Showing 195001 words to 198000 words out of 299981 words

Chapter 66 - Sarautar Mata By Makawa

04 Dec 2025

17677

yake don samun wata,nasa shi shagala da,diyaucin da nake mai a baya,
Anyi zamanin Lima yanzu gana Sadiy duk sai da nakai zuciyata nesa akan zaman gidan shi,
Ga fitinan mahaifiyar shi wacce take nuna min rashin kaunarta gareni a filin Allah,
Sai tsangwama da son jidalin da yan uwan shi ke min akoda yaushe sukaga daman yi min hakan
Ga makwabta da Umma take bi tana bata min sunan cewa wai banda kirki ina mata kaza ina mata kaza,
Sai dai yanzu wasu sun gane gaskiyan al,amarin don gaskiya tai halin ta,
Wanan abubuwan su na rike a raina nake mai kallon mutum mara adalci duk da nasihan da gwana taimin nace nayi hakkuri shi hali da sauyin namiji ba mai dorewa bane,
Hakan yasa nake karabawa kaina hakkuri ina shanye duk wani abinda nake ganin a gidan,.
Shikan shi na lura da cewan hankalin shi ba a kwance yake ba akan share shin da nakeyi,
Abin ya nadan damun shi sai dai dakewa yake baya nunawa kaman yadda nima nake shanyewa,
Kwata kwata na fita zancen al,amarin shi ban rawan kan da nake a bayan kamar yadda na saba yi,

****** ********* ******
Na idar da,sallah magriba ina zaune a dakina kamar yadda nake nisanta kaina da kowa a gidan,
Mama Hafsi ce tai sallama tashigo dakin ina ganin ta natashi zaune ina cewa mama ina wuni,
Guri ta samu ta zauna a saman kujera hakan yasani gane cewa da magana tashigo ke nan,
Bayan mun gaisa take ce min Aisha gurin ki nazo,
Nace cikin jin nauyi da yar kunya,da tau mama ina mai kara gyara zamana, don sauraren ta,
Yanzu Aisha irin rayuwan da kika zaba ki zauna da mijin ki kina gani shine mafi alheri a gare ki,
Murmushi nayi tare da,dukar da kaina kasa cikin dan kunya,
Mama tace duk irin halin da kike ciki da mijin ki a gidan nan nasani Aiaha,
Sai dai banji dadin ganin haka daga,gareki ba don wanan nasan ba tarbiyanki bane,
Aisha ko irin halin Sadiya kike kokarin koyo kokuma kin sauya halinki ne wanan tafiyan da kikayi, da sauri na daga kaina na dan kalleta
Aisha baki dauko wakanki hanyan alheri ba don har ga,Allah zunubi zaki kwasawa rayuwan ki,
Don shi namiji ko ke kadaice a,gurin shi tunkan hauni ne yau dadi gobe madaci, haka zama yake,
Balle idan ance ku biyu ne ko fiye da hakana a gurin shi dole ne sai mace tayi tana hadiyan wasu bakin cikin dana mijin tare da kawar da kanta ga,abinda yake tana daurewa ,
Badon komai ba sai don kada wanda suke tare su fahinci rashin jin dadin ta ga wurin shi,
Hakan yasa zakiga mata da yawa idan har suna bukatan dorewa a dakin auren su zasu dinga shanye bacin ran da na miji don komai ba mai dorewa bane zo mu zauna zo mu saba,
Don haka kiyi sauri gagauta tsakanin ki da maigidan ki tun mutanen gidan nan basu fahinci irin zaman da kukeyi ba,
Don wanan shegiyar kishiryar taki mara mutunci da zaran kin bari tagane tsakanin ki dashi wallahi zakice na fada maki a tsakar gida zata fito tana daga harshe tare da nunawa duniya komai duk da ita ma din ai ba wani zaman lafiya sukeyi ba tsakanin su,
Kece dai kike hasashen kan don baki san irin wainar da aka toya ba agidan nan kanki da bakyanan,
Ita kanta yaya din datai wanan hadin yanzu abin duniya yakai mata ko ina a tsakanin su don ba dadi daga ita har uwar Sadiya din duk anbata a tsakanin su,
Don kowa son danshi ya rufe mai ido suna ciwa juna mutunci da tonon asiri a,tsakanin su,
Yau aike Aisha Allah yai maki fada baikamata ba,ace kiyiwa Allah butulci haka,
Duba fa ki gani cikine tsoho a jikin wanda Allah ne ya baki kuma ya boyewa kowa ganinsa sai lokacin da yaso ,
Anyi zaton cewa kina dashi ne da akaita maki giri da cin fuska ana céwa wai baki haihuwa ke juyace aure shekara uku da kai baki taba batar wata ba,
Ba abinda ba,ai maki gorinshi ba a gidan nan ke har gorin arziki an maki yau waya fitar dasu daga kankin da ake ciki bakyace Allah yakawo sanadin ki kika biya mai bashin ba duka,
To aiko haka ya kamata ki godewa Allah kibar komai ga,Allah don shi yasan abinda ya dace da,bawan sa,
Wanan yarinyar Sadiya da kike gani ba yarinyar arziki bace idan kikai hakkuri wanan auren nasu bazai kai ko ina ina ba in fada maki,
Kuma kisa ido kiyi kallon dan zakice na fada maki wallahi saboda sam bata da mutnci,
Amma idan kin biye mata duk kuka bata kinga ta cuce ki ko ince kin cuci kankan ki,
Duk irin rawan kan da amarya tashigo dashi wallahi Aisha idan uwargida ta daure ta,shaye shi watarana, sai ta dara saboda namiji ba dan goyo bane,
Ni abinda zan fada maki kenan kada ki bari shedan yai galaba akanki ke ma ki gyara tsakanin ki da mijin ki kafin wani ya fahinci abinda ke a,tsakanin ku dashi,
Don wallahi Hamza yana kaunar ki Aisha yakuma san duk irin kyautata mai da kikeyi da biyayya haline dai irin na maza don haka Allah yayi su,
Kada ki yarda ki bata aljanar ki don wata wallahi, din kece zaki dawo kina dakin sani daga baya
Matan kwarai hakkuri aka sansu dashi don dadin su yana gaba,
Shiru tayi wanda haka ya,sani dan dago kaina na dan kalleta cikin natsuwa nace a murya mai sanyi
Mama nagode insha Allahu zangyara kamar yadda kikace,
Amma mama sai naga duk irin abinda nakeyi agidan sn babu maigani kiduba fa irin abinda yai min akan Lima na,shaye kamar abin baidamay ni ba,
Yanzu kuma akan sadiya sai yai ta takani yadda ranshi yaso don yana ganin kamar banda gata ko kuwa ban san abinda nakeyi ba,
Hmmm Aisha duk yasani wallahi yafi kowa sanin halinki bashiba ma ai kowa agidan nan yanzu yasan dadin ki,
Ko waurin girki ai sun san sunyi rashinki da bakya nan don nan za,a bar abincin da ta girks saboda nai ciwuwa saboda rashin iya aiki ga dan banzan kazanta da rashin mutunci da take wa mutane yadda ranta yaso,
Ke dai kawai barsu ai sun gani yanzu don Allah ya nuna masu gaskiya fada ba wanda ba,ayi ba dan dagawanan da kikayi a gidan,
Ni zan tafi dama shi yakawo ni don kawai na fada maki gaskiya kin san mu mata bamu da wani power akan maza sai yadda sukayi damu,
Kedai yi kokari ki nemi aljanarki kada wata ko shedan su rude ki kifada a halaka,
Mama na gode insha Allahu zanyi yadda kikace min
Amma ni da gaskiya na jaye komai nawane akan al,amarin shi don naga bai damu da damuwa na ba,
Kaiyya inji mama ai abin ba hakana bane kedai kawai komai dan lokaci ne irin hakan da kikayi ne sai a bata goma daya bai gyaru ba wallahi,
Ita bata zauna ba kema bata barki kin zauna ba don rashin fahinta irin namu na mata,ai kawai barsu da Allah yai maki yaki,
Daga haka mama tafita daga dakin nawa ina mata godiya tana cewa babu komai,
Zatafita suka hadu da,Sadiya a kofana sai ta,watsa wa mama harara tafara waka tana cewa munafunci dodo shi kanci mai shi,
Mama bata biye mata ba ta dan ci gaba da abinda takeyi a tsakar gida,
Sadiya ce da girki don haka ban fito ba ina nan ina nazarin maganan mama sai na fahinci duk zancen mama gaskiyane wallahi,
Don yanzu duk amaryan da za,a auro ita gurinta shine tazo ta fitar da,wacce ta sama agidan ko kuma tasa miji yai ta musguna mata har akai ga karshen hakkurin mace itama tafara tsula nata tsiyan duk gidan ataru a rikice ba zaman lafiya, ga kowa,
Hakane itama uwar gida idan an shigo mata da,rawan kai taga amarya na son kawo mata ci baya ga miji sai ta fara nata halin duk azauna ba mai dagawa wani kafa a tsakani miji ya koma kamar taya kowa na gara,shi yadda nata ra,ayin yake,
A karshe wace tayi galaba da ita za,a zauna takawar da dayan,
Amma idan kin zauna da halin ki na gaskiya da kowa yasan ki dashi sai dai tayi tsiyar tabarki nan don gaskiya bata faduwa kasa banza,
Don haka zan bi shawaran mama na ci gaba da zama da kowa yadda na saba a baya can ta kare masu a tsakanin su babu ruwa na,
Sai dai idan mutum ya shiga gonana a take zan mayar mai da martani baxan bada bashi ba,

****** ********* ******
Zaune yake a saman wani dutse dake daura da tsohon shagon shi yayinbda,abokan hiran shi wasu suke zauns saman benci da kuma tabarman da suke shimfidawa a majalissan tasu,
Bakomai ne a ran shi sai irin yadda Aisha ta sauraya mashi dawowan ta daga garin su,
Gaba daya ta,sauya mashi a,gidan nan duk wani halaiyan da,yasanta,dashi abaya yanzu babu shi sai guda guda, kawai,
Kwata,kwata sai nisanta kanta take da kowa agidan daga shi har mama hafsi da tafi sake jiki da ita da,farko yanzu ya kula cewa,basu wani dasawa a tsakanin su kamar farko,
Gashi yanzu dan tafiyan da,tayi na,farko tun bayan auren su ya,fahinci cewa ashe Aisha ta,zama mai wani jigone na,rayuwan shi gaba daya,
Don a halin yanzu Allah ya,saka mai wani irin bala,in sonta a rayuwan shi,
Abubuwa da dama sun faru wanda yasa ya fahinci ko wacece Aishan yarinya mai karamci da mutunci ga,sanin ya kamata uwa uba ga girmama,na,gaban ta,
Bazai iya cewa,zaman shi da ita,ga irin laifin da tai mai ba,wanda,yaji zafin shi har cikin ran shi,
Matace Aisha ta,rufin asiri ga,duk namijin da,ya mallaki irin ta a gidan shi, ya huta mai shi,
Wanan tafiyan da,tayi garinsu gurin iyayyenta,tadade zai iya cewa wani ishara ne daga ubangiji da ya fitar dashi da ga halaka,
Don yaso yayi sake na dafe da daman da Allah ya bashi,
Ya biyewa shedan da,shedaniyar matanshi dama mahaifiyar shi wace bai san dalilin daya sa take kin wanan yarinyar ba haka, su taru su kuntatawa yar mutane,
Boyar Allah ashe cikine a jikinta take ta faman mukurkusa tana yawan fada,mashi cew bata,da,lafiya maranta yana mata ciwo,
Amma,sai yake gani kamar kishine kawai na mata,don taga Sadiya nada ciki yana bata kulawa,
Shin wai shima yanzu dawani irin idone zai kalli wanan yarinyar dashi
Yarinyan da ta san mutunci shi dana iyayyen sa,da yan uwan shi amma ya wullakantata a kan wata mara mutunci can,
Gaskiya a tsakanin Umma da Sadiya ba zainiya cewa ga,wacce ta cuce shi ba,
Don dai ita Umma itace silar hadashi da wanan shedaniyar yarinyar da kowa yasan ba,wani tarbiyan kwarai ne da ita ba,
Ita ko Sadiya shu,umace ta karshe ba,tarbiya bs kunya a tare da ita ko kadan,
Yayi daya,sanin hada ta,dashi da akayi yafi a kirga don ba abokiyar zama bace ita,
Ga irin cin fuskan da takewa kowa a gidan yanzu yakai mai ko ina, daga,shi har iyayyen shi babu ragowa akan su,
Dafarko tanayi Umma najin dadi ashe abin zai dawo har a kanta itama,
Takance ke yar agwai taimakonki nakeyi don kinga yanzu inna haihu sai kawai ki dinga goya min Baby nikuma bada dadewa ba sai na kara sambado maku wani,
Darawa sukan yi kawai suna jin dadi wai Sadiya ta samu ciki, duk da bai daukan wanan zancen a lokacin don idan yai magana Umma takance ina ya fito,
Yau gashi bata,barkowa ba agidan kowa tanawa shedana son ran ta,
Kamar kada Aisha ta dawo da ciki sai bala,in ya karu mata kullun yanzu a cikin tashin hankali take a gidan,
Wai shi muna,fuki ne yasan matar shi nada ciki amma yaki fada mata tunfarko ya boye mata zancen,
Sulaiman Abokin shi ne da suke hira duk yamma a kofan gidan sune yakecewa,
Mijin Aisha angon Sadiya tunanen may kakeyine haka tundazu ana magana bakace uffan ba,
Dariyan yake yaiwa Sulaiman din tare da dunkule hannayen shi guri guda a,saman kirjin shi cikin dan murmusawa,
Yake cewa ina tunanen wani mutum ne abokin sana,a ta mutumin kirki dashi wallahi,
Aiko gaskiya kayi kokari ka jona dashi don mutumin arkizi ba,a sakaci dashi,
Zancen sulaiman ya tsaya mashi a rai sosai sai yake tunanen duk yadda zaiyi ya gyara tsakanin shi da Aisha sai yayi kafin abin yafi karfin zaton shi,

Nafito daga daki daure da zani agaba na sai dan karamin towel dana dan yafa akaina zuwa kafada na,
Ina duke a bakin randa ina zuba ruwa a bucket don na,watsa kafin maggariba yayi,
Sai ga Hamza yashigo dauke da buta a hannun shi da alama ruwan alwala zai diban masu a waje,
Cikin wata murya mai taushi da laushi nake ce ma Sannu da zuwa tare da karban butar daga hannunwan shi,
Ya karba min yana mamaki a cikin rashi don dazun da yashigo ko kallo bai isheni ba amma,yanzu sai gashi cikin mamakin shi na karba mai a mutunce tankar babu komai a tsakanin mu
Karban butar nayi na zuba mai ruwan tare da kokari mika mashi ,
Daidai wanan lokacin ne Sadiya ta fito da, dakinta tana cewa nagan ku muna fukai banza kawai wai kuna ci min amana ku fake ga zuba ruwa a roba kuna cewa wai taimako,
Ke dauki bucket din ki ki tafi inda zaki wanan yar fitina tafara jidalinta ke nan,
Haka zakace mana munafuki kawai rawa kan da kakeyi dan kaga ta,dawowa da dan abin duniya,
Har yafita yayin da take tsaye tana masifa ita kaida,a gurin,
Kai ke dai wanan yarinyar wallahi kin faye masifa ace mutum.kullun sai mutum yai masifa a raguwan shi na,safe daban na yama daban,
Kibawa kan ki lafiya kawai yafi amma wanan irin rayuwan bai ma ki kyau ba wallahi,
Rufe min bakikin ki tsohuwar munafuka kawai ai dakece ake hada bakin duk abinda akeyi a boye,
Cikin mamaki Umma ta bude bakin ta tana cewa Sadiya nice kuma mufuka yau gidan nan,



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABUIDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE


Duk abinda ke wakana a tsakanin Umma da,Sadiya ko kallon ba su isheni ba, banyi har aci a,sude don kan su, akeji saboda kaikaine ya koma a kan mashekiya
Don nice akaso aiwa wanan hadin kan aimin cin fuska yadda rai yaso,
Sai Allah ya kareni daga duk wani sheri da kule,kulen da aika yi akaina,
Matsala ta tsakani nada maigida na ne ban damu da,zancen su ba ni sam,
Don da,zaran na karbi girki mun shiga cikin rikici ke nan da,shi akan wai gudun shi nakeyi,
Sam yaki gane kaina tun da na dawo acikin ya,dan samu rangwamay ke nan akan fadar da mama tai min,
Yau ma kamar kullun ina zaune a bakin gado na na zuba uban tagumi fuskana babu sasauci a cikin sa,
Babu abinda nake tunane sai irin wanan rayuwan da na tsunci kai na a cikin gidan Hamza,
Tambayan da a kullun nakeyiwa kaina shine a haka zan zauna naita zama har na haihu abinda zan haifa ya tsunci kan sa cikin irin wanan rayuwan,
Jin an taba kofa dakina yasani saurin dago kaina duk da nasan cewa ba kowa bane sai Hamza,
Shigowa dakin yayi da,sallaman shi na dan dago kai tare da dan tsura mashi idanu,
Gaba daya naga duk ya canza min a fuska ya sauya min duk ya ramay yai baki ga,sutura,duk sun yi wani motsu motsu,
Sannu a hankali yakai zaune daga gefena kadan yana mai sauke ajiyar zuciya,
Cikin sanyin murya yafara min magana da cewa,
Aisha wanan zaman banzan danakeyi a rayuwa ta ya fara isata ace mutum ya zauna ba wani sana,a da yakeyi dan kudi na,shigo mai na rufin asiri
Sai da kullun mutum ya yini zaune a lalace ba wani abin yi a gaban shi,
Gashi banda wani dan uwa ko jigo da zan iya tunkaran shi don ya taimaka min
Cikin dan tausasa murya nace niko a ganina may zai hana kafara dan aikin karfi kana samun dan canji, don kaga girman kai shine ke cutuwar dan arewa,
Shiru yayi tare da dan furzar da iska daga bakin shi a hankali,
Yace in sha Allahu zan gwada hakan ko zan dan samu nayi nayi,,
Can kuma sai yadan tausa muryan shi yana cewa,
Ni abin ma duk yai min yawa wallahi a waje ba dadi gida ma ba,dadi mutun da iyalinsa suna gudun shi balle na,waje,
Nace cikin daure fuskana saboda na gane may yake nufi, haba, dai yaya ya kamata ace iyanzu ka fahince ni fa,
Bafa zan yarda na karya dokan likita ba don idan wahala,ya cika dani babu mai kula da al,amarina balle ya taimaka min, da ko zuwa asibiti ne balle gurin likita,
Hmmm Aisha Humaira ya kamata ace yanzu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login