni inda ma,watace ba wai Sadiya diyar mama Sa,a ba da suke kamar tip da taya da Umma,
Shiru mamana tayi tana kada kai tace duk abinda tayi ita da Allah ai don dai in bakici amanan su ba sai Allah ya fitar maki da amanan ki,
Don irin wanan aure ba,a kai ko ina yake watsewa saboda badon Allah akayi shi ba,
Yanzu abinda nake son ki da shi, shine ki kwantar da hankalin ki Aisha kada ki tayar da hankalinki,
Don kinga shi aure nufin Allah ne matar mutum kabarin sa,
Idan Allah yayi akwai aure a tsakanin su ba makawa sai sunyi shi don haka kada ki bari aji komai daga gurin ki,
Ki koma dakinki ki kwantar da hankalinki kici gaba dayin komai irin yadda kika saba,
Yanzu ya kamata ki kara zage damtsenki gurin kokarin kyautata mashi ke har ma da sauran jama,an gidan,
Kuma ai shi Hamza din bai nuna maki wani alaman cewa suna tare da ita yarinyar ba ko ya nuna maki hakan ne,?
Na hade miyau da kyat tare da girgiza kaina alaman a,a tace to kin gani idan ma hakane aiki barsu kawai mu ga iya gudun su,
Nace cikin sanyi murya da to mama insha Allahu zan yi yadda kikace din ,
Tace madallah yar albarka, hakanake so dake don kinga ba yadda zamuyi saboda shi dama namiji ne mijin mace hudu,
Dole ne a matsayinki na matar shi ta farko sai kinyi hakkuri da abubuwan rayuwa da dama don ke ce uwargida duk wani auren da zai kara ko diyar waye kece dai matar shi tafarko da kowa ya sani yakuma sanki dashi,,
Na dan kai wani lokaci a tare da mamana har kishiyar mama din ta gama girki takawo min amma sai na kasa cin koda cibi uku saboda damuwan da nake dashi,
Naima mamana sallama bayan takara kwantar min da hankali tare da min tuni cewa na dage da yin addu,a tare da sadaka don Allah ya bani rinjaye akan koma wace ce zata shigo min,
Tace duk safe na ambaci sunan Hamza da ita nace wallahu galibun Hamza da Sadiya sai na,shafa a fuska na,
Na kuma dage da fadan Subbahanallahi wallahamdullahi, Allahu akbar,,,

****** ********* ******
Ina zaune a bakin gado yana tsaye yafito wanka yasa tufafi a jikin shi yana fesa turare,
Sai binshi da kallon mamaki nake don yanzu baka raba shi da turare ko yaushe ga kokarin wanke mashin din shi ko yaushe fes zakagan shi tsab dashi ,
Ya juyo sai muka hada ido dashi tsarguwa yayi saboda irin kallon da nake mai,
Sai naga yadan murmusa min yace yaya dai nayi kyau ko, na dan tabe baki tare da kawar da kaina daga kalon shi da nakeyi,
Dawowa yayi ya zauna a bakin gadon kusa dani yana cewa naga kamar kina cikin damuwa mana Aisha ban son inganki kina min kallon rashin yardan nan da kike min yanzu,
Nace kai dai ke min kallon haka amma ni mai kai min da zan kama maka kallon rashin yadda gani nayi kawai kayi kyau shine nake kallon ka,
Murmushi yayi tare da kama min hannuna ya matse a cikin nashi yana cewa aiko na gode tunda na burge ki dama ke nake son na burge ai,
Wai ana sallama da Hamza inji wata a waje murya wani almajiri ne mai bara da robar shi mai marfi,
Cikin dan kamay kamay ya mike yana cewa kai ji min yaro wai wata kodai wani bari naga ko waye ke min sallama ya mike yafita yana dan gyara hannun rigar sa,
Namike muka fito tare nacewa yaron kawo robanka na baka abinci kaji,
Bai fitaba don yana gudun kada yaron ya fada min komai sai wani dan kamay kamay yake wai yana duban mashin din shi,
Kusan a tare suka fita gidan da yaron da ya,saka a gaba zuwa waje,
Bai dawo gidan ba,sai yamma naji karan mashin din shi wanda na haddace sautin karan mashin din a a kunnuwa na kamar yadda haka yake al,adan mata duk inda mace taji karan abin hawan mijin ta zata iya sheda shi,
Maimakon naga Hamza ya shigo sai Sadiya ce naga ta shigo gidan hannun ta dauke da leda baki mai giwa,
Umma wace take hango shigowan Sadiya tun daga nesa naji tana cewa lale lale sannun ku da zuwa har andawo ashe, sannun ku da hanya,
Na juya don naga wace Umma takewa wanan taron cikin raha haka banga kowa ba sai sadiya,
Ledan dake hannun ta tanufi Umma dashi tana fadin ga tsaraban mutanen Alairu sun ce a kawo maku,
Ina mamaki Alairu kuma Sadiya ta tafi shine Umma take mata wanan sannun da zuwan,
Banyi wa Sadiya din magana ba irin yadda na saba yi mata don ganin yadda take min ko yanzu, da ta shigo gidan batai min magana ba don haka nima na,samu corrauge din kyale ta, kawai,
Hamza ne yai karshen shigowa gidan naji Umma tana fadin Babana ashe harkun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login