Showing 192001 words to 195000 words out of 299981 words
a gidan nan haba dai yarinya sai kace iblishiya ,
Umma tana daki bakin ciki da takaici duk ya kumay ta sai jijiga kai take tana hadiyan zuciya don ta dauko wutan gasa kanta cikin gidan ta,
Hamza yana,daga kofan gida zaune a majalissan su duk suna jin irin hayaniyan da akeyi har zuwa fitowan Ibrahim yana huci,
Kunya da takaici duk sun rufe shi inda yake zaune cikin takaici da dana sanin auren Sadiya a rayuwan shi,
Tir da Allah dai kawai yan majalissan kofan gida suke mata don dama tunda ban gari ko ruwan sha,suka aika bata basu ko na,alwala balle wani abin, ta kai masu ko ina,su ma don ba haka muka saba zama dasu ba,
****** ********* ******
Saboda sanyin da akeyi dole kowa ya shige dakin shi don sanyi yayi yawa a ranan,
Daga massalaci Hamza gida ya dawo dakin Umma ya fara shiga ya,samu mama tana hada mata maganin ta yai masu sannu da jiki,
Sai Mama ce ke cewa fadan ka dai ya koma a kan Ibrahim dashi akai fitinan yau kuma,
Tsaki kawai yaja tare da cewa kai Allah dai ya kyauta wanan hali na,Sadiya baiyi ba wallahi,
Yace ina can gurin neman kudin da zan kai wa yan sanda gobe ne ranan da suka yanke muna mukawo ko su kaini kotu,
Duk na zagaye garin nan ban samu wanda zai ara min koda dubu goma ba ,
Mansur ne, kuma ina jin nauyin shi sosai don irin halarcin da yake min yaiyawa wallahi,
Tafiyan nan da mukayi zuwa garin su Aisha duk da kudin shi mukayi shi babu ko sisina acikin tafiyan,
Umma daga inda take zaune take cewa Allah, Allah ka taimake mu ka rufa muna asiri,
Amma sai naga ai ga matarka ta dawo da abin arziki daga garin su may zai hana ka tambaye ta tabaka koda buhu hudu ne ka,sayar kabiya kkudin,
Da Hamza da maman da ke zaune gefe sukace haba dai ai wanan ya zama rashin hankali,
Mama tace ai ita Humaira ta daban ce zata iya bayar da kudin batare da wani ya sani ba, kuma ta basu baya,
Amma dai daga dawowanta jiya jiya muce kuma zamu karbe mata,abinda tadawo dashi,
Ai sai a raina muna hankalin mu a dauke mu mayaudara muna mata wayyo ne kawai,
Ya mike yana cewa Allah dai ya rufa muna asiri kawai don komai akace Allah an kare zance ko, ya mike
Yana tambayan Umma ko ta ci abinci mama tace ai yau sai kwano duk ta cinye,
Murmushi irin na mara lafiya Umma tayi tace badole na ba yau kwanon miyana da nama aciki har tsoka biyar ga mai da kamshi na tashi a miya sabanin karni da zai daki hancin mutum,
Sa,a datu tace wallahi ni yau har karawa nayi don dadin abinci bansan yadda akayi na cinye shi ba tas har wanda na karo duk na ciye,
Allah ya kyauta yace tare da mikewa ya na shirin barin dakin sai mama take ce mai tau matar kadai ta tafi gidan su tunda magariba,
Hmmm, Allah ya kyauta yace, tare da dan guntun murmusawa, kawai,
Babu inda zaka in taga dama taita zama can har abada amma babu mai binta, a gidan nan,
Umma ce ke wanan magana haka a hasale cikin dan daga muryan ta,alamar ranta ya baci,
Hamza murmushi kawai yayi don takaicin da yake ji a ran shi,
Zaune nake abinka ga mai tsohon ciki gashi kuma na kwana biyu banyi aiki ba, sai naji duk yar gajiya ta kama min jikina,
Da,sallama dauke a bakin shi ya shigo dakin idanuwan shi a kaina inda nake dan gishingide gefen kujera na nai filo da kujeran,,
Maimakon nai mashi sannu da zuwa irin yadda na saba yi mashi, da,farko sai kawai na,share shi kamar ban san shigowan shi ba dakin,
A, hankali yakai zaune gefe yana cewa Yay Allah tare da zama ya mike kafafunan shi kan shi yana a masangalin kujeran, danake zaune a kai,
Shiru ne ya,dan biyo baya dakin dagani har shi ba wanda yai magana sai can cikin wata kasalaliyar murya naji shi yana fadin
Hummai, wai fushi kike danine ko kuwa don naga kamar har yanzu baki huce ba still kina jin haushina, haka,
Sai naji ya wani furzo iska daga bakin shi tare da dunkule hannayen shi guri daya,
Cikin yar muryan da ba zai iya fassarata ba nake cewa akawo maka abinci ne yanzu,
Cikin dan marairaicewa yace idan na samu zanci ai, tunda za,a bani ai na gode,
Mikewa nayi na jawo dan stol din dakina na aje mai a gaban shi tare da kawo mai ruwan sha mai sanyi,
Fita na yi don na kwaso shanyin da na shanya da yamman nan ,sai naji sallaman wasu mata biyu, sun shigo gidan,
Na dai karba masu sallama amma dana fahinci su Sadiya ce sai ban tsaya gaisawa dasu ba na shige ta gaban su kawai,
Suka bini da idanuwa caaaa suna kallon irin yadda na mulmule na koma gwanin ban sha,awa dani,
Dakin ta suka nufa a lokacin nai alkawarin nuna mata iyakarta nima, don daga kofan daki nake a zaune,
Yana daga ciki yana cin abinci hankalin shi kwance sai nake cewa badon naso ba yaya su Anty Hindatu da yaranta ?
Sai da yai yar ajiyan zuciya alaman cewa, yaji sanyin magana na, yake cewa, duk suna lafiya dazun na je na,fada masu cewa kin dawo ai,tace tana gaisheki,
Yana kai nan sai muryan Sadiya muka ji daga kofa tana cewa wai ana magana da kai, cikin wata murya kamar ta fada,
Da sauri naga ya,dago kai ya dan kalle ni tare da tsaki, yana cewa ita,wanan yaushe ta,dawo ne wai,,
Kodai yaushe ne sai ta jira idan girki yazo kanta sai bakin su, gan ka don yanzu ba lokacin ta bane,
Murmushi yayi cikin mamaki yake cewa kema kin koyo naki kalar ke nan,
Banyi magana ba sai saya kofan dakin da nayi tare da,sa sakata, ta cikin dakin,
Gurin na samu daga gefen shi na zauna ina jin muryan su daga waje mama hafsi nacewa, tunda sun rufe kofa ai sai kuyi hakkuri ku tafi sai da safe ko,
Mikewa naga yayi a zatona fita zaiyi amma,sai naga yana kokarin cire tufafin jikin shi ne,
Gurin da,na aje kudin da Mama Rahana ta ware mai na dauko tare da cewa gashi, wai kayi hakkuri dasu,
May ye wanan din yana kallon bakar ledan da nake kokarin mika mashi a lokacin,
Sai ya karba kafin na bashi amsa komawa yayi ya zauna a saman kujera daga shi sai wando a jikin shi, yana kokarin bude ledan dake hannun shi,
Kudin da yagani a ciki sun bashi mamaki don baiga na taba buhuhunan abincin dana zo dasu ba balle ya ce su ne, na,sayar na samu wanan kudin dake hannun shi,
Humaira wanan kudin fa haka masu yawa daga ina suka fito haka ?
Kudin da nazo da sune su mama suka cire ma wanan,
Ikon Allah duk kudi haka masu yawa nawane Humaira,?
Ban ce mai uffan ba sai naga ya mayar da kanshi a saman makari kujera yana fadin,
Allahu Akbar kabiran Allah na,gode maka da,kai min baiwan wanan matar mai karamci da mutunci da rufin asiri,
A hankali yace Humaira cikin wani murya mai rauni, na tabbatar da ke alheri ce a,gareni,
Kamar zai kara furta wani kalami sai kuma naji yai shiru yana mai sauke wani irin numfashi,
Tsayin yan mintina yashiga kirga kudin a hankali yadago kai bayan yagama yace har dubu ashirin da biyar Humaira ?
Idan kika bani wanan kudi masu yawa haka to ke fa ga ki da lalura a gaban ki,
Nace batare da nabashi amsa ba don ni baida wani bakin da zai min dadin bakin maza yanzu na yarda,
Akwai buhun masara dana dawa sai maiwa wanda za ai amfani dashi agida,
Na,shimkafa zan aje a gurina na dinga amfani dashi tunda matar ka bata son zaman lafiya a gidan nan,
Ni da ta samu a gidan banyi bakin ciki da,shigowan ta ba amma,sai itace take bakin ciki da zamana dakai,
Hmmm kawai yace mubar zancen sadiya kibani amsata kudin nan da,sai ku rage a raba,biyu kibar saura a gurin ki don kinga kina da lalura atare dake gashi yanzu ni banda hali kamar da,
Allah zai hore min insha Allahu wanda zanyi fitar kunya dashi, wanan din dai naka,ne, su mama suka cirema,
Kan shi, ya,sadda a kasa yai shiru yau kwana kusan shidda yana yawon neman koda dubu goma ne wanda zasu kai police station gobe wa,adi zai cika,
Sai gashi Allah ya,rufa mai asiri ta,dalilina a lokaci daya ta hanya alheri da,rufin asiri,
Hawaye ne suka digo mai a hankali sai irin cin fuskan da yai min akan sadiya kafin natafi gida ya,fara fado mai arai,
Saboda kawai ance tana da ciki yadinga nuna mata fifiko akaina,sai abinda tace a gidan akeyi,
Ashe ni ce mai daukr da cikin da ta,dace ace ya taimakaw da kullawa ba,Sadiya ba
Matar da ba matar rufin asiri ba gashi dan kudin ta daya karba,duk gari sai da kowa yasan abinda ke a tsakanin su,,
Amma acikin dare daya gashi Allah ya rufa mashi asiri ta hanyar wanan baiwar Allah,
Dubu bibiyun da mama Rahana ta bayar abawa su Umma da mama hafilsi nakara miko mashi yace wanan kuma fa,
Nace su mama za,a bawa, da Umma wai su ma suyi hakkuri daga haka na shiga shirin kwanciya kawai na bar shi nan zaune nan ya zurfafa ga tunane,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABUIDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,,
Ban yarda komai ya,shiga tsakani dashi ba don baima ga fuskan hakan ba, a gurina,
Kafin wani lokaci har nagama abin karyawa nabawa kowa nashi masu fita zuwa gurin neman kudi,
Na kaiwa su Umma nasu har ita mai jidalin na kai mata,nata a kofan ta ban dai shiga dakin ba,
Barcin Hamza ya koma ni kuma wanka nafito ina tsaye nake ina,shiryawa naji a na,wani irin sallama da karfi daga kofan shigowa gida,
Nake mamaki a raina waye kuma ke wanan sallaman haka kamar zai shigo,
Mama naji tana cewa Innalillahi wanan mutumin baya ko bari gari ya,waye sosai zai wani sallamawa mutane haka,
Abinshi yazo amsa don haka ai sai a fito a bashi Sadiya ce ke fadin hakana,
Muryan mama hafsi daga kofana take fadin Aisha idan Hamza idon shi biyu ki fada mai ga mutumin nan ya zo,
Nan na fahinci wanda ke binsa bashi ne yayo sammako irin haka,
A hankali nake tashe shi ya tashi ana mai sallama a waje,
Yana bude ido yaji muryan mutumin hamdallah yafara yi sannan ya mike da salati ya fita yana daga labule zai fita na hango Sadiya tsaye a kofan ta ta bishi da harara,
Murmushi nayi nace aiki, wai daukan dutse da yatsa mace ki sawa kanki mugun kishi irin haka,
Ina fitowa sai naga har Umma dake zaune daki ta dan rarafo zuwa waje duk sunyi zurun zurun gaba dayan su fuskan su na fuskantar kofar gida
Sai mamace ta yafa zuwa wajen itama Sadiya ko sai wani zabura take tana yan aikace aikacen karya,
Kasa kasa take magana cewa wai wanda yake da matsala shine harda kara shigewa barcin safe kamar wanda baisan mace ba tun farko,
Mutumin tare da dan sanda yazo hamza yana fita sai yake ce mashi, may yasa yadawo maigida ai case yana hannun police ne don haka goma akace su hadu police station ko,
Mama tace kai kabishi sannu mana a wanye lafiya don haka aiba komai bane,
Kaidai kayi hakkuri kawai take cewa mutumi n a cikin yar lalashi irin ta manya,
Mama don Allah ki barshi ki koma gida sai goma zamu tafi nida Baba Mudi police station din,
Suka tafi suna cewa sai an hadu din a police station din ai yau bazai daga mai kafa ba,sai ya sa,an daure shi,
Suna shiga gida mama ke cewa aida kabishi sannu yaron nan don yadan yi hakkuri tunda babu kudin kaga,ai da,sai a bashi hakkuri, ya kara ma,wani dan lokaci a gani,
Barshi kawai mama insha Allahu muna rabuwa lafiya dashi bari nai wanka mufita yanzu,
Sadiya kamar idanuwan ta zai fito don gulma duk ta matsu taji yaya za,a kwashe dashi da iyamuri mai kudi,
Don ita haushinta shine kawai ya shiga gurina ya kwana kuma harda kara kwantawa da,safe, wai barcin safe, da mace,
Fitan Hamza da yan mintina sai ga,su Kubura sun shigo tana goye da yarta a,baya yarinyar tayi wayau sosai,
Sadiya tana kofan ta tana zuba ruwan jarka a buket tadago kai suka hada ido da,Kubura sai kubura ke cewa,
Ke mai kika takane da bazaki gaida mutane ba ki wani ganni kin share kamar ba Sadiya tsami ba,
Nan suka tsaya kar ta,sankar suna fadawa juna bakaken maganganu acikin wasa wai, sukr sukar junan su,
Na karbi yar ta a bayan ta na,shiga daki itama tashigo take cewa mutanen illela baku so dawowa ba,dai nake gani shiru haka duk wanda na tambaya ace min wai baki dawo ba kina can har yanzu,
Mun gaisa tare da dan taba hira akan irin iskancin da,Sadiya take shukawa a,gidan,
Take cewa ai gara da,taiwa Umma haka tagani tunda tace bata da mutunci yanzu ta hadu da gamon ta ai,
Da,zata tafi har kofan Sadiya ta tafi ta daga labule tana cewa ita ta tafi don taga tana wani shan kamshi bayan tasan cewa,
Mijin kaunata ta,aure kuma,shine har zatayiwa mutane rainin senses
Ta kuru Aisha ta,samu wallahi da itace koda gigi bata shigowa gidan balle har taiwa mutane iskan ci,
Kallin su kawai mukeyi don dama kawaye ne tare suka tashi suna,rashin jin su tare kowa yasan kowa a cikin su sai dai ita,Sadiya tasan Kubura ta fita tsula iskan ci don ko yanzu zasu iya karawa intai wasa,
****** ********* ******
Bayan ya dawo yai masu Umma,bayanin komai ya kuma basu nasu da tsaraban da nace ayi amfani dashi a gida,
Sai suka shiga godewa suna sa albarka tundai ma mama Hafsi da ta zake tana ta yabona Umma,sai yar dariyar yake takeyi kawai, kunya da nauyi duk ya rufe ta,
Nasha godiya aranan gurin iyayyen shi har ma,da yan uwan shi ,hakan yasa Sadiya kara hakeni a ranta,
Nai kwana biyu na nafita batare da,wani abu ya shiga tsakanina da Hamza ba a gidan,
Sadiya ranan da ta karbi girki murya har kofan gidan don ta kasa boye zumudin ta a fili,
Allah yasa nasan halinta don haka nagama duk wani abinda ya dace nayi da wuri na shige daki abina don dai nasan komai tsiyan ta sai yamma zai bar dakina,
Yashigo gidan a gaji yasamu tana bakin gurin da muke girki baiko kai ga karasa shigowa ba take cewa ,
Yau dama yanzu nake zancen ka don man da zanyi miya baida yawa kadan na samu a roban mai,
Yace cikin mamaki tare da kallon ta wani iri haba Sadiya ai dai kya bari na karaso na huta kafin ki min zancen wani abu can,
Tace so nake na dora girki da,wuri na kare, shiyasa na tambaya,
Tau banda shi sai ki barni na huta ko don agajiye nake, kiyi amfani da kadan din da kika gani,
Har ya dan gwauta ta kadan sai take cewa amma da matar ka tai girki naga komai ka sayo mata a gidan nan,
Kana ta,wani rawan kafa akan dawowan Aisha don kawai kaga ta dawo da yan tarkace daga kauyen su,
Hmmm aikema sai kije kauyen ku ki samo min sai naita rawan kafa akanki,
Amma dai kasan muna da kauye zuwa dai ko?
Ai dan nasani yasa nake ce maki kema sai ki tafi ki kwaso min,
Nan ta,soma tayar da harshe tana son zancen ya koma masu na fitina sai cewa yayi na ban ba Aisha ko kwandala,ba, da,tai girki kuma ban sayo mata komai ba,
Ai tamayi kokari da tabar maki guntun man don itace ta,saya abinta,da kudin ta,
Bazan saye ba idon na,saya kake cewa hakan baza,a saya din ba,
Ina sharan dakina saboda yamma tayi don zuwa biyar na yamma duk na gyara ko ina nawa saboda sharan dare da,baida kyaun yi,
Nasharo dakina zuwa kofa har kofan mama hafsi sai ban sharo part din Sadiya da Umma ba,
Oho dai dadin abin nima ina d hannun yi basai an min bakin ciki ba don nima zan iya,
Murmshi nayi nashiga dakina ina dariyan Sadiyan wacce ke ta zuba hauka akan kishi wai ita kan miji take wanan hauka,
Ni batasan cewa akan umurnin iyayyen na dawo gidan shi ba don ni duk al,amarin Hamza yafita min akai,
Don nasan kuma na tabbatar kamar sauran maza