Sarautar Mata

Chapter 56 of 94

aka kira ya duba mace mai haihuwa sai suke ce minbai shine likita don shine yaje yai karatu a birni,
Tsam na tsamay hannuna daga cikin ruwan da nake tatse masu kamun kokon su,
Jakar da,na,zuba magani na aciki da sauran tarkacen aikina danake bukata nace wa wata diyar wani babana da take gida zaune mijinta ya rasu, tana zawarci da ta rakani, gidan naga mara lafiyan,
Mutane ne gidan ancika fuskan kowan su babu dadin gani don basu a cikin dadin rai sai faman shawara ake yadda za,a tafi birni da ita,
Nake cewa bayan mun gaisa a can na,samu gwagona na ko zan iya ganin mara lafiyan kafin a,wuce da ita,
Gwagona tace may zakiyi mata Ido, likita ma yace atai da ita can cikin gari aiki za ai mata,
Ganin na dage cewa zan dubata yasa sukace a bari na shiga gurin mara lafiyan na,fara dubata,
Tana cikin wani irin condition wanda ba,a,aon mai ciki ta kai a lokacin don bata da jini a jikin ta ga kuma maleria ya kamata,
Nadan dubata da kyau naga yan matsalolin da suke damun jikinta don haihuwan ba,zai iya zuwa mata a lokacin ba sai ta dan watsake tukun na,
Tausayin mutanen muna kauye naji irin yadda ake ta masu abu a cikin duhu ba tare da sanin gaskiyan al,amari ba,
Nakira mijinta da,wasu daga cikin iyayyenta nai masu bayani wasu sun yarda wasu basu yarda ba da zancen gaba daya,
Don ba kudi suka yarda dacewa a gwada shawarana a,gani nai mata allura nabata yan kwayoyi na kara duba lafiyan cikin ta,
Nace ya samo mata maganin karin jini abata don ta samu karfin a jikin ta amma sai yace min ai baida kudi nafitar da dari biyu nace a,sayo min sprite da tumatir din leda na hada na bata ta shanye su dukka,
Sai ga mai na kuda takai kwance sai barci nafito mutane su kabini da idanuwa caaa nakoma gida, nabar su nan,
Sai zuwa,magariba na koma gidan nasamay ta ta farka daga barci nace abata wani abu mai dan ruwa tasha koda koko ne ko shayi don tayi losing din afatay din ta bazata iya cin abinci ba mai nauyi sai harshen ta ya,warware tukunna,
Tana sha sai wani irin zufa take karyo wa wanda ya nuna ta samu lafiya a jikin ta lokacin nai masu sallama na,dawo gida,
Haba zance sai yafara yadawa ai wata,bakuwar likita tazo gidan Liman tsoho tunda safe wata,mata ce ta tayar damu wai na,duba mata lafiyan yaron ta yaki samun karfin jikin shi,
Tun wanan lokacin na zama wata mai kula da lafiyan yan uwa da abokan arziki
Da yake kauye ne sai gashi wanan Yunusa likita yai karana a gidan mai gari cewa na, zo gari ina son cutawa mutane ban da takardan kare karatu irin nasa,
Sai da magana tai magana koda ya fitar da nashi aka,duba nawa sai akaga ai nafishi ilimi sosai shi course kawai ma ya yi ba karatu ba,
Nakuma basu hakkuri da cewa ni yan uwana nake dubawa bawai sana,a nazo yiba agatin don bazan dade ba zan koma,
Nan ake fadawa maigari koni diyar waye a cikin garin yace Allah sarki yarinya kinyi kokari da kikazo duba yan uwanki Allah kuma ya baiyana muna inda mahaifinki yake idan yana raye, kowa ya,amsa da,Allahuma Ameen,
Ranan da na ce matat dan uwana zata haihu sai gashi cikin yardan Allah ta sauka lafiya inda na karbi haihuwan ta,
Sai dai na lura da ina,shakan karnin jinin nan duk sai naji jikina ya sake ba shiri nai mata abinda zanyi na koma gida a gagauce na ta shega amai dole na sha magani don ina gani nima maleria ne ya kamani,
Da safe a cikin ikon Allah ya tashi wasai dani sai dai ban son shakar karnin haihuwan da a ji wanda acan baya ba haka nakeji ba, idan ina karban haihuwa sai nake cewa watakila ita wanan nata jinin yana da karfine sosai,
Alheri sosai nake samu akan wanan harkan hankalina kwance don tun ina tunanen gida hat yanzu na,saba da mutanen garin ban tunanen komai kuma again,

****** ********** ******
Karfe sha biyun rana ko abin karyawa ba,ayi ba agidan tana daki kwance abinta,
Mama Hafsi tun da ta gane cewa za,ayi tsiya a gidan sai ta kwashi kayan sayarwan ta zuwa cikin uguwa,
Umma wace ta dawo da zuman ta karya tun a gurin wanke wanke ta hango kaya kwanoni kuda nabi yooo,
Gurin da na,saba aje mata abin karyawan ta tanufa sai dai babu komai sai sauran tuwon jiya dake acikin wani kwano duk ya bushe yayi bawa ga kuda na bin su yooo,
Daga inda take tafara kiran Sadiya Sadiya Sadiya ,
Sadiya wace take kwance tana ta kwasan barcin ta hankali a kwance taji iri kiran da Umma ke mata ta farka a gigice tana cewa lafiya wai haka,
Ta bude labulen dakin ta tana cewa a,a wanan ir8n kira haka kamar wani tashin hankali,
Ni wallahi ban son idan ina barci a dinga tayardani ban tashiba sai kaina ya dinga ciwo daga yau kada a kara tayar dani idan ina kwance,
Baki a bude Umma tace Sadiya kan ki dayw kuwa ?
Ni kike fadawa wanan magana haka ba ko jin kunya ,
Kunyan may fa don na,fada maki abinda ban so ban kuma ra,ayin ana min shi,
Eyy lalai kuwa kin kai ashe baki da kunya ban sani ba haka ,
Dama shine, dalilin kiran to ban girka ba don bashi nazo yi ba dama ta juya ta,shige daki ta gyara saitin fankan ta na kasa don ya bata iska da kyau,
Umma tana tsaye sororo cikin mamaki tace a ranta ashe haka yarinyar nan take batada kunya ko kadan a rayuwan ta,
Ga yunwan da,take ji dole ta nufi gurin murhu ta fara hasa,wuta don tasan cewa, har da yaranta dole su ji yinwa don sun saba karyawa duk safe da dumamay tuwo ko koko da kosai,
Tana can tana tunane ta tabo wutw da hannunta da,sauri tafara yarfar da hannunwanta don zafi daidai lokacin Ibrahim ya,shigo gidan yana ganin abinda ya faru yake cewa Umma lafiya ?
May zakiyi a gaban murhu kuma yanzu da wanan uwar ranan haka ?
Rai bace ga,zafin wutan da ta taba yana kona mata rai taceczan nema munw abin karyawa ne,
A,a ita Sadiya bazata fito tayi ba,sai ke tace tace batw jin dadi shiyasa nafito ni nayi,
Duk wanda ya shigo ya tambaye ta,amsa daya take basu shi dai ibrahim bai yarda ba yasan halin tsiyan sadiya ne ya motsa mata,
Sai ma fita da yayi a gidan don bai iya ganin takaici yace a ran shi,
Harshi uban tafiyan Hamza yashigo ya,samu ummu tana kashe kunu a gaban murhu tana gamawa ta mayar da,wutan abinci sama,
Can sai ga,Sadiya da cup din ta bata jira ma Umma ta zuba mata ba,sai ta,shiga diban kokon da kan ta,
Umma tana futowa taganta a duke agaban roban kunu tana diban kokon da kanta,
Ikon Allah wai yaya hakane kuma da zakizo kina diban baki ko iya jiran na,zuba maki,
Wanda ta diba sai ta mayar ta nufi daki da cup dina hannun ta,
Tana,shiga daki Hamza dake kwance yaganta da cup tazo ta zauna a tunzure gaban shi tana huci yake cewa wai may nene kuma,
Sai kuka tafara cewa harda abinci kuma za aimin iyaka dashi don kawai anga banda lafiya ban dafa ba,
Rai bace yafita yana cewa haba Umma yanzu kuma don bata da lafiya shine kunun mw baza,a bata tasha ba sai a hana ta duk da lalurar dake a jikin ta, kuma,
Ikon Allah ita Sadiyan tace ma na hanata kokon ko kuma kai,
Yace ai shike nan bari na fita na,samo mata dan abinda zata ci kada ta zauna da yunwa a jikin ta, yai mata illa,
Sai kawai yafita yana cewa gaskiya ni ba ai min adalci a gidan nan duk kokarin da nakeyi sai an muguntawa iyalina,,
Umma tabi Hamza da kallon mamaki akan Sadiya da itace ta nema mashi auren ta yake mayar mata da magana agaban sauran diyan ta,
Jin yafita yasa Sadiya fitowa da buta a hannun ta tana wani fisge fisgen kai, da tafiyan gadara wai ita an cuta mata a gidan mijinta yai cin mutunci,
Yadawo dauke da leda mai take away a cikin sa yawuce dashi daki duk suka bishi da idanuwa
Can bayan ta gama ci sai ta jefo ledan take away din ta tsakar gida miyar agusi ne da sakwara taci, sai ledan pure water mai sanyi da gwagwanin multina,
Ranan Ummatakai matukar hasala,da Hamza duk yadda,taso taboye bacin ran ta abin ya,faskara,dan sai da ta nuna mai hasalan ta a fili,
Sai taga dama zatai masu girki ko shi sai idan Hamza ya lalashe ta don ya gaji da,sayo abincin kasuwa kullun,
Umma tana ganin ikon Allah ranan Sadiya tsaye tayi tace ita bazata karbi abin girki a gurin Umma ba don ba Umma take aure ba dole kayan girki yadawo gurin ta daga ranan,
Umma kamar zatayi hauka don ta hango Sadiya zata raba ta da dan ta gaba daya idan tai sake,
Ga aiki yanzu kamar zai kashe ta agidan komai sadiya bata yi wai ita mai ciki ce sai abinda take so zata ci,
Shagwaba sai yadda tayi da kowa a gidan shiko gogan baijin kunya gaban kowa,sai faman tarairatan ta yake kamar zai goya ta a bayan shi,
Yanzun ma ko fita ya,daina yi sosai koda yaushe suna tare sai bakin jaraba da,sukeyi dare da,rana, a daki,
Tafiya ya kamshi dole ya tafi baxon yaso zuwa ba kwanan shi biyar a can yadawo,
Yasamu Sadiya tayi kaca kaca da mutanen gidan nan ya hau sababi da yan uwan har yakai ya kira baba Madu kan azauna a sulhunta,su,
Bayan amayar da jawabi ir8n rashin mutuncin da Sadiya takewa Umma har yakai yaranta Jibrin da Ibrahim sun ki yarda sunyi niyar lankada mata dan karen duka,sai da ta gudu zuwa gidan su,
Shine ita kuma mahaifiyarta ta fito zuwa gidan da nata masifan na aka rikice har mama,Sa,a tana cewa
Watau abinda takewa Yar Agwai shine yakawo a kan yar ta to ita gaskiya bazata iya dauka wanan cin fuskan ba wa yar ta, don ita yarta tana da gatan ta,
Ibrahim yace oho dama,ashe don bata da gata yasa kika dauko yar iskan yarki kika cinnawa mutane mugun abu ,
Umma ta hana shi magana ta koreshi daga gidan don kada magan tai nisa sosai,
Nan dai tace Sadiya ta koma ta shiga dakinta babu wanda ya isa ya kore ta a gidan tunda ba su ke auren ta ba,
Bayan fitan mama sa,a da,tawagarta ne mama hafsi tace ni dama nasan ai za a rina don badon Allah akai wanan hadin ba tun farko,
Anyine don aciwa yar mutanr mutunci yanzu kuma sai gashi ganwo ya juye da kaya akai,
Aisha dai ta huta ai kwana biyu yanzu za,agani mai mutunci a cikin su
Ba wanda ya tanka mata don ran kowa a bace yake a gidan saida yadawo ne su Sadiya da uwarta suka kwashi karya da gaskiya zuka fada mashi shiko ya hau ya zauna yana tawa mutane yankan kauna,
Baba Madu yace haba Hamza yau ina hankalin ka yatafi da har kabari mace zata hadaka da mahaifiyar ka haka da yan uwan ka
Sai lokacin ya dan sadda kan shi a kasa saboda ya dan dawo hankalin shi,
Baba yace Hamza kada ka manta da irin dawainiyar da wanan boyar Allah tayi da ku a baya yanzu lokaci yayi da zata ji dadi a,gare ku,
Musan man ma kai da da kowa ke yaba irin hankalin ka da kokarin ka, ga mahaifiyar ka da yan uwanka har da ma mu iyayyen naka,
Ga mata yar arziki maikirki da mutunci da Allah ya hada ka da ita tun farko,
Sai yanzu ne da rana tsaka zaka bata duk wanan alherin naka akan wata mace bakuwa
Baba Sadiya ba bakuwa bace don ita yar gida ce don diyar aminiyar Umma ce,
Koma,wacece bata nuna muna cewa ita ta gida ce ba don da batabar mahaifiyar ka tana aiki da kanta ba kuma tana ci mata mutunci,
Duk inda yafito don ya kare Sadiya,sai baba Madu ya nuna mai rashin dacewan haka a gare shi har dai baba ya ce kai Hamza barin fada maka ba,a kyauta ba,
Kayi gagawan bawa mahaifiyar ka hakkuri akan wanan zancen kuma a gyara,
Ke kuma Rabi na dawo a kan ki kin san halin yaran yanzu kokai ka haifi abinka,sai kai hakkuri dasu don haka ki dinga kawar da idon ki akan matan yayan ki don yaran yanzu basu da mutunci,
Don kinga a kwai banbancin rayuwa a,tsakani ita waccan ta farkon da,wanan da kika hada da hannun ki don haka sai kinyi hakkuri sosai akan irin zaman takewan gidan na dasu Allah ya kare ku daga duk wani sherin shedan daka iya hada ku fitina agidan nan kowa ya,amsa da,Ameen baba,
Ya juya gurin Hamza yace ka,roki mahaifiyar ka gafara don ka ga,haske a rayuwan ka,
Ya mike yana cewa ni nabar ku lafiya,
Godiya,suka fara mai har ya,fara tafiya,sai ya ja ya dakata yana cewa wai ina ita,wanan yarinyan ban gan ta ba tunda na,shigo,
Jibrin ne ya bashi ansa da cewa ta tafi garin su yau sati biyu ke nan da,tafiyan ta,
A lokacin Hamza yadago kai ya dubi dakina wanda yake a rufe da padluck yana tunanen yaune fa ya kamata ace nadawo don sati biyu ke nan ashe,
Baba yace Allah sarki Allah yadawo muna da ita, lafiya yarinyan tana da hankali sosai wallahi

****** ********** ******
Washegari Sadiya ta,sa habaici a cikin gida cewa oho dai gani nan bari nan tsakanin ta da Hamza dai sai mutuwa,
Ko bata da,kirki dai dole a zauna da ita tunda mijinta yana son ya don wasu banza basu son ta ita ko ajikin ta tunda ba zaman su takeyi ba,
Ba wanda yabi ta kan ta don duk sunji maganan da Baba yai masu a,daren jiya,
Da kwana biyu ciwon baya ya kama Umma gashi dole ta dan gi wasu aiyuka da kanta don ko kallo bata ishi Sadiya ba,
Dole zarah ce tazo daga gidan ta taiwa sister dinta,su Asmau fadan cewa gasu a gida har uwar su zata zauna tana ganin bakin ciki irin haka,
Shi ke nan don Aisha bata,gida sai su su kasa zama su taimakawa umma sai dai itace zata dafa ta wanke iyakar su ci kawai,
Mama Hafsi tace ai basu da laifi don laifin yaya ne da ta koya masu tun farko ai bazataga bacin rai ba,
Sai dai ace yar mutane ne zata zauna taita masu komai su suna zaune yanzu ai gashi ankawo wacce ko kallo basu isheta ba,
Zarah tacd ai yanzu dai kowa yaga ranan ita Aisha din don wallahi idan tana nan duk wanan abin bazai faru ba,
Nan dai tai masu fada dole aka,raba masu aikin da kowa zai yi a gidan,
Hamza ya,sayo wa Umma magani din tasha ta dan samu sauki tare da robb ta shafa a,gurin,
Aiko take sadiya ta hade rai wai tana son ya,sayo mata fruits ta gyara, bakin ta tun jiya yaki sayowa yana cewa baida kudi,
Amma ai gashi ya,sayowa Umma magani yanzu ina ya samu kudin da ya,sayo maganin dashi,
Ba,wani ya,fadawa Umma ba ita,da kanta taji zancen da,suke saboda kusa da, dakin su yake,
Ikon Allah inji Umma don tasan cewa Allah ya hada ta da mara kirkin yarinya,
Gashi tana jin ana mata yaya jiki amma ko tace mata sannu Umma bata,samu ba,daga gare ta,
Dole sai da Hamza ya,sayo fruits din sannan aka zauna lafiya a gidan ita dashi,
Zarah wace ke kallon ikon Allah tace yanzu kan kin kai ga irin sarakuwar da kike so yar bana tunda kin ce Aish yar kauye ce yar tsiya da,sauran su,
Duk da abin yai dan sanyi saboda mama ta je ta samu mama Sa,a akan tajawa yarta kunne don abinda take a gidan yai yawa sosai,
Yau gashi sai aci dafa duka da dare don dole saboda tace ita bata iya wahalan tuka wa kowa tuwo da cikin ta,
Bayan kwana biyu da Umma ta samu sauki tadan fito waje ta zauna don ta,sha iska,
Sadiya tana daki tasa wakan hausa remix sai faman bin wakan take tanayi tana rawan ta,
Hamza wanda ya dawo da leda wani yaron makwabta yana bayan shi dauke da leda yaron yakai ledan gurin da Umma take zaune,
Sadiya ta dago labule tacewa yaron cikin tsawa kai kawo ledan nan nan,
Umma ta dago ksi tace mata ni nada sakon a,sayo min dan ganye ne don na dan gyara bakina dashi,
Ai baice min naki bane don haka nace akawo min don ban yarda ni da miji na ai min isa dashi don ni wallahi wanan mulkin ba a kawo min shi,
Fitowa yayi daga daki yana cewa ke sadiya ki shiga hankalinki fa don bazan yarda da wanan irin cin fuskan da kike min ba,
Mahaifiyata ce zata zama abin wullakantawan ki koda yaushe tace ita ce taba,da sako to maye kuma na jinini haka,
Umma tace kyale ta babana akai mata ledan sai ta gyara ta juyo cikin yatsunan fuska take cewa adai bar maki ke k8 gyara ,
Aiko yai cikin ta kamar zai dake ta,ranan taga masifan shi saida mama tashigo tace ya kyaleta tunda yasan tana da lalura a jikin ta,
Kofan gida yya koma ya zauna yai tagumi yana tunanen yaushe wai Aisha zata dawo,
Kewan ta ne ya kamashi yarinya mai hakkuri duk abinda akai mata zata iya shanyewa ta hade a ranta batare da wani yasan anyi shi ba a gidan gashi yanzu dan tafiyan ta komai ya kara rikicewa a gidan dama ance mugu kariyan na gari ashe kuwa haka hausan yake,


Zan dakata anan sai bayan sallah idan Allah ya kaimu sai muci gaba mu kara jin yadda abubuwan suka kaya tsakanin Hamza da iyalin shi
Dafatan zamu

Download complete TXT · Novel page