Sarautar Mata

Chapter 57 of 94

sha ruwa lafiya Allah ya sadamu da rahamomin sa Allah yasa muna a cikin yantattatun bayinsa,
Ayi sallah lafiya yan uwa musulmai kada ku manta kusani ga,addu,oin ku don Allah,,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU

IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,,


Wasa,wasa watana daya da kwanaki a gatin mu sai a lokacin ne iyayyena suka fahinci cewa akwai matsala a tare dani,
Dafarko sunji dadin zamana irin yadda nake kula da harkan lafiyan yan garin gida da,waje,
Sai daga,baya da,suka,ji ban zancen tafiya ko kadan sai suka,fara tunanen ko akwai matsala a tare da nine,
Ban boye masu ba,alokacin da,suka tuntube ni na,fayyace masu komai nan wani wan mahaifina mai saurin fushi yace aikuwa bazan koma ba,muddin bashi ya kawo kafan sho cikin garin nan ba ,
Sai yasan cewa ke ma ya ce kamar kowa kina da gatan ki, don bai dauke ki a gaban mu ba,shiyasa suke ganin kamar baki da gata ko,
Wanan zancen yasa na kara sake jikina acikin yan uwa ina ta harkokin gabana batare da na,sa wani damuwa akan zancen ba a raina,
Al,amari na kiwon lafiya take mutum ke samun alheri daga wanan fannin, don haka ba karamin alheri na,samu ba a dan zaman da nayi,
Suna jin dadina nima inajin dadin don zaka ce a cikin su na tashi tun farko saboda yadda na sake jikina dasu tundai idan har ance mutum dan uwan haihuwa nane ,
Ranan da nazo garin idan baki manta na,fada maki akwai wasu yara da,suka daukan min kaya zuwa cikin gidan mu har na basu kyautan clean da,sabulu saboda taimakona da suka yi,
Wanan kyautan da nai masu yajawo min hanyan alheri sosai a gurin mahaifiyan yaran,
Don ba karamin dadi kyautan yai mata ita,aganin ta na yaba da yaranta da har nai masu alheri,irin haka,
Sai ga matar har gida tazo mi godiya nima da aka kwana biyu na tafi har gidan su mun jima da ita duk da ba hira mukeyi ba sai hakan yai mata dadi sosai, daga haka muka saba da Yarbuga, sunan matan ke nan,
Sanu sanu har shakuwa mai karfi yashiga tsakanin mu duk da ita ma,a gidan yawa take zaune tare da,sarakanta da matan yannin mijin ta,
Duk da ba,a garin mijina nake ba hakan bai hanani kula da duk wani hakkin auren Hamza da ke a kaina ba,
Mussan man gurin shiga na da kuma yadda nake mu,amulla da mutane gurin kama mutunci na,
Kunsan yan kauye da son ganin bakuwar mace tun dai da suka,ga na kwana biyu a garin sai suke zaton kila dai ni bazawara ce ko kuma budurwa,
Sau da yawa akan tuntubi yan gidan mu akan zance na sai suke fada masu cewa da aurena mijina yai tafiyane shine na dawo gida har zuwa lokacin da zai dawo sai na koma, dakina,
Yau ma kamar kullun bayan nagama duk wani aikin dana saba yiwa gwago a,shiyan mu da kuma dakin kwanan mu,
Sai na shiga wanka nafito na gyara jikina duk da ba wani kwalliya nayi ba ina kokarin saka hijjab a kaina ne gwago ta shigo dakin take kallo na a cikin mamaki,
Fita zakiyi ne Indo gwago ce mai tambaya na ganin ina,shirin fita zuwa unguwa,
Nace gwago gida malam kabiru zan tafi na duba jikin wanan yaron dana karawa ruwa jiya,
Gwago tace hakane amma dai Indo kikara kula da kanki duk da nasan kina yi to amma, kikara akan wanda kikeyi a baya,
Don kin san mutane yanzu sai a hankali don ganin da suke maki haka a gida suna daukan cewa ke bazawara ce,
Da,sauri na juyo ina fadin nashiga uku gwago kallon da mutane ke min ke nan a she,
Tace aikin san maza da zaran sun kyalla idon su ga bakuwar mace zaki ga abin ya,zama masu tankar gasa a gari,
Shine dan gidan hakimi ya turo wurin babanki wai suna kamun kafa idan har mijinki ya,sake ki ne,
Innalilla wa,inna alaihim rajjiun nasamu furtawa tare da kaiwa zaune, daga tsayen da nake ina cewa na shiga uku gwago kada fa fushin Allah ya hau kaina,
Tace ki kwantar da hankalinki Indo don kowa ya,shede ki da kamun kai a garin nan don har ma kin fi matan su tsare dokan aure din ke ga sock ga hijjab gudan babba da kike sakawa a jikin ki,
Don haka tashi kije Allab ya tsare ki yakare ki ga,duk wani mugun abinda ka kawo maki illa a rayuwan ki ,
Na ansa da hankali da fadan Ameen gwago amma gaskiya zan daina fita cikin gari yanzu sai da dare na,dinga fita,
Dariya gwago tayi tace ai baki tsira,ba ko a haka din don wani sabon sheri za a dauka a dagwara maki a ka,
Don haka fita da rana ya fiye maki fitan daren da kike gani shine saukin ki a,rayuwa, alheri,
Badon naso ba haka na daure nafita zuwa duba yaron da nakewa treating don naga yadda lafiyan ta,shi take,
Zamu dawo nabiya gurin aminiyata maman saudat muka dan gaisa sama,sama da ita nake fada mata zancen da mukayi da gwagona don haka zata rage gani na gidan ta don tsaron mutuncina,,
Take cewa ai haka maza suke ko ita ai akwai wani kanin mijinta baiyi auren fari ba ya matsa mata,wai tai min magana yana sona da,aure,
Cikin sauri nace wa iyazu billahi amma dai mutane basu da,akidar arziki saboda son zuciya zasu mayar dani bazawarar karfi da yaji,
Tun daga wanan danan na daina fita kamar farko idan ma kazo ne na duba ma mara lafiya zan tsaya a gida sai dai ka kawo yaron na fita na duba shi inga abinda ke damun mutum, iya kofan gidan mu kawai, ban zuwa gidan kowa kuma,,
Ganin haka yasa,gwagona kara tausaya min don tasan cewa ba karamin hakkuri da sanin ya kamata nake dashi ba , saboda ganin yadda a lokaci daya na kama kaina, ga komai don gudun zargin mutanen duniya akaina,

****** ********** ******
Tafe yake a,saman mashin din shi amma zuciya shi cike take damuwa dake tare dashi,
Saboda duk kwana kin nan ya,rasa abinda ke damun zuciyan shi wanda ba komai bane ya kara haddasa mai wannan yawan damuwa sai rashin kwanciyan hankalin da,bai samu a tsakanin matar shi da yan uwan shi har ma da mahaifiyar shi wani lokaci,
Duk itace sillar wanan auren sai kuma ya kasance yanzu abin daga baya babu dadi a tsakanin su,
Wanda yake ganin hakan duk laifin Umma ce wacce bata sararawa matar tashi duk da tasan cewa tana dauke da lalura a jikin ta,
Amma baisa su daga mata kafa,ba,su barta da halinta duk yasan cewa ita ma Sadiya ba a baya ba gurin takkalar magana, agidan,
Don kullun idan zaiji fitina daga itace zancen fitinan zaifara fitowa, amma sai ya take gaskiya wai, don kada ranta ya baci ya shafi dan dake a cikin cikin ta,
Tunda shi haihuwa yake so yanzu kamar zai tashi sama ya fadawa Allah, akan yana son ganin gudan jinin shi a duniya shima,
Ga Sadiya wacce ta kura mai ido don taga yadda zaiyi da ledan hannun shi, don ganin su Umma a,tsakar gida yayi,
Ga kuma su Umma da mama,da,sauran yan uwan shi duk idon su a kan ledan,
Cikin dakewan zuciya ya wuce su ya mika mata ledan yayin da yai murya kasa kasa yana cewa ta dan san mai ya ba,su Umma koda kwara biyu ne su ci,
Duk suna kallon abinda ke faruwa a gaban su take cewa wanan dan abinda baida yawa zai ce sai yabawa wasu sun ci,
Mama Hafsi batasan lokacin da take cewa ba amma dai ke wanan yarinyar baki da mútunci yanzu wanda,zai bawa mahaifiyar tashi kikewa wanan tsiwar ba kunya agaban kowa,
Ki dai ji tsoron Allah don kema uwace watarana zaki haifa ne ai maki duk yadda ki kaiwa wata,
Haba mama Hamza ya tare zancen da sauri a cikin bata rai yana fadin wanan ai mugun fatane kawai akewa mutum amma don Allah dan wanan zancen ai bakai ace an tsaya wanan zance haka ba,
Cikin mamakin shi duk wanda ke gurin yake kallon shi yadda ya murje ido yanawa mama hafsi tsawa akan matar shi,
Matar da tun suna kanana take faman dawai niya dasu a duniya ta dauke su tankar diyan da ta haifa da cikin ta,
Cikin mamaki shi mama take kallon shi ida ta iya bude baki da kyat tace Hamza kan ka daya kuwa don wanan yarinyar mara mutunci yau har idon ka ya rufe kana fada min magana iya son ranka,
Mama idan dai ba wani fitina kike nema ba a gidan nan banga dalilin yin wanan magana ba don dan wanan abin dana kawo mata don tana marmari kawai shine har abinda ya tsone ido, kuma,
Mama zatai magana Umma wace take zaune kamar ruwa ya cita tace barshi hafsi ,
Idon tani ce ya kawo mata abinda ma yafi wanan agidan nan bazan kara mai magana ba,
Sadiya ce ta saka wani irin kuka ta mike da ledan a hannun ta zuwa dakin ta tana cewa ita gidan su zata tafi don dai kowa ya tsane ta agidan ,
Ba yau ba tasan cewa mama hafsi bata kaunar ta akan Aisha take gwada mata kiyayya tau ita zata bar masu gidan bazata zauna da,su ba sai dai idan yana son ta ya nema mata wani gida ta zauna,
Ya juya idan iyayyen nashi suke yana fadin kin gani mama yau kun kai ga yadda kuke so
Ni ba zan yarda a rabani da mata ta ba muna zaman lafiya kowa a gidan nan ya tsane ta ba mai kaunan ta,
Ya bi Sadiya daki wace, take cewa cikin sabo hijjab din ta tana shirin barin gidan cikin kuka,
Zan bar gidan sai ku zauna da,wacce kuke kaunan zama da ita kullun Sadiya ce mai laifi,
Hamza yana cewa nace ki dawo babu inda zaki tafi don dani kike zama bada wani wani ba agidan,
Amma haka bai sa ta tsaya ba fuuu tabar gidan da kukan ta zuwa gidan su cikin kukan kissa da kisisina,
Hamza din yabi bayan ta a gigice yana lalashin ta yana bata magana akan ta dawo wai zai dauki mataki,
Suna fita mama ta juya inda Umma take tana fadin cewa yaya kinga irin annobar da kika jawo wa kanki a gidan nan,
Yarinya karama da irin wannan makircin manyan mata haka kamar wata uwar mata,
Umma tace ai da ki kyale su hafsi don duk abinda ake ina gani kyalesu kawai nake yi don ban son yawan fitina,
Yaya,bazan kyale ba don kona yaron nan yarinyar nan ke son yi a gidan nan,
Yana zaune da matar arzikin shi yar mutunci amma kikai ruwa kikai tsaki akan sai ya kara,aure wai Aisha bata da kirki,
Yau ga irin abinda kika daukowa,kanki a,gidan ruwan dafa kanki da kanki wanan makiran yarinyar idan ba,a yi da gaske ba,sai ta rabashi da kowa a gidan nan
Yanzu gashi yarinyar nan daga zuwa ganin gida wata biyu da dan kai iyayyen ta sun rike ta a can ,
Nan kuma babu wanda ya bi bayan ta a ga may ke faruwa da ita da,sunan sati biyu gashi har yau bata dawo garin nan ba,
Ibrahim ke tsaye wanda ya,shigo gidan don ganin fitan Sadiya da kuka dan uwan shi yana bin bayan ta a cikin tashi hankali yana son ya tambaya ko may ke faruwa sai kuma ya samu mama hafsi tana mayar da magana,
Can Hamza ya shigo gida rai a bace nan yake cewa cikin bacin rai shi gaskiya ba zai yarda a kashe mai aure ba don yana son matar shi,

Sai da yamma iyayyen Sadiya,suka kira akan cewa lalai sai ya canzawa Sadiya gurin zama tunda ba,a kaunar ta a gidan,.
Nan ya nuna masu cewa gaskiya baida zarahin yin haka yanzu sai dai ayi hakkuri akan zai dauki mataki akan al,amarin za a gyara komai,
Amma sai mahaifiyar Sadiya din ta iya nuna cewa sai dai mama hafsi tabar gidan don bazata yarda yar ta,ta zauna da ita gida daya ba bata kaunar ta,
Hamza dai hakkuri yake bayarwa cikin kwantar da kai yana cewa ayi hakkuri zai dauki mataki in Allah ya yarda,
Andawo mai da,Sadiya a daren don ita kanta ta fadawa mahaifiyarta a mayar da ita saboda,bazata yarda ta kwana gidan su ba kada a juya mata kan shi idan bata kusa,
Ba kunya washe gari ya nunawa mama cewa wai zata iya komawa garin su da ta,fito don shi zaman lafiya yake bukata a tare da iyalin shi,
Mama Hafsi take ce mai ya kwantar da hankalin shi, don
Itama tafi bukatan tabar masu gidan su tunda bai san darajan iyayyen shi ba ita bazata zauna tana kallon yadda yake wullakanta mahaifiyan shi a gaban ta ba,
Sai da Ibrahim yafito daga daki yanuna mashi cewa shima fa namijine cikin nuna,shi yake cewa babu inda mama zata indai don wanan munafukar matar takace, wace ta shigo don ta watsa muna gidan mu,
Yau gashi matar ka ta kwarai saboda mugun halin da ta sakata, tai tafiyan ta gurin iyayyen ta sun rike abinsu can,
Kana nan kana hauka akan wannan mara mutuncin matar taka wacce bata da kirki har kake wani zakewa akanta,
But Sadiya tadago labulen dakin ta fara surfawa Ibrahim zagi ta uwa ta uba tana aibanta shi da mugun kalamai, daga baki ta,
Umma dake ta hakkuri tana, hadewa don kada a ji muryan ta zancen bata san lokacin da tace ke ar, da halinki sadiya baki da mutunci ko kadan wanan mugun kalami irin haka ga dan uwan mijiki baki ko jin kunya ko nauyi,
Haba ai sai ta juya a kan Umma tana fadin dama duk bakin ku a hade yake nasani babu mai kaunata don ba don Allah kika yarda da,zancen auren mu ba,saida mamana tasan yadda ta shiga ta fita tafi karfin ki,
Don haka ni bazan kyale kowa ba a cikin ku aure ne da Hamza nayi sai mutuwa, babu yadda zakuyi dani,,
Duk wata bakar tsohuwa da bata san kama, mutuncin ta ba nima bazan ji kunyan ta ba daga yau,
Baki bude galala Umma take kallon Sadiya tana sauraren ta duk mamakin kalaman ta akanta ya cika ta,
Sadiya taci gaba da fadin dama nasan ki gurin son kai da nuna son diyan ki din haka idan kin shigar mashi ne an sayar maki sai mu kara dake,
Ni ba yar Agwai bace da kuka raina keda duyan ki kuke takata a duk lokacin da kukaga daman yi mata rashin mutunci, sai kuyi,
Sai hamza ne wanda yafito daga bandaki yake cewa ke ke ashe bance kada naji bakin ki a gidan nan ba kuma,
Ina bata tsaya sauraren shi ba,sai daga harshe take tana fadawa Umma da danta abinda duk yazo mata a,bakin ta lokacin,
Suna shiga daki mama hafsi tanisa tare da cewa, ki ga irin bala,in da kika kwasowa kanki da hannunki,
Lokacin da na nuna maki rashin dacewan haka, kikace ina bakin ciki da karuwan danki a fili, yanzu wa gari ya waya ?
Washegari da safe Baba Mudi yasa aka sallamawa Hamza inda yafito yana ganin Baba ne duk sai ta dan dabuce dan kunya da nauyin da ya kamashi,
Badon komai ba don ya dade suna wasan buya da shi don sam bai yarda su hada hanya da baba din don nauyin shi yake ji sosai,
Baya ce mai bayan sun gaisa Hamza idan nauyin iyali ya hau kan mutum sai ya hada da hakkuri don kowa da halinai aka zama dashi,
Kaga mu maza idan munkayi sake har mace tayi galaba akan mu ba karamin kona mu sukai ba, akan iyayyen mu,
Don haka kayi aniyan gyarawa da mahaifiyan ka kada ka bari shedan ya rude ka akan uwar ka don mace shedaniya ce idan ba,a dace ba,
Hamza ya gane nufin Baba ke nan yaji hayaniyar da akai a gidan tun shekaran jiya,
Don haka kunya da nauyi suka kamashi don yanzu hankalinshi yadan fara dawowa yasan Sadiya shu,uma ce sai dai babu yadda zai yi saboda gashi aure ya hada kuma har da rabo a tsakani,
Shi kuma gaskiya yanzu yana son haihuwa sosai don tun Umma na fadi bai dauka har yanzu abin ya shiga ran shi sosai,
Godiya ta sakeyi wa baba yana cewa ya gode insha Allahu za,a gyara da yardan Allah,
Sai kuma yaji abinda yake nokewa akan shi Baba ya sako zancen da cewa,
Kayi kokari katai ka taho da matanka don nasan cewa akwai dalilin da yasa takai har wanan lokacin a can,
Amma in katai koma manene zakaji don nasan iyayyen ta mutanen kirkine sosai, baza su rike ta har zuwa wanan lokacin ba haka kawai,
Yace cikin ladabi in Allah yaso Baba zan tafi idan na dawo daga tafiyan da zan yi,
Allah yaba da ikon zuwa inji ba yace shike nan ni zan tafi kasuwan Kalgo don yau na taka ci,
Yaiwa Baba a dawo lafiya ya juya zuwa gida yana tunanen zancen su da Baba shi dai gaskiya dattijon nan yana ganin mutuncin shi don mutum ne wanda yasan ya kamata,
Duk ya ya bashi diya a lokacin da ya ke da bukatan taimako yazo ya kasa rike mai ita yadda ya dace baisa yagan shi zai fada a masifa ba ya ki fada mai gaskiya,
Sai kuna zuciyan shi take ce mai itama Aisha may zai sa ta tafi ta wuce lokacin da ya bata ta dawo taje tai zaman ta, har wanan lokaci haka a gurin iyayyen ta,
Wanan dalilin da zogin ganin yana da wata mace a tare dashi yasa shi shareta kawai yana gani ai in tagaji zata dawo da kan ta tun da ba fada sukayi ba lafiya kalau suka rabu da ita don shi da kan shi ya kaita har tashan mota da zata wuce,
Indan da tana nan yasan duk wanan fitinan daya ki ci yaki karewa tsakani su Umma da Sadiya da baza,ayi shi haka ba,
Yawan

Download complete TXT · Novel page