Showing 162001 words to 165000 words out of 299981 words
kokarin cire hijjab dina don rana da na biyo a lokacin, akwai zafi,
Aisha yanzu abinda Hamza ya ke shirin muna kenan ashe wai kuma wani auren zai karayi, kwanan nan,
Murmushi maikama da yake nai mata ina cewa haka dai nima nake ji,
Bangane kike ji ba Aisha kina nifin bai fada maki zai kara aure ba da bakin shi ?
Na kada mata kai ina cewa hakane gaskiya don tsakanina dashi bai taba fada min ba sai dai alaman da nake gani gurinshi da yan uwan shi,
Kutubelesi amma yakai dan rainin wayo yanzu shi fadin ran shi har yakai a haka,
To ina ya fada maki ranan jumma,a ne daura aure da tarewa ko ?
Da,sauri na dago kai ina kallon ta cikin mamaki nace Jumma,a fa kikace anty hindatu ?
Kwarai kuwa wanan Jumma,an mai zuwa za, a daura aure kuma matar ta tare,
Take naji idanuwana ya ciko da hawaye amma sai na shayen su basu digo ba, nake cewa
Wai Anty Hindatu may Hamza ke nufi da ni ne wanan irin musgunawan yai min yawa a,rayuwa,
Tace cikin hasala tsabar rainin hankaline kawai irin na da namiji don sai su dauka ita diya mace bata da wani right a rayuwanta,
Nace cikin murya maikama data mai kuka anty ni wanan abubuwan sun fara isata wallahi,
Ina karama dani za,a fara cusa min bakin ciki da takaici a,rayuwa irin na da namijin,
Hmmm Aisha ke nan ki rabu da namiji kawai don idan auren nan ya motsa masu basu diban gaba balle baya,
Yanzu hakkurine kawai ya rage maki ga kowa a gidan, duk abinda kikasan kinayi mashi a baya kada ki fasa yi wai don kinga ya kara aure,
Kowa da irin halinta ake zama da it don haka shi da kanshi zai fahinci halaiyar ko wacen ku,
Ai dama shi zaman aure dan hakkurine duk inda mace take aure saida hakkuri,
Yinayi bari na bari inji manya, shine riban aure duk auren da babu ladabi da biyayya a cikin sa sunan wanan auren lalatace Aisha,
Kinga ko ita wanan din da Hamza zai aura kin santa tun farko kin kuma san halaiyar ta,
Don haka ni shawaran da zan baki ke nan don nasan akwai zafi ga duk matar da akaiwa irin wanan auren cin fuskan,
Ki dage kawai kiyi sunnan auren ki sau da kafa don ku zauna lafiya da kowa ,
Ki kawar da kanki ga duk wani borin sabon auren da zaki ga sunayi da ita,
Badon Allah za ai wani abin ba za,ayi shine don ke uwargida kiji haushi kawai,
Kinga idan kin biyewa haukar sai al,amarin ya kwabe gaba daya ke da miji ku koma ba zaman lafiya ko kadan,
Amma inadan kin daure kin share kin hadiye abin a ranki sai komai yazo maki a cikin sauki,
Ke ce dai uwargida don ba,a taba kai gaba baya dole dai tana bayanki komai shekarunta a duniya,
Abinda ta zo takeyi kada kema ya hanaki kokarin tarairayan mijinki, kai mai ruwan wanka idan ya dawo sanu da zuwa , abinci kiyi mai kyau idan kina da girki din kin rigata shiga gidan kin san abinda yake so da bukata,
Idan taga kin dage tabuga tabuga bataga daman ki ba sai kiga abin yafara fita a tsakanin su,
Don may ?
Don bakiba da kafa an wulkantakiba kamar yadda matan yanzu suke shiga da gurin ganin wace akasamu a gida ta nakasa ta koma baya,
Sai ta kawai zata dinga yin yadda rantake so indama yara gareki ana kokarin ganin an raba su da mahaifinsu an shiga tsakanin su,dashi saboda kissa da kisisina da akazo dashi,
Don haka wallahi kama mijinki ki rike hannu bibiyu Hamza yaro yanzu yake rigimar auren ne kawai Allah ya zo mai a rayuwan shi,
Idan kinyi hakkuri bakiyi sake ba duk irin wanan al,amari watarana sai ya zama tarihi,
Nasan bawai don kin kasa bane zai sa shi kara aure kawai sha,awan hakan ne dashi,
Don Allah Aisha kada kiyi sake tako wani hanya karki yarda ki watsar da daman ki na uwargida da Allah ya baki ,
Rike auren ki hannu bibiyu, ki kula da duk wani hakkin shi dake a kanki kinji,
Insha Allah indai muna tare zan taimaka maki daduk wani abinda ya dace ya taiwa kaunar ta a duniya, muddin kika kwantar da hankalinki,kinji,,,
Nace mata na gide anty yayin da idanuwa na suka kara cikowa da hawayen dana kasa mayar dasu,
Nace Anty nagode Allah yabar kauna nan naita mata godiya tana cewa babu komai Aisha, aike abin a taimakawa ne, don halinki na alheri,
Nan dai ta dinga rarashina tare da kara kwantar min da hankali,
Karshe tace min zanji insha Allahu kafin tarewan amaryan zatai min duk wani abindaya dace,,
Ta kuma kara jaddada min cewa kada na yarda na nuna damuwa ko kadan kodan Umma da yaranta tunda jira kawai ake aga damata asamu gurin yi min gori ko wulakanci,
Nai mata godiya sosai don nai matukar jin dadin wanan shawaran da nasihan da tai min sai nake jin kaina wata wasai dani, duk kuncin danake ji da farko yanzu sai na nemay shi na rasa shi baki daya,
Munyi sallama dasu nabar gidan inda ta rakoni take kara jaddada min cewa zan jita kafin ranan Jumma,a insha Allahu,
Nadawo gida ina kallon kowa yadda suke kallo a matsayin wace bata san komai ba,
Shi kan shi Hamza ina mamaki yadda naga yana shirin shi hankali a kwance baidamu da ya fitar min da hakkina ba na nima ya kamata na sani ai koda akwai shirin da zanyi kafin ranan,
Amma ina, sun mayar dani matsiyaciya banda abinda zan gyara dakina dashi, don haka jira kawai suke nasha haushi,
Sai shirin su suke tayi iyakata da su idanuwa don babu wanda ya sani a cikin zancen,
Zarah ce da farko taso sakani amma sai akai mata waigi dole ta daina komai dani iyakarta gaisuwa a tsakanin mu,
Ita ko mama ba,a shawaran komai da ita sai ma yawan wulakancin da take dan fuskan ta daga gurin su yanzu,
Da safe zai fita nace ina son shiga gidan mu inga Ummi na, kai tsaye ya ce min bazan shiga ba don kwanan nan nafaye fita zuwa unguwa,
Dole na hakura ba don naso ba sai mama ce nadan faki idon mutane na tura ta gurin Ummi don ta fada masu,
Zancen tarewan Sadiya da za,ayi ranan jumma a mai zuwa insha Allahu, Saura kwana biyu ke nan da za,a tare din,
Ba bata lokaci mama ta shirya ta shiga gidan mu tafada masu komai nan suka,shiga surfawa Mama Sa,a da Umma zagi kan wanan auren da suke son hadawa don cin fuska,
Duk na dan shiga damuwa rashi kowa a kusa dani amma kuma ina kokarin yin yadda Anty Hindatu ta koyar dani,
Sai Umma da yaranta su shige daki suyi ta gulmana suna dariya kyakyakya har mai shigowa zai iya jin sautin dariyan su,
Kitso da kumshi, na tambayi Hamza zuwa amma sai ce min yayi na nemo wace zatai min a gida,
Nadago kai a cikin mamaki ina tambayan shi wacece zan kira tazo gida taimin nawa zai bani nabawa mai kitson idan tazo tai min a gida,
Look Humaira ban fahince ki ba idan baki fahinci nufina ba sai ki bari, koke ba bahaushiya ba ce baki san hausa ba ko may,
Daga haka ya fice daga dakin ya barni raina a bace nace dama ashe zaka kara aure ne don ka zalunceni dama nasan baka sona tunda bakani akayi ba nemana kayi ba,
Nidai tunda baka sona ka sallamay ni na koma gidan mu kowa ma ya huta hakana,
Har ya kai kofa sai kuma ya dawo har gabana yatako yatsaya muna fuskantar junan mu dashi,
Humaira ke da bakin ki kike furta na sallamayki ki koma gida ?
Yakai dan tsawon lokaci tsaye a gabana yana mai tsura min idanuwanshi, kamar mai jiran amsa daga gareni,
Ya gyada kai tare da juyawa yafita yabar dakin zuwa waje, ran shi a bace sai zuwa sha daya ga wata mao kitso taxo take cewa wai nafuto inji Hamza taimin kitso da siffa,
Kamar nace na fasa banyi amma kuma,sai nai gudun sa idon mutane a kan mu,
Don haka ba don naso ba nazauna daga kofana muka fara siffan sai kitso daga baya,
Ance labari yana gurin masu kitso da siffa da sauran gyaran jikin mata,
Saida taga ba kowa, take, ce min kaii namiji ho ko may mijinki yagani gurin wannan matar da zai aura ?
Kin fa fita da komai da ake bukata agurin diya mace, sudai maza idan sun tashi aure sai kiga kamar idon su a rufe yake,
Murmushi nayi ina ce mata ai kinsan ance matar mutum,kabarin sa Allah ya nufi akwai aure a tsakanin su ne,
Tace zan maki kitso da siffa maikyau wanda za ce ko ce amaryan zan kuma dinga zuwa ina maki duk lokacin da kike bukata, ai maki,
Zuwa karfe hudu har mun idar naga Zarah tana girji irin na alfarma amma ban damu da nasan may takeyi ba,
Zan dora girkin yamma take ce min nabarshi kawai idan ta gama zata zubawa kowa a kwanon sa,
Juyawan da zanyi zuwa dakina sai guda naji da dirin mota ana cewa ayyurirrrr Amarya, yar shagali, yar biyan bukata, yar garali,
A hayye gamu mu mun iso ko ana so koba,a so yau Allah yayi aure tsakanin Sadiya da Hamza,
Ban juya ta kansuba dakina kawai na shiga sai faduwa gabana yake zama zanyi ko kwantawa duk na rude na rasa may zanyi a lokacin,
Gani ni kadai a dakin babu kowa nawa a tare dani duk hankalina ya tashi gabana yana ta faman faduwa,
Sai addu,a nake ina rakasu da kalman sunan Allah don samun rijaye akan masu sheri daga cikin su,
Inajin sai sannunku da zuwa Umma da yaranta suke masu tare da kwasan dariya suna cewa ku iso ga dakin nan,
Habaici da gori kawai ke faman tashi a gidan Sadiya da Hamza mutu ka raba ko yan bakin ciki basu so,
Wata kuma tace gidan nan sai an cika shi da yara harkofa gida don tsiya da talauci ya kare yau,
A hankali na runtse idanuwa yayin da zuciya ta yake min suya kamar zai tsage,
Muryan wata mace naji daga cikin su tana cewa haba kubar yin haka mana,arziki fa ya kawo mu ba tsiya ba,
Sai kuma naji wani murya a gaisawa da mutanen kofana masu sallaman suka nufo,
Ashe, Anty Hindatu ce tare da sisters dinta guda biyu suka shigo da sauri na tashi na rungumay ta sai kuka,
Tsawa ta daka min cewa nayi shiru kada na fara na bata tsarina na tashi nayi kwalliya naje nai masu sannu da zuwa,
Hakan ne kuwa mukayi nasha kwaliyana acikin dinkin wani atamfa mai ruwan brown color dinki shi yai matukar karban jikina,
Na fito zuwa gurin su idanuwan su ccaa akaina nai masu sannu da zuwa tare da gaishesu da aiki najuyo zuwa dakina,
Sun bar gida da yamma liss suma hindu sukaimin sallama ina ta masu godiya amma sai tace na bari kawai,
Hmmm ikon Allah washegari takwas na safe mukaji durin mota sai kayan gado da su wardrobe mirror mukaga ana,shigowa dasu sun ci uban na Sadiya nisa ba kusa ba,
Kowa yafito yana kallo saiga hindu da sisters din ta najiya da ma wasu biyu suka shigo nan suka hau gyara min daki,,,
Barkan mu da shan ruwa yan uwa tare da fatan samun rahamomin dake cikin wanan watan mai albarka
Kuyi hakkuri dani yan uwa muje zuwa labarin sarautar mata,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABUIDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,
Maza ki kwashe duk wani abinda kike bukata daga dakin don yanzu zamu gyara dakin,
Tsaye nayi sororo da mamaki ina kallonta ina kallon kayan cikin mamakin inda suka fito dasu,
A hankali nace Anty wanan kayan fa cikin fara kware zanin gadon da yake a shimfide take cewa,
Idan da kin kwantar da hankalinki dole muyi maki bayanin komai don haka sai banki ba nafara dan daukan abubuwan amfani na da nake so a dakin,
Kafin wani lokaci har an gama fita da komai anfara saka sabbin da aka,shigo dasu, ko,
Dakin sai ka rantse kace ba dakina wanda nakwana a cikin sa bane,
Aikin shape shape akayi shi sai muka bar mutanen gida leke tare da tabe baki,
Mama Hafsi wace bata gidan tana shigowata hango kayana,waje a,watse tafara tambaya wai may ye haka taga ko ina kaya a,watse,
Dakin ta nufa ta daga labule sai cewa tayi ayyururiii Allah sarkin dadi,
Ance mahakurci mawadaci yau Aisha duk wani, sa,an ki bai gwada maki komai sai ma,dai ki gwada mai don ba,a fiki da komi ba na daki,
Yanzu zauna kiji bayani abinda ke nan na samu guri daga gefen kujera na zauna ina sauraren ta,
Tace da farko dai wanan kayan bana kowa bane nawa ne na dakina da aikai min wasu sai na canza su ,
Niyyana zan sayar dasu sai ban samu wanda yay min cinikin su yadda ya dace ba,
Kayane na kamfani masu kyau sunyi ma dakina kadan ne shiya sa aka canza min aka,sayo min babban seti mai girma,
Yanzu tun jiya da muka zo naga yadda dakin ki yake ance idan kana tare da mutum to kaso shi don Allah, kamar yadda zaka so kan ka,
Dan haka na yanke shawaran kawo maki wanan kayan a matsayinki na kaunata kamar yadda na dauke ki, duk ranan da,Allah ya hore maki sai kibani dubu, ashirin akan su koda da kadan kadan ne,
Da sauri na dago kaina nake cewa dubu ashirin Anty hindatu ina ma laifin kice arbain ko hamasin wanan setin masu girma da kyau da tsada,
Tace aiko ashirin din ma akwai dalili da yasa zan karbesu a hannun ki,,
Har kasa nakai da gwaiwa na bibiyu ina mata godiya cikin bacin rai take cewa haba Aisha may ye haka dan Allah dai ki bar wanan dabian shi taimako ai takine ga bawa,
Anty tace na kwashe tsofin kayana nabawa mahaifiyata su don tana son suyi clearing din kofa na kada a iske komatse a gurin kofan idan an shigo,
Mama Hafsi na kira nai mata bayanin komai amma kuma anty tai warning din ta akan ta kama bakin ta kada tafadawa kowa, wanan zancen
Ba bata lokaci mamata shiga gidan mu gurin Ummina tafada mata komai takuma je gurin Mamana Rahana ta bata labarin duk tadda abubuwa suke gudana a gidan mu,
Guda mama tayi tace Alhamdullahi Allah mun gode maka Allah maji rokon bawan sa,
Mama Rahana tazo min da zanin gado maikyau cikin gidan shi sai dinki da taimin na fitan buki shadda da lace sai kulan abinci kala biyu suka saya min,,
Na rasa bakin da zanyi godiya dashi sai kawai na,daga hanayena i a godewa Allah tare da jero adduoin, godiya,
Wani irin sanyi sosai naji a raina don banjin k8shin komai kuma yanzu abinda nake ji daren jiya da naga an shigo da kayan Sadiya yanzu duk ya gushe a zuciya ta,
Don mutum zai iya cewa nice amaryan don yadda na koma wata fresh dani,
Umma bata gida har muka gama komai namu ta fita zuwa gurin shirye shiryen ta tunda farar safiya tabar gidan ,
Sa,adatu auta ce kawai a gidan aka samu sai ni don haka muka gama shagalin mu kafin a karasa komai,
Haba bayan sun dawo suka samu dakina ya sake ai fuskan Umma a lokacin kamar an aiko mata da sakon mutuwa take ji,
Zarah dai tazo ta daga labulen dakin ta shiga tana fadin kai, kai, kai, azziki, wanan kayan masu tsada irin haka lalai masha Allahu Allah ya kaimu ga danshin ku ke kan kin kece raini Aisha,,
Murmushi nai mata kawai sai tajuyo tana fuskanta ta tana cewa kai kunga wanan matar ba,a taba gane gaskiyan ki wallahi,
Muryan Umma ta kirata tana fadin ta,zo suyi batun dora girki don masu dawowa daga gurin daurin aure,
Ai kafin wani lokaci uguwa anji labarin na gyara dakina wai ya cunawa dakin sadiya goma albarka,
Sai misalin karfe biyu da rabi an sauko jumma,a aka daura aure a kauyen da mahaifin Sadiya yake zaune
Masu daurin aure suka dawo gida akayi liyafa sukaci suka sha daga abinda Hamza ya tanada domin su,
Yan uwana sunzo min zaman tausan gaba daga ciki harda kubura da yar ta tayi wayo sai dai uwar zaka kalla ka fahinci cewa ba dadi zaman,
Ba a bani abincin da zanba mutanen dakina ba duk na damu ina cikin bacin rai sai ga kannen Anty hindatu da kula har uku da abin sha sun shigo,
Nan suka shiga raba abinci a tsakanin su tare da abinsha sai kuma mutanen su Umma hankalin su yadawo a kan abinvcin dakina don kowa shi yake son ci,
Sun dibawa mama Hafsi da kuma, wata matar abikin shi da take zaune a waje saman tabarma,
Shinkafa da miya