Showing 159001 words to 162000 words out of 299981 words

Chapter 54 - Sarautar Mata By Makawa

04 Dec 2025

17684

dawo ne sannun ku da hanya ya kuka barsu can,
Gurin da nake zaune ina kullah kan karan yara da nake yi yanzu yadan duba don yaga ko ya zanyi amma sai kawai na basar kamar ban fahinci komai ba,
Amma kuma sai dai can kasan zuciya ta ji nake gaba daya kamar zuyata zatsage ta fito don wani irin kishine ya turnuke ni lokaci daya,
Ban mai sannu da zuwa ba tunda bai fada min zai tafi wani guri ba tun karfe tara da rabi na safe ya fita sai wanan lokacin da ya dawo,,
Mutum ya dawo daga unguwa, baki ko tariyan sa da ruwan sha Aisha, don kawai kishin banza da zaki sakawa kan ki,
Muryan Umma ce take fadin haka ani, don ganin yadda nayi ko in kula da zancen su,
Muryan Sadiya ce karshe take cewa kishi may zataiwa kishi ni da zan shigo naita haiho mata yara tana goyawa,
Kishin ta ai ba zai sa a fasa abinda akayi niyar yi ba don haka dama kin sauwaka wa rayuwan ki,
Kamar nai shiru amma ina zuciya bazata bari nai shiru ba a yau,
Na daga kai ina kallon Sadiya nace amay zanyi kishi anan wani bokon abune ban sani ba akanki ko wata sabuwar Sadiya ce aka canza ba wanan din dai dana sani ba,
Na girgiza kaina ina cewa ai da ki mayar da yukanki a kube indon ta Aisha ce mai sauki ne, anan, idan ban goya maki diya ba ai wadda ta kawo ki gidan ta goya maki tunda dama don shi aka shigo dake, gida,
Ina kaiwa nan na dauki kayan roban kankarana dana kulla zuwa cikin daki don in saka a fridge,
Ina jin yadda Umma ta ayayyako min tana masifa wai ko naki ko naso sai Sadiya yar ta tashigo gidan nan,
Simi simi Hamza ya shigo dakin cikin tsarguwa ina duke a bakin fridge yake cewa ke kada naji kin kara tankawa kowa akan zancen nan gidan nan,
Ban bashi amsa ba don sai yanzu zai min munafuncin su na maza a daki,
Shigowa Mama Hafsi ne ya dakatar da duk wani cin mutunci da rainin wayyon da aka kasa min a tire a na kwasa, da akeyi a gidan,
Simi simi Sadiya taiwa Umma sallama tana cewa zata,shiga gida don bata shiga ba da suka dawo, ko kallon inda take mama batayi bq balle ta san Allah yai ruwan ta,
Dakin nafito nabarshi ciki, don idan na tsaya a lokacin zan iya fashewa don wani irim haushi da takaicin shi ne ya kamani,
Don haka kawai sai naga fita daga dakin a lokacin shi yafi min alheri a raina,
Ina fita yafurzo wani iska a abakin shi tare da dan sake fuci mai nuna neman relief of mind daga mai yin sa,
Don kada na zauna sai na tsiri yin aiyuka don ya,kawar min da damuwa raina,,
Tun wannan lokacin mun dauki lokaci mai dan tsawon kowa tashi ke fisheshi a tsakanin mu don shi yana ganin cewa ya tsaya yai min bayani gazawan maza ne a,gare shi, don haka naje duk abinda zanyi nayi,
Wai wai muke ji ga mutane cewa an kusa daurin auren amma su basu fada muna ba,
Nima ban shiga shirgin kowa a gidan don ina gudun bakar maganan da suke yaba min wai da sunan wasa,
Don haka na kiyayye wa kaina daga haka don wani magana sai yai kokarin hanaka barci, ko walwala,,
Ganin yadda na kama kaina ban san may Hamza ya gani ba ranan sai gashi yana min magana da kan shi,
Humaira idan kin ce hardani zaki zarga a cikin al,amarin wanan auren da Umma ke son hadawa Humaira baki min aldalciba idan kika ce hardani zaki hada a cikin zancen auren nan,
Nidai kin san da hankalina bazan tafi gurin wanan yarinyar wai da,sunan so wanan zancen Ummane kinga kuma ban isa na mussa mata maganan ta ba,
Abin mata da miji nan yai ta min dadin baki yana kushe Sadiya a,gabana har naji na yarda dashi hankalina yafan kwanta kadan na daina fushi dashi,
Sai kuma Umma ta dawo tana jin haushin ganin mun shirya a tsakanin mudashi,
Nan ta fara azalzala kan ya kamata ya fara gyaran daki saboda a samu a daura auren nan kafin lokacin azumi yazo,
Ban damu ba don yadda nake samun yana nuna min kulawa yakuma sa wa ita sadiya din waigin shigowa har cikin gidan da take tana muna fitsara nida mama,
Don mahaifiyarta ta fada mata mama hafsi bata son ta ko kasheta tana iya yi,
Ita kuma sai tasha alwashi sa kafan wando guda ita da mama a gidan nan,
Nasan badon komai yakarawa mama bakinjinin hakaba,sai don tana tare dani,
Ni tun farko nasan Sadiya don kawar Kubura ce sosai kamar tip da taya suke kuma har sukai auren suna tare suna kawancen su,
Don haka duk wani iskancinta a tafin hanni na yake duk da ba wai ina kula su bane, don sun girmay min sosai ina kasa gare su, ga,shekaru,

****** ********** ******
Ranan wata alhamis saiga masu aiki sun shigo wai suna duban dakin dake kusa dana, Umma zasu gyara, shi alaman a nan amarya zata zauna ke nan,
Tun ranan suka fara aiki gyara duk da dai kwaskwarimane akaiwa ginan, sai sabon fenti da aka shafa tare da muna dakin girki, agidan,
Bayan duk shekaruna a gidan ruwa da iska dama da rani a wajen Allah nake girki na bako dan rufin kwano,
Tunda aka fara aikin nan yana can ya tafi Onisha kai kayan masarufi kamar yadda sukeyi ,
Saida yai kwana tara can yadawo a lokacin angama duk wani aikin gyaran gida baya garin shi,,
Zakace ai bashine ya bada kudi ai mai aikin ba irin yadda yai wani fuskewa bai damu da gyaran da akayi ba don ko kallon aikin baiyi ba, Kamar bashi ya,bada kudin da akai komai ba niko ga nawa wautan sai naji dadin haka don ko banza baima dai damu da amaryan ba,
Yadda nake mata kallon banza mara tarbiya honko shima sai nake zaton haka yake mata kallon,
Kwana biyu da dawowan shi, ranan da safe bayan nakai mai ruwa yai wanaka sai na fito waje don na kwashe kayan abinci zugurin wanke wanke, na hada nai komai na koma daga cikin daki don najira har ya fita,sai na dawo na karasa aiyukana,
Ina shiga na samu yayi kwalliya sosai, ya,sa,wasu shaddan shi sabbin dinki dayayi sky color dinkin yai matukar karban jikin shi,
Yana tsaye yana gyara hular da zai saka a kanshi,,
Na kalle shi sai na ga kwaliyan tashi tai min kyau sosai don shi dama mutum ne mai cikar halitta gashi da tsabta da iya kwalliya mai fitar mai da kwarjinin sa duk dai tallaka ne matashi mai farfadowa a lokacin,
A hankali cikin natsuwa nakai zaune daga bakin gadona,
Ban san lokacin da bakina ya bude nake tambayan shi,
Yaushe ne wai auren naka duk da dai nasan bawai lalaine kafada min ba,
Murmushi naji yayi batare daya juyo ya kalleni ba yaci gaba da kokarin saka takalma akafan shi,
Sai da ya,sa takalman ya juyo yake ce min may sanin zai kara ki dashi indan an fada maki, ko tsoro kike ji ne ?
Na dan murde fuska tare da tabe baki ina cewa ba wai tsoro ko wani abu nake ji ina,dai son sani ne kada ai min girshi,
Shiru yayi bai ce min komai ba yake cewa ni zan fita zan aiko da kayan miya don akwai inda nake son zuwa,
Daga haka yafita daga dakin inda nabishi da kallo ba tare da na,samu ce mai adawo lafiya ba,
Inda ya fita nan ya barni zaune ina tunane ni kadai a dakin ban san yadda,akayi ba,sai ji nayi a zuciya ta tana zargin wanan shigar da naga yayi gurin Sadiya zai tafi,
A,take tausayin kaina ya kamani, don sai nake gani kamar duk nice najawa kaina wanan matsalar rayuwa don ni da kaina nace wa Baba Mudi ya,aura min Hamza don kawai na tausayawa halin da Baba yake a ciki a lokacin,,,
Yanzu ga irin sakaiyan da nake samu daga gurin mahaifiyar wanda naiwa wanan mutuncin ba ragowa ko sanaiyar halarci a tsakani na da Umma ko kadan,
Wanda wanan halin har ya kai ga sanadiyar diyan ta sun fara nuna min tsana da kiyayya akan wai Hamza zai auri diyar kawar mahaifiyar su,
Don haka suke nuna min cewa ni barece banda, wani alaka ko farin jini a gurin su,
Gurin Mama Hafsi ne kawai nake dan samun sauki sai ko Ibrahim wanda bai yadda, da akidar ace wai a hade min kai wai ni banda kirki, banda mutunci, ina wa uwar su rashin kirki, da rashin mutunci ina,son shiga tsakanin dan uwansu da mahaifiyar su,
Wanan dalilan da,kullun Umma take fada masu a kai a yasa suke matukar jin haushina da zamana tare da,dan uwan su,
Sai suke ganin idan ya kara aure kuma ya auri Sadiya yar gida Umma zata samu sa,ida a gurin sabuwar matar tashi,
Nasa wa kaina damuwa sosai da farko amma daga baya sai kawai na hakkure da duk wani yawan cin fuska da,suke kokarin yi min na bar komai ga Allah,
Kamar yadda,basu damu da al,amarina ;a nima yanzu iyakata dasu gaisuwa ce kawai irin ta addinin musulunci,
Haka yasa suka kara sa min tsana da kahon zuka sai magana,suke sake min cewa,
Yanzu za a auro ta,kwarai wace ta dace da yayan su yar gaye mai mutunci yar gidan mutunci,
Su ai sai yanzu suka san cewa dan uwan su zaiyi aure, irin na sa,o,in shi shima zai kece raini a cikin sa,an shi,
Asamau kuwa har da karawa da fadan ai arziki zai sauko masu a gida don yayan su zaiyi auren gwadawa duniya don sai yanzu ya dace da mace mai siffan mata ta kwarai,
Ba yar raino ba auren wahala shi duk abinda ya samo kokari ake a kwashe a kai gida, gurin iyayye a boye,
Kwana biyu a fito dashi ana heleken cewa wai ansaya ne da kudin sana an da ko, tsintsiya ba,a iya saya dashi,
Kai Allah sarki naji maganganu na fitsara wanda ma bazan iya fadin su ba ,
Nakan shiga daki nayi kuka ni kadai sai nagaji babu wanda zai bani hakkuri,,
Bayan ya fita daga dakin ne naji motsin shi yana tayar da,mashin din sa zaifita, nadawo da hankalina don tunawan da nayi bai bar min kudin da zan sayo kayan miya ba ga kuma kayan wankin mu da,suka taru ban wanke ba,
Da,sauri na mike zuwa kofan fita waje na,samay shi har saura kiris ya fita daga gidan nake cewa yaya Hamza ya ja ya tsaya yana jirana na karaso inda yake tsaye rike da mashin, din sa yana jirana,
Nake fada mai bamu da man miya da maggi sun kare, sai sabulun da zanyi wankin kayan mu da,shi,
Haba Humaira yanzu mu kwana a guri daya dake bazaki fada min babu kayan miya haka ba,sai yanzun da nake shirin fita zaki zo min da zancen babu babu,
Na dan dago kai na kalle shi na furta a hankali da kayi hakkuri yaya mantawa nayi na fada ma tun da zun,
Ya saka hannuwan shi a cikin aljihun rigara shi ta gaba yana kokarin ciro kudi don ya bani,
Daidai zai mika min Umma ta fito daga dakin ta daga gurin da take a tsaye tana kallon mu take cewa,
Ikon Allah shike nan baza,a bar namiji ya zauna da sisi a aljihun sa ba sai ansan yadda akayi aka yaudare shi aka karbe mai canji,,
Kai wanan zamanin wai da may yai kama haka ace mata su dai abasu dai abasu,
Da kyat na iya hade miyau don bacin rai nace a cikin murmushi, Umma kinsan kayan miya ya kare tun kwana uku da,suka wuce shine nake fada mai babu su,
Har nawa zai baki akan wanan sayen kayan miyan don bazan iya sa ido kina kwatar kudi ba kamar kin samu banki,
Umma ai dari biyar ne kawai na bata bawasu kudine masu yawa ba hamza ya fada mata hakan,
I min shiru kai may ka sani da tace kwana uku babu a haka take miyan ba su,
Ai dai gaskiya ta kusa halinta a gidan nan wannan yawan barnan da kuma wullakanta abinci ai yazo karshe dai a gidan nan,
Ido muka hada dashi inda na facinci baiji dadin kalaman Umma din ba inda yake min kamar signal da ido na kyale ta kawai,
Najuya nafara tafiya nabar gurin Umma tana kara karasowa inda yake tana cewa dama nace ba yaushe zaka tafi gurin shi mahaifin Sadiya din kai kudin da kace sai ka,dawo zaka bayar din,?
Wani irin amsawa kirjina yayi wanda hakan ya sakani zaro idanuwa na don mamaki,
Shikuma hamza jin furucin Umma ya saka shi saurin dago idanuwan shi yana kallona,
Kawar da kaina nayi gefe guda ina mai ci gaba da tafiya na sai dai ina tunanen ko may naiwa,Umma har yai muni irin haka a tsakanin ni na da ita,
Har kofan gida suka fita shi da Umma don zancen ba wanda ake bukatan kowa yaji bane,
Na shige dakina ina mai tunane tare da kiyasta irin zaman da zamuyi a gidan nan tsakani na da su Umma da kuma ita sadiya har shima kan shi, Hamza din,
Kudin abinci ne fa amma saida Umma tai bakin cikin miko min su da yayi inaga wani abin bukatan can na daban, idan ya hada mu,
Don haka tunda Umma ta rufe idanuwan ta taimin haka nima na sha alwashin daga yau duk iya inda kudi ko kayan cefanen da suka bani ya tsaya nima a gurin zan tsaya ba zan sake saka naira na a cikin girkin gidan nan ba,

****** ********** ******
Zaune suke dashi da Mansur a kofan gidan su Mansur din zaune saman wasu fararen kujeran roba da Mansur din ya aje don baki,
Sai da Mansur ya gama sauraren bayanin Hamza din ya nisa tare da cewa, amma dai ka bani mamaki Hamza yanzu ace duk irin halarcin da kuma hakkurin da yarinyar nan Aisha take maka amma ke mata irin wanan sakaiyan haka,
Murmushi Hamza din yayi tare da dan girgiza kan shi yana cewa bazaka gane bane watau,
Bawai zanyi wanan auren bane don gazawan ita Aisha din a a zai kara aure ne don daurowan hakan agare mu
Saboda ina gani shine mafita da saukin mu baki daya amma ba wai nayi bane don gazawan ita Aisha din ba, wanan auren nawa ra,ayine kawai da kuma nufin Allah,
Well, tunda haka kace kuma na fahinci cewa kariga kayi nisa, a kan zancen ba matsala, Allah bada sa,a zan ce ma kawai, mansur yake fadin haka,
Idan time yayi sai ka,fada muna mu je gun daurin auren ko,
Murmushi yayi Hamza yayi, tare da dago kanshi yana cewa,ai auren coming Friday din nan ne za,a daura, insha Allahu bawai wani tsawon lokacine za,a dauka ba,
To Allah ya kaimu inji Mansur ya amsa mai
cikin dan jan numfashi yana furza iska daga sautin amsa, shi
Sai suka canza hiran nasu ya koma akan harkan kasuwancin dake faruwa a lokacin, bayan sunyi sallama
Mansur yana shiga gida ranshi a bace yake fadawa matar shi Hindatu zancen auren da Hamza ke shirin karawa kwanan nan,
Sun dauki lokaci maitsawo suna sharhi shida Hindatu suna yaba irin hakkuri da kuma sanin yakamata da nake dashi amma bai hana Hamza yana yawa musguna min ba duk da zamana karamar yarinya,
Sosai Hindu ta zage tana fada tare da,sake maganganu tana zagin Hamza da mahaifiyar shi,
A Cikin ikon Allah washegari na tashi da zancen zuwa gidan su Hindatu ina cewa ina son zuwa na dubo danta dake rashin lafiya,
Kamar bazai barni na fita ba amma kuma komay ya tuna sai yaga ai ya kamata din naje na dubu yaron saboda har asibiti suke alokacin shi baya gari,
Sam ya manta da zancen su da Mansur ya fada mai cewa zai yi aure ranan jumma,a mai zuwa
Ya manta cewa Mansur zai iya fadawa hindu matar shi komai,
Nashirya bayan nagama komai nafita sai dai banyi girkin rana ba saboda ba abubuwa da dama da zan bukata gurin girkin, ranan,
Kawai na shirya na rufe kofana na bargidan don ba kowa a lokacin duk sun fita zuwa tsabgogin su,
Sallaman da nayi a kofan falon ta yasata saurin lekowa daga inda take tsaye tana cewa maraba da Uwargidan Hamza,
Murmushi kawai nayi mata, sai dai ina mamaki a cikin raina ko da yake ba abin mamaki bane don sani yadda mijinta dashi Hamza suke,
Mun gaisa tare da tambayan lafiyan yaron yadda ya kara ji take cewa,Alhamdullahi ya,samu sauki,
Fita nayi zuwa dakin mama mahaifiyar Mansur nagaida ita sai nadawo gurin Hindatun,
Na zauna ina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login